Wani Mutum Ya Kashe Matarsa Saboda Ta Gina Makaranta Batare Da Sunanshi Ba.

Wani magidanci a Ogun mai suna Segun Omotosho Ebenezer ya lakaɗawa matarsa Bukola duka har lahira saboda ta ki miƙa masa makarantar da ta gina saboda ta saka sunan ta.
A cewar rundunar ƴan sandan jihar Ogun, wanda ake zargin da marigayiyar sun yi ta cece-kuce a kan kadarorin kafin ya lakaɗa mata duka har lahira.
A wata sanarwar da ƴan sandan suka fitar a ranar Litinin ɗin da ta gabata sun ce an kama mutumin ne bayan da ya gudu a lokacin da aka tabbatar da cewa shi ne ya kashe ta sandiyar dukan da ta sha a hannunsa.
Wanda ake zargin dai bai a sani ba, ashe marigayiyar ta aika da saƙon murya ga ƴan uwanta, inda ta sanar da su cewa mijin nata ya yi amfani da wani makulli ya buga mata a kai yayin da yake tsaka da dukan nata, kuma idan ta mutu to su sani mijin nata ne ya kashe ta.