NOVELSWASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

????sameemah a madubin gani????

Kwana na daya a asibitin doctor maryam ta sallameni saidai har na tafi gida bansan mai yake damuna ba kuma ban tambayi sameer akan hakan dannasan zancen gizo baya wuce na koki,bazai wuce shedanuna bane suka yin hukunci saboda ina shirin ketare iyakarsu.
Kwana daya kenan da zamana a wajen amma har cikin zuciyata bana son barin wajen saboda doctor maryam,domin wani abu naji a yana tsargamin cikin jikina fiyeda yanda nakeji a gameda hajiya fatima.
Haka badan nasoba na bi sameer muka tafi dama nima inada aikin dazanyi a office dina.
Washagari tun da safe na shiryah na bar gidan,dan kwata kwata banason wani abu ya hadani da mutanen gidan,saboda baraxanar cutar dasu da akemin a kowanne lokaci idan na kusancesu.
Ina dawowa na samu doctor maryam a falon suna magana da saleemah sai shagwaba takemata.
Har zan wuce sai kuma naji zuciyata ta kasa aminta da hakan,dawowa nayi zuwa cikin falon na zauna a kujerar datake facing dinta.
“Ina wuni doctor yah aiki”
Murmushin nan tayimin wanda yake sakani sukuni kafin ta ce,
“Lafiya kalau amma ban san sunanki ba gashi ninan fa dubaki nazoyi naga ya jikinnaki amma saleemah takecemin kin fita aiki”
Sunkuyar da kaina nayi kafin nace,
“Sunana sameemah”
Jin tayi shirune yasa na dago kaina dan ganin lafiya,amma sainaga tana ta maimaita sunan a bakinta kaaman mai son tuna wani abu.
“Ayyah to yah jikinnaki da fatan da sauki ko,amma da kin dan huta a gida ki na kwana biyune kafin ki fara yin wani abu mai bukatar motsa jiki sosai”
“Ahah ba komai naji sauki sosai ai babu matsala”
“Toh shikenan haka akeso ,ni bari natafi gida dama na tashi a aikin,saidai ina saka ran ganin ziyararki zuwa wajena kinji”
Daga mata kai nayi ina murmushi,dan harga allah inason na zauna da matar bansan mai yasaba.
Da zata tafi ma har waje muka raka ta nida saleemah tana kara tunamin na kawo mata ziyara.
Motarta tana kulewa a wajen saleemah taja tsuka tareda cewa.
“Aikin banza mutum yayi ta kalan dangi,an mallakemin uwa kanwar mahaifiyar tawama so suke a mallaketa”
“Ke saleemah ya isheki haka idan ba so kike kisake cin na jaki ba kumadu,dan wallahi rashin mutuncinki yafara isata,kibarni naji da halin danake cikima ya isheni”
Saurin wucewa dakinta tayi tana magana dan bata yi shiruba duk da tsorone kwance a kan fuskarta.
Ina shiga daki na cire kayana nayi wanka kafin na fito domin neman abinda zan saka a cikina,jinayi an rungemeni ta baya ina dubawa naga farouq ne .
“I miss you ummah,yajikinki daddy ne yace bakida lafiya dana tashi da safe ina neman ki zan tafi makaranta,yau ma kuma daddy yace karna dameki kina bacci”
“Uhm bana da lafiya amma naji sauki,nima ina kewarka farouq”
Murmushi yasakeyi na jin dadi,jin nace ina kewarsa nima,kitchen din muka shigs tare yana ta min surutu,duk da ban kulashiba amma ina sauraronsa,kuma nayi kewarsa sosai yini daya kawai.
Tare muka ci abinci kaman yamda muka saba,kana muka cigaba da kallo.
Bayan isha ina zaune farouq kuma yayi bacci a gefena sai ga sameer ya turo kofar ya shigo,zama yayi a drawer dake gefena ta gadon kafin yace cikin muryah mai dan kauri.
“Ya jikinnaki sameemah”
“Da sauki sosai”
