WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL
WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL
Magana muke jiyowa daga dakin Saleemah lokacin da muka shigo gidan,muryar ta babbar matace da alama kuma sameer yasan wacece,dan hannuna yasake da sauri ya nufi dakin saleemah din,nima nawa dakin na wuce domin canja nawa kayan.
Ina jin lokacin da Saleemah ta rako matar tana ta yimata shagwaba amma ban fitoba dan bana son shishshigi a lamurana sosai.
Can wajen magribane sameer yashigo dakinnawa yake cemin doctor maryam ce kanwar hajiyya fatima tazo,bata kasarnan taje karo karatu jiya ta dawo,zata fara aiki a sibitin cikin barrack dim,toh kawai nace masa dan yamzu yawancin lokuta yakanzo dakina yayi ta min hira koda bazan amsaba,nima har na saba da zamansa a kusadani yanzu shida farouq,idan babu daya sai na yi ta jina cikin kadaici.
Kiran sallane yasa ya tashi ya tafi masallaci,nikuwa da ba yi nake ba ina zaune ina cigaba da aikina.
Sake shigowa yayi a karo na biyu saikuma naga ya tsaya daga bakin kofar kamar mai nazari.
“Sameemah kinyi sallah kuwa fitata daga dakinnan?”
Tambayar ce tayimin wani giff a cikin kirjina har tasa nayi shiru narasa wace irin amsa zan bashi.
Shiru nayi ban ce komaiba sannan ban tashi daga inda nake zaune ba,har nabude baki zan cemasa bana sallah sai kuma naji yace,
“Shin mai yake damunki sameemah,tunda nake dake ban taba ganin kinyi sallah ba,nasan yanzuma cewa zakice bakya sallah amma kuma bahaka bane,saboda tun sanda nake zuwa office dinki ban taba ganin kin tashi kinyi sallah ba,wane irin al’ada ne zayyi wata guda yana zuba uhm?”
Gumine ya fara karyomin ta ko ina a cikin jikina,shin mai zancene ma tukunna.
“Ba wasa da sallah kike ba sameemah,kwata kwata ma batada lokacinki mai yasa haka,kuma ina kukada dake zaki saka farouq yaje masallaci amma ke bakya zuwa yij sallah,dan muyi bauta aka turomu duniyayr nan sannan wajibice akan kkwa babu wanda aka daukewa,Allah yana cewa a cikin alqur’ani :
Wama kalaqtul insi wal jinni illah ……….”
“Liya’abudun”
Nayi saurin karisamasa numfashina yana cikowa,yah sameer naji kuma zanyi yanzunnan.
Kallona yake da mamaki saidai shima tasa fuskar babu alamar wasa a cikinta.
Bandaki na shiga na dauro alwala jina ke kaman na junduma ihu saboda tunowa irin azabar da zan fuskanta.
Lokacin dana fito baya cikin dakin,hakan yasa nayi ajiyar zuciya tareda komawa na cigaba da abinda nakeyi.wayata naga tana haske,ina dubawa naga sunan husband,yaushe kuma haka ta faru,kenan shine yamin saving number sa.
Ɗauka nayi na kara a kunnena domin jin mai zaice,
“Kinyi sallahr ne?”
Uhm kawai nace masa a taikace kafin ya kuma cewa,
“Kizo dakina yanzu ina son ganinki to”
Daga haka ya kashe wayar,nima ajiyewa nayi ina tunani,mai zai cemin wanda ba zai fada a dakina ba.
Kawar da tunanin hakan nayi kafin na dauki gyalena na nufi hanyar dakinnasa,dadai nazo shiga dakinnasa na hadu da saleemah saidai banda harara babu abinda ta iya yi dan shakka ta takeji ba kadan ba kuwa.
Tura kofar nayi nashiga batareda nayi sallama ba,a kan kujera naganshi yana wani rubutu.
“Zaki shigo dakin mutum amma babu sallama,sannan idan anyimiki ma bazaki amsa ba koh”
Duk da hakan halina ne amma saina tsinci kaina da jin babu dadin yanda yake fadar hakan,bakina nabude kaman wanda yake ciwo na ce,
“Salamu alaikuma”
Amsawa yauyi tareda tahowa inda nake,kama hannuna yayi ya zaunar dani a bakin gadon shikuma ya zauna a kasa na,
“Barka da zuwa dakin mijinki karon farko tun aurenki,nayi farinciki sosai da kika amsa gayyata ta seemah”
Seemah!! Shine abinda na fada a cikin raina,yau kuma lallai kam.
Kama hannuna yayi yasaka a cikin nasa kafin yace,
“Ina matukar son rayuwa tareda ke seemah amma kinki amincemin muzama abu daya cikin inuwa daya,duk da nasan kema kina da bukatar hakan,ina sonki sosai sameemah amma naga alama kinfi son ki ganni kullum cikin kewarki da son kasancewa tareda ke koh”
Maganganunsa kashemin zuciya suke ba kadan ba,ko kadan banason ganinsa cikin wanann halin,hakan yana cutar dani,musamman da nasan cewar nice silar hakan,yah aureni yah fara sona nima ina sonsa amma kuma na kasa yimasa abinda kowacce mace zatayimasa,duk da zuciyata tana kin yarda amma nasan saleemah tafini a wajensa,tunda zata iya yimasa abinda ni bazan iya yimsaba,kaitona da zamtowa wani bangare na rayuwarsa wanda zai zame masa ciwo ba maganiba wayyo allah nah!.
