NOVELSWASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

Babu kowa a dakin sai karar ruwa a bandaki,hakan ya tabbatarmin da cewa tana wanka,zama nayi a hankali kwance na jirata har ta fito.
Lokacin data fito turus tayi a bakin kofar bandakin ganina a cikin dakinnata,abinda bata taba tsammata,shiru tayi kaman mai nazari kafim kuma ta matso zuwa ainihin cikin dakin.
Ta shi nay I daga bakin gadon tareda nufar inda take,duk da akwai tsoro cikin idonta amma hakan bai hanata tattaro jarumta ta yafawa kanta ba ta hanyar cewa,
“Me kike min a dakina kuma da wannan lokacin,akwai abinda kike bukata ne”
“Ba abinda nake bukata,kawai dai nazo yimiki tambaya ne,shin mai reza tayi miki kikayi mata wannan dukan lokacin da bananan jiyah”
“Au hhhhhh dama akan wannan dabbar ne kike wannan tambayar,ai said ki fadamin tun wuri,baki sakani tunanin wani abu ne ya kawoki ba”
“Duka na daketa kuma ko gaban waye zance na daketa,dama ina jin haushinta kuma tashigo har cikin falona,dan rashin mutunci,ko kuliya bazan yadda da zamanta cikin gidana ba bare kuma kare kazami,dan haka shiyasa na kamata nasa Samuel ya rike min itah na dakata,idan da abinda zaki iyah yi kiyi akan hakan”
“Oh haka kikace a ko gaban waye zakice ke kika daketa kuma ayi duk abinda za’ayi?,zakuwa kiga abinda mai itah zatayi yanzunnan,dan ko kasa da sama zata a hade a lokacinnan said nayi miki ninkin abinda kikayi mata,dama ina taraki da rainin dakike min,ko kina tunanin dan nazo garin da ubanki yake shikennan bazan iyah miki komaiba koh?”
Ina gama fadar hakan na bita da kyawawan maruka har gida biyu a ta kowanne kumatunta,fadawa kan gadonta tayi tanna ihu,hakan bai dameni ba sai ma komawa danayu nasaka key a kofar sannan na dauko bulalata dana ajiye a wajen.
Jijjiga ta nayi kafin na fincike towel din dayake jikinta na zuba mata itah gadon bayanta iyah karfina,murmushi nayi danaga ta shigeta sosai, ɗagawa na sake yi na zuba mata,a na ukunne naji bugun kofar tata da alamar sameer ne dannaji muryarsa……..

Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150

Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.

????Sadi-Sakhna________✍????????

(¯’•.¸,¤°’✿.。.:քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ.:。.✿’°¤,¸.•‘¯)

????•°• WASA FARIN GIRKI •°•???? {cigaban gidan gandu}

????19~20????

Duk da bugun kofar dayake yi kaman zai balle kofar hakan bai hanani cigaba da zambada mata ba,har saida naga bata motsi sosai,fatar jikinta kuwa duk ta yi ja sai zubar da jini takeyi abinka da Wanda hutu yah ratsashi sosai.
Shima bani na bude kofarba kallonsa kawai nayi a gabana ya fizge bulalar da take hannuna kafin yah wanka min mari.
KO kusa banji zafin marinba saima murmushi danayi masa ganin aika aikar danaso yi ta tabbata raina yayi fari tass kaman farin dutsi.
Karisawa inda take yayi da sauri yana dagata a hannunsa,wata harara ya aikamin kafin yah fice zuwa wajen da motarsa take.
Nikuwa ɗaga kafaɗata nayi ko a jikina,na rama abinda naga bazan iya bariba yah tafi a banza.

????sameer a madubin gani????

