NOVELSWASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

Lokacin da kwana uku yah cika munyi zaton zai koma,sai muka ga har anyi sati guda bai tafiba,hakan yasa mukayi tunanin koh hutu yah samu a wajen aiki yasa yazo domin yayi su da iyalansa,kuma ya kyauta hakan,dan itah kanta hajiyah maryam taji daɗin hakan.
Sannan sameemah har ta fara sabawa dashi dan koyaushe yana tare da itah,kuma duk sanda yah fita sai yah siyo mata abin wasa da kayan ciye ciye,wani abin ma bata iyah amfani da shi,kawai siyah yake irinna iyaye masu ɗokin irin na ƴaƴan fari.
Mukuma a namu bangaren muna tah shirye shiyen tafiyah zuwa gida,saboda iyayen hajara suna so taje ganin dangi,nima kuma inason zuwa ganin yah yanayin gidan yake tafiyah. Mun yanke shawarar nan da sati ɗaya zamu tafi,kuma zamu kai wata guda bamu dawoba.
A ranar da daddare kowa yayi bacci kasancewar daren yayi sosai,ba abinda mutum yakeji sai shirun duniyah kawai,kowa yan kwance yana hutawa.
Ban daɗe da zagawa bayi ba naji bugun ƙofar ɗakinmu,saida na kalli hajara wanda take kwance kafin na isa bakin kofar ina wasiwasin na buɗe ko kuma na barta,ina cikin hakane naji muryar hajiyah maryam da alamun tashin hankali a cikin muryarta tana cewa,
“Malam umaru kabuɗe ni ce,kayi sauri banida lokaci sosai”
Cikin sauri har jikina yana rawa na zare sakatar dakin da sauri.
Haɗa ido mukayi da itah jikinta sai rawa yakeyi lokaci zuwa lokaci tana waigawa baya kozata ga wani yana biyota.
Sameemah ce a hannunta wacce take ta bacci abinta,saurin mikomin itah tayi da sauri,zuwa lokacin hajara tah tashi,sai na miƙa mata yarinyar,tun kafim na tambayeta ta fara magana cikim sauri muryar tana rawa,
“Na roƙeku dan darajar allah,ku fitah daga gidannan a yanzu basai gari yah waye ba ku bar gariannan ma idan san samu ne,bazan iya yimuku bayanim abinda yake faruwa ba,saidai inaso ku riƙemin ƴata da amana a wajen ku,duk da nasan zakuyi hakan tunda nafi kkwa sanin halinku na mutunci,sannan ku kumin alkawari zaku riƙeta a matsayin ƴar da kuka haifa a cikinku,kar wani yasan gaskiyar iyayenta,na baku itah halak malak burina kawai tasamu gata da kuma rayuwa mai kyau koda bana cikin rayuwarta,kartayi maraicina ko kuma rashina”,
Tana gama faɗan hakan tah ciro wani ƙullin kuɗi a jikin rigarta ta miƙamin kafin ta cigaba da cewa,
“Ga wannan kuɗin,na aikina ne danayi na tsawon shekara kuda,wannan zai isheku hawa motah,wannan katin kuma na asusun bankine mabuɗin cirewar sunan sameemah ne,nabaku zaku iyha amfani dashi wajen inganta rayuwarta,amma idan kunga bazaku iyah amfani dashi ba saboda nasan halinku toh,ku ajiyemata idan ta girma ku bata a matsayin kyautata tace a gareta kuma ina rokonta,da tayi muku biyayya tamkar mahaifanta”
“Kuyi sauri ku fito yanzu nan kafin lokaci yah kure mana,kuma dan allah karku bari sameemah tah tako garin bauchi lo da wass”
Tana gama faɗan hakan tah fara haɗamana kayanmu da sauri,akwati ɗayah muka ɗauka ta rako mu bakin get ɗin gidan,hajara tana rungume da sameema a jikinta,duk da bamusan menene ba amma munsan abinda zai raba ɗiya da mahaifiyarta na kaɗan bane ba.
Hajara ce tayi karfin halin cewa
,”amma hajiyah maryam bazaki iyah guduwa keda itah ba ko kuma boye ta?”
“Dazan iyah hakan danayi tuntuni,ku tafi kawai wannan shine iyah abinda zan iyah,zanyi mata alkhairi daga inda nake ma”
Tana gama faɗamana hakan tah juya cikin gidan da sauri,hawaye yana zuba a idonta amma sai ƙoƙarin hanasu zuba takeyi,saidai ko daga ganinta tah ɗan aamu nutsuwa data raba ƴarta da koma menene yake tunkarowa.

