WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL
WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL
????* Sameer a mdubin gani*????
Lokacin da baba umaru ya,gama bada labarin abin yayi matuƙar ɗauremin kai sosai,dan tsawon wannan shekarun kallon sameemah nake a matsayin ƴar uwata ashe ba haka bane,dan yanzu gashi lamarin yayi zuwa yanda bana tsammani na samu kaina da zama mijin aure a wajentah,tabbas ina cikin cakwakiyah na wanne irin zama zamuyi da itah a can tukunna,danni shaidane bata tankwasuwa gata da ɗan banzan rashin mutunci na bugawa a jarida.
Duk labarin da aka bayar kamata yayi tafi kowa shiga cikin damuwa amma koh a jikinta saboda gasheshshiyar zuciyah ce da itah,sam baka sanin mai yake cikin ranta,nine zan zama shugaba aknata ko itah ce shugabar,saidai kowa yayi rayuwarsa dan allah yagani bazan takurawa kaina ba.
Ganin wani karbar katin da tayi a hannun baba umarune tareda ficewa a ɗakin yasa kowa yah bita da kallo,nima ganin hakane yasa na tashi domin shirina dan yau zan koma gida,dan na samu abinda zan saita kafin zuwanta nan da kwana uku.
Ɗakin da kayana yake na nufah,duk lakar da take jikina ta shika,banda faɗuwar gaba ba abinda kirjina yake yi,danni kaɗai nasan irin matsalar dazana fuskanta.
A katifar ɗakin na zauna,nafi awa guda kafin na fito da jakata a hannuna na nufi ɗakin ƴanmatan gidan inda sameemah take,yau ne karon farko da shigata ɗakin tun bayan raauwar ummah a ciki.
Tsayawa nayi ina kallon cikin ɗakin bayan nayi sallama.
Saidai ko sallamar bata amsaba bare tah ɗaga kai ta kallleni,uhmmm nafaɗa a raina.
“Ina sallama keba musulma bace bazaki amsaba,koh nima tsiyar taki zakimin dan kin rainani”
Nan ma bata kalleshiba sai amsa sallamar da tayi kawai,katin cire kuɗi na fitar a aljihuna na miƙa mata tareda cewa,
“Gashi wannan ki sayi duk abinda kike buƙata,saidai karki sayi sutura koh kuma abin amfani dukka akwai acan,idam ma da wani abun ki kiranj ki faɗamin”
“Bana bukatar kuɗinka saboda ina dashi basai ka baniba,kuma duk abinda nakeso zanyi ba wanda wani yakasaniba tunda babu wanda na dogara sashi bare yayi min yadda yaga dama”
“Dama badan kina dashi na bakiba,na bakine saboda kina da hakki a kaina na hakan,sannan karkiga dan zakizo gidana kinemi yimin tashin hankali ina gargaɗinki da ki shiga hankalinki”
Sabanin abinda na tsammata tayi,dan iyah murmushi tayi na gefen baki wanda sai mutum yah kula kafin yagane shi.
Nima juyawa nayi na fitah daga gidan zuwa cikin motata,baba umaru dama munyi sallama dashi ɗazu,bazan iyah sake tsyawa ba kuma,dan anyimin abinda kwata kwata naji babu abinda nakeso sama da bawa garin baya kk zanji sanyi a raina.
Tun a hanya kiran saleema yake ta shigowa,ina gani naƙi ɗauka dan tun ranar ɗaurin auren take ta ƙirana tun ina amsawa har na daina.
Kafin na isa gida saida tayimin ƙira ya kusa goma ina katsewa,dan idan na ɗauka bansan mai zan ce mata ba,dan haka kawai na barta idan na ja koma menene zanji daga gareta.
Banfi shafe wasu awanni masu yawa ba na isah garin porthacourt sakamakon gudun danakeyi yah wuce na hankali,burina na isa kawai domim nasan mai zanyi.
Ina shiga sojojin da suke bakin kofar suka buɗemin na wuce,tun daga bakin falon na tabbatar cewa na daeo gida,hakanma farfajiyar hajiyah saleema,dan komai da gindinsa yake zaune a falon,duk da babu datti amma fah babu tsari ko kaɗan irinna na ɗakin ƴa mace.
Fitowa tayi daga ɗaki muna haɗa ido da itah,babu sannu da dawowa bare yah hanya sai ƙorafi dayah min sallama,na kashe mata wayah danayi.
Dan takaici ba tsaya yi mata wani bayani ba nayi hanyar ɗakina,ina jinta tana biye dani har sannan bata daina ƙananan maganganu ba,jin abin zai min yawa goma da ashirin yasani dakatar da itah,tareda cewa,
“Dan allah saleema ki barni na huta tukunna koma menene sai tambayeni ,amma yanzu bakya ganin daga hanya na dawo,babu sannu da dawowa bare ruwan sanyi sai aukin ƙorafi,wai yaushe zaki sanja ne?”
