WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL
WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL
????sameemah a madubin gani????
Ina jin sanda yah bugomin kofar da ƙarfi bayan ya fishe,ko ba a faɗaminba nasan yah ji zafin maganar danayi masa,hakan yanamin daɗi idan mutane suka ɗaukeni a wata siga da zuciyarsu ta raya musu ba tareda sunyi bincike akai ba.
Kayan baccina na saka tareda bin lafiyar gado,har sannan ban daina murmushiba da kuma tuno yanda yake bin jikina da kallo,wanda kuma hakan zai ganshi yah bari,dan bana kowa bane na wane ni ka kadai.
Washagari da safe ina tashi da feɗuwa na sauƙo daga kan gado,dan yau kam nakoma sameemah tah kuma,na gaji da waccar wacce bata yin abinda taga dama,kokuma ta dunga barin abu idan anyi mata.
A wajen saka kaya dama wani wando na samu jean irin mai ɗamewar nan,sai wata me ɗan tsayi,itah ɗinma saboda rashin mutunci ban barta hakaba saida na ɗaureta ta koma dadai inda wandon zai fara,facing cap na ɗauko irin rigar na nasaka sannan na sneaker suma masu adon pink.
A taƙaice dai na fito kaman wata mawaƙiyah a ƙasar turai dama kuma ga farina mai harkene sosai.
Fitowa nayi falon dadai su saleema suna karya wa ita da sameer a table,farouq ma yana gefensu yana cin taliyar yara.
Ɗago min hannu yayi tareda cewa,
“Hi anty”
“Ya kke ka tashi lafiyah”
Dariyah yamin irin ta yara yana ɗaga kai,kallon iyayennasa nayi tareda ɗaure fuska kaman banice nayi wa yaron murmushi ba.
“Ku kuma na tafi juggling na exercise kwana biyu ina zaune har na fara tara cholestrol.
Sameer ne dayakai shayi bakinsa yayi saurin zubarwa har yana ƙwaruwa kafin yace,
“Me……menaji kince,excercise?”
“Ashe kaji mai nace ɗin kake neman na maimaita”
“Toh bazakije da wannan kayan ba kam”
“Saikuma kayi ai wai karuwa taga mai wa’azi”
Juyawa nayi na fita hankalina kwance,dan tundaga cikin falon na fara juggling ɗin ban fitaba.
Hanyar dazai kaini jejin cikin wajen na nufah,dan daman dan yaganine nace masa cikin wajen zan shiga,amma dayasan yanda banason cikin mutane daya sau ransa a inuwa.
Bani na dawoba sai can wajen tara da rabi,dayake tun bakwai na fita.
Wanka nayi tukunna na fito falon.
Wayata ca tayi ringing ina ɗauka naga baƙuwar lamba,saidai nasaka a kunnena naji ashe wanda aka bawa saƙon kawomin karnuka nane yazo yana bakin barinki sojojin an hanashi shigowa.
Fita nayi zuwa bakin wajen,dayake akwai tazara na jima ina tafiyah kafin na iso bakin wajen,su bingo suna kallona suka fara ƙoƙarin ƙwacewa a hannunsa.
Alama nayi masa da ya sakesu,dan daga gani a tsorace yake dasu sosai.
Aikuwa kaman jira suke suka rufo da gudu kaman sunga nama,tsugunnawa nayi na taresu,sai kaɗamin jela sukeyi.
Maganar wani soja ce tah ɗago dani wanda yakeyi kaman mai koyon hausa.
“Hajiyah zakina biyamu kuɗin ƙarba saƙo fah”
”kudin me kuma ana zaune kalau,ba abinda zan baku idan kunga kuma zaku iyah toh ku biyoni gidanan ku karba”
Har zai sake magana wani a cikinsu yah raɗa masa abu a kunne,yana jin hakan yah yi shiru yana juyah fuska.
A hanyane muna tahowa na kulada yanda raze taƙi sauri shikuma bingo yaƙiyin gaba ya barta kaman yanda suke wani lokacin,tsayawa nayi ina ƙaremusu kallo,sai a sannan na kula da yanda cikinta yayi faɗi yai ƙasa,kallon bingo nayi mai kama da harara,saurin juyawa yayi yana shinshina bushasshiyar ciyawar da take wajen,shafa kanta nayi kawai kafin na ce,
“Allah ya sauƙeki lafiyah”
Da haka muna tafiyah har muka iso kofar gidannamu,wannan wanda yayi mana tambayoyine lokacin farkon zuwana gidannan,dan na kula a duk cikin sojojin da suke gadi yah fi kowa iyayi da taƙaama.