Lokacin dana dauki saleema a hannu na na nufi motata ko motsi bata yi,lokaci zuwa lokaci nake leka ta a bayan mota inda na ajiyeta, amma koh motsi batayiba har muka isa asibiti.
A hanya na kira hajiya fatima nake fadaamta,dan bazan fara kiran alhaji musa a lokacin ba,nasan abin bazai tafi da kyau ba.
Kusan tare muka isa da itah dayake dama ta fita anguwa tana kusa da asibitin.
Har nursing suka karbeta suka turata a keken asibitin bata tambayeni mai yah faruba,saida muka ga anshiga da itah an fara magance ciwukan jikinta sannan an saka mata ruwa tukunna muka zauna,kallona tayi cikin kwanciyar hankali kafin tace,
“Menene yah faru haka sameer?”
Bata labarin abinda yah faru kawai nayi mata,shima wanda nasani kadai,na manta key din drawer tah ta office,ina dawowa naji kukan saleemah a dakinta,dana buga kofar kuma najita a rufe,jijjiga wa na cigaba dayi,amma ganin bazata budeba ne yasa na tafi dakina na nemo spare key na bude dakin.
Nan nasamu sameemah a tsaye a bakin gadon tana ta dukanta kaman an aikota.
Numfasawa tayi bayan taji abinda yake faruwa,saidai abinda yafito daga bakin hajiyah fatima ne ya bani mamaki inda tace,
“Amma yakamata a bincika dan aji mai tayi mata,idam babu toh inaga ita ma tana da matsala yakamata a binciki lafiyarta,dan abinda takeyi bana mai lafiyah bane,dannaso gano hakan lokacin da muke magana da itah a dakina,sannan kaman tana cikin kadaici sosai”
Kallonta nake da alamar mamaki,anyah kuwa ana samun irin wannan matan,wata tayiwa ƴarki irin wannan dukan amma kina kokarin sanin ko tana da lafiyah,ba ta ma yattaki kike ba.
Muna cikin hakanne alhaji musa yah iso wajen cikin rawar jiki dan yaji ance tana asibiti.
Tambayar abinda yah fari yafarsyi cikin daga murya,hajiyah fatima ce ta kamo hannunsa tareda bashi labarin abinda yah faru cikin kwanciyar hankali,saidai bata kai ga gama fada masa ba ya tashi da sauri yana danna waya yana fadin.
“Ina baza’a yiyu ba,ni dama tundaga farko banso zaman wanna matar kusa da ƴataba,kece kika nace sai an bi ta mijinta ,toh gashi nan tana neman kashe mana yarinya a aikim banza,kuma billahillazi babu mai hanani hukuntata a cikin garinnan .
Kai kuma ka shiryah zan yimana booking jirgi in anjima duk zamu tafi mu uku harda itah muje ayi jinyarta dan nan ba abinda suka iyah,awa guda amma har yanzu bata koh farfaɗoba”
Yana gama faɗan hakan yah amsa kiran daya shigo cikin wayar,dsyake a handsfree take kana jin irin girmamawar da na ɗayah gefen yakeyiwa alhaji musan.
“Kai ba wata doguwar magana nakeson muyi ba,inaso ka tura sojoji suje gidan sameer su ɗauko wata mai laifi,kuma so nake ku kaita ɗakin horo dayake a bakin daki”
Daga can mutumin ya amsa da cewa an gama ranka yah dade.
Duk da cewar abinda sameemah tah aikata bai daceba,saidai hukuncin akamota har cikin gidana kuma ɗakin dayake nata na aurena sainaji abin bayyimin daɗiba,koba komai yakamata a barni naji abinda yake faruwa,ba kawai akama matata a saka cikim cell,kuma sannan a saka gardawa suyi tah dukanta.
Sannan wani abunma wai saina ajiye aikina na bisu wajen jinyarta a wata ƙasa daban.
Haka muka cigaba da zama amma shiru babu alamar zata farka,anan muka kwana har washagsri kafin na tafi gida zuwa dauko kayana wanda zamu tafi can kasar Germany inda za’ayi mata maganin.
Banda kudi baya yiwa wasu wahalar cirewa menene abin tafiyah wata kasar,ita wacce aka kai wajen horo na kasa (dungeon)ai saita fita shan wahala ba kadan ba.
Ina isowa da mota naga nashiga cikin gidan,fayau naga falon bakowa sannan kuma babu alamar motsin mutum,dan farouq yana wajen nanny sa ita kuma zuhra tana wajen hajiyah fatima.
Dakin sameemah na leka,ina tuna yanda nake ganinta idan na shigo dakin,duk da wsni lokacin bata kulani har na fita.
Dakina na nufah na hada kayana,har na zo shiga mota sai kuma na nufi hanyar garden dannaga wulgawar mutum,yaseer nasamu sabon sojan da bai dade da zuwaba,abinne yabani mamaki mai yake a wannan yankin shida yake zaune a cikin bori camp.
Turus mukayi dashi yana shirin fitowa,dauke kansa yayi yana kkkarin wucewa,hannunsa dauke da karyar sameemah wanda take ta numfashi dakyar,jikinta duk zanen bulala.
Tambayarsa nayi menene yasameta,kallonta yayi tana hannunsa kafin yace,
“Nima ban Sabina,kawai jiya naga anty sameemah tana dubata ganin irin abinda akayi mata,daga nan ta ce nasayo mata maganin dazai warkar ciwon sannan na sayo mata bulala dorina mai kai biyu. Jiya kuma da azahar tacemin idan naji lbarin an kamata to na kulu mata da karnukanta kafin ta fito”
Hanya nabashi ya wuce da itah dayan ma yana biye dashi har suk bar wajen.
Shiru nayi ina tunani har na isa inda cell din da samemah take,wato karenta ta,ramawa dukan da saleemah tayi masa,kuma tasan za’a daure ta amma tsyi hakan,wannan wace irin macece ne?.
Da kyar mai kulada wajen yabarni na shiga wajen dan nafishi matsayine da nasan bazan samu kallonta ba.
A zaune na sameta an daure hannun ta baya,rigarta ta wani wajen duk ta yage saboda duka,hakika na tausaya mata ganin akan ceton kare ta saka rayuwarta a haka.
Karisawa nayi har inda take na tsugunna,dago kai tayi tah kalleni kafin ta kawar da kanta.
“Yanzu abinda kikaga yafi kenan,kisaka rayuwarki a haka saboda karya?”
“Hakan jai shafeka na ni kadai ya shafa,sannan bannemi taimakonka akan hakan ba,naga zan iyah shiyasa na yi,kuma da kake zancen na saka rayuwata a haka dan kare,ta cancantane wani ko da kudi yasakani bazanyiba,saboda suma zasuyi min abinda yafi haka idan ina bukata.
Karka damu dani ka tafi jinyar matarka yafi ka tsaya kana bata lokacinka annan”
Rasa ma abinda zance nayi lokacin da ta gama maganarta,tashi kawai nayi na fita ina fadin allah yah kyauta a raina.
Lokacin dana je har an gama sakata a jirgi dan haka shiga mukayi kawai muka tafi,nidai da da yadda zanyi da bazan bisu ba,saidai ko mai zanyi nasan alhaji Musa bazai fahimtaba,illah ma yace da saka hannuna akan hakan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button