NOVELSWASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

Shirye shiyen auren ake dan har an kusa saka rana biki ya fara kan kama,a zaune muke a dakina sameerah ta kawomim shayi na dare wanda yazam kaman jiki kullum sai nasha.
Kallonta nake da mamaki sanann da tausayinta ganin yamda ta tsurawa waje daya kallo ko kyaftawa batayi,danni kaina sshaida ce a irin soyayyar da take nunawa umaruje.
“Sameerah ki dunga hakuri,idan kika biye hakan zai iya kaiki yah baroki sannan kuma dolene a jarrabi bawa,amma idan kinga zaamn yana cutar dake yakamata kiyi wani abun.
Dannaga wani abun da gangam sukeyi dan suga iyay gudun ruwanki akai”
“Nasani salma nasan duk abinda yake faruwa,saidai na ma gode allaah da abin da na shuka nake girba dun daga nan duniyah,ba a barmin shi sai naje lahiraba,dan salma wallahi sai yanzu nake nadamar rayuwar danayi a baya,musamman idan malamin mu na makaranta yana fadan wani abun,sai naji ashe mu duniya kawai zuwa mukayi bamu karu da komai ba.
Inaji a jikina abinda nayine ake nunamim a gidannan,idna na tsalleke na tafi kaman na bar baya da kurane,dan haka zan cigaba da zurewa salma har zuwa inda zuciyata bazata iya daukaba,alkawari na daukawa raina bazan taba cewa umaruje ya sakeni ba saidia idna shine yaga yana bukatar hakan. Nagode salma sosai da nuna kulawarki dan a wajwnki ne kawai nake samun nuna kulawa mai kyau,dan ummah kan idan naje bata da magana sai ta na koma wajen boka a sake min aiki. Gaskiya nikuma naga ba abinda boka yake yiwa rsyuwar mutum banda kara masa wahala da kuma zefashi cikin hallaka,wanda nayi a baya ma ina neman yafiyar allah,dan haka bana bukatar sake dorawa kaina wani laifin wanda bansan iya kacin masifarsa ba”
Tana gama fada hakan ta dauki tiren shayin cikin sanyini jiki tayi hanyar kofa tareda yimin saida safe.
Lokacin data jamin kofar bansan sanda na fashe da kuka ba mai cin zuciyya,lallai munyi rayuwar dana sanj a baya kam.
Istigifari nake tsyi ina maida zuciyau har bacci ya daukeni.

Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150

Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.

????Sadi-Sakhna________✍????????

(¯’•.¸,¤°’✿.。.:քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ.:。.✿’°¤,¸.•‘¯)

????•°• WASA FARIN GIRKI •°•???? {cigaban gidan gandu}

????29~30????

????Sameemah a madubin gani????