“Aha mashaallah,abinda yake damunki yana damuna kasancewar bansan menebe ba,ita kanta doctor maryam tacemin batasan me yake damunkiba,ina sonki sosai shiyasa nakasa kauda maganar a cikin raina”
“Kayi hakuri”
“Bazancen hakuri bane saboda ba abinda kikayimin,kuma a yanda nake gani wani abune yake damunki wanda bazaki iya fadaba,kuma hakan yana damunki sosai,nikuma inshaallah sai nagano ko mai nene”
Saurin kallon sa nayi jin lafazin daya fito daga bakinsa,shima kallonnawa yake kafin ya tashi ya bar dakin,hannu na mika da niyyar kiransa sai kuma na fasa yin hakan,domin maganar tawa ba abinda zata rage tunda yai wannan kudirin a ransa.
Da tunanin hakan na gama aikin danakeyi na kwanta.
Yau nayi sa’a mutanennawa basuzo magana dani ba amma kuma wani abin da shima tashin hakalinne yah bayyano a daren,muryar wasu mutane da ba ta yan gidan bace ta doki dodon kunnena da tsakar daren.
Saurin tashi nayi na nufi hanyar fita daga dakin,ina bude kofar naji wani abu kaina dimmm,rike wajen nayi ina kallon mai aikata hakan,kafin nayi yunkuri naji wani yah fisgo gashina zuwa cikin falon,dayanne yafito da farouq a hannunsa sai kuka yake.
Raina ne yabaci ganin yaro bai musu komaiba amma suka yi masa wannan rikon.
Gefena na kalla inda sukayiwa sameer duka jikinsa yana zubar da jini amma hakan bai sa yah kwanta ba,saleemah kuwa sai kuka take ta rungume zuhra a kirjinta.
Kallonsu nayi cikin bacin rai nace,
“Me kuke bukata kukayi musu irin wannan dukan”
“Hhhhhhh lallai bakida kunya,har zaki tambati mai ya muke bukata,toh matsayinsa muke son yah rasa ta hanyar kawar dashi daga duniyar nan,sai musamu biyan bukata”
Wanda yake rike da farouq ne ya wanka masa mari saboda ya damesu da kuka,saurin tashi na yi na fizge daga wanda ya rike min gashi na daga shi na bugashi da akan tikes din,saida kansa yah tsage,jini na ne nakejin yana kara gudu acikin jikina da alamun karfina ma yafi na dadai mutane.
Kama wuyan wanda ya rike farouq din nayi na dagashi sama ina kallon cikin idonsa,jikinsa ne yafara karkarwa ga dukkna alamu yah kalli abinda yake cikin kwayar idona,jefar dashi nayi da karfi a kasa ko motsi bayyiba yah suma.
Wanda yake bayan saleemah ne yah kwada mata bindigar dake hannunsa dayaga ina nufo inda yake,riko wuyansa nayi ina magana cikin bacin rai da muryar da tasha banban da tawa.
“Mai ta aikata maka ka cutar da ita,mai yasa kuka kasance masu cutarwa iyee”
Matse makogarsnsa nayi da karfi,saida naga yadaina motsi kafin na zefar dashi,idona ne ya sauka akan wanda yake rike da sameer,da alama kuma shine shugabansu.
Tunkarar inda yake nayi,duk ya saitani da bindiga da kuma yimin alamar kar na kariso hakaan baiyyi tasiri a zuciyata,dan a lokacin kallonsa nake a matsayin wanda zai hallaka masoyina,kuma zan iya yin komai domin cetarsa saidai idan na gaza.
Maida bindigar yayi kan wuyan sameer din ganin ni bandamu da nawa rayuwarba,ya kuwa yi sa’a domin tsayawa nayi cak ina kollonsa da jajayen idanuwana,
“Koda ka kasheshi baxaka fita daga gidannan da numfashinka ba dan haka ka mika wuya tun ina cikin yanayin yi maka afuwa”
Daga gani gargadina bai shiga cikin kunnensa saima kokarin sai ta bindigar da yayi a wuyan sameer din,………,karar bindiga ce ta amsa kuwwa adakin tassssssss.

Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150

Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.

????Sadi-Sakhna________✍????????

(¯’•.¸,¤°’✿.。.:քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ.:。.✿’°¤,¸.•‘¯)

????•°• WASA FARIN GIRKI •°•???? {cigaban gidan gandu}

????35~36????

Firgicine ya cikani da tunanin kar ya kashemin yah sameer shikenan,saidai dana daga idona sainaga razanar da take kan idon sameer bata halin ciwo bace,da alamun ni yake kallo.
Inda yake kallon nima na bi da nawa idon,sai a lokacin naga ashe kan kirjina bullet din ya Saita na dama.
Mayar da kallona nayi kansa cikin ajiyar zuciya ganin a kaina abin ya sauka,saidai hakan dayayi yah nuna baya son nayi masa afuwar kenan.
Zefar da bindigar hannunsa yayi yana zagayani yana cewa,
“Well well ki sumar min da yara kina tunanin zan barki haka,da alamun dai soja yaje yah auro mai kamar maza,ga shikuma ita mutuwar tsaye take yi,gaskiya ta cika sojan”
Lokacin daya gama juyawar ya dawo dabana ne na damki wuyansa ina murmushi kafin nace,
“Ba suman tsaye ba dai fakon tsaye nakeyi,da alamun kaine zakayi mutuwar tsayen,”
Har nayi niyyar kafa masa hakorina sai kuma na matsar da bakina,amma duk da haka dai na yakeshi da farcena akan wuyansa,danaga jini ya fito da alamun farcena ya garwaya da jininsa sai kawai na wanka masa mari shima yah fadi.
Duk abinda ya faru akan idon sameer wanda shikadaine kawai bai suma ba a falon,farouq na dauka da zuhra a kafadata nayi dakina da sauri jin karar shigowar sojoji,da alamun karar bindigar ne yajawo hankalin su.
Bansan ya aka kareba ina jin dai sanda aka suka shigo suna ta magana,nikuma na kwantar da zuhra kenan,sameer ne ya shigo cikin dakinnawa da sauri muna kallon juna,karisowa yayi har inda nake ya kama kafaduna tareda yage rigar wajen da mutumin yah harbeni,wajen ya koma ya hade amma ba sosai ba saboda bullet din yana ciki,dole saina nutsu kafin na cire.
“Miye hakan yake nufi iyee,yakamata kizo mu tafi asibiti”
“Ahah niba asibitin da zanje kuma ina rokonka karka fadawa kowa ni aka harba,hakan ba komai zai haifarba sai matsala na rokeka”
“Yanzu kina nufin nayi shiru kenan duk da abinda nagani?,shikuma wannan ciwon ki kwana dashi a haka,kuma kina tunanin sai nayi yanda kikace”
“Ciwona ba matsala bace zuwa gobema bazaka ganshi ba amma idan ka fadamusu abin bazai tsaya iyah gobeba,mutumin daya harbeni kuwa ku barshi yah tafi kawai ,da kansa ma zai mutu nan da kwana uku,idan kuma baka yadda ba ka biyoni bandaki ka gani”
Babu yanda na iya haka na jashi badakin domin nuna masa hujja,saboda nasan taurin kansa zai iya zuwa yah fada,dan haka na kwammaci shikadai yasan ya nake da duk mutanen barrack dinnan su sani.
Almakashi na dakko na saka a wajen ciwon yana kallo na burkulo bullet din kafin na saka hannuna na fitar dashi na ajiye,ina gama fitarwa na ajiyeshi a sink din da ruwa yake fita.
Wajen kuwa kaman jira yake yafara hadewa da kansa.
Dakko bullet din nayi daya wanke da ruwa tasss na mikawa sameer tareda cewa,
“Nasan zasu bukaci ganin bullet din koda kuwa kacemusu a jikin bango yake,dan haka gashi,yanzu ka gane mai nake nufi,idan kacemusu a jikina yake zasuce ina ciwon yake sannan a wane asibitin nake,toh banida wannan amsar shiyasa na bukaci kayi shiru please”
Hannunsa yakai inda na cire bullet din yana dannawa maimakon ya karbi bullet din a Hannun a DA nake mika masa,
“Har yanzu bazaki fadamin komai akan abinda yake damunkiba duk da wanda idona yaganemin,saima kokarin rufe bakina da kikeyi,ina kallon yanda idonki yasanja kala,sanann kuma kinyi kokarin cizonsa a wuyah sai kuma kika fasa kika yankeshi da farce mai hakan yake nufi?”
“Nayi niyyar zuke jininsane amma kuma Akwai dalilin dayasa na fasa kawai na saka masa guba a cikin jininsa kawai,duk da haka kuma banason ka tambayeni mai yah faru dan bazan iyah fadamaka ba,sannan kuma ka dunga nesan kanka daga gareni tunda kaga illar danake dashi ga rayuwarka,komai dazai fito daga jikina hatsarine yayi gauraya da jikin mutum har ma da sauran halittu,please kadunga yin nesa dani sameer idan kana so ka rayu ko domin yayanka ma”
Daga haka na barshi a bandakin na dawo dakin bayan na damka masa bullet din a hannunsa,shima fitowa yayi yah fice ya bar dakin zuwa waje.
Da safe danaje dakin saleemah bacci na sameta tanayi haikan.
