Uncategorized

TAKUN SAKA 1-10

      Cikin sauri jami’in nan da yaji furicin budurwar ya dirgo a motarsu ya nufi wani mai taxi, magana sukai da babu mai jinsu, mai taxi ɗin ya miƙa masa key ɗin motar. 

       Sauran ɗalibai na ƙoƙarin tsaidama ƴammatan nan napep da basu shawarar su kai wadda ta faɗin asibiti dan da alama taji ciwo babba jami’in nan yazo gabansu ya faka taxi ɗin nan, batare da yin wani tunani ba suka taimakawa ƴar uwarsu ta shiga suma suka shiga.

         Sai da suka fara tafiya ɗayar budurwar tace, “Kai gaskiya kosu waye akan mashinan nan sun cika tantirai, dole ne a dinga cewa ƴaƴan manyan ƙasarnan sai sun sha kayan haukansu suke hawa power bike sunama mutane hauka da shi a tituna kamar nasune su kaɗai. Yanzu dan ALLAH bayan ALLAH ya taƙaita wahala ai za’a iya rasa rai ta dalilinsu ko?”.

         Wani banzan tsaki budurwar nan data jefa musu abu taja tana cije lip. A tsiwace tace, “Aiko a wannan karon ko duniya suka sha sun sako kansu a tarkon da iyayen nasu da suka saya musu mashinan sai sunyi dana sani insha ALLAHU. Dan wlhy har gidan ubanninsu sai nayi sanadin da za’a bisu ɗai-ɗai a kamo koda iyayensu zasu ɗauki mataki ne sai sunayensu ya ɓacin da bazasu sake gigin hawa power bike a cikin jama’a ba”………..✍????

*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

Duka gamayyar biyar din(1k)

1,000

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*????????????????????????????????????????????????

#team ZAFAFA BIYAR

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????._*

      

*_Typing????_*

             *_????TAKUN SAAƘA!!????_*

                *_Bilyn Abdull ce????????_*

_ZAFAFA BIYAR 2K22_

_________________________

Chapter Three

………..Hafsat tai azamar ɗago kanta tana dubanta, duk da hawayen da ke sharara a kumatunta na azabar da take ji a ƙafarta, cikin ƙarfin halin ta ce, *_“Muhibbat!_*  dan ALLAH karki sakamu a wahala da hatsabibancinki. Kwana huɗu kenan kacal da gama kashe wata wutar da kika kunno, indai dan nice karki damu, dama ALLAH ya ƙaddara sai naji ciwon nan koda bata sanadinsu ba, ina roƙonki kibarsu Ya Abubakar su huta da shegen tsokanarnan taki”.

        Harara Muhibbat ta zubama Hafsat da murguɗa baki tana juya idanu, harta buɗe baki zatayi magana sai kuma tayi shiru saboda isowarsu cikin harabar asibitin.

       Ko kaɗan jami’in nan baiso Muhibbat tayi shiru ba, amma kasancewar yasan aikinsa sai bai nuna hakanba, sai ma ƙoƙarin taimaka musu da yayi domin ganin an shiga da Hafsat taga likita akan lokaci.

      Da taimakon jami’in aka duba ƙafar Hafsat da ta samu tsagewar ƙashi, Zahidah sai godiya take masa saboda ƙoƙarin da yaketa musu, dan sunso su kira gida ya hanasu. Hanawar tasa kuma ta bama Muhibbat haushi, dan a ganinta ya cika shishshigin tsiyane kawai, musamman daya kasance duk wani motsinta sai ta ritsa idanunsa akanta.

      Tun tana hararsa a ƙasan ido da masa ƙunƙuni har takai ta fito fili tana dalla masa harara. Ganin dai ba daina kallon nata zaiyi ba a tsiwace ta ce, “Wai malam kallon fa? Dan ALLAH karka cinyeni a tsaye mana”.

