WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL
WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL
Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150
Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.
????Sadi-Sakhna________✍????????
(¯’•.¸,¤°’✿.。.:քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ.:。.✿’°¤,¸.•‘¯)
????•°• WASA FARIN GIRKI •°•???? {cigaban gidan gandu}
????13~14????
Komawa ɗakina nayi nikaɗai ina tsuka,haba irin wannan halin ai dole komai ma a fada muku.
Bayan sun kammala inna rabi ce kawai tazo mukayi sallama,sauran wai haushina sukeji,itama ciki ciki mukayi magana,a raina nace ai sai kuyi babu dama mutane basason gaskiyah kwata kwata.
Ina jin ƙarar tashin motar tasu,dan daga window na ma ina ganin kokuwar da sukeyi akan shiga motar.
Yau kwana na uku a gidan sameer,rabona da ganinsa tun lokacin da yakawomin kazar amarci,ko nace kazar al’ada,matar gidan kuwa rabona da ita tun a falo sanda aka kawoni,ina jin motsinta a falo da kicin,duk da yawancin muryar wata nakeji a ketchen ɗin daban.
Ganin zaman ɗakin ya isheni ne kwana uku yasa na saka wata doguwar riga bayan na fito daga wanka,babu abinda na saka a fuskata haka na fita zuwa falon.
Babu wanda na samu sai kallo shikaɗai yanayi,wajen abincin na wuce na zubo masa da miyah taji hanta na dawo falon wajen da kallon yakeyi.
Ina jiyo hayaniyar saleema ita da wani,da alama mijinnatane yake nan.
Can wajen kamar minti uku naga sun fito daga ɗakinnasa,sai shagwaba take yimasa shikuma yana biyeta kaman wata yarinyah,ta wani lafe a ƙirjinsa tana bubbuga ƙafa,
“Uhm uhm honey wallahi nikam zan bika mutafi,kayimin akawarin waccar tafiyarfah amma shine zaka cemin wai bazanje wannan ba”
“Kai saleemah da rigima kike,da da yanzu ba ɗaya bane,lokacin baya ke kadaice amma yanzu kinga ku biyune koh”
“Ahah ni bazan yaddaba,naga ita ba sonta kake ba auren dolene kawai da cika wasiyyah,dan haka nikam muyi tafiyarmu kawai”
Shiru yayi na ɗan wasu lokaci da alamun bai so ta faɗi hakanba saboda sun san ina jinsu,ita kuma da gangan ta faɗa dannaji haushi,kuma take mammanne masa dan ta nunamin ita kaɗaice a wajensa.
Kallonta yakeyi da alamar meta aikata haka,ita kuwa harda wani murguɗa baki alamar tayi ɗin.
Duk abinda suke ba iyah jinsu nakeba harda kallonsu,saidai ba kowane zai kula ina kallonsu,saboda na kware a wajen satar kallo da kuma ɗauke magana.
Ƙarasowa sukayi cikin falon har sannan tana maƙale dashi,wanda duk da ba damuwata bin ka idaba amma nasan ka idar amarya itace da miji,amma daga dukkan alamu a ɗakinta na kwana,kuma ma dannasam hakanne yasa ta shigaba da faɗar.
“Honeey jiya fah muna kwance da daddare na fada maka cewa,ni bazan yi sharing falo da wata ba,kuma baka ce komai ba,gaskiyah saidai tah koma ɗayah bangaren kawai”
Kallon fuskarsa nayi wanda yake min wani kallo da niyyar yana jiran yaga mai zanyi,bai san koda za’ayi shekara suna zancensu bazan yi magana ba saidai idan sakani sukayi a ciki.
Tashi nayi na nufi kitchen domin kaiwa plate ɗin danaci a binci a ciki.
Lokacin dana dawo suna dinning wajen cin abinci,cigaba nayi da kallon labaran da akeyi a ƙasar iraq cikin harshen larabci na ƴan ta’adda da suka kai hari.
Hankalina ya tafi gabaɗaya wajen labaran da ake yi,banzata ba sai gani nayi an sanja tasha zuwa ta zee world.
Kallon mai wannan aikin nayi,saleema ce a ɗaya kujerar da take gefena ta saka idonta akan tv,ga kuma remote a hannunta tana jijjiga ƙafa wanda tasa ɗaya kan ɗaya.
Dan takaici ma bansan abinda zance ba,dan ko kaɗan banida ra’ayin yi mata magana a lokacin bare kuma faɗa.
Shima kansa sameer yana kallon abinda yake faruwa,amma ko ƙala bai ceba.rintse idona kawai nayi domin tunano mai ma zan mata wanda zan huce.
Sauke idon nayi a kanta wanda nasan koba madubi a gabana nasan sun sanja kala daga yamda suke.
