NOVELSWASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

Muna zaune a garden din wani soja yazo wajen,saida yah saramim alamar jinjina kafin yah faɗi abimda yake tafe dashi.
“Ran shugaba yah dade,major nazeer yana son ganinki a office dinsa dake can headquarter idan kina da lokacin hakan”
Jim ina Tunani kafin nace masa yaje ina zuwa,juyawa yayi yah tafi tunda yah isar da sakon dayake dauke dashi.
Kallon yaseer nayi wanda shima ni yake kallo,dan murmushi yayi kafin yace,
“Kin cancanci fiyeda jinjina a wajen sojojin gidannan anty,domin kin saka kanki a kasada a cikin dare guda kika ceto musu da iyalansu,abinda su kansu basuda kwarin gwiwar hakan saida kika nufar dasu tukunna”
Uhm kawai nace kafin na koma dakina domin shiryawa zuwa kiran.
Riga da wando nasaka amma rigar zuwa gwiwa sai gyalen dana yane kaina dashi.
Duk kayan baƙaƙene sai hakan yah fito da farin fatata a cikin kayan.
Lokacin dana isa office din da sauri sojojin dake tsaron kofar suka bani hanya na wuce,kafin ma nayi magana.
A zaune na sameshi akan kujerarsa,yana kallona yah tashi tsaye tareda nunamin kujera yana murmushi,ƙara murtuke fuska nayi saboda kar ya kawomin wargi ma idan yaga nayi murmushi.
“Barkanki da zuwa,gaskiyah naji dadin amsa gayyata ta da kikayi,ba komaine yasa na kiraki ba saidan inaso naji shin a ina kika koyi salon fada da kuma aiki irinna sojoji haka,bayan a yamda muka san tarihi baki taba zuwa wajen sojojiba”
“A inda ake koya mana na koya,ko iya nan ake koyon aikin sojoji kawai,a ganina banyi laifiba bare a tsaya ana tuhumata koh”
Shiru yayi dajin amsata cikin izzah,can kuma sai yace,
“Banyi niyyar tuhumar ki ba sameemah,kawai abinne yabani mamaki,sannan kuma abinda kikayi kowa yagani ,toh idan aka tambayeni mai kikeso nace,yanayin aikine yazo da hakan,idam ma bakyaso a sani zamu iya boye hakan”
Tashi nayi na tsaya tareda zefa masa takardun shedata ta brazil wanda na karba a matsayin Raudah Abdulsalam.
Kallona yake baki buɗe kafin shima yah tashi tsaye yana kallona,
” mai kuma takardun wannan jarumar yake a wajen ki,ina dai wacce tah lashe gasar harbi da kuma hacking a akayi a kasar Brazil”
“Mtsww to mai zayyyi a wajena idan ba nawa bane,haka kawai zata dauki takardu ta banine,idonka baiga hoton da kyau bane,kawai badda fuska nayi ɗan kaɗan, sannan karka tambayeni ya akayi naje ko taya naje,dan ba faɗamaka zanyi ba,wannan ma dan nasan zaka dameni ne da surutu”
Takarduna nayi na fice daga office dinnasa.
Yau anyi sati da harin da aka kawo barrack din,kowa yah ɗan fara mantawa,saidai ganin girmana a idon mutane kullum kara hau hawa yakeyi,dan yanzu har matan sojojin zuwa suke har gidana su gaisheni,duk da ba magana nake yi musu sosai ba amma hakan bai damesu ba,dan sun kula halina ne hakan.
Karnukan da reza ta mutu ta bari kuwa,wanda nayi musu suna Blacky da kuma Darky,sun tashi cikin girma na musamman,kasancewar ubansu dama ba breed karnukan kasarnan bane,
Training nake yi musu na musamman,tun suna shan wahala su kasa motsi har suka saba yazamana yah bi jikinsu.
A cikin Satinne major nazeer yah turo request daga office dinsa kan cewar na dunga bawa dalibansu train din harbin bindiga sannan na yi masu koyon na’ura ma,kin amincewa nayi daga farko,dan har saida turo kusan sau uku kafin na karba,shima sai da naga dama tukunna,ranar asabar na tura masa da sign din na yadda,sannan kuma ran monday zan fara zuwa.
Ran lahadi major nazeer yah aikomin da kayan mai horo,saidai daga gani dinkasu akayi dan kayan irinna matane,sannan kuma da karamin hijabi a ciki.
Tun karfe bakwai na tashi nayi break fast naci na koshi,dan yanzu nikadai ce a cikin gidan,sai nanny din farouq wanda na aika ta dawo,saboda tun lokacin daya zo gidan yaki komawa gidan hajiyah fatima gun mai aikinta,ganin hakanne yasa nace su dawo nan shida itah su zauna,tunda a kwai wani dakin a wajen.
A kitchen din nasmaeshi yana tsaye,har na wuceshi sai kuma nadawo na ce,
“Menene naganka a nan wajen da wannan lokacin,akwai abinda kake bukata ne?”
“Eh aunty,uncle have muje makaranta da wuri yau akwai abinda za’ayi,kuma naga lokaci ya kusa gashin anty nanny bata tashiba”
Kama hannunsa nayi muka shiga dakina nayi masa wanka da brush kafin na aikeshi yah dakko kayan uniform din,da sauri yah tafi yana murna.
Kayan na saka masa kafin na zuba masa abinci yaci,na saka masa wani a cikin basket dinsa.
Tunda nafara sakawa yake tah murmushi ,lokacin dana bashi ma har yah tafi saida ya dawo da gudu yah rungumeni kafin yah juya da gudu yah fita wajen drivernsa.
Yau daya a rayuwata naji wani shauki wanda ban taba jiba yah soki cikin kirjina,saurin rike wajen nayi ina dan sunkuyawa,tambayar kaina nayi mai hakan yake nufi?………

Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150

Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.

????Sadi-Sakhna________✍????????

(¯’•.¸,¤°’✿.。.:քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ.:。.✿’°¤,¸.•‘¯)

????•°• WASA FARIN GIRKI •°•???? {cigaban gidan gandu}

????23~24????

Fitar da tunanin nayi a raina na wuce dakina damin nima nayi nawa shirin.
Kayan sunyimin kyau sosai a raina naji dadi sosai,ganin nasake samun wani aikin a karo na biyu.
Lokacin dan isa wajen da masu training din suke duk ansaka su cikin sahu na layi.
Dama daga gani suna jiran isowata ne dan idon su duk akaina lokacin da major nazeer yah ke gabatar dani,shima ina kallon dan alamun girmamawa dayake min,wannan al’adar sojane nuna girma ga wanda yafika matsayi.
Babu Bata lokaci muka fara abinda yah taramu wanda muka aiwatar dashi a wani fili na koyon harbin,dukkansu kowa ka ganshi yayi laushi kaman an yimasa duka,saboda aiki dani ba sassauci,kallon mugunta nayi musu kafin nace kadan ma kuka gani indai nice mai koya muku abu.
Direct wajen masu koyon tracking da hacking na wuce bayan na gama da masu harbin,zasuje wani ma yah cigaba daga inda na tsaya .
Sai wajen la’asar sukam muka tashi,domin aikin dana basu ba karami bane,kuma da gangan nayi musu hakan dan su san ba wasa ne yah kawosu ba.
Ina is a gida na hada gumi shirkiff ,wanka nayi nasaka kananan kaya kafin dare kuma yayi nafara nasu blacky dan zuwa yanzu suma sunyiwa sauran karnukan barrack zaryah tun daga yanzu suna kanana,dan jikinsu haryah fara murdewa irin na karnukan manyan yan daba.
Idan muka gama training kuma na barsu a jije su kwana suna maimaici,wanda bayyi ba kuma yakarbi hukunci mai tsanani,sannan bana barsu su saba da kowane mutum,daga ni sai yaseer,sannan abinci su koyaushe nama ne saidai a sarrafashi tah hanya daban yanda zai kara karfafa jikinsu.
Fitowa nayi daga dakin na wuce kitchen na hado custard,dan bana bukatar abinci a lokacin,farouq ne yah ganni kasan cewar babu islamiya yau yana gida,mikamin kofi yayi yana min kallon dolly irinna yara idan suna son abu,karba nayi na zuba masa dam ba lallai na shanye shiba.
Komawa falon mukayi muna kallo,wanda ni hankalina ma baya kai saboda duk cartoon ne,sai anyi abune yake taboni ya nuna min,ko banganeba to nake cemasa kawai.
Muna nan zaune har aka kira magriba,kallonsa nayi nace,
“Farouq tashi ka tafi masallaci an kira sallah maza”
Cuna baki yayi bayason zuwa,amma yana kallon fuskata yah tashi da gudu yah fita zuwa masallacin.
Jijjiga kaina nayi kawai bayan na kashe kallon,dan idan ban kasheba yazo yah gani bazai je lessons din dare ba yau. Kuruciyah da daɗi.