        Sosai yanda tai maganar ya bashi dariya, dan tsaf ya gama fahimtar itaɗin matsiwaciyace ta gaske. Sannan babu tsoro sam a cikin idanunta kona sisin kwabo. Komai baice mata ba, sai ma ɗauke kansa da yayi kawai gefe tamkar bai jita ba. Taja tsoki tana murguɗa baki da miƙewa tabar wajen.

       Can gefe ta koma tana ƙoƙarin sarrafa wayarta cike da ƙwarewa. Cikin ƙanƙanin lokaci kiran da tayi ya shiga, sai da aka ɗaga sannan takai kunne tana faɗin, “Assalamu alaika Yaya”.

    Amsa mata akai da ga can, kafinma ya gama rufe baki cikin shagwaɓa taci gaba da magana. “Yah Uthman muna hospital ne”.

         A tsananin tsorace muryarsa ta bayyana, “Hospital Auta?! Waye bai da lafiya?”.

         “Oh Yaya calm dawn, Hafsat ce taji ciwo a ƙafa amma da sauƙi, dan yanzu haka ma an gama mata gyaran sunce tsagewan ƙashine”.

        “Ya ALLAH! Auta wai sai yaushe ne zakuyi hankali ku kam? Yanzu haka a wajen shegen rawan kan nan naku hakan ta faru?”.

        “Na rantse Yaya bafa da gangan bane, wasu marasa kirki ne suka kusan turemu a power bike”.

       “What?!. Power bike fa? Ku miya kaiku kan titin da masu power bike kebi!!?”.

       Yanda yay maganar a tsawace ne ya sata zabura, duk cikin yayun nata yafi kowa sauƙin hali bayan Yah Abubakar. Sai dai kuma idan ya rikice tafi tsoronsa fiye da kowa a cikinsu….. Cikin katse mata tunani yace, “Zan turo muku Ammar yanzun nan danni naje katsina ne..”

         Yana gama faɗan hakan ya yanke wayar. Kasaƙe Muhibbat tayi tana kallon wayar, yayinda gefen zuciyarta ke ayyana mata neman mafita. A fili tace, “Tab Yah Ammar! Wlhy bazan bari ya samemu a asibitin nan ba wannan ɗan matsalar”. Da sauri tabar wajen zuwa inda jami’in nan mai amsa sunan driver-n taxi yake da Zahidah.

       “Zahidah tunda sunce zasu iya sallamarmu gara mu wuce gida, dan na haɗa gurmi wlhy”.

     Zahidah dake mata kallon mamaki tace, “Gurmi kuma! Nami to?”.

       “Humm daga kiran Yah Uthman fa na faɗa masa shine wai zai turo mana Yah Ammar shi yana katsina. Ni kuma wlhy banason Yah Ammar yazo asibitin nan ya samemu saboda yafi gidan haya matsala kema kin sani”. 

       Kafin Zahidah dake dariya tace wani abu jami’in nan yay saurin cewa, “Ai sunma sallemu daman, inaga ku shiga ku fito da ita kawai mana”.

        Harararsa Muhibbat tayi tana ɗaure fuska. “Ikon ALLAH sai kallo, wai ni kam bawan ALLAH ca’akai ka kula damu ne kokuwa? Taxi ɗinka muka hau ka kawomu inda muke buƙata, to sai mi kuma ya rage?”.

        Murmushi yayi idanunsa a kanta, “Sai ku bani kuɗina ya rage ƙanwata”.

       “Ya salam! Dan ALLAH kayi haƙuri bawan ALLAH. Wlhy gaba ɗaya mun shafa’a ne”. Zahidah ta faɗa tana laluben bag ɗinta.

      “Karki damu ƴammata babu damuwa. Nasan kuna a rikicene ai. Amma ƙawar nan taki ya kamata ta rage tsiwa”.

      Zahidah dake miƙa masa ɗari biyar tai dariya, “Kaga fita batunta ga kuɗinka mun gode sosai”.

     “Ai karki damu riƙe kawai sai na kaiku inda zaku yanzu sai na amsa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button