NOVELSWASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150

Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.

????Sadi-Sakhna________✍????????

(¯’•.¸,¤°’✿.。.:քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ.:。.✿’°¤,¸.•‘¯)

????•°• WASA FARIN GIRKI •°•???? {cigaban gidan gandu}

????17~18????

Cikin dauriyah dakuma san gwadawa nafara tada sallar,saidai bankai gayin ruku’u ba nayi saurin zama a wajen ina rike kaina,dan nasan yau kam bazanyu bacciba koda naso hakan,nasamu najima da fitinar boyayyun mutanen can.
Ina zaune a wajen mahaifiyar saleemah tah shigo dauke da wani kwano a hannunta,miƙomin tayi tareda cewa,
“Ƴata maza shanye wannan zai miki amfani kinji”
Girgiza mata kai nayi alamun banaso,mamaki hakan yabata
“Meyasa bakyaso,karki damu bamai cutarwane ba nice nake hadawa da kaina,sannan karkiyi tunanin zan cutar dake,dan wallahi har cikin rai na nakejinki tun lokacin da na hada ido dake”
“Nasan bazaki cutar dani ba,sannan nasan ba abun cutarwa bane,hasalima nasan menene kawai dai bana bukatar sa rayuwata ne,shiyasa”
“Kamanyah kenan,kina mace amma bakya gyara kuma”
“Ina gyara mana irinna wanka da wanki,saidai irin wannan gyaran dakike nufi nasan bazanyi shi a rsyuwar data ragemin sauraba,saboda wanda akeyi dan shi wato miji bana bukatarsa a rayuwata sam”
Zata sake wata maganar ne nayi saurin katseta ta hanyar cewa,
“Babu abinda yake hadamu dashi shiyasa”
Saurin daure fuska tayi lokaci daya kafin tace,
“Me saleemah tah aikata da har hakan ta faru”
,ƙoƙarin tashi take na dakatar da itah ta hanyar cewa,
“Babu hannun ƴar ki akan hankan,wanna zabina ne bana kowaba,kuma kiyi hakuri bazan iyah fadamiki daliliba,kawai ki dauka haka nake,sannan ki gargadi yar ki ta rage shiga harka ta idan tana son lafiyar ta a jikinta”
Daga haka na fito na bar dakin na zauna falo,dan hakan shine mafi saukina,narasa miyasa na yarda da matar har nake fadamata irin wannan sirrin,inaga idan muka dade zan iyah fadamata komai bansaniba,daga bay nazo ina nadamar hakan.
Ina nan zaune har sameer yadawo daga aiki yazo ɗakarmu,sallama nayi mata saidai yanzu babu murmushi akan fuskar matar,sai kallon tausayi da take bina dashi,shareta nayi tareda cewa ke ta shafa kuma,bazan sake dawowa gidannan ba gaskiya,duk da zuciyah ta tana son dawowa gidan koda kuwa a gobene.
Kwanaki sunja da tafiyah ta garin porthacourt ko kuma nace da zamaan a can,har surayyah ta haihu mace sun saka mata sunana,nidai da sun nemk shawarata da basu saka mata suna na ba,saboda ina tsoron kar wani abun yasameta ,sannan wane abin kirkin na ajiye da har na cancanci hakan, bayan suna da mukayi waya da burgu yake cewa yaji labarin zainab ma ta kusa haihuwa,toh kawai nace dan banga ta inda hakan yah shafeniba,ni har na manta dasu ma saida yah fadi hakan tukunna.

????sameer a madubin gani????