Jumbura daki tayi irinna sakalai kafin tace cikin muryar shagwaba,
“Haba honnnney,yanzu hakama zaka ce dan gaka ina damuwa da kai,fisabilillahi tun yaushe ka bar garinnan,sannan tun kwana uku da suka wuce yakamata ace ka dawo,amma baka dawoba sai ma kashemin waya dakayi bayan na ƙiraka,wai meyasa kake min hakane “
“Ni babu abinda nayi miki saleemah,kawai akwai abinda yasa na tsaya ne,kuma idan kikayi haƙuri inna zauna zan sanar dake,domin kema yah shafeki”
Daga haka na juyah na wuce ɗakina ina riƙe goshina,wanda nakejij kaman zai iyah darewa a kowanne lokaci.
Wanka na shiga naji ɗan dama dama,ina fitowa na samu saleema a bakim gado tana jirana,ban yi mata magana ba sai da na shiryah kafin nazo na zauna,anan na kula ashe abinci ta taho dashi,ta wannan bangarenne kawai take burgeni,dan idan na faɗamata abu tanayi,sannan kuma bata fiye yimim musuba,barta dai a shagwaba kam har da ta siyarwa.
Jawo kwanon abincin tayi tah juba,duk raina bayaso saboda na ƴan aikine,ita kuma babu dama tah dafa abinci da kanta,wannan sam ya zama abinda tah maidashi haramun a gareta.
Kaɗan naci kafin na ajiye cokalin ina kallonta,wanda tunda nafara cin abincin ta tsura min ido tana kallona,
“Uhm ……dama saleema akwai abinda nakeson baɗamiki,kar lokaci yaƙure ban faɗamikiba kice ban kyautaba”
“Uhm ina jinka honey mai yah faru ne?”
“Da farko kinsan ni mijine ke mace sannan kuma an halattamin auren mata guda huɗu idan ina da dama koh?”
“Tsaya tsaya haka,banason jin wanann bayanin gaskiyah,dan wallahi babu kishiyar dazaka yimin ana zaune kalau,nasan ma bazaka yi ba ai,dan haka a bar wannan zancen”
“Amma yah kamata ki dunga tsayawa kina jin karshe magana,dan aure ba zancen za’ayi bane an riga anyi ne,dan yanzu haka ma amaryar jibi za tare kuma samee…………..”
“Karka cigaba da faɗin abinda kunnuwana bazasu iyah ciggaba da jiba sameer,me kake nufi,aure!!!,kuma ma har an daura,nan da wasu kwanaki matar zata zo ta zauna a gidana,kuma itama tah mallakeka kaman yanda nakeyi,inaaaaaa hakan bazai taba yiyuwa ba kama canja zance amma ba wannan ba …………kasan mai kake faɗa kuwa??”
“Nasan mai nake faɗa mana salee…………”
Tun kafin nagama magana ta watsamim wani kallo wanda tunda nake bansan ta dashi ba ta bar ɗakin da sauri tana bugomim ƙofar ɗakim kaman zai karye.
“Yah salam”
Shine kawai abinda na faɗa,dannasan shikaɗai zai kawo min mafita akan abinda yake shirin tunkaroni.
????Sameemah a madubin gani????
Lokacin da mai lallen ta zo ma kaman bazan tashiba,da jinake wani baƙin ciki yana taruwa a cikin kirjin lokaci zuwa lokaci,samun waje tayi tah zauna ba kin katifar sameerah ta da,tana sunkuyar da kai kaman mai tsoron haɗa ido dani,ƙoƙarin katse shirun ɗakin nayi tah hanyar cewa,
“Miye sunanki?”
“Hamiddah”
“Karki yimin mai yawa,shima dan babu yanda zanyine kawai shiyasa zanyi”
Tasowa tayi tah fara haɗa kayan yin lallen,har tah gama.
Wata shawara ce tah kawo kaina cikin ƙanƙanin lokaci,aikuwa nayi shu’umin murmushi.
Bamu daɗe da farawa ba muka gama,dan cewa nayi tayimin zanen da tasan ba’ayi a lalle kaman zanen kwari da na su ƙadangare,kallona take da mamaki kafin tah fara abinda nacemata,dayake ta iyah zane kuwa,sosai hotunan ƙwarin suka fito kaman suyi magana harda kala ta saka musu,ɗaga hannun nayi ina kallon zanen yamda yah fito raɗau a hannuna,dan duk mai tsoro ƙadangare da kuma su dandoriyah to yana gani nhannu na zai fita da gudu,daɗi ne yah isheni koba komai zuciyahta tayi ɗan sanyi danayi tsiyah.
Tana gama lallen koh nace zanen tayi shiru tareda ɗan matsawa gefe,sai kallon abinda yake hannuna da kuma ƙafata takeyi.
“Ai baki gama ba,ina so kiyimin zanen maciji ya nannaɗe wuyana,ina zaki iyah?”
“Eh zan iyah anty”
“Yawwa toh yimin yayi biƙi sosaifah”
“Toh anty”
Ina gama faɗan hakan na cire rigata nabar iyah zani ɗaurin kirji,lallen da sake haɗawa kafin ta fara zanen
Wanann sai da ya ɗaukemu lokaci domin so nake ya fito kaman na gaske,aikuwa nima kaina sai da naga kyau na macijin,rai na fari tass yayi ganim abinda nake shirin aikatawa yah fara tafiyah yanda nake so.
Kuɗin aikinta na bata ta tafi,kitso kuma shagon gyara nake son zuwa saboda kawai abinda nake son aiwatarwa.