TAKUN SAKA 1-10

“K da wa kuma?”.
Ummi ta faɗa tana juyowa gareta fuska a ɗaure.
“Wannan mugunne fa Junaid Ummi. daga na shigo ina tsaki ya hau zagina kamar nasan da zamansa ma a gidan”.
Baki Ummi ta buge mata, tai saurin ja da baya daga jikinta tana dafewa.
“Wannan bakin naki da kanwa bata jiƙa a cikinsa shi zaisa kiyita shan wahala a wajen mutanen gidan nan Tanee. Mara kunyar banza matsamin a hanya”.
Gefe Hibbah ta matsa gudun kar Ummi ta sake kai mata wani dukan hawaye cike da idanunta. Sai da taga ta koma kitchen ɗin sannan ta nufi ɗakinta zuciyarta na ƙara jin tsanar mutanen gidan nasu. Da ace zata samu wata dama a hannunta koda ta yini guda ce sai ta bisu da bulala hansin-hansin, musamman ma Hajiya Mama da Abba da wannan azzalumin Junaid ɗin. Mukulli ta murza a ƙofar tata dan batason sake magana da kowa.
Tunda Ummi ta jiyo ƙarar rufe ƙofar Hibbah sai tai murmushi, tasan hakan na nufin tayi fushi, ba kuma zata buɗe ba sai Yah Abubakar yazo ya lallasheta ko jarabar danna Computer ɗin tata ta motsa. Watsar da ita tai ta cigaba da aikinta saboda bataso magriba ta sameta. Cikin ranta tana tunanin yaushe Junaid ɗin ya dawo ƙasar? Dan bataji alamun murna da ga yaran gidan ba sam. Rashin mai amsa mata zancen ya sata watsarwa ta cigaba da aikin gabanta.
Harta kammala ta shige babu wanda ya shigo a cikin samarin ƴaƴan nata, fatan dawowa lafiya tai musu sannan ta shiga wanka.
A ɓangaren Hibbah ma wankan tayi, kasancewar tana fashin salla tana kammala kintsawa ta fito, dan ta tabbatar Ummi ta shige. bakuma zata sake leƙo falon ba sai bayan sallar isha’i. Yayunta kuwa bata tsammanin yau zasu kwana a gidan ma. Musamman Yah Abubakar da Yah Usman da yace yana katsina.
Study table ɗinta ta haye dake can gefen falon a wani ɗan lungun. An shirya mata wajen tsaf da kayan karatu na musamman saboda kasancewarta ƴar gata, sannan haziƙa wajen sanin sirrin sarrafa Computer.
Tun ana ɗaukar lamarin nata shashanci har takai yanzu Yayansu Abubakar naci da ga tagomashin ƙwazon nata ta hanyar aikinsa na tsaro. Dan yasha sakata ayyuka masu muhimmancin gaske ana kuma samun nasara tunma bata kai haka shekaru ba. Wannan dalilin ne ya sakashi tsaya mata wajen ganin ta cika burinta akan zurfin nazari game da na’ura mai ƙwaƙwalwa.
Cike da ƙwarewa ta kunna Computer ɗinta saboda aikin data tarkatarma kanta na bibiyar masu power bike. Dan ta ɗauka alwashin kosu ɗin ƴaƴan uban waye sai ta gano su insha ALLAH.
Babu wanda ya shigo gidan sai Ummi data fito bayan sallar isha’i tace ta tashi taje taci abinci tunda babu wanda ya dawo a yayun nata har yanzu. Da to ta amsawa Ummin, tana gani ta koma ciki ta cigaba da aikinta cike da zaƙuwa.
Ummi dake jiyo motsin Hibbah ta shiga ƙwala mata kira ganin dare ya farayi. ta tabbatar kuma inba da gaske tayi mata ba, zata iya kaiwa biyun dare akan Computer ɗin batare da gajiyawa ba.
*_Tanee! Tanee!!_* wai bazaki tashi a gaban Computer ɗin nan kije ki kwanta ba sai na ci ƙaniyarki ko?!”.
Hibbah dake zaune a cikin falon daga can gefen study table ta ƙwaɓe fuska tamkar zatai kuka. A kallo ɗaya zaka fahimci tarin ƙuruciyar dake tattare da ita, dan kwata-kwata bazata gaza shekaru goma sha tara a duniya ba. Jin tahowar mutum ta bayanta ta miƙe da sauri a gaban Computer ɗin tana faɗin, “Wayyo Ummi nafa kusan gamawa wlhy”.
