AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 41-42

Ameelah tayi rau rau da ido kamar mai shirin yin kuka, ta daura hannunta akan kypat tafara typing

Ameelah “waye dan Allah, menai maka na zagi”

New no ” ni bawan Allah ne kamarki amma ba irin jinsin kiba, ni aljanine, yanzu haka duk abinda kike yi ina kallonki, watar Allah ukubar Allah tana tattare da macce mai hali irin naki, yanzu haka ina kusa dake, la’ananna wacce bata san darajar Amanar aure ba”

 Bashiri ameelah ta fara duba gefe gefen ta cike da tsoro tatashi tsaye, tana kallon falon, 

Saida Ta tabbatar da komai aciki sannan tamayar da edonta ga wayar tana duba sakon daya turo, tsaki taja a zuci take fadan “wannan yama rainamin hankali, ni zaicewa ba mutum bane,
Cike da bacin rai da kuma raini tafara masa reapply

Ameelah “to idan kai ba mutum bane kafito naganka, ko angaya maka ni matsoraciyace “

New no ” hahaha ai bazan fito kigan niba domin ku bil adam bakuda karfin halin ganin tsarin halintarmu amma zan taba kyankyawan gashin nan naki ki tabbatar da cewa ina kusa dake “

Ameelah “?? eh nayarda kataba din…mtsw”

Taja tsaki tana kokarin rufe data taje ta kwanta domin taga karfe 3:10,
Ta rufe Datar tayi tsaye tana tunanin mutumen,

Jitayi an fizge gashinta da karfin tsiya, wata irin mahaukaciyar ihu tasaka, ko juyowoba bata yiba tafadi kasa somammiya,
( nida nake gefe saida birona yafadi, saboda tsoro, koda naduba gefen abdul shiharyakai bakin kofar fita daga falon, lolllx …nayi kamar nabisa amma sainace to idan nabisa yazaayi nasan halin da ameelah zata shiga saina tsaya)

Kamar daga sama hilal yajiyo ihunta a cikin baccinsa, a gigice ya farka da sunan ameelah a bakinsa, yaduba bata kusa dashi, a gigice yatashi ya nufi bandaki, yaga bata ciki da gudu yafito yanufi falo,
A kwance yasame kasan cafet, da gudu yakarasa gurinta ya daga kanta yana girgizata yana kiran sunanta amma shiru, ya daura hannunsa a akan hancinta yaji bata numashi, a gigice yatashi yakoma daki yadauko makullan mota, yafito ya tallabota, ko takalmi babu a kafarsa, yafita waje a mota yasakata gidan baya, sannan yayi sauri yaje ya bude gete yadawo yashiga motar ya tada motar yafita, bai tsaya kulle gidan ba adu ar fita daga gida yayi yabarwa Allah sarkin iko… Domin yayi ikonsa akan gidan nasa,

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button