NOVELSWASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

Tun daga wannan lokacin farouq yakoma kirana da mommy,dan a cewarsa yanzu babu wanda yake kuladashi saini,nima banyi kokarin hanashiba dan yanzu yaron ya shiga raina sosai.
Washagari da safe aka bada sananrwar dawowar general musa daga jinyar yarsa daya tafi yi a kasar Germany,hmm abin ma ba tsari ko kadan,tun wata biyu da zuwansu ta warke amma tace baza ta dawoba sai anyi mata aikin fata an cire duk tabon zanen bulalar dayake jikinta,wannan ne ya daukesu har tsawon wata hudu acan.
Nikuwa naji labarin dawowar tasu amma babu abinda nayi a ciki,tashi nayi kamar kullum na shirya farouq zuwa makaranta,nima na fita nawa aikin,a hanya duk sojoji sai sara min sukeyi,dayake yawancin dalibaina ne dana yaye wata uku da suka wuce,sannan su san bana wasa sanann bana mugunta ko zaluntar wani,da haka na kankaro mutuncina a wajensu.
Yau ban tashi da wuri ba,dan farouq ma daya dawo daga makarantar safe anan na bashi abinci yaci yah kawanta,sai la’asar tukunna na sabashi a wuyana zuwa gidannamu.
Dan zuwa lokacin nasan su yah sameer sun dawo,kuma da gangan na ki dawowa da wuri duk da nasan tahowar wajen azahar zasuyi.

????sameer a madubin gani????

Tun jiya da akacemin zamu taho nakejin kamar nayi tsuntsuwa,babu yanda nayi haka na zauna a kasar badan komaiba sai dan kar na taho ace matata ce tayi mata illah amma na barta na tafi,haka badan nasoba mukayi tsawon wata hudu acan.
Kusan karfe daya dadai muka iso Nigeria,itah dama direct wucewa sukayi gidansu,nikuwa wani sojane ya dawo dani gida,tun karfe biyu nake tsaye a bakin kofar gidana amma bahu sameemah ba alamunta,ina taje oho bansaniba.
Har naje sallahr la’asar nadawo ina tsaye kenan na hango wata mace ta dosoni da kayan coach a jikinta,abinne yaban mamaki yau she aka samu mace mai bada horo kuma,ni kadai na tambayi kaina.
Ga kuma duk Wanda tayi karo dashi sai yah bata girma kaman wata general.
Saida tazo tab dani naga ashe sameemah ce,dan tsabar mamaki kasa cewa komai nayi,ga kuma farouq a wuyanta yana bacci.
Wuceni tayi ko magana bata minba ta bude gidan,danji komaiba dan dama ban yi tunanin sun gaisuwarba ko kuma maganar.
Bin ta nayi a baya bayan ta bude gidan,sai kuma naga ta nufi dakinta da farouq din a wuyanta,nima binsu nayi dannsan nawa dakin bazai shiga ba saboda kura.
Sanda nashiga dakin har farouq ya tashi ita kuma ban sameta ba tana bandaki,kallona yayi da mamaki sai kuma ya rungemeni da karfi yana dariyah.
Karar budewar kofar bandakice tasa shi sakina da sauri yana ja dab baya,sai kuma ya dan sunkuya tareda cewa,
“Barka da hanyah daddy ka dawo lafiyah?”
Dan Mamakin Sabin halin dana ganshi dashi ma kasa magana nayi,bai jira amsata ba yah juya wajen sameemah wanda take rike da hannun kofar bandakin.
“Kiyi hakuri mommy bazan kara haka ba”
“Apology accepted”
Tana fadan hakan ya tafi da gudu yah wuce bandakin ta hanyar data bashi a kusa da itah.
Wajen kaya ta bude a kusa da nata inda naga kayan farouq a ciki an gogesu.
Wasu riga da wando ta fitar marasa nauyi sai kuma tah fesa musu turare kadan ta ajiye akan gadon.
