WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL
WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL
A ranar na fara yimana shirye shiryen kayan ita dai hajara kallona kawai takeyi,dan nasan idan zanyi shekara ina abu indai ba faɗamata nayiba bazata tambayeni ba.
Ranar tafiyarne na kaiwa iyah kayan sameer saboda yana zuwa makaranta shi,kuma ma yayi girma a tafi dashi gashi bamusan wajen ba muma tukunna.
Mun daɗe muna tafiyah a mota sai gamu a garin bauchin yakubu,hajara kam duk tah galabaita saboda jijjigar mota ,gashi dama koba mota amai takeyi inaga ta samu dalili.
Mai adaidaitah sahu muka ɗauka zuwa anguwar rail way inda tayi mana kwatancen gidan.
Shima kansa mai adaidaitan baisha wahala ba saboda gidan ba a lungu yake ba,kan hanyane inda kowa zai gane.
Kuɗin na bashi kafin na ranƙwafo da hajara zuwa jikina muka fitah zuwa bakin gidan.
Duba takardar ta take hannuna nakeyi sannan kuma ina sake duba gidan,”anya kuwa shine?” nafaɗa a raina,dan gaskiyah giraman gidan bayyi kama da wanda za’a gayyaci kamanni cikinsaba.
Ganin ba sarki sai allah ga kuma matata tana bukatar taimako ne yasa kawai nayi shahada da tunkari kofar gidan,saboda mun riga mun zo kuma ai babu batu komawa.
Wasu inyamuraine masu kayan sojoji suka buɗe mana kofar gidan,saboda tsabar tsoro bansan lokacin dana mika masa takardar hannu na ba,saboda dama tace idan nazo nabawa ɗayah daga cikinsu,zasu barni na shiga.
Hakan kuwa akayi ina mika masa yabani hanya wuce ina mamakin toh wane irin aiki kuma zanyi,danni a iyah tunanin gadi nakawo da tace zata ban aiki a cikin gida kuka zan iyah zuwa da iyalina,toh kodai ba nan bane,dan nan kam suna da mai gadi,wanda koh kare bazai nuna masa gadin ba ,dan ga ganinsa a fuska ma zaka tantance.
Nidai ban sare ba muka cigaba da tafiya a hankali saboda yanayin tafiyar hajara da bata sauri saboda rashin karfin jiki.
A bakin wata kofah muka tsaya saidai itah karamace amma dai tafi kofar shiga ɗaki girma,da wata yarinyah muka,haɗu tah yimana iso zuwa ga matar gidan.
Shiga mukayi tareda itah bayan tah dawo tacemana mu shiga.
Tabbbb danƙari wani kayan sai amale aradu,ai ina arba da inda aka shigo damu na saddaƙar da cewa ba’a Nigeria nake ba kawai,dan wajen badai ado ba kam.
A ƙasan wajen muka samu waje muka zauna inda mai aikin tacemana mu tsaya.
Bata daɗe ba kuwa sai gata ta shigo bakaman sauran masu kuɗiba da zasu iyah barka a zaune har awa guda.
Sallama tayi mana tareda nuna mana kujera akan mu zauna,nidai duk hankalina bai kwanta da zaman kujerar ba saboda kar mu bata musu,amma kasancewar ƙasan da sanyi ga kuma yananyin jikin hajara sai muka koma kan kujerar.
Har ta gyara zama zata fara magana sai kuma tayi saurin kiran wata a cikin gidan,saida ta bayyana naga ashe wacce ta rakomu ce,
“Yawwa blessing kawo musu abin sha da abinci mana,kinga har na fara cikasu da surutu kafin na bansu wani abu(juyar da kanta zuwa ga inda muke sannan tah cigaba da cewa).
Afuwan malam umaru,naga mai ɗakinnka ma kaman batajin daɗi sainaga kaman ma ƙaruwa zamu samu,yamzudai bari na saka akaiku ɗakin dazaku zauna kuci abinci ku huta daga baya sai muyi magana koh?”
“Toh shikennan babu matsala duk yanda kika ce ranki yah daɗe”
“Kacemin madam kawai,itah kuwa tah kirani da sunana Maryam,allah bamu ikon zama na fahimatar juna”
Daga haka ta tashi tayi hanyar wan beni,itah kuwa hajara tun gaisawa da sukayi bata ce komai ba sai murmushi da take kawai,duk wanda yaganta yasan akwai alamun gajiyah a tareda itah.
Ɗakine mai matsakaicin girma amma yah ƙawatu kam matuƙa,gashi an shareshi tasss sai ƙamshi yake fitarwa mai daɗi da kuma sheƙi.
Wacce hajiyah maryam ɗin takira da blessing ce tasake dawowa ɗauke da kayam abinci,godiyah nayi mata na ɗawainiyha damu kafin tah fita a ɗakin.
Kallon hajara nayi wadda samu bakin gado tah zauna tana ɗan riƙe ciki.
“Ciwo cikin yakeyi ne”
Batayi magana ba sai jijjiga kai da tayi,nima bansake tambayarta ba nayi hanyar banɗaki domin ganin menene babu,saidai da mamakina naga komai yana inda yake gashi na zamani,dan ma allah ya taimakeni nasan yanda ake amfani da banɗakin zamani da hakan sai yaban wuyah.