Lokacin daya shigo gidan dakina ya shigo da gudu har yana tuntube,kallonsa nayi da takaici,badama baya son zama waje daya kullum cikin rigima yake.
“Yanzu farouq bazaka tafi a hankaliba kaman ana binka a baya?”
“Aunty yi hakuri,dama sauri nake karki tafi wajen su blacky kibarni tunda kince yau kam zanje koh?”
Shiru kawai nayi ina tunani,kusantuwa ta da yaron kullum kara yin gaba yake,ina tsoron kar hakan yajawo matsala idan iyayensa suka dawo.
Sai nayi niyyar yimasa fada sosai ko nesan tashi daga saikuma na kasa,saboda kama da yakemin da sameer haka ummah tah,sannan bayan wannan inajin yaron a cikin jikina sosai.
Dan sunkuyawa nayi na kama kafadunsa kafin nace,
“Suna cizo sosai sannan kaga dare yayi ka bari gobe sai muje da yamma idan ka dawo daga makaranta koh”
Daga kai yayi alamar yah amince,sai kuma yayi murmushi,gyara masa gadon nayi yah kwanta bayan na bashi chocolate din dare,duk dan kar yah biyoni,dan nanny dinnasa wani lokacin ba gidan take kwana ba tana wajen mazan sojoji,kuma wai ita suka bawa tarbiyyar yaronsu,dan sati guda kenan bata gidan.
Zuwa yayi yah fadamin akan yana tsoron kwana shikadai kullum,wanda nima na kula da hakan.
Tun daga lokacin na dawo da duk kayansa zuwa dakinnawa,shima dayaga hakan murna yayi tayi,ko yaushe sai yah shiga yah fita,wai yah zama dan dakina.
Tun daga lokacin idan na tashi nayi abin karyawa sai na tasheshi na shiryashi nima na shiryah,idan muka gama komai saina fito na kulle gidan shikuma na kaishi wajen mai kaishi makaranta.
Idan ya dawo kuma sai yaje inda nake bada horo mutaho gidan tare,idan nayi mana abinci muka ci,saina shiryashi cikin kayan islamiyyah bayan yayi sallah,duk da bana takurashi amma yah sani idan yah yi ba daidaiba ina horashi yanda yakamata,dan banason sakalci ko kiyuwa ko kuma raini ga wanda suka fishi.
Shi ma daya ga haka yana kokarin kiyayewa,koda ya manta yayi da sauri yake bada hakuri idan yah tuno mai zai biyo baya.
Yanzu nakan barshi yaje wajen su blacky shikadai bayan na tabbatar sun dan saba dashi bazasu cutar dashi ba,dan karnukan sun sanja kama zuwa wani abu mai hatsari ga duk wanda yah gansu,saboda zaman cikin jeji da kuma bada horo mai tsanani.
*
Zuwa yanzu nasamu wata guda uku kennan da karbar matsayin mai bada horo a cikin bori camp dake cikin porthacourt barrack.
Na sauya abubuwa da dama a cikin haron daliban,ciki harda kara tsawon lokacin yin train,sannan banda wasa ko shiririta,yanzu na zamo kusan duk taro da za’ayi a cikin wajen toh sai an turomin takardar gayyata,wani nakanje wani kuma nace bazanjeba,dan haka suke hakuri dani,bana nuna respect ga kowa,dan wannan dabi’ar ita kadai na rasa a cikin aikin sojan,wato respect ga na gaba dasu.
