WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL
WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL
????sameemah a madubin gani????
Ina fita bakin titi na samu mai adaidaita sahu nayi masa kwatancen office ɗin ƴan vigilantee,mun dan dade muna tafiyah kafin muka iso wajen,a bakin wajen na sauƙa na bashi ƙudinsa kafin na wuce zuwa cikin wajen.
Bansamu wani wahala ba na ganin shigaban kasancewar babu layi kaman office ɗin dana je a baya.
Wani na samu aciki ana sallamarsa da alama aikin yazo nema shima,dan ƙaramin matashine mai jini a jika,bai dade da shigaba sai gashi yah fito yana murmushi da alamun yayi nasara,nima shiga nayi na zauna a kujerar da take kallon shugaban.
Karim farko takarduna ya ƙarba,ya dade yana dubawa kafin ya dauko wata takardar a gefen sa ita ma yah duba,ɗagi kai yayi yana kallona kafin yace,
“Sameemah umar koh?”
Daga masa kai nayi alammar ehh,zare glass ɗin dayake fuskarsa yayi kafin yace,
“Saidai kiyi haƙuri,amma ma’aikata sun cika a nan bazai yiyu mu baki aikiba”
“Hmmm yallabai kenan,waye ya hana a bani aiki anan wajen,sannan menene dalilinsa”
Tun kafin yabani amsa na tafi wani tunani,irin kallon da sameer yakemin lokacin dana zo fitowa daga gidan,sannan shekaran jiyah naji kamshin wani turare a dakina wanda ba nawa bane,tabbacin wani yah shiga ɗakina kenan,wato yah plan ɗina na cigaba da aikina shiyasa ya min haka.
Dakatar da shugaban nayi tareda cemasa,
“Karka bata bakinka,nariga nasan wanene yasaka ka hanani aiki anan wajen,na gode da bani aron lokacinka”
Takarduna na ɗauka na fice daga office ɗin.
Tun daga bakin titin na danna ƙiran burgu a wayah.
Ringing biyu tayi yah amsa,duk hayaniya ma da alaamun yana kan hanyah,saidai tunda yana jina shikenan.
“Kai burgu”
“Na’am shugaba jar wuyah amarya a wajen major yah akayi ne”
“Ba surutu na ƙiraka kayimin ba,ina so kaje anguwarmu inda na bada ajiyar su bingo,kasaka minsu a manyan motoci su kawomim su garinnan,yau ba sai gobeba,so nake zuwa gobe sun iso wajena”
“Amma shu…….”
Kittt nayi saurin katse wayar dan banason wani dogon surutu kuma.
Alllah allah nake gobe tayi su bingo su kariso,so nake na koma ainihin sameemah da kowa ya sani,banason hakurinnan danakeyi da kuma yin shiru akan abu,zuciyata batajin daɗin hakan,saboda bada wannan sameemah na daceba sam.
Shikuka sameer zai san yahana a bani aiki,badai zaman gidansa yakeson nayiba ,zai san yah sakani zaman gida kuwa.
Wani mashin ɗin na hau zuwa gidan,tun daga bakin ƙofar shiga falon nakejin murayar wata a falon,koh sallama banyiba na shiga.
Haɗa ido mukayi da wata wacce bazata wuce sa’a taba,daga yanda suke zance mutum zai san abokiyarta ce.
Har nakai bakin ƙofar ɗakina naji tayimin magana,hakanne yasa nadawo daga shiga ɗakin,
“Amaryar bakyaa laifi,babu maganane,sunana suhaila budurwar Ahmad abokin mijinki,koba komai zaki zo mugaisa koh”
“Toh koh shi Wanda kika ƙira da sunan saurayinnaki ban sanshiba,ko na sanshi ma ba tsayawa zanyu mu gaisa ɗinba,bare kuma ke da kike matsayin budurwarsa”
Ƙarisa maganar nayi ina kallon cikin idonta tareda da ɗaga girata kuda ɗaya dan tasan ma da gaske nakeyi,sakin baki tayi tana kallona da mamaki,bantsaya jin mai zata sake cewa ba nayi cikin ɗakina.
????saleema a madubin gani????
Tunda aka kawo sameema cikin gidana akayi kwana uku naga babu abinda yake shiga tsakanin sameer da sameema sai hankalina yah kwanta,sai kuma nafara ɗaura ɗamrar mallakewa mijina niƙaɗai ,dan na nuna mata ita bata isa ta ƙwacemin shi ba.