“Ko ki mayar da tashar da takeyi ɗazu ko kuma nayimiki abinda ba kya tsammani,sannan idan na ƙirga goma baki mayar ba,shikansa tv to daga yau yah tashi a aiki bazai ƙarayiba,sannan duk wanda yaje gidannan abinda zai biyo baya bazai yimasa daɗiba.
Sanann abu na ƙarshe ina baso kike na karya ki karal ki tashi daga aikiba toh karki kuskura a zantukanki kisake sakoni a ciki,dan abin bazai yi miki kyauba”
“Heee me kike tunanin zaki iyah yimin,toh dama jira nake ki tanka dannaji ɗazu kinyi shiru,toh idan baki saniba ba’a shigo sansanin zaki a taba ɗansa a fita lafiyah,dan haka ke ba komai bace a cikin garinnan ma bare kuma gidannan,dan duk abinda yake gidannan toh ki sani mallakina ne nikaɗai,komai kika taba alfarma aka yimiki,dan haka dole nayi yanda naga dama,babu abinda zaki iyah,idan ba hakaba kuma nasa a hukuntaki kuma babu mai ƙarbar ki a hannuna koda kuma mutum zai saida gidan gandu”
Zuwa yanzu maganar na kula bada iyah ni kaɗai take ba harda shikansa uban gayyar,dan taga kissar bazata kaitaba sai ta koma gargaɗi kawai.
Murmushin gefen baki nayi,ita ana ta tunanin ƙananan sojijin da ubanta yasa suyi gadinta,wasuma a cikinsu koh training cikkeke basuda shi sune zasu iyah yimin wani abu,saidai nayi mata uxuri ai zaman yamzu aka fara zata yi abinda bazan ƙyaletan ba.
Kallon agogon falon nayi wanda yah nuna goma dadai,mayafin kai na na gyara kafin na koma ɗakina domin ɗauko takardun aikina,akwai abinda nakeson yi banida lokacinta.
Lokacin dana fito daga ɗaki na fita waje sameer yana ƙoƙarin tayar da motarsa zai fita.
Kallon kallon muka sake yi,sannan ma bai yimin magana ba,nima kuma banyi alamar zanyi masanba,yana fita da motarsa nima na fita daga gidan zuwa office ɗin ƴan vigilantee na garim porthacourt.
????zainnb a madubin gani????
Kallon zanin dayake jikina nayi wanda yayi duƙun duƙun dashi kaman an tono ni a cikin toka,dam takaici ta kuma wuyah inaga nayi kuka yafi cikin kwando daga kawoni gidan yunusa,wanda koh wata ɗayah banyiba,gashi jiyane tun waccan satin yakamata naga al’adata inaga ma cikine dani,wayyo allah na da wanne zanji haka.
Wallahi ji nakeyi kaman na gudu a rasani gabaɗaya ma.
Muryar inna laraba naji daga cikin gida kaman goge tana ƙirana,tun safe nake gindin murhu har gashi la’asar tayi amman koh gyaran ɗaki banyiba,gashi miji na maidashi sabatoto,naje anyi masa asiri bashida aiki sai cemin toh duk abinda nace kuwa.
Amsawa nayi a ƙasan maƙoshi kafin na gita dan jin menene dalilin ƙiran.
“Wai a Ina kika makalene tun d’azu nake kiranki kaman an aiki bawa garinsu”
Shiru nayi ban bata amsaba,toh mai zance bayan tagama fadanta kuma.
“Kowa yunwa yake ji kizo ki raba abincinnan mana,ko so kike ki kashemu da yunwa dama kin washemu,ga altine ma yar mijinki tazo,ƴaƴanta sai yunwa suke ji,kizo kobasu abinci dan basu saba da yunwa ba”
Takaicine ya isheni,mai take nufi kenan,ni na saba zama da yunwar ne aka fadamata kome?
Dan babu yamda na iyha haka na je gaban ƙatuwar tunkuyar na fara zuba shinkafar,jajir da itah bata da maraba da dawa,daɗinta daya ma banice da tuwon dareba,zan samu na nakwanta na huta kafin wani jiƙon kuma.
Ina gama rabon na ɗebi nawa na tafi ƙofata,dan dama nikaɗaice a ƙofar yunusa yah tafi aikin ƴan sanda an turasu garin darazo a jihar bauchi.
Burina bai wuce yah samu sugama training ɗinba yasamu aiki a wani garin na bishi,ko na huta da wannan uƙubar da ko yanzu aka barni da itah na azabtu yanda yah kamata kuwa.
Tsabar gajiyar danayi koh abincin dana shigo dashi banciba,ina kwance ina ta tunani har bacci yah ɗaukeni bansaniba.