TAKUN SAKA 1-10

“Sake ni!”
Ya faɗa cikin kaushin muryar da ya maido hankalin kowa kansu. Girgiza masa kai Usman ya shiga yi alamar bazai barsa ba. Dan yasan dama badan Ummi da ke dakatar da su ba babu shakka da tuni Umar yayma Abba dukan mutuwa a gidan harma da Hajiya mamar kanta… Da ƙarfi Yaya Umar ya fisgi hannunsa da ga cikin na Usman. Hakan yasa Ummi azamar sakin Ammar tasha gabansa.
Cikin idonsa ta kalla batare da tace masa komai ba. A take yay ƙasa da kansa yana lumshe idanu da cije leɓensa da ƙarfi tamkar zai huda shi. Murmushi tayi tana kamo hannunsa cikin nata. Gaba ɗaya ƴaƴanta tasan lagonsu da hanyar sauke fushinsu. Shiyyasa a kowane lokaci take samun nasarar ladabtar da kowa cikin salon da ya dace. Babu wanda ta sake yima magana a cikinsu, sai kamo hannun Hibbah dake sharar hawaye har yanzu tai tana bin jikinta da kallo tamkar mai neman wani abu.
Da sauri Hibbah ta ce, “Ummi basuyimin komaiba fa, babu abinda ya faru ki kwantar da hankalinki”.
“Ai sun sakaki a tarkon da za’ayi miki ne!”.
Yaya Abubakar ya faɗa a tsawace cikin faɗan da kowa baisan yana da shi ba. Dan shima bai cika hayaniya ba sosai, amma yafi Usman da Muhammad zafi a wasu lokutan.
Ya riƙe ƙugunsa da hanunsa ɗaya, ɗayan yana murza goshinsa cike da damuwa. Yanda ya ke ɗan kaikawo yasa su fahintar akwai matsala kenan. Ummi da dama yin komai ta ke cike da ƙarfin hali ta kafesa da ido.
Zaune Yaya Abubakar ya kai saboda jin zai faɗi, dan shi kaɗai yasan a wane irin damuwa ya ke game da halin da Hibbah ta ke ciki. Gaba ɗaya ƙuruciya ta hanata fahimtar ramin da ta jefa kanta a ciki mai haɗari ne………
“Abubakar mike faruwa?”
Ummi ta katsesa tana takowa gabansa. Idanunsa da ke jajir ya ɗago yana kallonta, ya ɗan furzar da zazzafar iska yana girgiza kansa. “Ummi tabbas akwai matsala, rawar kanta ta kaita ga jefamu cikin ramin da sam ita bazata fahimci haɗarinsa ba….”
Duk da hibbah a tsorace take da yanayin Yaya Abubakar ɗin, tai saurin katsesa ta hanyar faɗin, “Yayanmu wlhy babu abinda ya faru fa. Kawai dai sun sakani na bibiyar musu masu power bike ɗin nan dana sanar maka ne. Amma da ga haka basuyi min koma………”
Tsawar da ta sakata kasa ƙarasa zancen ya daka mata. Ta maƙale a jikin bango jikinta na rawa saboda bata taɓa gamo da fushinsa irin haka ba. Shima tsaye ya miƙe yana nunata jikinsa har rawa yake ga idanunsa sunyi jajur. “Idan bakimin shiru ba wlhy sai na ɓallaki a gidan nan yau. Bance miki ki jirani a inda kike nazo na sameki ba? Su masu power rider ɗin da kike tunanin ba komai ba to sune tawagar ɓarawon nan da ake nema ruwa a jallo mai suna *Master!*, shine ya wawashi maƙudan kuɗaɗe jiya a asusun matar gwamna. Kowace hukuma ta jami’an tsaron jiharnan an basu awa ashirin da huɗu ne domin kawosa a mace ko a raye. Ba jihar nan da ƙasarnan kawai ba, hatta duniya baki ɗaya idonsu akan wannan mutumin yake. Amma shine k kika jefa kanki cikin abinda bakisan mafarinsa ba. Su waɗan nan jami’an da suka ɗaukeki zasuyi amfani da ke ne kawai su sami cikar burinsu, sunansu ya sake fiwowa a idon duniya. Kece zakiyi aikin amma sune zasu fito matsayin masu aikin. A tunaninki shi ɗin mahaukaci ne, kosu suna son matsalar tasa ta ƙare ne da wuri? Kuɗaɗen shigar da suke samu su dakata. Kafin yau an sha yimasa tarkuna da sukafi wannan haɗari amma bai kamu ba. Da ga ƙarshe kuma duk wanda yay masa tarkon ana nemansa ne a rasa ma baki ɗaya, ya ɓatar da shi. Wannan yasa a duk lokacin da ya aikata laifin manyan ke makalewa su saka ƙananun ma’aikata yin aikin, da ga ƙarshe suke nuna sunyi aikin ma duniya, wanda yay aikin kuma rayuwarsa ta faɗa a haɗarin da babu wanda zai sakejin yanda akayi, kuma basa wani ɗaukar matakin bashi kariya ko cetosa. Shekarunki goma sha takwas kacal da wasu wattani a duniya Muhibbat! Bama ki gama karatun gina rayuwar taki ba amma kika jefa kanki a wannan haɗarin saboda kunnen ƙashinki. Wannn kunnen babu wanda ya isa ya faɗa masa yaji sa”.
