NOVELSWASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan kamar awa d’aya kowa yah hallara a falon,har da matan da nayi musu gargadi farkon zuwa na gidan sameer,ashe suma kannen mahaifiyata ne wanda suka uba daya,kallona suke da alamar sun ganeni,yayinda nima din nake kallon su din.
Alhaji musa ne yafara gyaran murya kafin yace,,
Toh hakika wannan abin mamakine,ashe muna zaune da y’ar mu har tana kishi da tamu y’ar amma bamu saniba said yanzu,babu abinda zumuce said yiwa allah godiya.
Sannna kuma zamuso jin ya hakan ta kansace kafin asan yanda za’ayi”
Nidai banyi magana ba har yah sameer yagama basu labarin rayuwata a gidan gandu tundaga farko har karshe,kama daga labarin zamana a palastine da kuma zamana a kasar Brazil,har da yanda aka sha fama dani a akan aurensa na ki amincewa,siada aka cemin wasiyyar mahaifiyata ne tukunna.
Abu d’aya ne naji dadinsa daya boye sirrina na halittata bai gada ba,hakan yayimin dadi sosai,kuma yasa nakara yarda da sameer fiyeda yarda da nayi masa a baya.
Lokacin daya gama bada labarina babu wanda bai yi ta’ajjubiba,hajiya maryam kam harda kukanta wiwi wai ta tausayamin,nidai ban dau tausayin a matsayi sosai ba tunda ta barni ta tafi.
“Hakika gaskiya munyi mamakin yanda ta sameemah ta rayu a wajenku,sannan kuma bamu da bakin godiya akan hakan,dolema said munyi shiri munje har wajen Malam umaru munyi masa godiya bisa namijjn kokarin dayayi akan rayuwar ita sameemah.
Duk nan mu yan uwantane ga hajiya fatima mamar saleemah,itance yayar mahaifiyar ta wanda suke uwa daya uba daya,sai hakiya delu kanwarsu ce itama ,saikuma hajiya bebi itakuma kanwar mahaifinki ce wanda shikuma amininnane da muka tashi tareda har girma,zamane ya kaishi garin baushi a lokacin baya.
Toh haka kaima sameer dama kai dan gidane sannan faruwar hakaan tasa munakara yarda dakuma son jawoka cikin danginmu,kuma gashi kana auren wa da kanwa.
Dama saleemah tun suna yara ta girmi sameemah da shekara hudu,dan haka dama yayrtace,to a yanayin zamansu cikin gidanka ma tarigata shiga,dan haka idan wata matsala ta faru kar wani yaji kunyar zuwa yah tunkatemu a cikinku.
Abinda akayi a baya kuma a sai a yayyafe,musamman ke sameemah da na nuna sonkai akan lamuranki har hajiya fatima tana nusar dani,ashe bansaniba kedin Y’a tace kema,wanda zan iya komai dan samun farin cikin ki.
Dan lokacin da maryam ta zo gida duk jikinta faca faca babu wanda baiji tsoroba ,mun tambayeta tace ta bada ke ga wasu Wanda ta yarda dasu,tun daga wannnan duk tambayar da mukayi mata bata bada amsa,idan muka takurata ma said ta birkice sai an dade ta dawo hayyacinta.
Tun daga wannan yanayinta ya sauya,kullum tana zaune ita kadai,bayan an debi shekarune ta ce zata koma karo karatu India,ban hanataba saboda a ganina zata samu nutsuwa,daga haka ta tafi karo karatu,da ta gama ma tayi zmanta a can tana aiki,sai yanzu allah yayi dawowarta da rabon zata gamu da y’ar ne ashe.
Daga haka aka fara hira kowa yana fadin albakrkacin bakinsa,nidai shiru nayi amma a labarin da aka baya akwai abinda babu shi a ciki,tambaya nayi wa akaina cewa,toh ina mahaifina,me mahaifiyata ta gani da har ta zabi a rabuwa dani a lokacin danake da kananan shekaru,sanann me yasa take shiga firgicin idan anyi mata maganar meya faru? Ko ita ma bazata iya bada labarin halin da take cikiba kaman yanda nima bazan iya bayarda labarin ba,kenan haka take yamda nake nima?,kai anya kuwa?.
Wannan amsoshin banida su sanann bansan waye zai bani amsoshinsu ba a halin yanzu,kuma koma menene ba shakka suna da alaka da yanyin halittata danake ganin ta sha banban da ta sauran bil’adama.
Sallah aka fara kira ta azahar inda kowa yah tashi domin yin sallah,bin hajiya maryam nayi a baya wanda take a matsayin umma ta yanzu,domin naga shin itama bata iya sallah kamanni ko kuma ita tanayi.
Dakin babu kowa sai motsin ruwa da alama alwala takeyi,zama nayi a kan gado har ta fito murmushi kawai tayi min da muka hada ido nima na mayar mata.
Hijabinta ta gyara ta tada sallah har ta gama ta fara addu’a ina zaune,mamaki abin yaban ganin tana sallah ta normal babu abinda ya sameta,nikuma bana iyaww,to ni da ita ba iri daya bane,wa na iyo kenan idan ba ita bace.