Tun da muka yi maganar nan da yah sameer nakeji wani irin yanayi yana jiyartar cikin jikina yana taruwa a cikin kirjina,tun yana min ina iyya daurewa har yah zamo na farajin zafi a cikin kirjina,”mai hakan yake nufi?”
Shine tambayar danayi wa kaina amma banada amsar hakan. Da haka bacci yah daukeni,saidai bankai ga jina cikin duniyar baccin tsulum ba mutanena suka bayyana cikin siffa ta bacin rai.
~~~me like nu fine Wai,kina nufin zaki bar soyayya ta huda cikin zuciyarki wacce take haramun ce ga kowanne namiji yha shigeta,to hakan bazai taba yuyuwa ba dole ki tashi daha yaudararren maganar daya miki matukar kina so ki karisa guntun rayuwar da ta sauramiki a cikin su lafiya”
Kowanne lokaci cikin kwarin gwiwata nake tsayawa a gabansu,saidai yanzu ma nemi wanann kwarin gwiwar narasa shi,sai ma sunkuyar da kaina danayi kawai ina jinsu har suka gama masifarsu mai hade da gargadi suka bacewa ganina.
Tambaya daya anan shine”shin zan iya abinda suka umarceni da yi,wato cire ɗigon soyayyar yah sameer data darsu a cikin raina a daren??”.

Da safe dana tashi kokari nayi na katse duk wani tunani daya shafi abinda yah faru a daren jiyan daga cikin raina,saboda halina ne banason duk abinda zai dunga tsayawa a cikin raina yah dunga yawo lokaci zuwa lokaci.
Ina Bude kofar tawa idona ya sauka akan fuskar sameer wanda ya dam jingina a jikin tasa kofar yana kallona,Murmushin dayake aikomin daga wajen dayake tsayene yasa na saduda na mika dukkan ragamar danayi niyyar rikewa daga farko,”wayyo allah yazanyi da wannan halittar da take kokarin keta rayuwata ta,shiga”
Takowa yake a hankali har yah iso inda nake tsaye,hannunsa yasaka mai laushi sosai kaman ba na namijiba yah dago fuskata izuwa ga tasa.
Kallon kallo muke yi a haka kowa yana enjoying yanda zuciyarsa take shigomasa da shauki.
“Dafatan wannan kyakykyawar kanwartawa kuma matartawa tanajin abinda nake ji a cikin raina,sannnan kuma da yanda na kwana cikin begenta da kuma son kasancewa a kusa da itah”
Har zuciyata tana kokarin sallamasa kaman yanda take da burin na barta tayi abinda take some tun lokacin dana hada idona dashi.
Saidai kuma abinda zai biyi baya nake tunanin,ni ba kowacce sauran yam adam ce mai yanci ba,kowa yana da ikon yin abinda yaga dama,amma ni bana da wannan ikon koda nayi niyyar yin hakan.
Jan numfashi nayi mai karfi kafin na sauke hannunsa dayake kan fuskata nayi saurin shigewa kitchen,nasan abinda nayi ban kyautaba kuma bazai ji dadin hakanba,saidai hakan shine yafi masa kuma yafimin,yaj kamata nayi nesa dashi tun ina da damar hakan.
Shiryawa nayi kana na shiryah farouq muka bar gidan,saleemah kuwa tun lokacin da aka dawo da ita ba wani haduwa muke sosai ba.
Duk hanyar dazan bi dan naga na gujewa haduwata da yah sameer abin yaci tura,dan koyaushe yana mkaale dani yana min murmushi ko kuma bani hakuri wanda nikaina bansan mai yayimin ba.
Yauma ina cikin aiki a office naga yah shigo yah samu kujera yah zauna,dago idona nayi na kalleshi kafin na cigaba da yin abinda yake gabana.
Gyara kwamciyarsa yayi akan kujerar dan dama bansa a raina zai fita lokacinba,har nagama aikina na tattara kayana yana zaune yana danna waya,wucewa nazoyi ta wajen dayaje zaune aikuwa karaf naji ya zawoni zuwa kan cinyarsa,zuya idona nayi zanyi magana yayi saurin nunamin bakinsa nayi shiru.
Hakan kuwa na tsinci kaina dayi wato bin umarnin daya bani.
Tashi yayi daga kwancen dayake yah hada kirjina da nasa ya rungemeni sosai,banyi kokarin raba jikinnamu ba dan bazanyi karyah ba ina tsintar kaina cikin farinciki idan hakan ta kasance.
“Meyasa sameemah kike guduna a kkda yaushe,sau nawa zan fadamiki nesanta ni da kike daga kusadani Yana cutardani,sau nawa bakina zai cigana da furtamiki cewa Yana sonki sanann Yana kaunarki,kece mahadin rayuwarsa,sameemah babu karyah a cikin maganar daake miki.
Dagoni yayi domin naga hakikanin gaskiyar a cikin idonsa wanda ko ban ganiba nasan abin hakane,cigaba yayi da furta kalmomin da suke sakani jin ina raye,ta wani bangaren kuma suke kasheni sannan suke kara nisantani daga gareshi,yaushe bakina zai iyha buduwa yah sanar dashi halin danake ciki,anyah kuwa zan iyya zure wannan rayuwar da muke ciki.
A duk lokacin dana kwanta na tashi sai shedanun sunyi kokarin mallake jikina da kuma ruhina,wanda dama hakan shine burinsu kuma sun fara samun nasara.
Hannuna na saka a bakinsa domin banason cigaba da jin wanann kalmomin da dama nariga nasan suna cikin ruhinsa,
“Yah sameer kayi shiru da fadin wannan kalmomin nasan dama Akwai su a cikin zuciyarka kuma da gaske kake duk abinda ka fada”
“Idan Har kinsan da gaskene meyasa kika kasa bani dama sameemah akan mu koma zaman da kowanne ma’aurata suke,ko baki da lafiyane,idna akwai wata matsala ki fadamin”
Saurin kallon idonsa nayi tareda jijjiga masa kai da sauri,da hankalin sa yana kaina sosai da zai gano shock din dana shiga a lokaci guda.
Ta shi nayi daga kan cinyasa nayi waje,shima dayaga hakan biyoni yayi muka tafi gida,a hanyama babu wanda yace wa kowa komai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button