TAKUN SAKA 1-10

“Malam gara dai ka amshi kudinka kai gaba, dan bazamu sake shiga motarkaba ɗan sarkin shiga sharo ba shanu”. Muhibbat ta faɗa tana hararsa.
Saurin toshe bakinta Zahidah tayi itama tana hararta, “Wai nikam Hibbat kodai wadda tai miki wankan jego bata gasa bakin nan bane da baya barin kowa. Ina laifin bawan ALLAHn nan, kigafa ƙoƙarin da yay mana akan Hafsat”.
Hibbat ta buge hannun Zahidah da haushi, “To dan kuma ya taimakemu sai ya ishemu da shishshigin jaraba. ALLAH ni banason shishshigi da ƙwala kai a faranti irin na wasu mazan”.
Tana gama faɗa tai shigewarta ɗakin da Hafsat take. Duk binta sukai da kallo, kafin Zahidah ta maido kallonta ga jami’in. “Ayya dan ALLAH kai haƙuri. Ita haka take sam ba’a gane kanta tamkar mai aljanu”.
Ƙaramar dariya yayi yana sosa tsakkiyar kansa da key ɗin taxi ɗin. Yace, “Kinga karki damu ni salon natama birgeni yakeyi, irin waɗanan sam ba’a cutarsu a duk inda suka shiga. Je kawai ki fito dasu na kaiku kafin a sake kirana ɗan shishshigi”.
A yanda ya ƙare maganar cikin langaɓe kai kalar tausayi yasa Zahidah ƙyalƙyalewa da dariya tana shiga ɗakin domin su fiddo da Hafsat..
Da ƙyar Muhibbat ta amince jami’in nan mai taxi ya ɗaukesu zai maida gida. Dan ko sai kumbura take a motar tana ƙananun ƙunƙuni alamar bataso hakan ba. Shi dai yakanyi murmushi lokaci-lokaci idan ya ɗago ya dubeta ta mirror yaga yanda take cika baki da iska tana harare-harare……..
★.★.★.★.★.★
Kamar yanda aka saba yau ɗinma tuni media ta ɗauka. Gidajen redio dana televisions harma da yanar gizo mutane sai tofa albarkacin bakinsu suke. Dan lamarin wannan gagarumin ɓarawo ya daina bama mutane tsoro sai al’ajabi da mamaki. Kullum ji suke jami’an tsaro na farautarsa, mai makon ya tsorata ya ɓuya sai ƙarama gawurta yake a al’amuransa. Gashi babban abinda zai baka mamaki manya-manyan ƙusoshin ƙasar masu lasisin iya ɗaukar mataki yake bi yana yashewa da saka rayuwansu cikin tarkuna. Dan da wahala ya kafa maka ƙahon zuƙa daga ƙarshe baka koma ƙarƙashin binciken hukumar *EFCC????* ba, ko ka ƙare rayuwarka da ciwon paralysis saboda barazanarsa idan yay dirar mikiya aka kaddarorinka da kuɗaɗenka. Yanzu dai yanda ya yashe asusun matar gwamna bawai ya barta bane kenan. Duk da neman da ake masa ruwa a jallo cikin kwanaki ƙanƙani zai sake silalowa ya danƙara mata wani harbin mai zafi har sai ya kai rayuwarta ƙasa kwance zai barta.
Duk yanda ƴan jarida sukaso jin ta bakin jami’an tsaro da gidan gwamnati akan wannan al’amari abin ya gagara. Sun haƙura dole suna bada labarin iya abinda idanunsu suka gani da ɓarnar da wannan mutumi ya tafka a baya kafin wannan ɗin.