Fita tayi zuwa kitchen inda nima na bita a baya,amma ko kulani bata yi ba.
“Yanzu sameemah ko ba magana babu bare sannu da dawowa”
“To mai kakeso nace maka,tunda gaka kadawo ai na ganka ko tunda ba makahuwa bace ni”
Hmm kawai nace kafin na dawo falo na zauna ni kadai ina tunani amam narasa na menene.
Can Bayan wani lokaci farouq yah fito da sauri bayan yah saka kayan da ta fitar masa dazu,a hankali ya shigo falon kafin yah samu waje a kusa dani yah zauna sai murmushi yakeyi idan muka hada ido.
Nima Murmushin nay masa kafin nace,
“Yaushe yaron daddy yayi hankaline haka uhm?”
Bayyi magana ba sai murmushi kawai dayake yi,muryar sameemah ce daga cikin kitchen tana kiran farouq.
Da sauri yah tashi yana cewa ganinann mommy.
Plate ne a hannunsa na abinci yana zuwa yah ajiye min a gabana,sannan yah koma kitchen din da sauri yah kawomin ruwa a jug da kuma cokali.
Wannan karon tare suka fito shida ita tana rike da wani plate din a Han nun ta.
A jiyewa tayi a kasan carpet din da cokali biyu a ciki sannan kuma da kofin ruwa guda biyu.
Har yah zauna a daya gefen tace,
“Jeka canja tashar nan zuwa taka”
“Toh”
Remote ya dauka ya maya zuwa tashar yara mbc 3,daga wrestling din dana kunna.
Ɗaukar abincin nayi ina ci,saidai rabin hankalina yana kansu sameemah yanda suke cin abinci,da kuma yanda yake diban abinci a gabansa a hankali yana kaiwa bakinsa,yaushe ya,sauya daga yanda yake zuwa haka oho,sannan ina nannyn sa take shima oho.
Mai aiki na kira daga bangarensu dan su sharemin dakina ,ita kanta dana kirata saida tayi mamaki,daga gani sun dade basu shiga sashenba.
Har na saleemah ta gyara tsaf kafin tazo ta fita,zuwa lokacin ana magriba.
Kama hannun farouq nayi nace,
“Abban zo mu tafi masallaci tacan muje dauko mommynka”
Saurin zame hannunsa yayi yana kallon sameemah.
“Zaka iya tafiya amma iya yau kawai,hakan ma kuje da abbannaka ka fada masa yau ba karatu”
Muna fita na tambayeshi menene,
“Uhm uncle ne mai yimin lesson,amma sabone dan ummah tah kori wancan din tun ranar data ga yah kun na min waka muna ji,yanzu uncle yaseer ne yakemin,ummah take biyansa,tace idan ban jeba yah zaneni,sannan kuma tace idan an ce nayi abu banyiba ya fada mata”
Muna cikin tafiya a hanyar mu ta zuwa gidan su saleemah yana tamin tadin abinda yake faruwa ,jijjiga kai kawai nayi tareda Mamakin hali irinna sameemah,yamzu a yanda take zata iya bawa wani tarbiyya amma kuma idan ita ce bazatayi ba koh?.

Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150

Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.

????Sadi-Sakhna________✍????????

(¯’•.¸,¤°’✿.。.:քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ.:。.✿’°¤,¸.•‘¯)

????•°• WASA FARIN GIRKI •°•???? {cigaban gidan gandu}

????25~26????

Lokacin da muka shiga cikin gidan ma suna zaune a falo har da abokananta,sakin hannuna yayi yah tafi wajen hajiya fatima da gudu,dan ko ta kan saleema bai biba,ita ma bata wani kulaba sosai.
Gaishe da hajiyah fatima yayi kafin yah je wajen saleema ya gaisheta da kuma yimata yah hanya,har da abokannata,dukkansu tsayawa sukayi suna kallonsa da mamaki kaman yanda nayi a baya.
Wata ce daga cikin matan ta fito da chocolate ta bashi,bai mika hannu ba said jijjiga kai da yayi.
