NOVELSUncategorized

WA ZAI FURTA 15

???? *WA ZAI FURTA?*????
              1⃣5⃣

*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri’a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.**KINA RAINA MAMAN WEEDAD*

*Domin ki…… beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*

      *****************
*Federal University dutsinma*

Anwar din nan ya mayar dani sakarai. Shi girman Kai ya hana ya fito yace Yana Sona shine yake ta gewaye gewaye, bai San halina ba, a dole yanda banzayen Yan matansa ke zubda class suna crushing din sa nima haka yakeso nayi….. Ba dai Bilkisu ba, ko Zan mutu bazan ce Ina son sa ba.
Zan daure na cije na nuna mishi ban San inda ya dosa ba inaga idan yaji uwar Bari *Zai furta*.
   Ya fada bisa gado…… Ya kalli sama .
Sadeeq ya kalleshi an dawo fa!
    Baka ga missed calls Dina ba?
Ina so ince ka amso Mana abinci *M&M*…… Abdul din fa ya daina dafa indomie ne?
Kai ubanka da indomie din Nan, Wai me yasa kake son gana Mana azaba?……
Ya kyalkyace da dariya azabace cin indomie?
Nifa bazanje wani *M&M* ba kawai muyi normal life na student kada mu banbanta……  Ubanwa yace to baka sai Mana gida ba ka kawo mu hostel?
Ya Kara murmushi….ba za ka gane ba..
Ban ganewa wallahi…. 
Ranar da aka ganoka tabbas ka shiga uku…..in shaa Allah har na gama babu wanda zai sani,
Ya bude ledar da Bilkisu ta bashi kamshi ya doki hancin sa, rantsattsen agogo ne Mai tsada cikin cover……. Kai ya tashi zaune.
Menene?
Bilkisu ta siya mun agogo wallahi.
Ya fada Yana daga Shi sama……. 
Hmmm, wannan babbar kyauta ce, ka daina cinyewa Yar mutane kudi fa.
   Yayi murmushi ya cire na hannunsa ya mayar da nata…….
Anwar a fidda maganar wasa ka dubi girman Allah ka sai Mana gida ko ka Kama Mana haya mubar wannan kwamachalar…… 
So kakeyi nayi ma wata ciki….. Ya zaro ido.
Yes! Bari na fito maka a mutum sak!
Dan ubanka yanda Yan matan nan ke kawo man hari kana tunanin idan na ware baxasu bini daki ba? Ko ni katako ne da Zan ga mace daga ni sai ita na……. Shikenan, ai shikenan next year by now mun Fara bankwana ma.
   Wayarsa tayi Kara ya dauka……. Ya Dan kalli sadeeq buga mun sixteen million times 42 please……….
Bayan ya ajiye sadeeq ya hado musu oat suka Sha sannan suka tafi masallaci.
   Akan hanyar su ta dawowa yace sadeeq  Ina son ka Sami Suleiman kace kada na Kara ganin sa da Bilkisu……. Dalili?
Ya katseshi.
Haka Nan…..
Zancen banza kenan, haka kawai sai ka raba su babu dalili?
Yaron banza ne bana son sa…..kada ka tsani Dan mutane. Kowa yasan Shi mutumen arziki ne idan kana da wata hujja ka fiddo kafin ka yanke zumunci.
  Kana ganin wasa nake ko?
Wallahi semester din nan takunkumi Zan sakawa Bilkisu akan Shi saboda Shi kadai take kulawa yaron Yana da mugun shisshigi.
Anwar! Anwar!! ….. Idan son yarinyar nan kakeyi…….. Wai Kai me yasa baka ganewa? Dole sai Ina son ta Zan Sanya doka akanta???? 
Ni Sona takeyi da take Sanya mun doka inabi?
Ko kasan yarinyar nan juyani takeyi kamar waina?( Masa ).
Kuna dai juya juna.
Kuma duk laifinka ne, ka zauna wurin kallon ruwa kwado yayi ma…..
Sadeeq Banda wani personal business da yarinyar nan da ya wuce friend, kawai bana son tana kula Suleiman period.
Mtseew to ka jaraba ai Bilkisun ba bakuwar ka bace na tabbatar akan Suleiman tana iya kyaleka kwata kwata…… Da gaske? Ya zaro ido.
Lallai dole naci uban yaron nan.
Sadeeq ya tuntsure da dariya, Allah gamu fareka…. Sai ka maida hankali toh.
  Kai da Bilkisun duk munafukai ne kowa Yana fama da ciwo ya gwammace ya mutu da ya fitar da cutar……
Kamar ya?
Kai ba bahaushe bane?
Ya doka tsoki……. inyamiri ne ni.
    Yaushe Anas yace zai dawo?
Sunday.
Ai Kaine ka kwaso mu badon na shirya ba wlhi.
  To ya zanyi?
Ya kalleshi ya zakayi? Wani ya tilasta maka?
Ya kada kafada tare da watsa hannu yace ko daya.
   Zaku kaisu idan Kaya ne.
Ina tausaya maka ranar da wani zai maka shigar kutse……
Ku bakwa ganewa, yarinyar nan tana Sona fiye da duk wata yarinya da ke hauka a school din nan, na rasa girman Kan da ya ke hanata *FURTAWA*……. Kai ba sai ka *FURTA* ba?
  Mtsew….your are not well.
   Ya kwanta bisa gado, ka dafa Mana shinkafa muci da miyar can Mana.yayi murmushi ka canza maganar Kuma? Toh
Yanzu kuwa ya Fara Shirin aiki.
  
