NOVELSWASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150

Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.

????Sadi-Sakhna________✍????????

(¯’•.¸,¤°’✿.。.:քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ.:。.✿’°¤,¸.•‘¯)

????•°• WASA FARIN GIRKI •°•???? {cigaban gidan gandu}

????27~28????

Hakanne yasa na cika da bakinciki har na fara miki fada,banida niyyar sakaki cikin kadaici sameemah duk abinda yah faru yah fi karfina ne sannan ina baki hakuri akan rashin fahimatar dake tun daga farko”
Duk da bana kallonta amma nasan maganganuna suna shiga cikin kunnenta,samun waje ta samu ta zauna a bakin gado,yayinda nima na bita na zauna a gefen ta tareda jawota zuwa cikin jikina sanann na cigaba da maganar danake yi.
“Bazan tursasaki ki yarda da abinda nake fadaba,saidai ko wata rana zaki iyah bincike akan hakan,ki yafemin da barki cikin wannan halin,bazan gazaba waj en baki hakuri a koyaus Koyaushe ,idan bazaki damuba inaso naji mai yah faru dake har kikabar gida sannan a ina kika tsinci kanki”

????Sameemah a madubin gani????

Shiru mukayi daga ni harshi,ina jin yadda zafin jikinmu yana gauraya zuwa guda d’aya,
Wani irin yanayi nakeji yana shiga cikin jikina wanda na ji a duk lokacin da farouq ya matso kusa dani,duk da banason yanayin saboda yanda yake saka zuciyata yin rauni a lokaci da ya,amma kuma bazanyi karyaba yana sakawa najini kaman ina raye nima kaman sauran mutane,duk da cewa zuciyata bugawa take saboda ina tsoron kar na cutar dasu acikin kowanne irin lokaci.
Musamman danaji dalilin tafiyar yah sameer daga gida sai na tsinici kaina da son kai saboda kullum tawa matsalar nake gani ba matsalar wasu ba,hakan yasa nake kara ganin laifin mutane fiyeda abinda sukayimin.
Dago da fuskata nayi ina kallon fuskarsa wanda yasake matse jikina acikin nasa kaman zai maidani cikin nasa.
Haka kawai bansan mai nene yasami shiga cikin kaina ba na tsinci kaina da bashi labarin yanda nayi kokarin tafiyah birni aiki da yanda yan fashi suka taremu na cececi sauran yaran ta hanyar mika kaina garesu har zuwa yanda nayi rayuwata a kasar palastine da kuma kasar Brazil. Abu daya na boyemasa shine yanayi halittata da kuma dafin dayake kwance a cikin jikina harda kuma shaidanun danake magana dasu.
Wanda kuma nayi hakanne saboda lafiyarsa,dannasan idan suka tabbatar yasani to zasuyi kokarin hallakar dashine wanda hakan shine abinda har karshen rayuwata bazan yafewa kainaba.
Dora habar sa yayi akaina kafin yace,
“Kiyi hakuri da rayuwa sameemah hakika munga jarabawa kuma muna kan gani,saidai ko kusa ban fada rayuwar da kika shigaba,ke jarumace nasake fada ke jarumace sameemah,wanda ko cikin maza ba kowane zai jure abinda kika jureba,saidai ina fatan wahalar rayuwa yah tsaya miki iya haka,sannan kuma yah baki ikon karbar hakan a matsayin kaddararki,ina fatan nacigaba da zama dam uwa a gareki mai sharemiki kuka,sannan ina saka ran kasancewa miji nagari agareki idan kin bani damar hakan,sannan kuma uban y’ay’anki”
Gabana ne yah buga rigifff,saboda nasan abinda yake hasashe ba abune mai yiwuwa ba koda kuwa mun so hakan a tsakaninmu,yau daya a rayuwata naji babu dad’i kasancewata daban da irin rayuwar mutane,saidai cikin sauri na katse tunanin hakan daga cikin raina tareda cire jikina daga na yah sameer ta hanyar matsawa gefe.
Shima dayaga hakan light kiss yayimin a kumatu tareda da cewa “saida safe”

????salma a madubin gani????