“Ummah ta hanani shan chocolate,da tana siyamin amma daya sakani ciwon ciki shikenan sai ta daina bani saboda da muka wsjen likita cewa yayi ta daina bani chocolate,kuma tace ko an bani kar na sha”
“Wacece ummah taka wacce bansan ta ba”
“Anty sameemah nake cemata amma yanzu nakoma cemata ummah”
Wani ashar saleema ta ruga tareda mikewa tsaye ta kamo farouq a hannunta,
“Dan ubanka ita ta haifamin kai tayi zafin nakudarka da zaka cemata wata ummah ina raye da raina,iyee wato ta lahantani ta turani neman magani kai kuma ta mallakeka ko saboda taga bazata haifi nata ba “
Hajiyah fatima ce tayi saurin fincike yaron a hannunta har yah fara kuka,sannan ta fara mata fada,saidai babu alamar fadan yana shiga kunnenta.
Share masa hawayen take tareda tambayar sa meya faru,cikin kuka yafara cewa,
“Ammee ba ita tace na dunga cemata ummah ba nine na fadamata,saboda lokacin da nanny take barni nikadai na kwana a daki da daddare sai da safe ta dawo itace ta maidani dakinta take kwana dani,kuma kullum take shiryani zuwa makaranta da wuri,idan na dawo ta bani abinci sannan ta kori mai yimin lesson saboda baya min karatu ta daukomim wani,idan banida lafiya ta kaini asibiti,har kudin makaranta ta da aka ce na kai ina gani da kudinta ta bayar na albashinta,dan a gabana tayi waya tace su biyata kudin zata yi wani abu dashi,da muka je makarantar tabiyamun sannan ta tari mai mashin ta dawo gida.
Koyaushe ita take kuladani tunda kuka tafi,da nanny ta dawoma korarta tayi da daddare,banyi bacci ba ina ji tana ce mata wai,ta sallameta bazata bari ta bata tarbiyyata ba ta tafi can wajen sojojin da take zuwa wajensu,kuma ammee….”
Yah isa haka farouq duk munji mai kace sannan nasan da gaske kakeyi,shin kanason cigaba da zama a wajen ta?”
“Eh ammee zan zauna a wajenta mommy kuma ta rike zuhrah”
“Toh shikenan a wajenta zaka cigaba da zama idam har abbanka ya yarda”
Jiyowa yayi yah kalleni na daga masa kai da sauri,har saleema zatayi magana hajiya fatima ta zefa mata wata harara,da sauri tayi shiru.
Da muka tashi dawowa harda hajiyah fatima muka dawo wanda alhaji musa yah tursasa mata akan sai taje tayiwa sameemah gargadi.
Bayan mun shigo hanyar gidan muna zuwa saitin gidannawa gurnanin wasu abubuwa suka doki dodon kunnenmu,kallon saleemah nayi wanda itama ni take kallo lokacin da wasu hallotu masu kaman zakuna suka bayyana a gaban mu.
Farouq ne dayake gidan baya yah bude yah fita da sauri lokacin da muka tsaya a gabansu a bakin kofar gidan.
Nima fita nayi da sauri domin taro shi kafin suyi masa illah,saidai ban karisa fito da kafata ba naga yah tsugunna a gabansu sukuma suna shinshina shi.
Ina karisawa kusa da su daya yah boyeshi a bayansa dayan kuma yana min gurnani na alamar karna kariso.
Dariyah farouq yah tuncire dashi kafin yace,
“Daddy barin naje gida na danna muku alamar bada damar shigowa”
Daga haka yah shige gidan da gudu,muna nan tsaye saida wata koriyar danja ta haska kofar gidan kafin kkwannensu yayi nasa wajen,jikinsu har wasu juyawa yake saboda tsabar murdewa.ga kuma rigar bullet da aka saka musu,tunda nake banda ba kallon karen farauta haka ba.
Karisawa mukayi cikin gidan babu wanda yace wani abu har muka isa falon.