Ruwan mai ɗan zafi na haɗa mata a bahon wanka,wajen cin abine dai saida aka kai ruwa rana tukunna.
Muna cikin hakanne kuwa blessing ta sake dawowa,ɗauke da magani inji hajiyah maryam na masu ciki,dayake itama cikinne da itha kuma bai girma sosai,dan zayyi wata ɗayah dana hajaran.
Ina bata maganin kuwa tah fara baccin farin ciki wanda rabonta dashi har tah manta ma.
Kwanan mu uku a gidan kafin hajiyah maryam ta nemi ganina a falon baƙi.
Gaisheta nayi tah amsa batareda dogon jawabi ba tah shaidamin cewar aikina shine bayin fulawa safe da yamma da kuma kula dasu akai akai.
Mamaki abin yabani jin ɗan karamin aikin da zanyi kuma aka bani muhalli da kuma albashi ga uwa uba abinci mai rai da lafiyah,dan kwanan mu uku har mun murmure daga ni har hajara,wanda yanzu tah koma kaman ba itab saboda. Magananin da ta ke sha da kuma samun abinci mai gina jiki.
“Nasan zakayi mamakin ganin karamin aikin dana baka,amma bakomai bane dama nayi niyyar taimaka maka,kuma bai kamata mutane masu amana da rike mutuncin alƙawari su ƙare ba,kayimin abinda bazan mantaba nima,inshaallahu dama ina da niyyar buɗe shago toh zan baka ka riƙemin nan gaba,amma a halin yanzu wannna shine kaɗai hanyar dazan tsimaka maka”
Farin cikine haɗi da jin daɗi suka kamani har na rasama da wanne irin baki zan gode mata irin kyautar da tyimin haka.
Itama ganin na diriricene yasakata saurin barin falon tana murmushi,da alamun bata son godiyar tawa kenan.
Nikuwa hakan bai wuceba dan dana koma ma na faɗawa hajara tun kafin na rufe baki tace zatayi mata godiyah tsakanin itah da itah.
Tun daga fita godiyah ba itah hajara ta,dawoba sai wajen karfe tara ba dare,abinne ya ɗauremin kai inda na tamabayeta mai yah faru,nan take cemin wai hira suke tayi irinna mata ,musammaan ma akan ciki da kuladashi,da kuma tsabtar jiki da tah muhalli.
Sannan tace mata idan cikin yakai wata biyar zasu dunga zuwa awo tare.
Tun daga lokacin daga na fita sai hajara ta tafi sashen hajiyah maryam tanan tayata ɗan ayyuka ita kuma tana koyamata abubuwa,musamman da yake karatun nursing tayi saidai bata aiki a kan hakan.
Nima bana hanata zuwa tunda ina ganin sanji a abubuwa da dama a game da zamanta da hajiyah maryam ɗin,kuma bata zama cikin kaɗaici sai ma wani haske da ta ƙara saboda kyakykyawar kulawa da take samu a wajen hajiyah maryam ɗin,matar da ba abinda zan iyah saka mata dashi sai alkhairi.
Wani muhimmin shirye shiye aka fara a gidan na tarbar dawowar mai gidan wanda yake aiki a kasar India,mukan mu ganin hajiya mairo tana murnar tarar masoyinta yasa muma muka fara tayata murnat duk da bamusan shiba bare jin labarinsa,hajara kamma a can ta yini suna ta aiki.
Can wajen la’asar misalin karfe uku ji karar shigowar motoci,tab nan fah abin yazama abun kallo,dan kuwa inaga duk girma da faɗi irinna farfajiyar gidan saida suka cika da motoci kaff,babu koh masakar tsinke.
Mudai muna tsaye daga bakin ɗakinmu wanda yake ɗan gefe da inda motocin suke fakawa ,mun zubawa sarautar allah ido.
Can bayan sun gama shigowane kuma sai dukkan sauran motocin suka baɗe suka fito.
Samarine da mata farare kall ba irin na kasar nan ba,duk da akwai masu surkin bakin fata a cikinsu,sanye suke kkwannensu da kaya baƙiƙƙirin kaman zunubi.
Dukkan layi sukayi a jikin jar motar da take tsakiyah wanda itah ce kaɗai mai banbancin kala a cikinsu,dan duk sauran baƙaƙene.
Na gaban motarne yah fito kafin yazo yah buɗe bayan motar. A ɗan jima kafin mamallakin motar yah jefo ƙafarsa waje,kafin yah fito da dukkan sauran jikinnasa.
Kyakykyawane na fitar hankali,dan koni dana ke na miji naga kyawunsa bare kuma mace,.
Kayane a jikinsa farar shadda ƙal,da kuma baƙar hula da takalmi shima baƙi siɗik, taku yake cikin kwanciyar hankali har yazo yah wuce falon hajiya mairon,yayinda sukuma sauran naga duk sun koma motarsu sun bar gidan,sai jar motarce kawai take nan da kuma wanda yah tuƙota.