Tun da nazo gidannan ko na muka zo nida sameerah babu wanda yaji dadin gidan.
Ni kullum a gaban mijina da akwai da babu duk dayane,ita kuwa sameerah mijin ma bata ganshi ba,dan yanzu an shiga wata na hudu kenan da barin daga kasar,yah tafi can wai an turashi da sunan karatu yana ta sharholancinsa.
Tun daga yanzu banyi shekara da aureba amma danasanin auren nakeyi ,kullum cikin aiki mukeyi,idam kuma kasamu ka kwsnts baka da aiki sai tunanin yanda rayuwarka zata kaya washagari.
Nida sameerah sai murna muke hajiya mairo zasuyi tafiyah itah da alhaji bala zuwa kasar india,zataje a duba mata kafarta.
Dan yanzu mun hade kanmu nida itah,dan dolen uwarmu,koba komai naka nakane,da muka uwar bari sai muka hade kanmu,amma hajiyah mairo batada masaniyar hakan.
Muna gani suka shiryah suka tafi sai rankwada kai takeyi,shikuwa duk yanda tayi sai ya yi mata sannu,bakinciki kaman zai kasheni danna tsani hakiyha mairo kaman na kasheta nakeji ,shegiyah tsinannaniyah.
Ita kam zainab taji dadi yamzu,duk da a baya itama tasha wuya,yanzu suna can ita da mijinta da kuma yar ta.
Waya san halinda sameemah kuma take ciki oho. Da haka dai muka rakasu sai hararar mu takeyi,nidai dauke kaina nayi a raina nace zaki san kin gasamu aradu,wallahi duk saina juye tijarar daki yi mana a kanki.
Zamuyi shiri muna nan zuwa kanki muma.
Aikuwa hakanne ta faru,dama munyi shirin idan sun tafi muyiwa alhajin kira,dole yah barta ya dawo koyana so ko bayaso,daga nan zanyi duk dabarun dazanyi na naja hankalinsa izuwa gareni,idan ta dawo bata da ikon yin komai sai abunda muka yi.
Ni da sameerah kullum muna kulla yanda komai zai kasance cikin sauki ba tareda a ansha wahala ba,maida hankalina kan sameerah nayi kafin nace,
“Nikam inaga sameerah idan har alhaji yha dawo da hankalinsa toh bazan yi masa asiriba zan jawo hankalin sa ne da duk dabarun danake dasu,saboda nagane duk mallakar asirinnan aikin banzane idan ya karye shikenan ya barka a tutar babu”
“Kuma fah hakane salma yamzu kina ganin umaruje da bani yake soba,duk lokacin da asirin yah fara karyewa sai na rasa kansa bare gindinsa fah. Gaskiya nima na gane,idan har zan iya shawo kansa zuwa kaina da karfin kissa irin ta mata to ina ga hakan za’ayi,muje kawai na biki muyi musu kiran a tare,idan mukayi sa’a kafin ta dawo mun shawo kansu sai muga ya zatayi kuma”
Hakan kuwa akayi mukaje wajen malami mukayi masa bayani sanann muka bashi suanan alhaji bala da dansa,da niyyar idan sun dawo tamu basirar zamu hada muyi amfani da itah a kansu.
Washagarin ranar da muka je wajen malamim kwatsam muna zaune sao ga alhaji bala ya shigo gidan,bamuyi masa maganar ina hajiyah ba sai sannu da dawowa da mukayi musu,sameerah ce tayimim signa akan ma dam gwada action,aikuwa cikin dakewa na matsa kusada shi dama nayi kwalliya nasha turare.
Karbar jakar hannunsa nayi niyyar yi,abin mamaki kuwa sai ya sakemin ita dukka kafin yayi hanyar dakinsa,shewa mukayi nida sameerah marar sauti kafin na bi bayansa da Sauri.
Bai koreni ba haka bai yimin magana ba har na hada masa ruwan wanka ya,shiga sannan na kaimasa abinci.
Har yagama cin abincin ina zaune a gafensa amma bayyi magana ba,hada kayan abincin nayi da niyyar fita zuwa kaiwa kitchen sai naji ya zawo hannuna tareda cewa,
“Salma Idan kin kai abincin ki dawo,inajin kaman jikina babu dadine shiyasa na kasa yimiki magana,daga gani dai kaman ba yau aka kawoki gidannan ba amma kuma sai naga kaman ni yau na fara ganinki a gidan kai na ya daure sosai”
Saurin saka hannuna nayi a bakinsa kafin nace,
Shshh alhaji komai ya wuce yanzu,bari nakai na dawo”
Gyada min kai kawai yayi,ina fita muka tafa nida sameerah wanda muna cikin hakan mukaji alamar jefar da jaka a kasa,dukknamu bakin kofa muka kalla inda umaruje yake tsaye,kallon sameerah yayi cikin takaici kafin yace,
“Mtsww ni wallahi narasa ma maiyasa ma dawo akanki,kwata kwata ma ya akayi na aureki oho,aikin banza kawai,dallah kawomin abinci ni”
Jikinta yana rawa ta gyda masa kai,nidai wucewa nayi na ajiye kayan kafin na zo na wuce wajen alhajin,dan dama ba magana nake da umaruje ba.