Sameemah muka samu farouq ya dora kansa akan cinyarta sai surutu yakeyi itakuwa ko magana batayiba.
Daga kanta tayi ta gaisheda hajiyah fatima wacce muka shigo tareda ita,daga ni har saleema kuwa ko kallon inda muke batayiba.
Hajiyah fatima ce tafara magana cikim dattako kaman yanda ta saba.
“Da farko ina baku hakuri dukka sannan zamantare dole saida hakuri musammman kai sameer wanda suke karkashinka.
Duk da bansan mai yah hadaku ba a baya amma ke sameemah ga saleema nan ta dawo dakinta bayan lokaci da bata nan sai kuyi hakuri a cigaba daga inda aka tsaya.
Idan wani abune ku sanar da mijinku ba kudau hukunci a hannu ba”
Saleemah ce tayi saurin cewa,
“Kuma a ja mata kunne kar ta kara gigin aikata min wani abun dan hukuncin dazai biyo baya bazaiyi mata dadiba.sannan kuma ta bani hakuri akan abinda tayimin kafin zance yah wuce”
“Ke Wacce kika aikatawa kin bata hakurine har ta mutu?”
Hajiyah fahima ce tace,
“Wacece ta mutu kuma?”
“Ita tasani ai ki tambayeta kiji”
Kallon tane yakoma kan saleemah wanda cikin borin kunya tace,
“Danna yiwa karyah hukunci manene,da har zaki hadani da itah a daraja”
Shiru kowa yayi nan na zayyanewa hajiyah fatima abinda saleemah tayi da kuma,amma bansan karyar ta mutuba saida ta fada yanzu.
Ran hajiyah fatima in yayi dubu yah baci,bata san lokacin data zabgawa saleemah mari ba,
“Yanzu duk wahalar dakika saka mutane a she kece ummul aba isin faruwar komai,wai kishi haukane harda zaki kama dabab ba abinda tayimiki kiyi mata duka da tsofon ciki har ta mutu ita da wssu daga cikin yan cikinta,wannan wane irin zaluncin ne haka,nidai bansan halin wa kika daukoba dan duk dangina babu wanda yake da wannan halin”
Kuka saleema ta rushe kafin tayi hanyar dakinta tana cewa,
“Wallahi saina fadawa mommy maryam duk abinda akemin nasan ai zata bi bayana idan taji abinda kae min.”
Babu wanda yah kulata bare yasake bi takanta,itama hajiya fatima tashi tayi domin tafiyah,anan take fadawa sameemah ta,bata farouq halak malak idan tana da bukatar rikeshi,godiyah kawai tayi kafin tayi Murmushin da bakai yi nisa sosaiba.
Da safe da,wuri na tashi domin akwai meeting da major nazeer yah bukaci ayi.
Na shiga kitchen din da niyyar dan hada wsni abu naci naga sameemah ta,juya baya tana wsni abun,mantawa da abinda ya kawoni nayi na tsaya ina kallon bayan ta yanda yake murzawa da kuma juyi.
Lallai allah yayi halitta anan,shine abinda nafada,dan kunkuminta ma kadai abin kallone bare kuma duk jikinta,ganin kallon bazai kaini bane yasa na karisa tareda sakala hannuna a kunkuminta,saurin jiyowa tayi muka hada ido har numfashinmu yana haduwa dana juna.
Juyawa tayi ta cigaba da abinda take amma ta saka daya hannunta ta ture hannuna daga kan kunkuminta batareda tace komaiba,nima banyi kokarin maida hannunba sai cewa danayi.
“Ina kwana maman farouq,idan abin karyawa ake hadaamsa a danyi dani please ina bukata”
Bata cemin komai ba saidai daga yanyin kallon nasan maganar bata bata mata raiba ko kadan.
Daga haka na juyah na koma dakina domin na shiryah.
Lokacin dana fito shima farouq yah fito da jakarsa a bayansa shida sameemah,da alama ita ta shiryashi.