A falo ma duk abinda mukayi nayi zaton zata tabani ko kuma tayimin wani abu,dama na shiryah ɗaureta zan sa ayi a ɗakin horo har sai kammanninta sun canja,sai kuma ta shafawa kanta ruwan sanyi batayi komaiba,sai ma ficewa da tayi daga gidan.
Ina zaune niƙaɗai a ina bawa zuhra nono,ina kuma chatting a whatsapp sai ga suhaila tah shigo,da tayi nayi niyyar mushige daki amma sai muka yada zango a falon kawai.
Tafawa mukayi bayan na faɗa mata abinda na aikata da safen.
Muna cikin hakanne sai gata ta shigo,da alama wani waje ta je,signa suhaila tayimin nima nayi mata lokacin da sameemah ta kusa shiga ɗakinta.
Ina jin duk maganar da,sukayi da kuma amsar da sameemah ta bata,nidai bance komaiba sai gyara ƴa ta danakeyi wacce take bacci a cinyata.
Kama baki suhaila tayi tana kallona jin irin amsar da sameema ta bata.
“Ke kiji wannan matar,wannan magana haka,kaman ana bata action,uhmmm gaskiyah kin gamu da aiki daga gani,sai fah kin dage,dan ma kincemin baya kulata,amma duk da haka saifah kin dage,ba a shaidar ɗan kuturu sai yah shekara da ya tsunsa tukunna”
Murmushi nayi kawai,danni kaɗai nasan irin abinda na shuka zam aiwatar a gidannan,duk abinda zanyi na kori sameemah a gidana to zanyi,domin itah ɗin hatsarine zaman ta cikin gidan.
Hirar mu muka cigaba da suhaila kuma duk bata wuce akan sameemah bane.
Sai wajen magriba kafin suhaila ta tafi gida,lokacin sameer ya dawo daga aiki suka gaisa ma a waje.
Tare muka shigo dashi,ina kalllonsa yama kallon gefen ɗakin sameema,haushine yakamani duk da nasan ba komai ne a tsakaninsu ba,jakar hannunsa na karba tareda kamo hannunsa cikin tattausan hannuna duk dan na ɗauke hankalinsa daga tunanin ta,kallona yakeyi da idonsa da sukayi ɗan ja saboda yawan aiki.
Nima sansanyan kallo nake aika masa wanda nasan yana narkar da zuciyarsa a duk lokacin danayi masa,musamman idan yana a yanayi na buƙata.
Ɗakinsa muka shiga yah rage kayansa yah shiga banɗaki,nikuma na ajiye jakar tareda zuwa ɗauko abincin da kareematu mai abincina tayi.
Lokacin dana shigo ɗakin har yah fito daga banɗakin yah saka ƙananan kaya marasa nauyi,hada ido mukayi dashi,lokaci ɗaya na karanci duk abijda yake kwance a cikin idonsa,kirjina yabada ƙarar bugawa fatt,saboda nasan in yana wannan yanayin bana karewa da ɗadin jiki,dan sai nayi gashin jiki tukunna.
Kawar da tunanin hakan nayi a raina na cigaba da zuba masa abimcin,saƙƙowa yayi inda nake zaune daff da dani,ɗan matsawa nayi kaɗan domin bashi damar cin abincin,saidai daga fuskarsa nagane bahakanne a gabansa ba.
Ko kuma mai yah tuna sai kuma naga ya jawo plate ɗin abinci yah fara ci.
Lokacin dayah gama an ƙira sallahr magriba,dan haka alwala yayi yah tafi masallaci,yayinda nima nayi nawa ɗakin.
Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150
Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.
????Sadi-Sakhna________✍????????
(¯’•.¸,¤°’✿.。.:քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ.:。.✿’°¤,¸.•‘¯)
????•°• WASA FARIN GIRKI •°•???? {cigaban gidan gandu}
????15~16????
????sameer a madubin gani????
Har na isa masallaci babu abinda nake sai tunanin yanayin gidannawa,a yanda halitta ta take nasan nayi ma saleema karfi saboda yanayin jiinta,idan har nace zan tursasa mata toh zan iyah shiga rayuwarta.
Bangaren sameema kuwa banajin koda mun shryah zan iyah zaman aure da ita,saboda har yanzu idanuna sun kasa ganinta a matsayin matata sai ƙanwata.