A hanyar dawowa ta daga wani wajene na tsaya nayi nama ɗauri guda biyu,duk da nasan cewar akwai a gida amma ihsani yana da dadi.
Lokacin dana shigo har zan wuce dakin saleema sai kuma naga danaje dakinta na sake dawowa na sameema wanda yake farko gwara na mikawa sameema inyaso sai na kaimata nata,gashi na gaji daga wajen aikin da muka tafi,dan kwannan kullum cikin harim yah ta’adda da yan boko haram muke.
Ban kwarkwasa kofar ba shige wa kawai nayi danna san a bude yake dama.
Duhune dakin hakan yasa na kunna wutar dakin tun daga bakin kofah,saurin runtse idona nayi saboda ganin irin kayan dayake jikinta.
Daga ita sai pant da breezier a jijinta baƙaƙe,duk da cewa ana zafi amma ai zata iyah kunna AC idan tana bukata.
Ido daya ta bude kaman wata munafuka kafin ta mayar dashi ta rufe tareda juya bayanta.
Hakan da tayine yasake dukan kirjina kaman ana sokamim wani abu,dan yarinyar babu karyah akwai zubin halitta mashaallah,dakyar na samu na tattaro wasu yan guntayen kalmomi nayi amfani dasu wajen cewa,
“Wannan wace irin kwanciya kikayi sameemah,sannan wannan kayan kuma fah”
“Ina ruwanka da kayana,kwanciya kuma wacce naga dama zanyi,tunda dakinane,kona kiraka dakinne bare kayimin kutse cikin rayuwata”
Duk maganar da takeyi ta dayah bangaren takeyi,dan tajuyah bayanta can,murmushi nayi dan dama nasan hakan zata faru,domin kwata kwata batada burki a bakinta wajen yin maganar da ranta yakeso,kaman wata GOYON GWAURO,batasan tauna magana ba kwata kwata.
Ficewa nayi daga dakin tareda kashe mata wutar bayan na ajiye mata hakkinta.
Dakin saleema na nufah ,saidai ina zuwa na jishi a rude kirib,nasan ba bacci tayi ba duk da kwankwasawar danayi amma bata budeba,kome nayi mata itakuma oho,….kai mata! Na fada a raina.
Da safe da wuri na shiga dakin saleema,a zaune na sameta a tsakiyar gado,zuhra kuma ta kama bakin gadon tana ta zuwa tana dawowa irin na yara masu koyon tafiyah.
Duk sallamar danayi mata bata amsaba,haka maganar danyi mata,
“Ina miki magana kinyimin shiru wai me yafarune haka,nace miki kishiryah zamuje bikin samun matsayi na abokina a katsina koh”
“Bazan jeba,ka dauketa ku tafi ,kodan kana tsoronta,saika nunamin fada kukeyi a haka itama,amma daga dare yayi saika shige dakinta kuyi ta soyayyarku,wato kun maidani shashasha,toh allah ya toni asirinku,da idona naga shigarka dakinta kuna magana,dan haka ka dauketa ku tafi amma ba niba kam”
“Mai kike nufi,wai daman dan kina ganine nake kin shiga dakin sameemah?,toh tun wuri kisanja tunani,babu abinda zaki hana a alakata da itah haka rabuwarmu,batun abinda yakaini dakinta kuma bakya bukatar sani tunda kin baiwa kanki amsa,batun zuwa da ita kuma zanje da itah dunta kin ce hakan”
Fita nayi daga dakinnata daga haka,dan gsskiyah ta fara bani haushi,mutum bashida aiki said kishi kuma akan abinda ba hakaba.
Dakin sameemah na nufah lokacin tah fito a wanka,fuskata babu alamar wasa bare tayimin taurin kannata daya zame mata jiki.
Ina Mamakin yanda duk daure fuskata amma koda wasa tayimin kallon ta ga kwarjinina batayi,abinda koh maza ma sai na maji tukunna yake kawomin wargi.
“Ina so ki shiryah bamu je wani waje yan zunnan”
“Wai nikam mai ………”
“Sameemah banason jin dogon surutunki a halin yamzu,kedai kawai ki shiryah mu tafi,ba dadewa zamuyi ba”
Na boye matane saboda nasan idan ta san inda zamuje koh tsafi nake da baƙar zaba bazatajeba.
Da haka allah yabani sa’a ta shiryah dim.
Sauke ajiyar zuciya nayi ganin ta fito da wani material a jinkinta purple,yayi mata kyau kuwa sosai,baƙin gyale ta yafa irinna adon kayan.
Mota muka shiga babu wanda yake cewa wani abu har muka dau hanyar barin gari.
Kallonta nayi tah gefen ido dan naji mai zatace,amma bata ce komaiba saima danna waya da takeyi lokaci zuwa lokaci takan daga ido ta kalli titi.
Tabb wannan wace irin mutum ce haka,na faɗa a raina.

????sameemah a madubin gani????