Abincin ta zuba masa nima ta zubamin kafin ta,ajiye masa wanda zai tafi dashi makaranta.
Wucewa tayi dakinta kaman mai saurin yin wani abu.
Nidai dana ga cikina ya dauka fita nayi zuwa wajen motata domin zuwa headquarter.
Kowa yah hallara ana zaune amma wasu har sannan basu zoba,mutsutsuka idona nayi domin ganin wacce ta shigo cikin hall din kuma ana fadin wai mai kulada tsaron duk camp din ce dakuma kulada harkar horo.
Bakina saki ina kallonta musamman yanda tasha kaya ga kuma hade fuska da tayi kaman wanda take fagen daga.
Nima dauke kaina nayi daga kanta ganin ko inda nake bata kallaba.
Shugabane ya shigo tareda masu tsaronsa aka fara meeting,shima daga gani kallom mamaki yake yiwa sameemah kaman yanda nayi mata.
Major nazeer ne ya tashi yafara zayyana irin gwagwarmayar da sameemah tayi a cikin barracks din da kuma irin nasarorin data kawo harma da daliban data yaye da kuma jajircewarta a wajen aiki.
Duk wannan bai basu mamaki ba sai da suka ji cewa nice Raudah abdulsalam wanda suke jin labarinta.
Da haka aka gama meeting din kowa yah koma bakin aikinsa,nima office dina na shige daga nan,dayake nawa a wani branch din ne daban ba ainihin cikin barrack ba saida nayi tafiya zuwa cikin gari tukunna.
Bani na dawo gidan ba sai wajen magriba hakam badan nagama aikinba sai dan kawai na hakura sai gobe na cigaba.
Tun daga shigowa nake jin kamshin abinci a kitchen,ko ba tantama nasan ba saleemah bace a ciki,aikuwa hasashena ya zama gaskiyah domin sameemah ce daga itah sai boxer na mata iyah gwiwa,sauran fararen cinyinnan duk a wake,wayyo matar nan zata kasheni ina ga.
Mtswww naji tsuka a bayana,ina juyawa naga saleema ta cika tayi fam,muna hada ido da ita ta juya ta bar wajen tana cewa,
“Aikin karuwamci kawai”
D’aki na shiga na canja kaya kafin na fito zuwa masallaci.
Lokacin dana dawo gidan tsitt dashi kaman ba mutane kowa yana dakinsa.
Leka dakin samemah nayi farouq yana zaune a tsakar daki yana assignment,ita kuma tana nade masa kayansa na makaranta.
Zama nayi a gaban gadon ina kallon yamda yakeyi,lallabashi nayi yah fita falo domin yah cigaba da yin assignment din.
Ta shi nayi na nufi inda sameemah take tsaye,hannuna na sakala a kunkuminta na jawota zuwa jikina,shiru mukayi daga ni har ita ba wanda yace komai,wani irin yanayi nafara jina a ciki sanadiyyar yanda dumin jikinta yake shiga cikin jikina.
Bakina na kai wajen kunnenta cikin muryar dani kaina bansan inada itah ba na fara yimata magana.
“Menene yah faru lokacin da bana nan,yah akayi kika hau matsayi kuma baki taba fadamin nabaki umarnin yin hakanba,amma kinsan ke mallakinace koh?,sannan ya akayi kika zama Raudah abdulsalam,please ki fadamin,duk da nasan kina da taurin kai amma bana son kiyimim gardama kinji”
Shiru nayi daga hakan ina hura iska cikin kunnenta a hankali yayinda hannuna kuma yake yawo a cikin ta da kuma kan kunkuminta.
“Baka bukatar sanin amsar hakan,idan ma kana bukatar sani toh kaje ka tambaya mana,amma bani zaka tsare domin samun amsarka ba.
Juyo da fuskarta nayi izuwa kan tata fuskar ina fesamata kallon da yake dauke da ma’anoni dayawa ,mun dade muna kallon juna kafin ta dauke idonta daga kaina,banso hakanba saboda hada ido kadai da mukayi ba karamin kawo wani shauki cikin zuciyata yayi ba.