Ya janyo waya ya Kira Bilkisu,
Tana kokarin fere doya  Aisha na warming Miya daga gefe Kiran ya shigo,
Ta ce hmm sannan ta daga …..
Hello, Ina wuni……
Ya lumshe ido Yana son gaisuwar ta yarinyar nan nada da’a sosai.
Lafiya, ya kike?
Qalau.
Keda waye nake Jin motsi?
Aisha,
Kuna meye?
Girki.
Me ye ne ?
Kai ai da gangan akai tamabayo……
Doya da Miya.
Zanci…..
Aikuwa baka cinsa sarkin roko……. Ya tuntsure da dariya har Yana sarkewa da miyau…. Aisha ta kura Mata ido tana kallonta. Keda waye?
Ta bude Baki ta Mata alamar Anwar ne ba tare da sautin ya fito ba.
Rowa Zaki mun?
An maka……..
Shikenan. Ki shirya anjima zamu je na siya Miki wani Abu cikin kudin Dana tara ko kuwa?
Ka dai ka siyo ka kawon ba sai munje tare ba.
Saboda me?
Haka Nan.
Karya kikeyi ba Kya son samarinki su ganki Dani…….. Sadeeq ya kalleshi Kai da wa??????
Harar sa kawai yayi.
Kinji?
Ni nakeyin karya?
Eh, ko gaskiya Kika fada?
Kai Ni ban iya abinda ka iya ba….. Meye na iya Wanda Baki iya ba?
Neman magana…… Ina mamakin yanda ake cewa baka magana kana da jiji da Kai amma Ni wallahi nace surutu gareka ga roko……. Ya Kara yin dariya…. Ke Kuma rowa gareki ko?
Rowar me?
Meye ka ce na baka na Hana?
Abinci.
Mtsew…tayi murmushi badai zance kazo kaci ba .
Muma ga sadeeq na dafa Mana shinkafa Mai dadi Ni na kawo Miki?….. Na koshi aci lafiya.
Allah kuwa….. Bana ci na gode malam .
Kai lazy baka dahuwa sai an dafa an baka ko?
Inji waye? Nafi sadeeq  iya girki ko kina musu?
Eh.
In dafo in kawo Miki Zaki ci?
Noooo, ta fada da sauri. Yayi murmushi yarinyar da kinji akul.
Ta ce hmm.
Zan zo anjima kinji ko?
Okay.
Ki gaishe mun da Aishar Bari na dauki wata waya…… Ya katse Kiran.
Ta kalli Aisha Anwar case ne.
……… Gaskiya ai Yana bala’in yinki. Anwar Dan gadara Shi yake Kiran mace kinji yanda ake surutun miskilancin sa kuwa?
Inaji amma nake ga kamar hada Sheri….. Wallahi da gaske ne.
Yan matan ne basu da  zuciya. Kinga wulakancin da ya ringa yi ma khausar har kuka take mishi…. Jakka kuwa ki Sami fareeda yarinyar nan Bata da zuciya wallahi….. Ke Aisha namiji munafuki ne kedai baki sani ba ko Yana gewaye wa.
Last semester gab da za ayi hutu da yazo cewa yayi zance ya fito ya biyo wurina Kuma kema kinsan kilan bai wuce mufeeda ko wannan dayar banzar Yar aji hudu.
  Hmmm, kawai Aisha tace.
    Salim bai dawo ba Ina Zan Sami aron mashin?
Sadeeq ya Fara maka mishi uwar harara ai taurin Kai da wulakanci ya Hana ka siya Mana sai kaje ka hau kabu kabu……… Wohohoho….. Wai nawa mashin din yake in siya a huta?
150-200k wannan range din.
Mtsew…… Ka shirya gobe ka shiga katsina ka siyo Mana…… Ya buga ihu.
Ya shako wuyansa….. Koda wasa ka nuna inada alaka da hakan ubanka zanci….. Bazan fada ba cika ni mugu…… Ya wuce har ya Kai bakin kofa ya waigo wane police station ne DPO ke Zama a garin Nan??……. Ya zaro ido DPO? Lafiya meye zakayo wurin DPO?
   Zan sa ya ma Dr Dan Musa warning da Suleiman akan Bilkisu………. Wata muguwar dariya ya saki munafuki karshen tuka tika tik… Yanzu ka *FURTA* mun abinda nake son…… Dawowa yayi zai Kara shako Shi yayi bisa gado…. Allah ya baka hakuri.
 Amma Ina baka shawara zaka tona asirinka a banza saboda zasu so sanin wanene….inji waye?
Ba zai fada ba. *This is legal warning* …… Ya fice da sauri Yana duba agogo.
Ya daga murya inzo in raka ka??……. Da ga can waje yajiyo Yana surfa mishi zagi.
    Yana sauka achaba Aisha na zuwa zata tsallaka titi….. Aisha. Ya Kira sunan ta.
Laaa Anwar Barka da dare an dawo lafiya?
