NOVELSWASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

????Saleema a madubin gani????

Tun naji furucin daya fito daga bakin sameer mai kama da dafin maciji na tashi na tsaya,ji nake duniyar tana juyamin duk illahirin jikina rawa yakeyi ga kuma wani tashin hankali da baƙin ciki da suka taru a ƙirjina,numashina har sama sama yakeyi.
Ɗakina na nufah ina haɗa hanya dan ko hanyar idanuwana basa gani sosai,babu abinda yake amsa kuwwa a cikin kai na kalmar da sameer yah faɗa ta,aure aure kishiyah kishiyah.
Da ƙyar nasamu damar sakawa Zuhra riga(mai sunan mahifiyar saleemah,hajiyah Fatima)na sunkuceta sai bakin motata,shikuwa farouq bai dawo daga makaranta ba ta isilamiyya,idan yah dawo ubannasa yasan yanda zayyi dashi.
Ikon allah ne kawai yah kaini gida,sa’a ta ɗayah babu nisa duk a cikin barikin sojojinne,saboda girmansane yasaka ni ɗaukar motar dan idan na ce zanje a ƙafa toh zam iyah yin kusan wata a ganina ban ƙarisaba.
Ina kashe motar na fitah daga motar da gudu zuwa cikin gidanmu,har na kai bakin ƙofah na tuna nabar ƴata a cikin motah,da gudu na koma na ɗaukotah kafin na shiga cikin gidan.
Akan kujerar falo na dire zuhra dan ita haushinta nakeji ubanta yah shafamata,mai aikin gidan nagani zata wuce madafar abinci.
“Ke zo ki ɗauki yarinyar nan ki kula da itah sannan ki bata madara”
Zuwa tayi tah ɗauketa ni kuma na yi ɗakim mommy da gudu har ina tuntube,babu abinda nake buri sai,wanda zan samu na faɗawa mai yake faruwa,sannan kuma da wanda zai rarrasheni.
Ina shiga na faɗa kan mommy wacca take naɗe kayan ta ƙanana akan gado,kuka na rushe dashi wanda dama na daɗe ina riƙeshi,sai yamzu yah samu damar kwacewa yah fita.cikin shshshekar kuka nafaɗamata abinda yah faru.
Tana gamajin labarin tah tureni daga jikinta tareda cewa,
“Dallah ni matsa kiban waje,dan mijinki zai ƙara aurenne kike wannan kukan kaman wata sakaryah,ke kuwa kina hankali kuwa?,kai kai wallahi alhaji yajiƙa aiki daya shagwabaki,ya maida ke bakisan kinemi abu ki rasa ba,sanann ya maidake bakisan kiyi haɗaka da wani ba akan abin duniyah,saidai yanzu alhamdulillahi gwanda da yayi auren koba komai zaki koyi darasin haɗa abu da wata,kuma zaki san duniyah ba kullum abinda kake so kake samuba koh ake yi maka ba”

Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150

Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.

????Sadi-Sakhna________✍????????

(¯’•.¸,¤°’✿.。.:քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ.:。.✿’°¤,¸.•‘¯)

????•°• WASA FARIN GIRKI •°•???? {cigaban gidan gandu}

????9~10????

Matsawa nayi daga jikinta na bar ɗakin,da wanne zanji da kishiyar da akayimin koh kuma da faɗan da takemin,idan tana wani abun saikace ba itah ta haifeniba matar ubace,nidama nasan batasona kaman yanda abba yekiyimin,kullum cikin yin faɗa take da hantarata.
Kuma wallahi ban haƙuraba daddy yana dawowa zan faɗamasa,bazan bar gidan bama anan zan zauna har sai ya saketa tukunna kaman yamda ya aureta.