Juyawa tayi ta kalleni,saida tayi magana kafin hankalina ya koma kanta.
“Ina sallah zakiyi,kije kiyi alwalar mana ai na idar”
Uhm kawai nace nasake zamana,
“Period kike kenan?”
“Uhm “
Ina jin dar dar na fada mata hakan,saboda kar naje ta ganoni kaman yanda hajiyah fatima tayimin.
Daga haka dagani har ita babu wanda yasake cewa komai har lokacin tafiya gida yayi.
Yah sameer ne yazo daukarmu amma sai alhaji musa ya dagatar dashi ta hanyar cewa,
“Major in a ga da ka barta taje gidan ummah koda sati d’aya tayi kafin ta dawo dakinta,hakan ina ga zaisa su fahimci junansu koda kadanne”
Jijjiga kai yayi alamar ya yarda da maganar alhaji musan,amma nikam ban so hakan ba saboda banason zama sa mutumin da zai dunga ganin mai nakeyi,shiyasa naji dadi da dakina nikadai nasan mai nake aikatawa a gidan sameer.
Murmushi hajiya maryam tayi alama taji dadin hakan sosai,dan daga gani tana so na dunga zama kusada ita.
Hakan kuwa akayi ina zuwa gida na hada kayana da safe yah sameer ya ajiyeni a kofar gidan hajiya maryam,farouq kuka ya dunga yi akam sai mun tafi tareda shi,hakan kuwa akayi inyaso sai driver ya dunga zuwa yana daukarsa a can,nima dama bazan ji dadin barshi din ba,saboda mun saba kwana tare.
Lokacin danazo fitowa ciki ciki Saleemah tayumin a dawo lafiya tareda cewa na gaida hajiya maryam,nima daga mata kai kawai nayi.
Ina Shiga Gidan na samesu a zaune,yarinyar da muka samu a gidanne rannan tazo da gudu ta karbi akwatin hannuna tareda cewa,
“Aunty Sannu da zuwa dama ummee tace zakizo ki zauna damu”
Murmushi nayi mata tareda cewa,
“Eh hakane amma sati d’aya zanyi kawai”
“Ayyah duk da haka naji dadi Sosai”
“Toh humairah kai mata akwatin mana sai ki dawo ko”
Saurin jan akwatin tayi farouq yana binta a baya.
“Ina kwana ummee”
Nafada domin kama sunan da yarinyar da ta kira da humaira take fada mata.
“Lafiya kalau sameemah,ya mijinki da kuma yar uwarki”
“Duk lafiyar su kalau”
“Mashaallah barkan ki da zuwa to,bari na gama kawo abincin dama yanzu na gama”
Binta nayi kitchen din domin dakkowa abincin,hira muka dan farayi saidai duk akan zaman da tayi dasu baba umaru take fadamin,wani lokacin idan ta tambayeni na bata amsa,wani kuma na daga kai kawai,dan harga allah nakasa sakewa da itah duk da ina da bukatar hakan.
Hakadai zamannamu ya cigaba da tafiya,har nayi kwana uku a gidan,zuwa yanzu nafara sakewa da ita muyi hira,saidai har yanzu bata fadi abinda nakeson tayi magana akaiba shine mahaifina,nikuma na kasa tambayarta hakan, duk da shine abinda ya tsaya min a raina.
Ranar ta hudu danayi a gidan muna zaune muna kallo ,duk saina jini wani iri saboda bana zuwa wajen aiki,kiran sallah ne ya doki cikin kunnena,humairah ce ta shiga dakinta domin yin sallah,ummee ce take kallona taga ko zan tashi amma babu alamar yin hakan,
“Sameemah har yanzu kina period ne?”
“Eh ina yi”
“Bakiyi Kama da mai period ba sameemah,dan tun a farko na gano hakan amma na zubamiki ido kawai,meyake faruwa da bakya sallah kina matsayin musulma kuma hakan bai dameki ba,kina tunanin hakan zayyi miki kyau barekuma wanda kike tareda su,meyasa bakya sallah sameemah,sannan kuma bakiyu kama da wanda bata da ilimi ba,menene yake faruwa?”
“Akwai abinda yake faruwa ummee,saidai idan har zaki iyah fadamin ina mahaifina yake,sannan kuma manene yasa kika badani ga ummah,kuma meyasa kike firgicewa idan aka tambayeki mai yake faruwa,to nima zan iya fadamiki dalilin dayasa banayin sallah”
Lokacin danayi maganar mun kai wani lokaci amma babu wanda yayi magana a cikinmu,kowa yana zullumin abinda ke cikin zuciyarsa.
Tashi tayi cike da damuwa ta wuce dakinta,ina nan zaune humaira ta zo falon tana cemin naje ummeee tana kirana.
Ina Shiga na same ta a zaune da carbi a hannunta,gabana ne ya buga dan ba abinda nake tsoro ya carbi,tun horon da mu’allim yayimin dashi,tambaya nayiwa kaina cewa mai take shirin yimin dashi to.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button