Yayinda a gefe kuma jama’ar gari suketa tofa nasu. Wasu najin daɗin abinda yakeyi ɗin dan bawai a satar kuɗin manyan ƙasar kawai ya tsaya ba, har ƴan fashi da suka addabi mutane da ƴan ta’adda yakan kama waɗanda har yanzu babu wanda zai iya cewa ga inda yake kaisu ya ɓoye. duk da kuwa shima ɗin mai laifi ne a bayyane, wasu ko na jifansa da ALLAH wadai saboda suna ganin bashi da maraba da ƴan ta’addar da yake kamawa ai. Yayinda ƴan kanzagi ke zaman rubuta shaci faɗi su yaɗa a kafafen yanar gizo game da shi da ayyukansa…………..✍
*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI……_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*
*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k)
*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*????????????????????????????????????????????????
#team ZAFAFA BIYAR
*_ALLAH ka gafartama iyayen mu????????????_*
*_Typing????_*
*_????TAKUN SAAƘA!!????_*
*_Bilyn Abdull ce????????_*
_ZAFAFA BIYAR 2K22_
_________________________
*_Chapter Four_*
………..Suna baro cikin asibitin Muhibbat ta kashe wayarta dan ma kar Yah Ammar ya sameta.
Tun farkon shigowa anguwar tace a saukesu. Amma sai Zahidah tace sam basu yarda ba a kaisu har ƙofar gida. Zata fara masifa Hafsat ta ce, “Kiyi haƙuri ya kaimu saboda bazan iya taka ƙafarnan ba Hibbah”.
Shiru tayi bata sake tankawa ba har suka iso ƙofar gidan su Hafsat daya kasance a farko, sai nasu Zahidah, Muhibbat ce ƙarshe. Saboda ciwon dake tare da Hafsat ɗin ya sakasu cewa a tsaya ƙofar gidansu. Zahidah ta bama mai taxi kuɗinsa tana godiya. Amma sai yaƙi amsa. Mamaki ƙarara a fuskar Zahidah da Hafsat. Sun buɗe baki zasu magana yay musu alamar suyi shiru.
“Basai kunce komai ba, inhar da wannan mai bakin tsiwar tare da ku anta kaiku waje ƙyauta kenan babu ko sisin ku”. Yay maganar idanunsa akan Muhibbat yana wani sassanyan murmushi.
Hararar da yay tsammani ta watsa masa, cikin takaici tabar wajen batare da tace komai ba. Kira Zahidah da Hafsat suka shiga ƙwala mata suna dariya, amma ko waiwayensu batai ba harta ƙarasa gaban wani gida mai baƙin gate. Sai da ta kama murfin zata shiga ta waigo, ganin har yanzu mai taxi ɗin na tare da su yasata jan tsaki akan laɓɓanta ta ce, “Maye kawai”. Daga haka ta shige ciki.
Gida ne da zamu iya kiransa babba a girma da ginuwa. Dan a ƙalla akwai ɓangarori biyu zuwa uku a cikinsa. Ɓangarori biyu na farkon shiga gidan sunfi haɗuwa da tsaruwa, zakaga hakan tun daga wajema kafin ka kai ga shiga ciki, sai dai kuma ɗayan dake daga ciki ya fisu girma, amma bai kai su ƙyawu ba.
Harara ta zubama sashen guda biyu tana taɓe baki, tana gab da wucesu taja tsaki a zuciyarta wanda batai zaton ya fito har waje ba.
“K!! Dan ubanki wa kikema tsoki!!”.
Wata buɗaɗɗiyar murya mai cike da hargowa ta faɗa. Cak ta tsaya ƙirjinta na bugawar tsoro, tabbas da ace tasan mugun nan ya dawo gidan da bazata shigo ba sai magriba. Jin takun tafiya a bayanta alamar ya taso ya sakata juyowa. Ƙiris ya rage ya iso gareta, babu shiri ta kwasa da gudu zuwa sashen can ciki tana ƙwala kiran sunan Ummi!.
“Ya ilahi! Tanee lafiyarki kuwa? Wai sai yaushe ne hankali zai game jikinki kisan girma ya fara zuwa miki!”.
Ummi dake ƙoƙarin fitowa a kitchen riƙe da ludayin miya a hannu ta faɗa. Dai-dai isowar Hibbah cikin falon itama a guje. Bayan Ummi taje ta maƙale.