Watarana ne ina zaune major nazeer yah kirani,nayi mamaki daya nunamin wani office an kawatashi wai nawane,sun bani alhakin kulada horon sabin sojoji,sanann kuma ga kudi da,suka bani mai yawa,wanda kuma zasu cigaba da biyana wata wata,kallon office din nake har da motar da take bakin wajen mai paint din sojoji,kuma wai tawa ce.
Biki akayimin na hakan ,wasu manyan sojojin daga wasu jahar ma saida suka hallara,musamman dasuka ga irin aikin danayi da kuma sabon salon horo dana kawowa barrack din.
Gaskiya nayi mamakin abinda sukayimin ban zata zai kai har haka ba,sai ganina nayi na daukaka lokaci guda an bani matsayin mai bada horo da kuma saka hannu cikin tsaron wajen,zan iya gyara duk abinda naga dama a kuma lokacin danake so.
Yanzu daliban dana yaye a cikin wata hudu gwarazan da suke cikin su sune suke gudanar da wasu ayyukan,ni yanzu banida time sosai,koyaushe ina office.
Farouq ne yah shigo office din da sauri yana narai narai da ido,kallonsa nayi naga har hawaye yakeyi.
“Menene yah faru ka dawo da wuri haka”
“Ba …..ba cikina ne yake ciwo ba”
“Wani Abu kaci ko,bayan na hanaka”
“Ahah anty”
Ajiye aikinnayi na kira yaseer ya karisa dan yanzu shine mataimakina,kuma nina bukaci hakan,mahaifiyarsa takanas tazo tayimin godiya.
Daukarsa nayi dannaga harda sakalci yau yake ji daga gani.
Gida muke je na ajiyeshi a bakin gado,bandaki na shig na hada masa ruwan wanka,lokacin dana fito har yah cire kayan makarantar,koh magana banyimasa ba yah shige bandakin,dan zuwa yanzu babu abinda bai saniba na dokokina basai na fada da bakiba.
Fita nayi na hada masa abinci. Kallonsa nayi lokacin daya fito daga dakin sanye da gajeren wando irinna sojoji da kuma farar T-shirt.
Mika masa abincin nayi,yana karba yace,
“Nagode ummah”
Saurin kallonsa nayi jin sunan daya kirani dashi,daga haka bai sake cewa komaiba har muka gama cin abincin yah fita zuwa gidan major nazeer wasa,dan tanada son yara.
Har sannan kalmar mommy bata daina yawo a cikin kaina ba.
A satinne na kira meeting kan cewar bai dace ace an saka kaso na sojoji a bakin wani gida kawai dan tsaro ba,sannan kuma kamata yayi ace sojoji guda biyu a kowanne gida,shima kuma za’a dunga sanjawa wasu su tafi training wasu kuma suje wajen iyalansu.
Cikin saurin bukatata ta karbu dan hakan shine yah fi,a kofar gidanmu kam,duk sallamar su nayi nasaka iyah guda biyu da rana,idan dare kuma yah yi su blacky ne suke tsaron bakin kofar,ko kafi uwarka kokari baka isa ka wuceba sai sun baka dama,shima sai na yadda tukunna,ta hanyar ganin hotonka a camera kofar gidan,idan na yadda zan kunna green idan ban yadda ba sai na danna red,toh dole ka juya badan kanaso ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button