Qalau, je Kira mun Bilkisu….. Tayi jimmm sannan ta ce toh ta juya Shi Kuma yayi tsaye maimakon yabi bayanta.
Tana tafe tana masifa, je Kira mun Bilkisu kamar wata barar sa..mtsew. Haushi na da Shi Sam bai da manner of speaking Yana magana a gadarance da Isa na tsani wannan wulakancin wallahi.
   Tana wankin toilet ta shigo…. Kizo inji Anwar.
Ta dafe kirji…kin ban tsoro wallahi.
Ta harareta kawai zata juya….. Aisha Wai ya akayi?
……. Pad Zan jarbo Ina sauri ya ganni kawai ba wata magana Wai *je Kiran Bilkisu* irin yarinyar nan wacce ya ajiye….
Kiyi hakuri kin dai San Hali…… Eh amma ki ringa kwatanta mishi wata rana Zan yankwana Shi….. Kiyi hakuri dai, jira mu fita tare Dan Allah. Idan mun Gama Zan rakaki….. Wai injira ki wurin sa?
Baki da hankali wallahi idan yamun wani dizgin inyi Yaya dashi?,
Bazaiyi ba, idan ya ganmu tare bazai…… Wallahi bazan je ba. Kina tare da Anwar seems like you don’t know him ko? Mtsew taja guntun tsoki ta fice abinta.
  Ikon Allah. Kai Anwar nikam tawa ta sameni…….. A yanda yayi rantsuwa tabbas idan ban fita ba shigowa zaiyi.
  Ta dauraye hannun ta, Daman Riga da wando ne jikin ta, ta zumbula hijab har kasa ta Dan fesa turare kadan ta fito…..
  Bashi babu alamar sa, ta juya ta waiga ba kowa, tana niyyar komawa ciki har ta saka kafa daya ciki kiransa ya shigo…… Ta dauka hello……. Kin fito Kuma kin koma.
Ni Banga kowa ba kana Ina?
Bakin titi….. Bakin titi Kuma? 
Eh. Ki karaso…. Meye zanyi a bakin titi?
Kina da gardama ne Wai? Just come here simple and short why are you arguing?? Ya kashe wayar.
Wai ni zai mulka? Irin yanda yake juya Yan matansa Nima haka zai juyani? Ta doka tsoki ta wuce ciki…..
Kofar taki buduwa daman tanayin haka some times, da kyar ta bude tana saka kafa Yana saka tashi…… Ta firgita, ta tsorata sannan ta razana ainun. Gabanta yayi mummunan faduwa ta zaro ido tare da bude baki zatayi magana …..ya riga ta, kina daukar maganata wasa ne?
An fada Miki akwai Wanda nake tsoro ko shakka duk dutsinma?….. Babu, Dan girman Allah kayi hakuri muje tayo hanyar fita yasa hannu ya maidata… Ban gama ba……. Sai kawai tayi kneel down na tuba Dan girman Allah muje waje idanunta sun Fara kwal kwal alamar zata Fara kuka…… Ya buga tsoki ya juya.
Ta Mike da sauri ta janyo dakin ta datse ta bishi da gudu.
  Tafiya yakeyi yaki tsayawa…..
 Ta Kara sauri ta tari gabansa Wai Ina zame je ne saboda Allah?
Me yasa kika zabi bani wahala da bin yarda nake so?.
  Kayi hakuri wallahi daddy ya ce baya son fitar dare Anwar kada a sanar dashi zanji Babu dadi……. Da Yan iska yake nufi ni Kuma ba Dan iska bane…… Ikon Allah ba haka nake nufi ba.
Okay to wuce muje….. Zan siya miki sweet ne da kudin aikina…… Wallahi da wasa nakeyi maka kawai na fada ne….. Ni Kuma da gaske na dauka saboda haka wallahi sai munje.
   Shikenan, suka jera.
Tayi murmushi ko ke fa? Amma ke komai sai anyi tsiya tukun.
Me kike so?
Duk abinda ya maka…….
Kinga agogon ya mun kyau? Ya nuna Mata . 
Um, kawai tace .
Na gode fa, Allah ya Kara dalili.
Amin.
Zaki ci nama suya?
A’a na gode.
Kaza fa?
Bana ci.
Shawarma…… Nifa bana bukatar komai.
Lallai yau zamu kwana a titi…… Ta kalleshi da sauri. Ya bita da ido Daman so kawai yakeyi su hada ido….. Allah matukar Baki ce ga abinda Zan siya Miki ba haka zamu kwana…… Biscuits. Tayi saurin cewa. Muje ka siya mun biscuits.
  Ya yi Yar dariya ko kefa?.
  Napep! Ya daga murya. Shi Kuma ya tsaya. Ta kalleshi da sauri…… *Abis supper market* zamu je Nan kadai Zaki Sami biscuits din da kike so….. Anwar, biscuits ko anan akwai Dan Allah…… Mtsew Allah ya raba ki da gardama. Muje ko in daukeki…… Kafin ya rufe Baki har ta tsallaka titi.