Ina kallonsa yana min kallon gefen ido lokacin da yah kama hanyar barin cikin gari,nasan dan yaga mai zancene koh yah fuskata zata nuna.
Bai san duk maganar da suke shida saleemah ina jinsu ba,dan tundaga dakina ina jin duk abinda suke fada,saidai idan ban ga damar jin abinda za’a ce ba,ta wannan ma nasan nisan jin maganata yah fi na sauran mutane duk da bansan su ya suke jiba.
Lokacin dana ji mai yaca nayi niyyar idan yazo nace bazanjeba,amma kuma ta wani bangarena na zuciyata yace na bishi mutafi dannaga mai ita saleemah zatayi.
Har muka isa garin bayan azahar babu wanda yayi magana nidashi,a bakin wani katafaren gida yah tsaya,wanda tundaga bakin kofar gidan mutum yasan nairah tana kuka a ciki.
Harabar gidan an kawatashi lokacin da muka shiga,da alamun a wajen za’ayi walimar da mukazo dominta,lallai mutane ma,yanzu haka kawai na bata lokacina tundaga wani gari nazo waje dan walima,kawai dan ace nazo?.
D’aki guda aka kaini domin na huta na kuma yi sallah na ci abinci,saidai iyah cin abincin nayi da kuma hutawar.
A wajen taronma bamu wani dade ba muka juyo da niyyar komowa gida,saboda tafiyar hanya,babu yanda abokinnasa bayyi dashi mu kwana ba amma yace yanada aikin da zayyi washagari.
Lokacin da muka dawo gidan yayi tsitt kowa yayi bacci,muna zuwa yah shige dainsa koh magana bayyiminba,nima na wuce nawa dakin,dan daga ganin yanayinsa ba karamin gajiyah yayi ba,saidai dauriyah kawai.
Sanda na shiga daki ban yi niyyar kwanciya ba,dan ko alamun wata gajiyah banjiba saboda nasan jikinnawa yasha banban dana sauran bil’adama.
Har nayi shirin zuwa dubo su bingo amma kuma dana leka window sai naga dare yayi sosai.
Dole na ha kura badan nasoba,saboda tunda muka shigo nakejin kaman wani abu yasamesu,da kyar na daure na kwanta akan zuwa gobe naga yamda suka yini.
Da safe kuwa tun kafin nayi komai na fita wajen su,da kayan baccima a jikina gyale kawai na yafa.
Ina zuwa wajen naga reza a kwance,yayinda shikuma bingo yake kwance a gabanta yah tsura mata ido.
Karisawa nayi inda suke,mai zan gani……..! A kwance take tana nishi,duk jikinta zanen bulala ne raɗa raɗa,sai jini yakeyi.
Tabdijan,lallai an tabo rina a kaba,tambayar bingo nayi akan wanene yayi mata haka?.
Jan rigata yakeyi yana tafiya har zuwa inda Samuel yake zaune yana jiran kofah,haushi ya fara a gabansa ,shikuma dayaga haka sai dauki dutsi ya zefeshi dashi.
Duk abinda suke na ina kallonsu daga nesa,dana cije fatar bakina saida tah fashe dan bakin ciki,babi abinda ake fada a cikin kaina sai irin kalar hukuncin dazan yiwa Samuel ko zan huce haushin danake ji.
Bingone yadawo inda nake said kuma yayi cikin gidan yana min alamar na biyoshi.
Ina cikin hakane Yaseer yazo wucewa,wani sojane sabon zuwa wanda nake haduwa dashi a wajen training can Bori camp Idan Naje kallonsa. Bayan mun gaisane na tambayeshi tareda cewa,
“Yaseer Akwai abinda zakayi ne?”
“Ahah aunty,Akwai matsala ne?”
“Eh toh zaka dan kulamin da wata karyane anyi mata duka kuma tana da ciki,akwai abinda zanyi kafin na dawo”
Muna magana har mukaje inda reza take,shima kansa saida ya tausaya mata,amma ina famasa wanda yayi yace zai aikata,dan suma mugunta yake musu sosai,a raina naji dadin wannan labarin,koba komai zan samu damar hukun tashi da dalili mai karfi.
Komawa nayi inda bingo yake,muna tafe har bakin dakin saleema,karkada mun jela yayi a bakin kofar dakin kafin yah juya yah fita.
Kama Baki nayi ina jijjiga kai,wato harda itah a wannan aikin kenan dan taga jiyah bana nan nabi sameer koh,sai yanzu na tabbatar babu abinda suka mata kawai zallan mugunta ce,zakuwa taga yanda ake mugunta akanta.
Komawa nayi inda yaseer yake na aikeshi ya siyomim magani,nikuma nasaka musu abinci suka,duk da yanda take ciki amma hakan bai hanata cin abinci dayawaba abinka da dabba.
Lokacin dana koma falon saleema ta fito,hankalinta kwance kaman babu abinda tah aikata,dan ko wanka daga gani batayiba daga ita said kayan bacci,cuna min baki tayi da muka hada ido,nikuwa Murmushin gefen baki nayimata,da tasanni sosai da zata gano mai Murmushin yake nufi,saidai kash bata masaniyah akan hakan.
Lokacin da ta koma dakintane naji alamar sallamar yaseer a waje,fita nayi na karbi sakona,maganin kam karba yayi yace zai bata,sannan zai dunga kulada ita,godiya nayi masa bayan na bashi maganin.
Komawa dakina nayi tukun kafin na fito na nufi dakin saleeman.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button