NOVELSWASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150

Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.

????Sadi-Sakhna________✍????????

(¯’•.¸,¤°’✿.。.:քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ.:。.✿’°¤,¸.•‘¯)

????•°• WASA FARIN GIRKI •°•???? {cigaban gidan gandu}

????33~34????

Shiru dakin yayi babu wanda yace wani abu jin abinda likitan yah fada,sai shine yasamu kwarin gwiwar cigaba da cewa.
“Sannan kuma koda mun sallmaeshi zai iya samun wata guda kafin yah fara tafiya saboda yanayin buguwar da yayi,wannan shine sakona a gareku ina fatan ku kasance masu tawakkali da kuma karbar kaddara a duk yanda tazo muku”
Dukkanmu juyowa mukayi domin fitowa daga office din,a bakin kofar muka hadu da alhaji bala shima dawowar sa kenan daga tafiyar dayayi yaji abinda yah faru,rabewa yayi ta gefenmu yah shiga office din zuwa wsjen likitan.
Mukuwa hanyar dakin da umaruje yake muka nufa dukkanmu.
A kwance yake yana kallon sama,an saka mayafi irin na asibitin a kunkuminsa zuwa kasa,in ba kaji abinda yake faruwa dashi ba bazaka ce baida lafiya ba.
Samun waje hajiya mairo tayi ta zauna kusada shi tareda yi masa sannu cikin murya mai dauke da damuwa.
Kallon hajiya zulai tayi kafin tace,
“Ina hajiyah zulai zancen daurin aurennan saidai a daga sai yah warke koh?”
“Wane daga auren kike magana akai hajiya mairo,kunnenki bai jj abinda yake damun danki bane,amma duk da haka kike kokarin hadashi da dana,toh wannan zancen babu shi kwata kwata,dan ina ji ina gani bazan hada Y’a ta da juyaba wanda bazai haihuba”
Itama Mufeedah share hawayen dayake idonta tayi kafin tace,
“Gaskiyar ummah ne bazan iyah aurensa bayan nasan bashida lafiya,koda an daura auren ma dole za’a warwareshi bare allah yah taimakeni ba a dauraba dama,dan haka sali alin babu abinda ya hada”
Baki hajiya mairo tasaki tareda cewa,
“Hajiyah zulai kinsan abinda kike fada kuwa keda yarki,kanmu a hade zamu hada wannan auren amma dan kawai wani abu yah faru shine zaku watsamin kasa a ido?”
“Kai kaji hajiya mairo dan allah,banda kina so ki cutar da Y’a ta dan kinga ba y’ar ki bace naki yarda shine laifina,wannan ai son kaine,ina ganin fah yanda kike zaluntar y’ar wata dan kawai tana auren danki”
Har hajiya mairo zatace wani abu alhaji bala yayi saurin katseta ta hanyar cewa,
“Hajiyah mairo ya isa haka,gaskiyar tane abune na kowa yana da hakki dan haka tunda bazata iya aurensa ba shikenan,kuma koda anyi auren tace bazata zauna dashiba dole a raba auren haka shari’a tace”
Kuka hajiya mairo ta fara ganin abin yama neman fin karfinta,babu wanda yah kulada ni a cikin dakin sai lokacin da alhaji baka yamin magana,dukkansu harda hajjya zulai da suke shirin fita daga dakin kallonsu ne ya dawo kaina.
“Kema kina da zabi sameerah akan zama da umaruje,kindai ji mai likita yace kan cewa bazai kara haihuwa ba,shin zaki zauna dashi ko kuma kina neman takardar ki a wajensa na ya sawwakemiki?”
Saurin jijjiga kaina nayi tareda cewa,
“Zan Zauna dashi abba”
Kowa kallona yayi da mamaki harda hajiya mairo da take share majina,magana alhaji bala yasake yi a karo na biyu cikin tabbatarwa,
“Shin kin yarda da zabin da kikayi,idan harkin amince ki zauna dashi akwai sharadin banason kuma wata maganar ta fito daga baya,idan ma lokaci kike so a baki na tunani duk za’a baki amma kiyi tunani”