  Ya dunga mata dariya. Ta turbune fuska….. Gaskiya bana Jin dadin abubuwan nan Anwar bana son abinda kakeyi mun….. Kiyi hakuri.
….Ina zakuje ne?
*Abis supper market* Anwar din ya fada Yana kallonta .
Ta harareshi kallon Kuma na menene?
Wallahi na tsani kallo rayuwata…… Na sani. Yace Yana dariya.
Ka sani Kuma bazaka daina ba?
Ya kyalkyace da dariya Nima na tsani kallo fa ta Yaya Kika San Ina kallon ki?.
  Yanzu Ina amfani wani ya ganmu a Sanya Ni a bakin fudma ace har mun Fara fitar dare sai ma a ba abun wata fassara wallahi. Mtsewww.
  Fassarar me?
Ta mishi banza…..
Kinji?
Ta harareshi, ya kamata ka daina zuwa mun da dare gaskiya bana iya masifar Yan matanka kullum sai an mun zobe kamar za a dakeni…… Basu iyawa. An fada mun tsoronki sukeyi tun lokacin da Kika Mari kawar mufeeda…… Au ka sani ma ashe.
  Yap. Yace Yana murmushi.
 Dai dai sun kawo ya Mika mishi kudin suka shiga.
Ranka ya dade….. Ma’aikatan suka taso .
Ta kalleshi da alama regular costumer ne Kai.
Murmushi kawai yayi.
Kije ki zabo biscuits din da kike so.
*Short bread* daya is okay….. Ke bana son gidadanji kije ki kwashi Kaya kinji ko idan kina Jin kunya Kuma muje na Taya ki ya zungureta da hannu…. Kamar ta bude kasa ta shiga don kunya yanda aka Mata ratai da ido.
   Sam ta kasa nuna ko daya…… Ya Kira yaron ya ce duk layin Nan sauko shi, tayi Yar dariya tunanin ta zolaya ce yakeyi.
Da sun Kara gaba yaga wani kalar biscuits din sai yace wadannan ma duk safko dasu…….
     Wasa wasa ta ga abu da gasken gaske bata San lokacin data janyo Shi baya ba *Kana qalau* kuwa?.
 Ya Kai fuskarsa daidai saitin tata kamar zai yi kissing dinta…tayi baya da sauri yayi kasa kasa da murya *Yi kokari ki dizga ni*….. Kamar zatayi kuka ta kalleshi ka dubi girman Allah….. Me yasa kike son yi mun irin wannan magiyar Mai tsada?
  Ya katseta hannuwan sa duka a kirji.
  Ka ce su mayar da biscuits din can….. Wallahi duk wadanda suka sauko bazasu koma ba, idan Baki sa hannu kin dauki Kaya ba Zan siye duk biscuits din dake super market din Nan…… Ta zaro ido….
Kamar me Zan Dauka?
 Na bani ni Bilkisu kawai take nanatawa a zuciya…… Duk abinda kike so perfumes, cosmetics, drinks… everything.
…… Dabara ta fado Mata, okay na amince amma kaga Yanzu duk Ina dasu ka Bari semester tayi nisa Zan biyoka…… Yau fa sai kin dauka Kuma zamu Kara dawowa hakan ma ba laifi bane.
 Kamar ta daura hannu a ka ta yi ta ihu…. Ta kalli yaron kaga zo daukon *women million din can please*, Kuna da Apple juice? Eh hajia Mai sanyi ko marar sanyi….. Kamar ta zageshi don takaici, ta daure tace bani marar sanyi.
Suka Kara zagayawa ta dauki robar chewing gum banana. 
Ta kalleshi wadannan sun isah na gode.
Are you sure?
Um. Tace da kyar.
Biscuits din da yasa aka kwaso anata packaging a kwalaye manya…… Assorted biscuits ne na kwalaye da gwangwanaye…
Tayi tsuru duk da diririce.
Watau Anwar gidansu akwai kudi shine yake boyewa yace karkashin sadeeq yake komai sai ya nuna sadeeq ke dashi ko zaiyi.
Hmmm, kawai take cewa.
  Yasa hannu ya fiddo ATM wasu dunkulallun dollars suka fado…….. Ta bishi da ido jikinta sai karkarwa yakeyi ta Fara tsorata da al’amarain sa.
  Ya Dan kalleta Yana Yar dariya, ajiyar sadeeq ne…..mtsew taja guntun tsoki tayi gaba.
  Ya biyota da sauri ki jira zasu bayar da mota akai mu kayan sunyi yawa……. Ta rike kugu ta tsare Shi da ido sannan tace *WHO ARE YOU??gg?*

