Labarai

Tsohon Direban Shugaba Buhari A Lokacin Mulkin Soja Ya Samu Tallafin Kayan Abinci

Tsohon Direban Shugaba Buhari A Lokacin Mulkin Soja Ya Samu Tallafin Kayan Abinci
Burinsa har yanzu ya yi ido huɗu da Shugaba Buhari

Malam Sani Adamu yana ci gaba da samun tallafin abinci daga wurare daban-daban na jihar Borno.Malam Sani tsohon soja ne kuma shine direban Shugaba Muhammadu Buhari a lokacin da yake soja.

Har yanzu dai Malam Sani Adamu yana kan bakan sa na ganin ya yi ido biyu da tsohon maigidansa, wato Shugaba Buhari. Idan ba a manta ba, a kwanakin baya Malam Sani ya yi dan takaitaccen bidiyo akan yana son ya ga maigidansa Shugaba Muhammadu Buhari. Amma har yanzu Allah bai yi ba.

Tun a shekarar 2016 ne dai Malam Sani yake ta son ganin Buhari ido da ido amma har yanzu hakar sa ba ta cimma ruwa ba.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button