“Bana bukatar lokaci nayi tunani,dan dama hakan shine zabina tun kafin hakan ta faru,nayi wa zuciyata alkawarin cigaba da zama dashi cikin kowanne yanayi da kuma hali har karshen rayuwata,saidai idan shine yayi ra’ayin sawwakemin saboda yagaji da zama dani,toh yanzuma hakanne idan yaga bazai iya zama daniba xai iyha sawwakemiin ,kuma ina mai sake bashi hakuri bisa hanyar damabi na aureshi ba tareda yardarsaba,dan haka duk abinda zaimin bazanga laifinsa ba ko kadan kuma zan cigaba da zama dashi har karshen rayuwata ……saboda ina son..sa sosai har zuciyata,haihuwa kuma dama allah ne me bawa mutum kuma zai dauke a duk lokacin dayaga dama,dan haka banida matsala da rashin haihuwarasa a gameda zamana da shi,ina fatan allah ya bashi lafiya yah tashi kafadunsa”
Ina gama fadan hakan na rushe da kuka wanda dama yake cina kwana da kwanaki,ganin abin zai min yawane yasa na bar dakin da sauri nayi waje domin na samu zuciyata ta yi sanyi koda kuwa dan kadanne.
Na dade a zaune a waje ina ta tunani sai wajen azahar tukunna na raba na shiga dakin,babu kowa sai hajiyah mairo itada yusrah,shikuma umaruje akan gadon ,babu wanda yake cewa komai a cikinsu,nima daga sallma ban sake cewa komai ba na shige bandakin kaman wata munafuka.
Fitowa nayi na shimfida dan kwalina a gefensu na tada sallah,lokacin dana idar na dade ina addu’a kafin na shafa na koma gefe na Zauna.
Dire bane ya shigo dauke da kula a hannunsa inji salma wai,karba hajiya mairo tayi ta bude,shikaface da miya sai kuma farfesun hanta a daya kular na marar lafiya.
Had’a ido mukayi da ita nayi saurin dauke nawa idon zuwa gefe,zuba abincin tayi a plate ta mikawa yusrah sannan ta zuba farfesun a plate daga gani umarujen zata bawa,tashi nayi da sauri na karbi nasan daga hannun sa akan zan bashi,xuciyata tana dardar dan banyi tunanin zata sakemin plate din ba sai kuma naga tasake min.
Plate din abincin yusra ta dauka tareda cewa,
“Ummah inaga muje waje mudin ko”
Batace komai ba amma kuma tabi bayan yusrah suka barmu mu kadai a dakin.
Hannuna nakai a hankali na taimaka masa yah tashi kadan kafin nasaka masa filo a bayan kansa,nishi yayi irin na maijinya idan ya motsa inda yake masa ciwo.
Sannu na fara jera masa har bansan iyah yawan yanda na fada ba,kallona yake kaman mai son cewa wani abu sai kuma yayi shiru,abincin na diba kadan a cokali na fara bashi,da haka har yaci da dan yawa kafin ya matsar da kansa,ruwa na debo hade da maganin da zai sha a lokacin na bashi.
Saida naga yasha tukunna na juya domin barin wajen gadonnasa,kamo hannuna naji yayi tareda jawoni zuwa kusa da shi.
“Sameerah”
“Na’am. …..Akwai abinda kake bukata ne”
“Ahah hankalin ki kawai nake bukata ki bani”
Juyawa nayi muna kallon juna idona har yakawo hawaye,
“Meyasa kika amince da zama dani duk da kinsan abinda yasameni?”
“Karima miyasa kacigaba da zama dani duk da kasan cewa cutar dakai nayi ta hanyar aurenka a da yaddarka ba?”
“Saboda ina jiran wani lokaci dazan sallameki amma kafin sannan saina hukuntaki a gameda abinda kikayimin”
“Nikuma na amince da zama dakaine saboda ina sonka sannan nayi alkawarin zan zauna dakai a duk halin dakake ciki,domin kaine mutumin da a dalilinsa nasan wace irin rayuwa nake ciki kuma harna fito daga duhu nagane gaskiya”
“Banbancinmu dake kenan sameerah ke macece da duk wanda yagane yanda kike to yayi dace,ina rokon da ki yafemin abinda nayimiki sannan ki bani damar farantamiki idan har nasamu ikon hakan”
“Nima ina rokon ka yafemin sannan kuma kabani damar shiga zuciyarka da gaskiya da amana bada guru ko laya ba”
“Ina farin cikin karbarki cikin zuciyata sameerah daga wannnan ranar ,ina fatan allah yah bamu zaman lafiya mai dorewa”
Murmushi nayi shima ya mayarmin da kwatankwacinsa,daga haka muka fara hira muna dariya kaman ba jinya yake ba.
Satinmu guda aka sallamomu daga asibiti saidai an hadomu da wheelchair saboda har yanzu baya tafiya da kansa sosai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button