Zaman damuke yi da itah a gidan ma ya isheni bare kuma zancen wani abu daban.
Da ƙyar na samu na yage tunani a cikin raina nayi sallah.
Bayan an gama sallah ma ban koma gida ba sai addu’o’i da nakeyi dan samun kusancin ubangiji da kuma neman sauƙi akan abinda yake shirin faruwa.
Sannan ya,zabamin abinda yake mafi alkhairi a game da mafarkin danakeyi na sameema da kuma dukkan ayalina a cikin wani yanayi marar daɗin gani.
Lokacin dana ɗauko hanyar gida goma ta kusa,sojojin da suke patrol ɗin dare har sun fara,ɗaga min hannu sukayi tareda buɗemin kofar gidan na shige.
Har nayi niyyar wucewa sai kuma na shiga ɗakin sameema,duk da nasan bata son ana shigemata ɗaki,saidai ba ra’ayinta nake biba nice da iko da itah ba itace take da iko dani ba.
Murda ƙofar danayi a hankali ko a rufw yake,saidai cikin sa’a naji kofar tah buɗe.
Ina gama shiga ɗakin ita kuma ta fito daga banɗaki ta towel a hannunta ɗaya kuma tana goge ruwan daya taba gashin kanta.
Tun daga ƙasa idona yafara yawo a jikinta,yah wuce dogayen kafafunta farare masu matsakaicin ƙiba,har zuwa laffaffen cijinta da ko kaɗan bai ɗago towel ɗinba,saukewa nayi akan fuskarta wanda ita ma ni take kallo,saidai muna haɗa ido da itah ta ɗauke kanta tareda zefar towel ɗin dake hannunta ta nufi gaban madubi.
Yanda take yin kowane motsinta sia yake nuna kaman dani takeyi,amma itah a nata bangaren yi kawai take.
Lotion ta ɗauko ta ɗage towel ɗin har zuwa kusan kunkuminta kafin ta fara shafa man.
Babu abinda nake ayyanawa a raina sai yin salati da kuma yiwa zuciyata gargaɗin kan cewa,abinda take gani fa miliyoyin mutanene suka gani kuma suka taba,dan haka babu abin zan hankali akan abinda ya riga yagama zaga duniyah.
“Wai binciken kazo sake yimin koh kuma yau turoka akayi ka tsareni da ido duk abinda nakeyi”
Duk da abinda ta faɗa gaskiyane ita nake kallo,amma yanda ta faɗi ina kallonnata sai abin yah bani haushi.
“Mai zan kallah akan abinda yah riga yagama zaga duniyah,kowa yah gama kwasar romonsa yah bari”
Murmushi tayi saidai har yanzu bata ɗago tah kalleni ba,saima tashi da tayi ta nufi wajen kayanta na bacci,ɗauko wasu pink tayi masu kyau ta ajiye akan gado kafin ta juyo ta kalleni,
“Toh zan iyah sanin mai yah kawoka ɗakin wannan karuwar da karfe sha ɗaya na dare har kakemin wannan kallon ,bayan kana da mata,ko ta kasa kashe maka kishirwarka ne kazo muyi cinnki.
Saidai kasani farashina yana da tsada sosai,amma karka damu nasan zaka iyah biyah ai,yanzu sai muyi ciniki,dama kuwa na dade ban sayarda hajata ba gashi na samu costomer da wannan daren,kuma kaima ka taki sa’a da bakayi booking ba bare kuma bin layi kawai ka samu a kyauta”
Duk baƙincikin danake ciki a yinin ranar nan baikai kwantan kwacin maganar da sameema ta faɗa min ba,wannakuwa anya mutunce,abinda nah fada a ransa kenan.
Ganin koda nayi niyyar faɗar wata kalmar bazata samu damar fitowa ba,juyawa nayi kafafuna suna rawa ga raina yana tafarfasa.
Ɗakina na nufa dan ban ra’ayin ganin itah kanta saleema ma a lokacin,tambaya nayiwa kaina ,meyasa nake jin haushi dan ta faɗi hakan,meyasa nekjin maganar tayimin zafi?,nidai ba kishinta nake jiba koh?.
Kodah yake dole nayi kishinta ai ƙanwata ce.
Da wannan amsar zuciyata ta yada har na kwsnta bacci bansan sanda barawon baccin ya ɗaukeni ba.