NOVELSWASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

Tun kwana uku da haihuwata gidan yafara cika da mutane,saboda al’adar dakan yaji.
Shikansa idan mutum yagani dauka zayyi sunan akeyi,anty saleemah ce ita da surayya akan komai sai shige da fice sukeyi.
Ranar da ta cika kwana bakwai da haihuwa aka rada mata suna HAJARAH taci sunan ummah mu,wanda ranar ma saida nayi kuka na koshi,musamman yanda yarinyar ta dauko wani abu irinna mahifinta wanda yake kama da ummah nah,bazan taba mantawa da ita ba.
Nida kaina na sakamata lakabi da ummulkhair saboda boye sunan,shikansa yah sameer ya ji dadin lakabin danayi mata dan ta cancan ci fiye da hakan.

** * *

Shekarata biyu da haihuwa nayi niyyar zuwa garin palastine wajen mu’allim da kuma shaheedah,sai kuma wajen ogah binlad danna san yana ta nemana har yanzu.
Tare muka tafi dukkanmu umarah,inda bayan mungama su hajiyah fatima da kuma anty saleemah suka dawo Nigeria nikuma muka wuce kasar palastine nida yah sameer da kuma Y’a ta ummulkhair.
A bakin kofar gidan mu’allim muka tsaya nida yah sameer wanda yake gefen prison din yara dana zauna a baya,shiga mukayi da sallama matarsa ta amsa,bude baki tayi dan da alama ta ganeni.
Gaisawa mukayi kafin ta kaini dakin mu’allim din wanda yanzu yah tsufa sosai karatu yake bayarwa a gida,dan tun randa na fada musu shugabansu yana munafurtarsu matarsa take fadamana yah daina zuwa kungiyar a gida yake karatu.
Shima lokacin daya ganni yayi mamaki sosai,saidai yayi farinciki ganin yanda na koma uwa kuma mata ta gari abar alfahari ga yan uwa musulmi.
A nan muka yini har dare kafin muka koma masaukinmu,washagari gidan su shaheedah naje,saidai mamanta tace tana kasar aurenta da yara hudu,sshaheed ne suke tare shima da matarsa da yara uku,ba wani gaisuwa sosai mukayi dashi ba dan ba shiri mukeyi ba.
Ogah binlad kuwa danaje inda muke zaune van samesu ba sai filin wajen kawai,bansan kuma wazan tambaya inda suke ba dan haka dole na ha kura watakil sunyi wani wajen daban.
Haka muka koma masaukinmu yah sameer yana ta yimin kallon alamun tambaya,shareshi nayi dan gaji sosai so nake na huta.
Muna zuwa na fada bandaki nayi wanka nazo na bi lafiyar gado,ina dosana hakarkarina naji kukan ummulkhair a falo,shareta nayi na kwanta dan yarimyar ta fiye fitina ba laifi.
Bankai gayin baccin na moreba naji yah sameer yans jijjiga kafada ta,tashi nayi na zauna ina lumshe ido tareda cuna baki.
“Menene kuma yah faru”
“Hhhhh uwata tayi kashi a tashi a gyara mata,kuma ma anyi sallah la’asar sannan ke kikacemin zamuje sha iska”
“Uhh haba yanzu ba dama na huta wai,naga kashin kaima zaka iyha wankewa”
“Kinga comon tashini kin faye bacci kwannan da kuma shagwaba baccin y is haka,kuma sonake ki bani labarin duk abinda yafaru dake a kasar nan”
“Naji dama nasan zaka tambaya,yanzu bari na gyarata mu fita tukunna”
Ta shi nayi babu yanda zamyi,kai rainoma babu dadi fah,ina yi mata wanka tana tirjewa tana rigima da haka na shiryata muka fita zaga cikin garin dan gobe zamu koma gida.
Mun dade muna zagayawa ina fadaasa wajajen da mukayi aiki wani lokacin a ganomu muyi ta gudu.
Dariya yadungayimin wai allah ya hada y’ay’an sa yar rigima da kuma daba,saida yaga naji haushi raina ya baci kafin ya daina yana bani hakuri,aikuwa yajawa kansa dan daina bada labarin nayi yayi ta tambayata amma nayi shiru.
A Gidan hajiyah fatima muka yada zango lokacin da muka dawo dan itama anty saleemah tana can,ana ta dariya wai na dawo da tsarabar kasar palastine na ciki.
Babu abinda zamuce sai allah ya barmu cikin sunnar manzon allah.
Alhamdulillah nasamu sauyi mai kyau daga duhu zuwa haske,allah yahadani da miji gwarzo mai sona da kuma bani kulawa,ga kuma abokiyar zama dana samu wacce bazata cutar dani ba koda a bayan idona.
Yanzu aiki na gaba shine yanda zanyi na inganta rayuwar gidan gandu daga rashin kyakykyawan muhalli da jahilci zuwa wayewar kai da kuma waje mai inganci.
Idan allah yana taimakonka ba abinda zai gagareka musamman idan kasamu gwarzon abokin rayuwa kamar yah sameer.

ALHAMDULILLAH ALA KULLI HALIN.

Godiya ga allah subhanahu wata ala daya kawomu samun nasarar gama wannan littafin,allah yayi mana mai kyau da iyawarsa.

Sannan godiya ta musamman ga wanda suka bani goyon wajen

Daga taskar sadi-sakhna __✍????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button