****************
    *KADUNA RIGASA*
Ta fada bisa gado ta saki kuka….. Ya karaso Ummi tashi ya dagota…. Kiyi hakuri wallahi ba abinda kike tunani bane I just hugged her….. I don’t want hear about it.
Naji but kiyi hakuri ya rungume ta, I was confused these days. 
  Tsakanin Miji da Mata sai Allah cikin second zancen ya sauya launi ya shawo kanta ….
  Kuka sosai Amira keyi tana cewa tabbas na ma kaina wauta me yasa na bayyana Mata abinda yake so da Wanda baya so? Me yasa na sakar Mata ragama…
 Tabbas ya shiga rudani ya kasa tantance daya cikin biyu… Ta Kara rushewa da kuka.
  Yayi lamooo bisa cikinta, ita Kuma tana shafa kansa…. A hankali take magana.
Kafi son matarka Dani,  har Yanzu ka kasa sabawa da ni matsayin matarka, a kullum…
 Ya rufe mata baki da hannu, I’m sorry baby, Ina sonki musamman Yanzu da Kika dawo normal wife kina biyayya ga sharudda na sannan kina kula dani….
Me yasa kake saurin kamuwa Koda kuwa wani abun munyi shine saboda makircin mu na Mata?..
Yayi shiruuuu….. Ya kasa magana hakika ya gano inda zancen ta ya nufa, ta yi murmushi hakika Yana da kyau ka Zama jarumi Mai iko da bukatar sa.
 Kiyi hakuri please I’ll change….. Hmmm Allah yasa zaka iya.
Kuma Ina rokon ka Dan Allah idan kasan har Yanzu kana kokwanto akan son da kakeyi mun…. Ba wannan maganar Ummi ya fada tare da janyo ta jikinsa….. Wallahi Ina sonki fiye da yanda kike tunani sometimes Ina rasa meke damuna amma na gano bakin zaren na Miki alkawarin zakiga canji.
Please am sorry dear.
Ya Kara rungume ta……..✍????

*Zainab wowo ce*????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button