Ya ƙare maganar da takawa inda take maƙure a bango jikinta na rawa ya damƙi kunnenta da ƙarfi yana murzawa cikin yatsun hannunsa. Rawa jikinta ya farayi tana girgiza masa kanta saboda zafi.
Sakin kunnen nata yay yana dungure mata kai, yayinda sauran yayun nata da Ummi keta faman ambaton (innalillahi wa-inna ilaihirraji’un) a zukatansu. Yaya Abubakar ya cigaba da faɗin, “Ba wanann kaɗai bace damuwar Ummi, tunda har basu sami nasarar kamashi ba zargi zasu ɗarsa akanta itama. Dan zasu raba hankalinsu ne yanzu akan tunanin ko shine ya shirya komai wajen yin amfani da ita. Dan duk harin da jami’an tsaro ke kai masa ba’a taɓa cin nasara kamar nata ba da ya gudana cikin kanƙanin lokaci. Yanzu da zarar sun fitar da bayanai wa media cewar sun haresa, harin da kuma aka samu ci gaba a cikinsa fiye da na baya, to kowacce hukumar jami’an tsaro sai sun bibiyi yanda hakan ta kasance ta karƙashin ƙasa, walau jami’anmu nan gida kona ƙetare da ke nanuke cikin case ɗin kamar yanda suka saba mana kutse a cikin ayyukan daya shafi ƙasashenmu. Mu kuma bamu isa muyi koda tari akan nasu ba. A ƙarshe kowa ya bincika ita zai gano. Duk kuma zasu kasance wajen bibiyarta da mu kammu ba tsira zamuyi ba. Shima da ta aikata komai dominsa ba barinta zaiyi ba na sani.
“Ya ALLAH!”.
Ummi da ke neman faɗuwa ta faɗa tana fashewa da kuka. Da sauri sukai kanta gaba ɗaya suna ƙwala mata kira. A wani irin sarƙe numfashinta ya fara fita, ta fara tari.
Rikicewa suka sakeyi, yayinda kukan Hibbah ke ci musu zukata matuƙa. Cikin bada umarni Yaya Muhammad ya ce su dagata a kaita asibiti. Yanda ya faɗa ɗin haka sukai, sai dai suna fitowa harabar gidan ƴan sanda na shigowa. Basuyi yunkurin bi takansu ba. Sai dai muryar Abba da sukaji yana nuna Ammar da cewar shine ya kashe masa yaro ya saka hankalinsu rabuwa biyu.
A ɗan firgice Yaya Usman ya furta, “Kisa?”.
“Eh mara mutunci, ko ƙarya zan masa ne? Tun ɗazun likitoci suke akan Junaid amma babu alamar numfashi tare da shi, dan haka ku kamasa, inhar na rasa ɗana shima sai an kashesa.”
Tarin Ummi ne ya ƙara ƙarfi, sai ga jini na fitowa ta hancinta. Hankalinsu ne ya sake tashi. Sai a lokacinne Abba ya lura da halin da Ummi take a ciki. Maimakon ya saki batun ƴan sanda ya shiga sahun masu kula da ita, sai hakan ta gagara. A kausashe ya bama ƴan sandan damar kama Ammar yana tabbatar musu pretending Ummi keyi kawai.
Ganin duk sun shiga mota ƴan sanda kuma sun cukuykuye Ammar dake turjewa dan hankalinsa nakan halin da mahaifiyarsu ke ciki bata tasu yake ba. Yaya Muhammad ya cema Yaya Usman ya fita yabi ƴan sandan dan susan inda za’a kai Ammar ɗin. Su kuma zasu kai Ummin asibitin.
Badan yaso ba ya fita domin bin umarninsa. Dan duk da an haifesu babu wani yawan tazara a tsakaninsu hakan baya hanasu respecting junansu saboda ƙyaƙyƙyawan training da suka samu da ga mahaifiyarsu…….
★★★★★★★★★★★
A lokacin da wancan tashin hankali ke baibaye da ahalin Hibbah, anan headquarters ɗin ƴan sanda ƙoƙarin fitar da bayanan harin da Hibbah ta kaima master sukeyi. Sai dai kamar yanda Yaya Abubakar yay hasashe sunansu ne ya fito matsayin waɗanda sukai aikin. Sun kuma tabbatar nan da lokaci ƙanƙani zasu gurfanar da Master a saman gwiwoyinsa gaban duniya.