NOVELSWASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

????sameemah a madubin gani????

Tun ranar dana gwada yin sallah na suma,dana tashi naji ni a wani yanayi daban,babu abinda zuciyata take buri sai cutar da duk wanda idona ya sauka akansa,kullum zugani ake akan na bar wajen mutane na tafi inda nafi dacewa dashi.
Lokacin da wani mutumi ya zubamin wani abu naji wani duhu ya lullubeni dan dama yaushe nasaba da kasancewa cikin duhun.
Ta shi nayi na samu jikina daure da wani abu kaman zare,amma duk yunkurin dazan yi nayi amma na kasa tsinkewa daga zaren,sai kuma na kula da yanayin siffata yana sauyawa zuwa wata kala daban irin ta mutanen danake gani a cikin mafarkina.
Duk da bansan wane lokaci nake wajenba amma nasan na dad’e a jikin wannan zaren danan tsana a rayuwata,da kuma mutumin dayake zuwa yama konamin jikina da wani ruwa.
Ina jin Karar bugawar zuciyoyi suna zuwa kusada inda nake,amma duk sanda wannan zuciyar tazo ina jin kalar nata sautin yasha banban dana sauran,duk da cewa suma sauran zuciyoyin inaso naga sun matso kusada ni amma nafi burin wannan zuciyar ta matso kusadani,kodan na fita daga kangin abinda suka zagayeni.
Shikadaine idan yazo nakan samu kaina da dagawa yana kallonsa,saidsi babu yanda na iya haka nake ganinsa ya juya ya tafi,duk da inason yah matso inda nake amma nafisan yakasance a nesa saboda kar na cutar dashi.
A inda nake ɗaure ina jin karar takun sawun wani ruhi yana tunkarowa inda nake,dan tun daga nesa nake iyah jiyo karnin jininsa yana dukan hancina.
Tun daga bugawar zuciyarsa na tabbatar wannan ruhinne wanda yake tamkar haske a baƙar duniyata,ba abinda zuciyata take muradi sai kasancewa dashi a kowanne lokaci.
Duk da nisanta dashi yana cutar dani amma babu yanda zanyi,domin idan na kasance mai yi wa ruhin soyayyar gaskiya,toh bazan so ifiritan ta suje jikina su cutar dashi ba.
Hannuna na kalla wanda farcen yayi tsawo yana zubar da jini,ga kuma gashin kaina dayayyi wani tsayi kaman na sabuwar fatalwa,ɗaga idona nayi na kalli ruhin daya shigo ɗakin,tun daga idonsa ya nuna bayason kallona a wannan halin,saidai babu yanda zayyi,domin hakan shine ƙaddarata,wanda bana tunanin zai iyah cika alƙwarin daya ɗauka na fiddani a cikin wannan halin.
Saboda duk maganar da suke ina jinsu,yanda yake fadar zai iya komai duk wahalar sa idan har zan samu lafiya matukar bai sabawa mahaliccinsaba.
Dawowa nayi daga tunanin dana tafi ganin ya wuce wani layi a gabana yana shirin karisowa daf da inda nake,kallonsa nake da alamar gargadi wanda nasan ya fahimci mai nake nufi,amma kuma bashida niyyar juyawa da baya.
Hannunsa yasaka a kunkumina tareda jawoni zuwa jikinsa ya kankameni,a duj tsawon zamana a wsjen yau ne kadai najj wani abu wai ita nutsuwa ta jiyarci jikina,sannan bakin dana dulmiye a ciki yafara wsshewa ina kallon hasken daya zomin dashi a gabana,har na samu kaina dason yi masa magana saboda abinda naji yana cewa,
“Kiyafemin sameemah,koda kowa zai ji tsoron zuwa inda kike ni bai kamata na yi hakanba,ko umma idan tana kallo bazata yafeminba saboda nima na taak rawa wajen zamowarki haka dana kasa rike ragamar kulada ke wsnda aka bani.