Yamzu zamanmu da alhaji bala ba yabo babu fallasa,saidai abin farincikin shine kullum kara sakewa muke dashi,sannan mukan zauna muyi hira dashi ta fahimtar juna,har sameerah wani lokacin ma da ita ake hirar,kasancewar umaruje har yanzu tsakininsu abin yaci tura,dan dama ba da soyayya sukayi aurenba,yah aureta ne ba a cikin hakalinsa ba,shiyasa abin duk yaki daidai tuwa.
Muna nan nafara jin kaman banida lafiya,nice ba nice ba kullum cikin kawanciyah da kuma amai,alhaji na samu na fadawa halin danake ciki.
Nan da nan kuwa muka tafi asibiti,gwajin farko aka tabbatar da cewa cikine dani,koni kaina banyi farincikin da alhaji bala yayiba,kaman shine haihuwarsa ta farko.
Dawowa gida mukayi bayan sun damin bincike akan komai lafiyya,sameerh ma ta tayani murna sosai,dan ma sa’a ta daya cikin baya bani wahala sosai kaman yanda yah fara a farko kafin naje gwaji,kaman dama jira yake musan yana nan.
Soyayya Mike zubwa nida alhaji bala kaman wasu yara,komai nayi biyeni yake babu ruwansa,danshi kansa naga yayi laushi dayaga hanyar dayake a baya bamai dorewa bace.
Cikin yana da wata hudu wanda yakama hajjyha mairo tayi wata hudu kenan a kasar india,dan duk a zatonta alhaji bala yana Egypt wajen wani program yanda ya fada mata.
Rana tsaka ta tashi dawowa hakn ma dan sunyi waya da yusrah ne ta fadamata cewa alhaji bala yana Nigeria duk tsawon watannin nan,aikuwa kaman iska haka hajiyah mairo ta tayar,ko gama zamn batayiba ta kamo hanya ta dawo.
Muna kitchen nida sameerah muna abinci,na dawo falo kenan na zauna saboda sameerah tace na huta kawai,ina zama saiga hajiyah mairo ta shigo,idonta dama a kaina yake kaman zai fado kasa,musamman da taga abinda yake gabana wato ciki.
Tun daga cikin idonta kana ganin kalar bakin cikin da ya kunsa,dan nasan tayi datasanin zuwa neman maganin,da ta bar kafar kawai ta rube.
Kaina tayi da niyyar turmusheni akan kujerar daidai kuma da fitowar alhaji bala daga cikin dakinsa,saurin dakatar da hakiyah mairo yayi Yana cewa.
“Baki da hankaline da girmanki da komai kike kokarin cutar da ita,bayan kuma ga ciki a jikinta,idna wani yayiwa yarki haka zakiji dadine iyee,to wallahi karanaji na gani mairo,idan kuwa kika kuskura naga kin sake cutar da wannan mutanen a cikin gidamnan kaman yanda kikayi a baya,toh a bakin aurenki,ke sai kibar gidan in yaso kawai,tun da ba zaman lafiyay kike so ba”
Yana maganar cikin daga murya,daga gani ransa yah baci sosai.
Daga haka yah juya ya fita daga gidan,nikuwa kallon zakisan dawa kike nayiwa hajiyah mairo wanda dan takaici har kwalla idonta yakeyi.
“Yaushe haka ta faru,wane asirin kika yiwa mijina dan ubanki”
“Wane asirin na karya dai,babu boka ko malam sai zalllan kissa,idna kema kika cigaba zaki samu naki rabon fiyeda nawa ma tunda kin fini saninsa”
Shiru tayi kaman ta dauki magana ta sai kuma tayi dakinta da sauri kaman ana jefata,dukkuwa da kiba irin ta jikinta.
Haka zaman ya cigaba da kasancewa tsakanimmu dani da hajiyah mairo babu wanda yake shiga harkar kowa,saidai sameerah kam tana shan wahala a hannunsu,musamman da suka ga tana kula dani.
Karyah babu irin wacce hajiyah mairo batayiwa umaruje akan sameerah,a dole sai ta saka yah musguna mata.
Zancen da tayi na auren yar kawarta kuwa yana nan babu fashi sai shirye shirye sukeyi.
Duk wanda yaga sameerha sai yau tausaya mata,don ta rame ta fige kullum tana cikin tagumi,gashi wani irin so take yiwa umaruje kamar ta ci babu.
Dan yanzu karatun ta nutsu tayi sallah bata wuceta,har makarantar dare ta shiga saboda rage zama a Gidan ma Yana rage mata kewa.
Domin kusam kullum Mufeedah tana gidan wai tazo gaishe da hajiya mairo,shikuwa umaruje sai rawar kafa ta tashi,koda idon sameerah baya sa ya dauke idonsa,saidai ita ta bar musu wajen.
Takaicin hakan nake gani gashi banida ikon yin komai akai,koba komai sameerah yar uwata ce,ganinta cikin hakan yana tabani sosai zanyi,dan nima ta kaina nake,ni kadai nasan wahalar danake sha a cikinnan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button