Kabani wajen na wuce,kafin na maimaita sau biyu,idan kuma ba haka ba wallahi zan iyah shiga na fita aikin soja sai yah gagareka a rayuwarka.
“Ina zakije a da wannan dabbobin,ko karnukan sojoji baza’a basu damar wucewa ta nan ba,bare kuma wannan”
Tahowa nayi zan wuce sai ya tare kofar dan yaga mai zanyi,tafiyah nake zuwa wajen get din,nima ban fasaba,har saida nazo gaf dashi amma yana tsaye bai ko motsa ba.
“Nayi maka last warning ka bani waje na wuce tun kafin raina ya baci”
“Bazan ……..”
Tun kafin ya karisa maganar nayi masa wani naushi a hanci,taga taga yayi yai baya zai fadi,amma duk da kokarinsa saida yah daku da kasa,ta gefensa na tsallaka na wuce koh kallonsa banyiba,injinsa yana rike da hancin yana face majinar dole.
Direct cikin falon na shiga suna biye dani har dakina,saleemah tana zaune a falo sai ganinmu tayi mun shiga,tashi tayi tana kallona har na wuce dakina.
Gyalen dayake wuyana na cire kafin na jawosu muka fito zuwa kicin,robobi guda biyu na ɗauka a wajen set ɗin robobi,ja da kuma koriyah.
Abinci na diba na cika kowacce roba kafin na fita,suna biye dani kaman jela har garden din cikin gidan.
Ajiyewa nayi tareda komawa debo ruwa,a hanyar komawar ne mukayi karo da sameer wanda dawowar sa kenan da key din mota a hannunsa,
“Meyasa kikawo karnukanki gidannan batareda izinina ba,bayan kisan koh sanda muka je gida ma ba sonsu nakeba,kina mace mai zakiyi da karnuka hakan ma a kina mayar aure,abimda kike yakamata ke a ganinki”
“Kai wanda kakeyi na ya kamata ne,karnuka kuma nawane ni naga damar zama dasu shiyasa na taho dasu,kuma babu mai fitar dasu a gidannan,dan zamana sukeyi,idan zasu var gidannan saidai mu tafi tare”
Kedai kika sani,amma koda wasa karna kuskura naji akan wasu wata maganar ta fito,idan kuwa ba hakaba zasu bar gidannan koh kinaso ko ba kyaso”
Kafi kowa sanin halina akan hakan,amma idan aka daboni bana shiru saidai koh maima yah faru”
Daga haka yah juya yabar wajen zuwa cikin gida,saida na tsaya na tabbatar suna cin abinci kafin na shige cikin gidan.
Hayaniyah na ji a falon inda na tsinkayo muyar saleema tana faɗin bazata zauna da karnuka a gida d’aya ba,harara ta bini dashi dana shigo da alama bataso zaman karnukan ba,nikuwa babu yanda zatayi dani nan gani nan bari ɗumamen mayyah.
Satin su bingo ɗayah a gidan har sun washe da gajiyar mota,babu inda basa shiga a cikin gidan,ɗakina kuwa saidai idan gari bai wayeba,duk da reza bata fiye zuwa wajena ba saidai idan na je inda suke,kasancewar cikine da itah.
Sojan dana bigewa hanci kuwa,wanda naji sunansa wai samuel,kullum muka haɗu sai yah harareni da alamun zamu hadu,ni har dariyah ma yake bani.
Fita exercise yanzu da bingo nake zuwa,tun sameer yana masifah,har kusan marina yayi amma ban fasaba,kwata kwata banajin daɗin zaamn gidan,bayyi kama da inda zan zauna ba a yanayina,dan ma nakan je cikin maakrantar koyar da ƙananan sojoji da akeyi wani lokacin ina kallonsu,hakan yakan dan debemin kewa,sannan kuma mukan fita yin training nida bingo,dan ɗan barshi danayi a gida har yayi laushi wajen gudu.
Tun da safe naji motsi a ɗakina amma bana su bingo bane ,ƙin juyowa nayi saboda nasan waye a wajen,
“Nasan ba bacci kike ba,nazo na fada miki cewa ki shiryah zan kaiku gidan su saleema ku yini,saboda tunda kikazo basu gankiba,yakamata kije su ganki”
“Bazan jeba mai zasu min idan sun ganni din”
“Kinba ba gardamarki nazo jiba,magana ce na fadamiki kishiryah nan da karfe goma zan kaiku,saura kuma naji wata maganar ta fito kuma”
Lokacin dana jiyo wayam naga wajen babu kowa da alamar har yah fita bayam yayi maganarsa ta karshe.