A daren muka fara tafiyah har da gudu gudu,domin muma babu abinda yake cikin ranmu sai ƙoƙarin ƙubutar da rayuwar baiwar allah da take bacci a bayan hajara,batasan ma me akeyi a duniyarba.
Kafin gari yah waye har mun kai wani kauye dayake kusa da bauchin a hanyar gidanmu,tsaywa mukayi domin hajara ta huta saboda gajiya ga kuma goyon yarinyah ƴar shekara biyu.
Anan muka tsaya muka sayi ƙosai muka ci,kafin muka tsaya jiran motar garinmu a wajen.
Cikin sa’a kuwa saiga mota bata cikaba muka shiga sai gida.
Da tsakar rana sai gsnimmu akayi babu tsammani,sai tambaya suke mai yasa muka taho yau bayan sai wani satin,cawa muka kamawa takeyi kawai,sauran mutan gida sai tambayar hajara suke akan suga ƴartata,ba musu kuwa ta sakko da sameemmah wanda take tah bacci abinta,jin hayaniyane yasata farkawa,aikuwa tana ganin inna Hauwa matar mumkaila wanda amaryace a lokacin zata ɗauketa tayi saurin maƙalrewa a jikin hajara,tana kukan rikici.
Kowa mamaki yakeyi da kyau irin na sameemah har ma kyau na kayan jikinta,marasa haƙuri kam ma har saida suka yi magana irin su inna ramatu.
Nidai daga ni har hajara babu wanda yace wani abu,sai sunane muka ce musu an samu sabani ne sunan ta sameema ba maryam ba kaman yamda aka faɗamusu,dan haka bamu sha wahala ba wajen boye ainihin tarihin sameemah a wajensu.
Tun daga lokacin sameemah ta ware tamkar ƴar gida,dan dama ta saba damu sosai musamman ma hajara.
Shekarar sameemah huɗu hajara tah dara ciwon ƙafa,wasa wasa ana tah magani amma ciwo sai gaba yake yi,sannan nikuma kulawar danake bawa sameema sai yah fara zuwa idon mutanen gida,hakan yasa dana ga za’a samu matsala na fara ja baya da lamarinta ba kaman da farko ba.
Haka na shigaba da kulada itah,har zuwa wasu shekaru inda tace itama ga garinmu.

Wannan shine iyah abinda nasani a game da abinda yake faruwa,
Ina mahaifin sameemah bansaniba kawai nasan yana aiki a india sannan kuma mahaifiyarta bansan koh tana rayeba,dan maganar da take yi mana kaman wasiyyah haka take yinta.
In kuma tana raye bansaniba,dan nasan danginta amma ban san a wane gari suke ba,abinda nasani shine itah ba ƴar garin bauchi bace kawai.
Amma tabbas tah kargaɗeni akan kar na sake na barki kije garin bauchi.

????~~~????

Yana kawo nan a labarin sa saida kowa ya zubar da kwallah na tausayin hajiyah maryam da kuma tunowa da mutuwar inna hajara musamman ma inna rabi an taso mata da tsohon mikin mutuwar ƴar uwarta mai sonta,banda sameemah wanda fuskarta babu alamar rauni a cikinta,saima kallon gefe da tayi kawai.
Tashi baba umaru yayi ya ɗauko wani ɗan akwati ƙarami ja.
Buɗeshi yayi da wasu lambobi yah ciro wani kati a ciki,na shaidar sumun asusu a banki.
Miƙawa sameemah yayi tareda cewa,
“Wannan shine abinda mahaifiyar ki ta bamu akan cewa mu baki idan kin girma ko kuma muyi amfani dashi,saidai bamu taba ba dan aduniya babu abinda bazamu yiwa jinin hajiyah maryam ba,dan tayi mana abinda bazamu taba mantawa dashiba.

Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150

Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.

????Sadi-Sakhna________✍????????

(¯’•.¸,¤°’✿.。.:քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ.:。.✿’°¤,¸.•‘¯)

????•°• WASA FARIN GIRKI •°•???? {cigaban gidan gandu}

????7~8????

????Sameemah a madubin Gani????

Duk abinda yake faɗa ina sauraronsa,har yah ɗauko wani akwati yah miƙomin wani kati wai inji mahaifiyata,dan kuwa wai ne,dan jin zancennasa nake kaman a mafarki,kar ba nayi ina kallon katin batareda nace komai ba,sukuwa sai kallona suke dan ganin mai zance,inna rabi kuwa idonta yayi luhu luhu na munafurci,saika ce addu’a take wa ƴar uwar tata idan ka tsareta,kowa sai munafurci na iyah shege.
Tsallakewa nayi na fita a ɗakin na barsu sai ta’ajjabinsa sukeyi wanda bashida dalili,babu yanda za ayi na tsaya wannan abu tunda na samu abinda nake buƙata shikenan kawai.
Kayan aikin na cire badan na soba,duk da ina da taurin kai amma idan na ɗau alkawari nakan iyah ƙoƙarina dan naga na cikashi.
Ninke kayana nayi na adana dan ban cire ran cigaba da,aikina ba koda nan gabane kuwa.
Inna rabice tah shigo ɗakin har sannan idon ta bai washeba da kukan munafurcin,dan haka sukayi a mutuwar ummah ɗin,duk wanda yagansu sai yayi zaton idan dare yayi kwana zasuyi suna yi mata addu’a,amma kowa ana yin sallar isha ta sau baki tayi bacci.
“Yamzu kam tunda kinji mai akace sai kizo kuka ki tsefe wanan kan kuma da kuma lalle saboda yin kwallliyar amare kaman kowacce amarya idan za’a kaita ɗakinta.”
Kallonta nake ina mamakin katsalandan irin na wannan matar,itah ko gajiyah batayi da shiga rayuwar mutum,narasa ma mai zan mata ta rabu dani,dan nakula koh zuciya batayi koh wacce irin magana mutum yafaɗa mata.
Ko magana banyi mata ba na jawo system ɗin na fara wani aikin,dan shiru ma amsa ce idan tana da hankalin hakan.
Aikuwa haka tah fita,nayi zaton tah haƙura ashe nacinta yah wuce hakan ashe,dan kuwa dawowa sukayi da baba umaru,
“Meyasa kika kasance mai taurin kai ne sameemah,kince idan aka faɗamiki mai yake faruwa zaki amince kibi mijinki gashi yanzu kuma an faɗamiki amma har yanzu abu bai sanja zani ba”
Toh tanan suka bullo kuma,mai yasa akeson takurani ne haka,kullum hankakin kowa yana kaina dole sainayi abinda yake so,wai baza’a barni na yi abinda nakeso bane?,ɗago kai nayi na kalli baba umaru tareda cewa
“Toh shikenan naji zanje wajen kitson amma daga nan bazan karbi koh komaiba,sannan bayan shi babu abinda zan sake yi,koda kuwa me zakuyi kuwa”
Dan nasan idan ba haka nayi musu ba zancen bazai wucewa,jijjiga kai kawai baba umaru yayi kafin yabat ɗakin yah barni daga ni sai inna rabi,wanda duk tabi ta takurawa rayuwata.
Haka babu yanda zanyi na ɗaga wayah nakira burgu sabon ango,shima saida yayimin tsiyah tukunna abinda banaso kafinnan na faɗa masa saƙona kan ya turomin mai kitso da fulawa,amma kar ta daɗe,dan idan yakai yamma na fasa.
Saida yah sheƙe da dariyah kafin yace,
“Amaryah amarya ranki yahdaɗe amaryah,da girman kujerarki amaryah a wajen ogah sameer gashi………..”
Ban gama jin abinda yake faɗaba ba kashe wayar dan ba abinda nakeson ji ba kenan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button