Rintse idona nayi tareda saurin kawar da bakina daga nasa bakin wanda yake kokarin hadawa da nawa,bazanyi wanann gangancinba ban shirya ganin gawarsa a gabana ba tukunna,ina cewa zan iya rasa komai bayan ummah tah sai yanzu nagano duk zancene,rasa wannan ruhin da baisan komai ba sai soyyayyata abune da bazan iyah zurewa na sam,dan haka bazan iya yin abinda zamyi danasani ba koda kuwa zuciyata hakan take matukar bukata.
Kamo fuskata yayi yana kallona ko akwai abinda yake damuna,saidai ko kusa naki bude idona wanda nasan zuwa yanzu sun tashi daga kalar irinna bil’adama,kamani yayi yah rungumeni a jikinsa yana magana cikin sanyin rai.
“Seemah narasa gane mai yake damunki,nace miki idan bakya da lafiya ki sanar dani bazan iya zurewa zamanmu a haka ba sameemah,ni namijine mai matukar bukata,na fadamiki idan wani abune nayi miki ki fadamin zan gyara,amma idan kika hanani kanki abin zaimin yawa seemah,bazan iya dauka ba sam,ina kaunarki sosai fiye da yanda bazan iya misaltawaba kiyimin afuwa da kuma uzuri dannima haka na tsinci kaina ciki.
Horonki yana gasanj ba kadan ba,bansan har zuwa yaushe zancigaba da jiranki ba,koda babu ke dole zan kara aure saboda bazan iyah zama da mace daya ba,amma yanzu tunda na aureki banda burin sake Lauren wata macen kece dama zabina na dade ina jin wani abu a game dake tun kina karama sameemah,nasha kuka daki ina tambayar kaina mai yasameni nake sha’awarki bayan kin kasance muharrama a gareni,saidai daga baya ganin abin ba zai wuceba yasa na yanke hukuncin nesanta ki daga inda nake tun lokacin da ummah tana da rai.
Amma yanzu ke halaliya tace sameemah karki bari wani abu a cikin ranki ya dakushemana farin cikinmu,inason yin rayuwa dake har zuwa lokacin da numfashina na karshe zai fita”
Saurin zare jikina nayi daga nasa ina matsawa can gefen gadonnasa,wani abu naji yazo ya tokaremun makogaro,ganin banida ikon yin abinda mijina yake bukata daga gareni,duk ina bukatar sallma masa kaina amma bazan iya ba domin gangar jijin ba mallakina bace,an riga an gama iko da ita.
Wani irin kuka na fashe da shi karon farko kenan bayan ummah ta ta rasu sai yamzu na samu ikon yin kuka.
Wani irin zafi da tafarfar fasa zuciyata takeyi yayinda nake jin wani zafi yana tsaga sassan jikina,duk da haka ban sareba saida na tattaro sauran kalomomin dake bakina nafara cewa,
“Kayi hakuri yah sameer! Kayi hakuri mijina ! Kayi hakuri masoyina.
Hakika da ina da ikon aikata abinda kake bukata dana aikata,koda kuwa hakanne zai kawo karshen wanann wahalelliyar rayuwartawa,banida ikon yin nesa dakai ko kuma yi maka musu saidai hakan baya cikin abinda zan iya aikatawa.
Barinka kana isowa har kusan jikina ma ka tabani ba karamin kokari nayi ba akan hakan yah sameer,inajin kunyar kaina a halin yanzu,ban taba jin banason yanayin halittata ba sai yanzu,amma babu yanda zanyi hakan shine kaddarata dama tun farko banida ikon hanawa barekuma canjawa.
Ni wata irin matace sannan kuma wata irin masoyiyace wanda bazata karu da mijinta da komai ba sai kawo masa damuwa da kuma hatsari,zan kasance mai son kai idan nace kacigaba da nuna min so ko kuma tunawa dani,dan haka kayiwa allah badanniba sai dan allah yah sameer ka koma rayuwarka da kakeyi a baya kaman kk wanne mutum mai farin ciki,ka barni nacigaba da rayuwata kaman yanda nakeyi wacce banajin tausayi banajin shauki sanann banjin dadi,ta hakane kowa zai zauna cikin farin ciki nima kuma na rayu ina kallonku kusa dani “
Shiru nayi da magana ina cigaba da rusa kuka mai tsima duk zuciyar wanda yake saurarona,kirjina na rike gam wanda yake barazanar fashewa da hannuna,shima sameer dayaga haka rarrafowa inda nake yayi idonsa yana zubar da kwallah,wamda nasan ganin halin danake cikine yah saka shi.
Rike dukkan hannayena yayi da nasa hannun kafin yace cikin karfin hali.
“Menene yake faruwa da rayuwarki sameemah,kiyimin magana naji kinji ki daina rike abu ke kadai haka”
Bude bakina nayi zance masa wani abu sai kuma naji bakina yah cika da wani abu mai dandanon gishiri,zubar dashi nayi da sauri,anan naga ashe jinin ne har da guda guda,wani tarin ne yasake sarkeni da karfi mai matsanancin ciwo.
Jinine yake ta zuba daga bakina kaman famfo wanda da kadan kadan naji jikina yana shikawa har saida yah zamo dishi dishi nake ganin komai,bude idona nayu dukka akan fuskar masoyinna wa kafin namayar na rufe da sauri wani duhu ya lullubeni.