NOVELSWASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150

Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.

????Sadi-Sakhna________✍????????

(¯’•.¸,¤°’✿.。.:քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ.:。.✿’°¤,¸.•‘¯)

????•°• WASA FARIN GIRKI •°•???? {cigaban gidan gandu}

????41~42????

????Hajiya maryam a madubin gani????

Auren soyayya mukayi da Abdul wahab ina sonsa yana sona,saidai abu dayane yake hadamu dashi shine kullum zancensa akam yanda zayyi kudi a dunga kwatancensa,ni kuma duk sands zai fadi haka sai na yi masa wa’azin akan yanemi zabin alkhairi,ban dauki abin amatsayin wani abuba saoboda a ganina idan har ya girma ko kuma allah ya xaunar masa da sana’arsa ta Engeneer to zai bari.
Saidai ashe abin ba haka yake ba.
Muna nan zaune yah samu nasara sa’anarsa ta bunkasa yazamana sai a tsallake manyan Engeneer azo wajensa neman wani abu ko aiki,abin yabani Mamaki da farko amma sai na dauka cewa iko ne na allah.
Kwanci tashi bayan shekarar uku da aure sai wasu kamfani suka kirashi aiki zuwa kasar india.
Da farko nayi zaton tare zamu tafi saboda naga aikin yana kawo masa kudi amma sai yace zamu koma garin bauchine da zama saboda zai saka kasuwamci ne a can.
Kasan cewar nasan aikinnasa tun daga farko sai vandamu sai nasan mai yake gudana a can kasar india ba.
Haka muka zauan yana zuwa akai akai amma daga baya sai zuwansa ya ragu.idan ban mantaba nayi barin ciki har sau biyu a can,kafin na samu cikin sameemah,amma kwata kawata bana tuna nayi barin sai yamzu,kumma dukkansu sai yazo nake barin kafin ya tafi,cikin sameemah ne har aka goyashi na haifeta bai saniba,lokacin dayazo tana da shekara kusan biyu sannan,dan har na yayeta ma.
Nayi farincikin zuwansa sannan nayi bakin cikin rashin zuwa wajena akan lokaci,koda badanni ba yakamata yazo yaga y’ar sa wadda yake da ita kwal a duniya.
Lokacin daya dawo sameemah kin amincewa tayi dashi saboda bata son mutane sosai inba wanda ta saba da suba,amma dayake yana zanta a jiki da kuma siya mata kayan wasa sai ta sake dashi a kwana uku,naji dadin hakan sosai ganin yanda yake janta ajiki kuma yake nuna mata so matuka.
A tsakanin zuwansa na sati biyu kusan kullum sai sun fita shida sameemah idan zasu dawo sai na gansu da kayan wasa ko kuma su minti da biscuit.
Abinda yasakani shiga firgici kuma bazan taba mantawa dashi ba matukar ina cikin hayyacina shine:
Wata rana muna zaune dashi sameemah na cinyata shikuma yana zaune a bakin gado muna hira,sai nace masa bari naje wajen hajara hira,tunda shi yacemin magana zayyi mai muhimmanci shida abokan business dinsa.
Daukar sameemah nayi muka fito,har munzo bakin kofar fita daga falonnawa naga tayimin fitsari duk da wayonta amma ta iya wannan tsiyar idan taso,dungerata nayi kafin na koma dakin domin dauko mata pant,abinda naji ne yasaka ni cikin firgici da tunanin anya kuwa ba mafarki nake ba ,
“Eh duk yanda muka tsara ya tafi,kuma munyi nasara jininnata yayi daidai da wadda kujerar mulkin take bukata,nidai burina shine idan kun karbeta ni kubarni na dawo kasata da zama,tunda na baku wacce zata maye gurbina,yakamata nadawo gida kar a fara zargina da aikin danakeyi,inason zaman aure kuma da matata da kuma rike kamfanina,y’ay’a ne nasan zan samu wasu nan gaba,tunda nabaku wata daga jinina wacce zata maye gurbina shikennan…………eh na bata abun ta cinye na tsawon kwana ukune sannan nakaita wajen da kukace din ma,abinda ya saura shine gobe zan bawa su muhiddeen ita su taho da ita,kuma ina so ku kuyi wani abu ta yanda za’a manta da ita a rayuwa,ya zama tamkar ba a haifeta ba kwata kwata…….”
Numfashina ne yake hawa sama sama har bansan lokacin dana kankame sameemah a jikina ba wacce nakejin za’a rabani da ita,rababwar da bata da maraba da kashe rayuwarta,dabara ce ta fadomin da sauri nayi hanyar dakin su hajara ina bugamusu kofa.
A lokacinne na basu sameemah halak malak kuma nace kar suyi abinda zai kawota garin baushi koda wasa.
Sunyi dani nazo mutafi saidai kuma a sanann bata rayuwata nake ba sai ta Y’a ta wacce nake da ita d’aya.
Ina Shiga dakin naji an shake wuyana da wani abu,maganar Abdulwahab nani yana cewa,
“Ina Kika kaimin Y’a ta,sannan miyasa kikaji abinda bai kamata kijiba a rayuwarki”
Fazge wuyana nayi na kalleshi cike da tsana nace,
“Natsaneka Abdulwahab,ka cutar dani sanann ka cutar da Y’a ta kwaya d’aya danan mallaka,saidai kasani burinka bazai cika akan taba,dan bazaka sake kallonta ba har abada,na kwammaci naga gawarta dana baka ita ka hallakar da ita kaman yanda kake akan hallakar”
Wata fizgowara yasake yimin,zuwa wannan lokacin yafita a cikin hayyacinsa,dan ina ganin sanda jini yake fita daga hancinsa da bakinsa,amma ko digon tausayinsa banjiba dan a lokacin babu abinda nake buri daya wuce naga gawarsa a kwance a gabana.
Shakeni yayi yana magana amma banajin abinda yake fada,da haka har jijinsa ya shika na samu na kwance,ina gani yana wani abu yana fita daga bakinsa baki marar dadin gani har ya mutu,wani irin kara naji a cikin kaina wadda tasani shiga firgici har na tsinci kaina a garinnan wajen yaya fatima bansan ya akayi ba,amma na kasa furta koda kalma daya data shafi Abdulwahab.
A tunanina na tsetar da sameemah daga sharrinsa ashe van saniba suntiga sun hada ruhinta da nasu,sun cigaba da cutar da ita a tsawon lokacinnna ba tareda sanin kowaba,allah sarki baiwar allah,sun zalunceta da yawa,allah ne kadai zai saka mata abinda ubanta yayimata………….”