Kwantar da zuhrah nayi a gefenta naje wajen kayanta domin na saka mata,tunda banida kayanta a wajena kaman farouq.
Ina cikin saka mata wando saleemah ta tashi,kalonmu take dason tunowa mai ya faru,daga gani ta tuna abinda yah faru daren jiyan daga yanda ta razana,karisowa wajen danake tayi da sauri ta dauki zuhra ta kankame a jikinta,nima ganin hakanne yasa na juya domin fita daga dakin.
Can kasan makoshinta tace,”nagode sosai ta kulamin da y’ay’a na da kikeyi”
“Basai kin him in godiya ba hakkina nne nima na kare iyalina indai ina da damar hakan,allah ya tsare gaba”
“Ameen ya Allah “
Daga haka nabar dakin na nufi nawa domin shirya farouq zuwa makaranta,saidai yanda jikinsa yake rawane yasa na cire masa kayan inyaso gobe sai yaje idan hankalinsa yadawo jikinsa.
Zaman gidanne ya isheni saboda yanzu na saba da zuwa aiki,saidai gidan dole yana bukatar mai dan lafiya,saboda saleemah tana daki yini tayi jikinta yana rawa,ga zazzabin da takeyi kumadu.
Can wajen rana ina kitchen sameer ya shigo da alama har sannan a wajen caae din suke,kitchen din yah shi go tareda kama hannuna yana kallon farcena,nima kallon sa nake da alamar mai ya faru,saida yagama kallon dan kansa kafin yah dago ya kalli idanuwana.
“Menene a jikin farcenki sameemah,jiya da daddare ina kallon lokacin da kika yanki mutuminnan a wuyansa,yanzu muna masa bincike mukaji yana ihu amma ba na horon da muke masaba sai dan abinda yake wuyansa. Mun kaishi wajen likitoci sun ce cell din cikin jijiyoyinsa ne suke mutuwa a kowanne bayan sakanni,wajen yayi baki kuma tafiya yake yama mamaye dukkan ilahirin jikinsa”
Sunkuyar da kaina nayi dan bansan mai zance masa ba,gashi nasan idan ba fada masa nayi ba zai barni ba.
“Nima bans an mai yake damuna ba haka na tashi na ganni,ummah ma tasani kafin ta rasu ita ce ta nunamin yanda zan boye halittata daga idon mutane ,duk abinda ya cijeni ko kuma ni na cijeshi ko kuma wani bangare na jikina yah shafi cikin jininsa to zai rasa ransa,sannnan duk ciwon danaji baya minti daya yake warkewa”
Zare ido sameer yayi shikadai yana nazarin wani abu wanda banida masaniya akai,dan murmushi nayi kafin nace,
“Yah sameer kana tsoro kar na halaka ku ko,wannan abin shikadai nake gudu a rayuwata sannna shine abinda yakasance tamkar bakar razana a gareni wanda nake kwana kuma nake tashi da shi.ko yaushe tunanina shine taya zan nesanta masoyana daga sharrina,a kokarin hakan dole sai na zamo Wacce suka fi tsana saboda munanan halinta,ta hakane kawai zasu kauracemin koh ban umarcesu da hakan ba. Burina shine kayi nesa dani yah sameer abinda kake tunanin bazai taba yiyuwa,bazan iya soyayya dakai ba mu yi rayuwar aure har mu haifi yara. Haka nake kuma bazan iya sanja hakanba koda ina da ra’ayin hakan,saidai ina so kasani bazan iya cutar da ahalinka ba koda inada bukatar hakan,akan haka na kwammaci na kasance cikin azabtarwarsu ko kuma su daukeni daga rayuwarnan kaman yamda suke da bukata”
Hawayene yake zuba daga idanuwana wanda kwannan nakasa gane kaina,abu kadan sai nayi kuka inda ina gaban yah sameer sai naji ina rauni. Abinda banyi tsammani bane ya faru,wato rumgumeni ya sameer yayi sosai a jikinsa kaman zai maidani cikinsa,nima hannuna na saka a bayansa na jagayeshi a jikinnawa kaman wata zata kwacemin shi.
Cigaba nayi da kukana a hankali ina jin yar nutsuwa tana shiga cikin zuciyata,shidin haskene a gareni da banaso nayi nesa dashi sai dai haakan ya zamemin dole.
Cikin muryar damuwa yacemin,
“Suwaye suke da niyyar daukeki daga gareni sameemah,kin kasa bani wannan amsar meysa haka?”
“Bazan iya baka amsar ba koda ina da bukata nima kayi hakuri”
Cireni yayi daga jikinsa zai share hawayen dayake fuskata,saurin rike hannunsa nayi danaga ciwo a hannun wanda mutanen suka ji masa,jijjiga kai nayi ,
“Ahah karka kai hannunka fuskata ,duk da ban taba gwadawa ba ina tsoron hawayena yayi maka illah yah sameer,bazan iya yafewa kaina hakanba idan ya faru”
Murmushin ya fahimta yayi min kafin yace,
“Yanzu kenan idan kikaji ciwo komawa yake ya dinke da kansa? “
Murmushi nayi masa kafin na dauki wukar na yanka a tafin hannuna,har yakai hannunsa zai rike sai kuma wajen ya koma yanda yake tamkar ban yanka ba.
Daga haka muka cigaba da hira ,duk da kowa zukatansu a cunkune yake da zullumi iri iri amma hakan bai hana mun turasu kasan zuciyoyinmu ba mun rungumi kaddara.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button