“Ai ba Ummi ɗin bace, mai kunnen ƙashi nine”.. Ƙyaƙyƙyawan saurayi mai tsananin kama da ita da bazai wuce shekaru ashirin da takwas ba ya faɗa a bayanta tare da kai mata ranƙwashi bisa kai. Tsalle tai zuwa gefe tana fasa ƙara duk da kuwa bai sameta ba. Ya balla mata harara yana kai hannu kan mouse ɗin Computer ɗin ya kasheta baki ɗaya. Dai-dai lokacin da yake ɗagowa ya nuna mata hanyar ƙofar ɗakinta yana faɗin, “kama gabanki kafin jikinki yay tsami anan”.
Idanunta dake tara ruwan hawaye ta shiga ƙyaƙyƙyaftawa. Cikin narkewar fuska tace, “Yah Umar dan ALLAH ka barni wlhy zuwa 12 zan shige na kwanta. ALLAH akwai abinda nakeyi mai muhimmanci a ciki”.
Charger ɗinta dake jikin socket ya fizga da nufin kai mata duka. Da sauri ta dirga wani uban tsalle da ihu tare da kwasa a guje zuwa hanyar ɗakin nata.
“Wai wane irin salon iskanci ne haka za’a dinga damun mutane da ihu kamar ƴaƴan rashin ƙwaɓa!”.
Wata murya mai kauri da amo ta faɗa daga bayansu. Basai an sanar musu wanene ba, dan haka Tanee dake gab da shiga ɗakinta ta ida afkawa da sauri tana rufo ƙofar. Umar yaɗan rumtse idanunsa yana cije lip ɗinsa na ƙasa da ƙarfi alamar son saisaita kansa dan jin zafin furucin mutumin da aƙalla zai iya kai shekaru Hamsin da huɗu zuwa da biyar
“Wai dan iskanci ba magana nakeba akaimin banza saboda rashin tarbiyya!. To dan uban mutum dai duk yanda yake kallona nine uban ubansa ma bama shi ba. Sannan kuma mijin uwarsa ne ni!!”.
Murmushi mai ɗaci Umar yayi yana haɗiye abinda ya tsaya masa a maƙoshi saboda kallon da Ummi dake fitowa tai masa. Yaja numfashi a sarƙe da faɗin, “Kayi haƙuri Abba ba wani abu bane ba. Nine da Tanee”.
“Eh lallai ai basai ka faɗaba na gani kai da taɓararriya ne, to ubanmi kale mata da har takema mutane ihu kamar wadda ake lalub….”
Cikin ɓacin rai Ummi ta katsesa da faɗin, “Kai Umar wuce ka tafi sai da safe”.
Zuwa yay ya wuce yana faman taunar lips ɗinsa dan shi kaɗai yasan tuƙuƙin baƙin cikin da yakeji a cikin ransa game da ƙanin mahaifin nasu da a yanzu suke kira da Abba saboda maye gurbin mahaifinsu da yayi dalilin ƙaddarar mutuwa, tabbas badan mahaifiyarsu ba da ko kallon hanyar da sukabi tuni kawun nasu bazai ringayi ba. Amma dasun yun ƙuro itace mai taka musu burki.
Umar na ficewa Abba ya saki wani shegen tsaki da nufar hanyar ɗakin Ummi. Itama bayansa tabi a fusace. Suna shiga cikin ɗakin a zafafe tace, “Halilu ina rabaka da jifarmin ƴaƴa da mugayen furuci amma baka kiyayewa. Ka sani idan ada ni dasu mun ɗauka wulaƙancinka da tozarci wlhy yanzu bazamu ɗauka ba. Dan badan ina takama yaran nan birki ba a kanka bisa dalilin mahaifinsu da tuni sun tabbatar maka da suma sunkai girma. Idan kuma bazaka bariba to lallai zan buɗe musu ƙofar dana rufe domin maka hijjabi akan hakan…..”
Wata wawuyar dariya ya saki yana faɗawa saman gadonta. Cikin salon iskanci da izgilanci yakai ƙafa ya taɗota sai gata ta faɗo kansa. Yunƙurawa tai zata tashi ya birkiceta zuwa ƙasa ya koma samanta. Dogon gashin da ALLAH ya azurtata da shi duk da tsufa yasa ya fara sirkawa da furfura ya damƙe cikin hannunsa tare da ɗan kwalin kanta ya fisga da ƙarfi, tare da sak ɗayan hannunsa ya danne mata baki…………✍
*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI……_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*