????sameer a madubin gani????

Kuka ummeee take kaman ranta zai fita,duk dakin babu wanda baiyi kuka ba haka ya girgiza da al’amarinba,tabbas babu abinda ya gagari allah,kuma duk mai imani yaji labatin sai ya tausayawa rayuwar sameemah.
Hajiyah Fatima ce ta jawo ummee jikinta ita ma tana share nata hawayen a kan fuskarta.
Malaminne ya numfasa kafin yace,
“To yanzu tunda munji abinda yake faruwa aikin bazai dade ba za’a fara,saidai amma zai bada matujar wahala da kuma daukar lokaci,saboda sun riga da sun cakuda da jikinta da kuma gangar jikinta na tsawon lokaci,dan haka zamu dauki lokaci kafin mu rabata da abinda yake jikinta,idan aikin yayimin karfima sai munkaita wajen malamina tukunna,amma kafin sannan zamu fara dadai kokarinmu.
Daga haka ya sallami ummee tunda ta samu lafiya,baba umaru da alhaji musa kam basuce komai ba sai jinjina lamarin da sukeyi.
Komawa gida malamin yace muyi saidai mu dunga zuwa muna kallonta,duk lokacin da muka zo sanda yake tsaka dayimata magani haka zamu dunga jiyo ihunta da kuma karar wata irin dabba da takeyi.
Yau kimanin tsawon wata biyi kenan da kulle sameemah a gidan malamin,kullum sai na je dubota amma daga waje yake bada damar hangota kawai,saboda shiga wajen hatsarine sosai,koyaushe cikin saka magani ake,saboda hana wasu shedanun shiga jikinta,dan idan abin yayi yawa bazata iya daukaba.
Duk da munsan malamin yana kokari saidai kuma kunsan dan adam dason cigaba da gwada wani salon musamman idan wannan din babu cigaba.
Yauma hanyar gidan malamin na nufa,dan hanyar ta kasance ta bina ce a kkwace rana,a bakin gidan nayi parking na shiga,sallama nayi masa amma kuma babu alamar mutum a ciki,hanyar dakin sameemah na kalla wata zuciyar tana cemin naje wata kuma tana cemin na bari sai ya dawo.
Bin ra’ayin zuciyata nayi wanda ta mato akan san ganin masoyiyarta,a hankali nake tafiya zuciyata tana bugawa kadan kadan har na wuce inda muke tsayawa idan mun zo ganinta.
Kofar na tura na sameta a daure kaman ko yaushe,kayan jikinta da aka daureta dashi har ya sanza kala,ita kanta yanayinta harda fatar jikinta ya sauya,ta fita akan halittar jikin dan adam.
Duk da haka ban yi alamar zan tsaya daga karisawa izuwa gareta ba,dan hakan shine abinda zuciyata take ra’ayi .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button