Sameemah inasonki sosai,har yanzu ban fidda ran zaki dawo gareni muyi rayuwar da muke da burin yi ba,kiyi yaki da abinda yake jikin ki sameemah,karki bari suyi galaba akanki,ke jarumace nikaina nasani matata jarumace,zaki iya sameemah kituna muna jiranki zamu iya komai dan gsnin kin fita a wannan kangin da izinin allah,amma zaman ki a wajennan yana cin zuciyata,komai nafara idan na tuno inda kike bana iyawa ……………”
“Yyyyyyaa…..sssammmeerrr”.
Saurin dagowa yayi ya kalleni dayaga nayi magana,abinda bai taba tsammaniba,duk da maganar bata fita sosai ba kasancewar na dade banyi ba amma nasan yagane abinda na fada ,nima naji dadin hakan dana ga yaji sunansa dana ambata.
Hawaye naga ya ciko a idonsa sai kuma naga yana murmushi,kai na yarike yasake rungumeni a jikinsa yana fashewa da kuka,dago kai na nayi kafin na dage nace,
“Wanke jiki datti banaso sune suke so ni banaso,ka wankemin datti banaso ba dadi datti jikina da jini”
Saurin kallon jikina yayi da alamun ya gane abinda nace,tsugunnawa yayi wajen kafafuna inda jinin daya fito daga jikina ya daskare babu dadin gani,duk da banajin komai sai karnin jinin mutane amma nasan akwai wari a tattare dani.
Sautin wata zuciyar naji tana matsowa inda nake,wacce take saka firgici a cikin rai na,gurgana nin danayi ne yasaka sameer dagowa ya kalli bakin kofar,tashi yayi tareda tsayawa a gabana yana kallon malamin.
“Meyasa kashigo har nan wajen sameer,bakasan hadarin hakan ba ko?”
“Ba abinda zai faru malam,saida ina ga yakamata a tsaftace mata jikinta,dan tace dattin yana damunta,ga kuma al’ada da tayi a jikinta”
“Yaushe tayi maka magana da har ta fadi hakan,idan magana zata fito daga bakinta to ba yaren dazaka gane takeba,sunayine dan a kuncesu”
“Amma malam da hausa tayi magana,kuma tace wai kazanta suke so ita bata so,kuma suna kara karfi a hakan”
Shiru malamin yayi kaman mai zullumi,nikuwa fargabata kar ya kori sameer daga inda nake ,ajiyar zuciya nayi danaji yace bari ya nuna mana bandaki,amma sai an zagaye dakin tukunna da tsari.
Juyowa sameer yayi tareda since igiyar datake hannuna,yi nayi kaman zan fadi naji ya rike ni gam a kirjinsa ko kyankyamin bayaji.
Irin daukar amarya yayimin tareda nufar dakin da aka nuna masa,a jiyeni yayi a gaban wani baban baho wanda yake cike da ruwa.
Kayan jikina yafara cirewa a hankali,har yagama rabasu da jikina.
Wani cup ya dauka a gefe yana debo ruwan yana wanke abinda yayi cinyoyina zuwa kasa.
Lumshe idona nayi ina jin azabar da ruwan yakeyi akan fatata saboda na hadashi da wani abin,da kuma sanyin da hannunsa yake haifarwa akan fata ta yana maye gurbin zafin.
Bayan yagama wanke dattinne ya daukeni zai sakani a cikin ruwan,hannunsa na rike ina rokonsa da idanuwana,murmushi yayi kafin yace,
“Kiyi hakuri kinji,babu abinda zai faru kisaka hakan a cikin ranki,komai zai zo da sauki,ina tareda ke kinji”
Sauke ajiyar zuciya nayi kamin yasakani a cikin ruwan,ina kallon yanda yake kallon jikina amma haka ya kawar da duk abinda yake cikin ransa ya wanke ni tass.
Wani kaya ya dauKa masu duhu ya sakamin.doguwar rigace amma tana da laushi sosai.
Motsin shigowar wani naji hakan yasa na matsa jikinsa da sauri ,shima ya rungumeni yayi sosai wanda hakan yasa naji nutsuwa a cikin raina.

Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150

Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.

????Sadi-Sakhna________✍????????

(¯’•.¸,¤°’✿.。.:քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ.:。.✿’°¤,¸.•‘¯)

????•°• WASA FARIN GIRKI •°•???? {cigaban gidan gandu}

????43~44????

????sameer a madubin gani????

Tun lokacin da sameemah ta fada cikin hali na rashin lafiya ban taba jin tsoronta koda da na minti daya bane,saidai zamanta a wajen babu mutane a kusada ita yana cimin tuwo a kwarya,musamman kazantar wajen.
Bayan na gama yi mata wankan na saka mata kaya kamanta har ya fara dan dawowa duk da kowaye ya kalleta yasan ba lafiyar ta kalau ba,ita ma kanta naga taji dadin tsaftace jikin.
Karar shigowar mutunne yasa ta manne a jikina kaman wanda za’a yankata,har yaron malam din ya kawo ruwan magani ya ajiye amma bata dago idonta ba.
Kawowa nayi kusan fuskarta amma ta hade rai tareda kawar da baki,nima bata fuskar nayi tareda nuna mata da gaske nakeyi,saida taga ina kokarin cireta daga jikina kafin tayi saurin kaiwa ruwan maganin bakinta,shima tana hawaye da kuma cuno baki.
Kurba biyu tayi ta mayar da kanta kan kirjina tayi shiru.
Lokacin danazo tafiya rikeni tayi tana gunzin kuka kamar ana zare ranta,kallon malamin nayi nima zuciyata a karye,dan har ga allah banason barinta nima,sunkuyar da kai yayi kafin yace,
“To gaskiya sameer ban san ya zacayi ba amma fitarta waje a kwai hadari sosai,baga iyah mutane ba harda ita kanta,saboda zamanta ananne yasa har take iya control din kanta wani lokacin,amma idan ta fita gaskiya rabata dasu ba abune mai sauki ba”
Nima kaina na fahimceshi,haka duk da zuciyata tana so amma na cireta daga jikina na fita da sauri,dan banason jin ihunta kuma tanayine danni ba dan kowaba.
Haka Har rayuwa ta sake daukar mu zuwa sati biyu,amma babu wani cigaba sosai,kullum ina zuwa na dubata nayi mata wanka sannan na bata magani saboda ni kaidaine take karba tasha a wajena batare da anyi mata dole ba.
Idan ka ganta fes da ita amma wani lokacin sai fatar jikinta tayi duhu gashinta ya tashi,to a lokqcin ne muke gane cewa ba ita bace.
Kowa hankalin sa a tashe yake,saboda yanayin da sameemah take ciki,har saleemah ma takan damu tazo ta ganta,idan tazo tayi da kuka kenan tana lekata,ummee kuwa ba’a magana,dan in ka ganta ta bar kan sallaya to wani uzurin zatayi.
Ranar ina office malam ya kirani akan wata magana,da sauri nabar abinda nake nayi hanyar gidansa.
Ina zuwa na tarar su baba umaru da su ummee a zaune da alama kowa yana wajen ni ake jira.
Kallona yayi tareda cewa,
“Wato abinda yake faruwa sameer shine,malamina ya dawo daga sudan jiya,wanda nake da niyyar turaku wajensa,saidai ba anan yake zaune ba yana cikin kauyene,sannan fita da ita zuwa can akawai hadari sosai,zakuyi matukar kokarinku wajen ganin kuna tareda ita kafin a isa can din,kar ku bari ta bace muku ku rasata a jejin zuwa wajensa. Idan kukaje kuce nina turoku munyi magana dashi akan matsalar,inshaallah za ‘a samu dacewa da izinin allah,amma fah saikun kula sosai,karku bari a samu matsala idan ba hakaba kuma bazata taba warkewa ba sai wani tsananin ikon Allah”
Tunda mukaji yana wannan gargadin munsan ba abune mai saukiba,saidai munji mun gani inshaallah zamuyi da izinin allah.
Shirye shiryen tafiya wajen maganin muka fara,dani da ummee da alhaji musa da kuma baba umaru.
Muna shirin tafiyar ne wani labarin daban shima yazo mana wanda yasa muka daga tafiyar zuwa bayan kwana uku.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button