Kara dago da fuskarta nayi nasake hade kallon da muka fara a baya,dan murmushi nayina dan gefen baki kafin nasake cewa,
“Please kanwata kidaina amsa magana a haka idan na tambayeki,banajin dadin hakan,idan ina yimiki wani abu wanda bakyaso ki fadamin,nayi alkawarin dai nawa inshaallah,amma kallonki kina abu cikin kadaici kaman bakya da kowa hakan yana damuna”
Ture hannuna tayi cikin zafin rai wanda bahaka takeba lokacin dana fara maganar,da alama na tabo mata wani tabo a cikin ranta wanda yake mata kaikayi.
Yin gaba tayi kadan yanda bana ganin fuskarta kafin tace,
“Sai a yanzu dana girma tukunna kadaicina yake damunka,lokacin danake tsaka da bukatar lokacinka ka tsallake ka barni a garin da babu wanda yake bukatar yaganni na kwana na tashi a raye baka ji zafin hakan ba sai yanzu da jikina yah fara daukan hankalinka tukunna ka tabbatar da cewar ni matarkace a yamzu ba kanwarka ba koh? ……..kaine sanadiyyar daka sa na kulle zuciyata sannan nadaina yarda da kowa a cikin duniyaranan,na yarda kunci yacigaba da lullubeni har lokacin suka sauramin na bar cikin duniyarku suzo”
Saurin jawota nasake yi jikina a karo na biyu wannan lokacin zuciyata tayi nauyi dajin kalmar da take fitowa daga cikin bakinta.
“Mai kike fada haka sameemah ,ki fayyacemin komai naji daga bakinki,duk abinda kika san zakiyi mim wanda zai dauke wannan kadaicin a rayuwarki na yarda kiyi,ko horo kike bukata kiyimin na barin ki lokacin da bakida yawo naji na dauka zan karba duk da bayin kaina bane hakan.”
Kallona take da alamar bata fahimceni ba,nima daga mata kai nayi alamar haka ne,
“Tun bayan rasuwar ummah da kwana uku komai yah sauya daga cikin rayuwata,ba abinda na tsana kona budi ido na gani kaman ke da kuma yan uwan ummah,abin yana damuna kuma nasan akwai abinda yake damuna,a duk lokacin da kika matso kusa dani ji nake kaman na shakeki har sai kin daina numfashi,domin duk wani laifi da akayimin sai na ji kece kikayi sanadiyyar yinsu.
Ana nan bayan kwanaki sai ya zamana garin ma yah fara fita a cikin raina,kullum da kyar nake kwana nake tashi har yah zamo nafara aman jini musamamn idan ina cikin gida,wata rana ne da muka fita daga garin nida abokina sai naji babu ciwon danakeji yah tafi kaman an zare shi. Hakan yasa na tatttara kayana nabi wani soja a anguwarmu saboda na samu abinda zan dogara da kaina,sannan na nemi magani na dawo domin kulada ke.
Lokacin dana samun gidan dazan zauna nayi murna sosai,hakan yasa na shiryah naje har gidan gandu domin daukoki,saboda ina tsoron abinds yah cutar dani kema zai iyah cutar dake,saidai mai zam tarar wai bakyanan kin shiga duniyya haka aka fadamin.
Nayi bakin ciki har kuka nayi,shin mai zam je duniya na fadawa umma akanki da wane ido kema zan kalleki idan mun hadu.
Ban sake haduwa dakeba sai lokacin dana ganki kin fito daga mota lokacin nayi aure naje da saleemah,tambayar danayi miki amsar farko danaji shine budurcin ki kika bayar aka baki itah.
Bayan tsawon lokaci dana dauka ina nemanki gari yah gari amma sai na karbi wannan amsar……..rudu fargaba da tashin hankali gameda bakin ciki su suka tattaru a cikin zuciyata lokaci guda.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button