Tsuka nayi na juya na cigaba da baccina saboda safiyah bata wayeba sosai,dan dai yah ci sa’a bana rude kofa ne shiyasa yake shigowa yanda yaga dama.
Jeans da t-shirt nasaka sai kuma kimono dana ɗaura akai baƙi da mayafinsa.
Lokacin dana fito saleema tana gaba da zuhrah a akan cinyarta faruoq kuma yana gidan baya,sameer ne daya taho daga bayana yake magana.
“Ke wannan wane irin kayane,koh gidan kawarki bazaki je dasuba bare kuma wanda suke kaman a matsayin surukanki,dan su tamkar iyayena ne a garinnan”.
“Kai suke matsayin iyayenka amma ba niba,ni bani da wasu surukai kuma ban shiryah yin wasuba,idan kuwa dole saina canja kayannan,toh wallahi bazanje na saidai na zauna,na gaji da wannan juyin,saikace zanje ganin Annabi.”
Jijjiga kai yayi alamun na isheshi,hakan nakeso,wayace da aka daura masa ni baice ba zai iya ba,buɗe gidan bayan nayi inda farouq yake na shiga.
Yaron ne ya ɗago ya kallaeni fuskarsa dauke da murmushi yaca,
“Morning aunty”
Tun kafin nace wani abu,saleema tace,
“Idan kasake gaisheta sai na cire ma harshe,mai shegen surutu kawai,wanda yake gaisuwa ake gaisarwa,ba wanda bai san darajarta ba”
Sameer ne ya katseta daga maganar da takeyi,
“Ke saleemah bana son irin wannna halin,bai kamata ki dunga nunawa yaro hakaba,karna sake ji”
Maganar su suke tayi har muka zo gidan banyi saka musu bakiba.
Shiga mukayi cikin gidan,babbane sosai dan yah fi wanda muke ciki girma,dan jikin bangon gidanma abin kallone ga wanda bai taba ganin irinsa ba
Zama mukayi a kujerun gidan dukkanmu,saidai jin alamar sakkowa mutum daga daga samane naga sameer ya sauka daga kan kujerar a yah zauna a kasa,kallona yake da alamar nima nayi,a raina nace kana ruwa kenan,idan ni zan yi yanda kace.
Kara bude kimonon dayake jikina nayi tareda sake gyara zamana a kan kujerar yanda jeans din jikina zai dan fito waje.
Cize baki sameer yayi yana kallona cike da daya sanin tahowa dani,hmm wayace yah taho dani.
Dattijuwar matarce ta zauna a akan kujera fuskarta cike da fara’a,.
Muna hada ido da ita naji matar ta kwantamin arai duk da bansan mai yasaba,jinai bakina yah bude ina gaisheta bayan banyi niyyar hakanba.
Nikaina nayi mamakin hakan bare kuma mutanen da muka taho da su.
Yar magana kadan muka yi da ita sameer yah tafi,da niyyar zai zo daga baya yah daukemu,nidan shiru nayi in kallonsu,duk da banajin gidan ya isheni kaman yanda nakeyi idan naje wani gidan,abin yabani mamaki sosai,dan matar har ɗakinta ta jani,akan nayi sallah.
Kallonta nakeyi dan bansan mai zance ba,itama kallon nawa takeyi bayan ta shimfidamin sallayah,ita kuwa saleema tunda taga mahaifiyarta ta kukani,tayi fishi da mamar tata ta fi dakinta,da ubanta yadawo kuwa wajensa ta nufah.
Tun daga nan na kula ubantane ya sakaltata ba mahaifiyarta ba,dan daga idon mahaifiyatata ina ganin rashin jin dadinta game da halin y’ar tata.
“Uhm dama hajiyah ina period ne”
“Period kuma,amma bakiyi kama da mai period bah,danna karanci likitan matane,babu abimda bansaniba akan mata sai abinda baza’a rasaba. Saidai ban saniba koh bakya son yi ina nan ne”
Tana gama fadar hakan cikin murmushi ta fice daga dakin,bandakin cikin dakin na shiga jikina a sanyaye,dan babbban abinda duk duniyah bazan iyaba shine sallah,koda na nayi niyyar aikatawa nasan bazan iyaba.
Alwala nayi na fito zuwa inda sallayar take,kallonta nake kaman mai nazari kafin na dorah ƙafata akai.
Runtse ido nayi saboda jin wani abu kaman allaura ya huda kafata har zuwa cikin kaina,idona yana rufe nasake ɗaga ɗaya kafar nasake ɗorawa akan sallayar.