Ɗakina na gidan na nufah,ina kuma danna ƙiran wayar SUHAILAH,tsuka naja ganin tana ta ringing amma bata ɗaga ba sai daga baya kafin ta ƙirani.
“Sully kina ina ne wai,ina ta kiranki baki ɗauka ba,akwai matsala fah”
“Matsala kuma wace iri,banganeba mrs major,fayyacemin naji mai ake ciki”
“Hmmm ke miyema bai faruba aikawai sai kinzo,dan zancen baxai yiyuba a waya”
“Toh shikenan gani nan zuwa,dama yamzu na dawo daga makaranta,cin abincina kenan,bari nayi wanka nazo naji mai yake faruwa”
Ajiye wayar nayi bayan nagama wayah da suhaila,nasan ana jimawa zan ganta,safa da marwa na fara a ɗakin tsakanin kujerar madubi da kuma bakin gado,duk abin duniyah yah isheni,lokaci ɗaya har na rame na fitah hayyacina,dama haka mata suke ji idan za’ayimusu kishiyah?,tabbb gaskiyah abin babu daɗi,dole ne muyitah,koh ni koh itah,duk da bansan ma wacece ba.
Sai kusan magriba kafin suhaila tazo,ita kanta nasan a lokacin uzuri takemim saboda babu laifi tasha madifa tafi cikim kwando.
Itama bata wani bani shawara gamshashshiyah bah,duk daga nayi kwalliyah,na dunga jan ajina,sai kuma kar na bari tah rainani,kallon suhaila nake lokacin da take faɗan hakan,lallai bata san me ake jiba idan akayi maka kishiyah,dan taga batada mijinne bare kuma zancen yimata kishiyah,toh yaushe ma zan zauna da itah har nafara wannan shirmen na jan aji da kuma kwalliyah.
Ita kanta surayyah ganin nayi mata shiru yasa itama ta kama tura saƙonta a wayah,ni hakan ma yafimin da wanann zance nata.
Daddy yana shigowa tun kafin yah zauna na fito daga ɗakim ina haɗe fuska,kallona yayi da alamar damuwa a fuskarsa ganin yanayin dana ke ciki.
“Ƴar daddy mai yasameki haka?”
Kallon mommy nake wanda take zabgamin harara kaman idonta zai fito,hakan bai dameni ba saima ɗauke kaina danayi ina kallon inda mai sona yake wato daddy,
“Daddy inadai wai sameer ne yaƙara aure…..”
Ina gama faɗin hakan hawaye ya fara zuba a idona,daman yau kam ai idon cike yake da hawaye.
Cikin razana da kaɗuwa daddy yafara magana ransa a bace,
“Aure kuma,daga aura masa ke kawai sai yahsake aure,ni naga ga mahaifiyarki nan ban sake mata abokiyar zama ba,sai shi ne zai wani yi miki kishiyah da yarintarki kawai dan ya bata miki rai”
Ina jin haka na sake rushewa da wani kukan ina ɗora kaina a kafaɗarsa.
Dan tsabar takaici dayah shaƙi mommy buɗe baki kawai tayi tana zubawa sarautar allah ido,dan kam abin yah fara bata mamaki.
“Kutt yanzu alhaji abinda zaka ce kenan,kana ganin tah baro gidanta ta dawo gida sai tijara takeyi da girmanta ,ba ƴar yayeba harda ƴaƴa biyu,da a ƙauyene ma tah kusa auren ƴarta shine kake wani rarrashinta harda ɗaure mata gindi dan kawai mijinta yah ƙara aure?,toh wallahi bazan yarda da hakanba,yau ɗinnan basai gobeba zata koma ɗakinta,idan kuwa tah kwana a gidannan akan wannan abin,toh kuwa zanyi fushi da itah”
Binta mukayi da kallo nida abban,wanda shima bai ji daɗin mommyn tace ba,saidai babu yanda zayyi tunda ta faɗi hakan toh bazata sanjaba tana nan akan bakanta.
Dadare na fara da kafafuna ina kiran daddyn,ganin hakanne yasashi ɗaga wayah ya ƙira sameer akan yazo yana son ganinsa,nikuma yah lallabani na tafi ɗaki kafin sameer ɗin yah ƙariso.

????Sameer a madubin gani????

Tun lokacin da saleemah tah bugamin ƙofar ta fitah ina jinta har tashin ƙarar motarta,wanda dama nasan sai hakan tah faru,abu ƙaramima take kaiwa ƙararsa bare kuma al’amari irin wannan.
Baccine ya ɗaukeni na wahala a wajen,dan kaina ji nake kaman zai sare gida biyu.
Sai can wajen magribane naji ƙarar buɗewar ƙofar dakinnawa,farouq ne ya shigo da kayan islamiyyah a jikinsa,kaina yah ɗale da sauri yana dariyah,nima wani sanyi naji yah jiyarci zuciyata,dan rabona da ɗannawa nayi ɗan kwana biyu,muna nan zaune sai kuma na tashi nayi masa wanka kafin najashi muka shiga madafar abinci.
Taliyar yara na yimasa,dan dama kowane yaro yana sonta,da farinciki kuwa yah karba ya nufi falo da gudu.
Nima bin bayansa nayi ina murmushi,sai surutu yakemin maganar bata fitah,wani nagane na bashi amsa wani kuma saidai kawai na kalleshi,yara manyan gobe
Waya tace tayi ƙara ina dubawa naga abban saleemah ne,nasan za’a rina wai an saci zanin mahaukaciyah
Ɗauka nayi tareda yin sallama cikin girmamawa,cewa yayi na sameshi idan anyi isha a falon sa,amsawa nayi da toh kafin na kashe wayar.
Wajen anty talatu (nanny ɗin farouq)nakaishi bayan yagama cin abincin nikuma na wuce masallaci.
Lokacin dana dawo anyi isha,farouq na dauka a motah muka nufi gidan su saleemah.
A falo nasameshi a zaune,saleemah tana gefensa idonta yayi luhu luhu,na ɗan ji tausayinta a raina amma kuma ta wani bangaren dama inaso tayi hankali,tasan ba kullum ake kwana a gadoba.
Zama nayi akan daddumar da take kasan falon tareda gaishe da alhajin. Dadai lokacinne itama hajiyah Fatima ta shigo fuskarta ɗauke da murmushi,daga gani alhaji Musa bai so shigowar ta ɗakinba saidai baice komaiba.
“Yawwa sameer ina jinka,yarinyah tah daho tana kuka wai tacemim ka ƙara aure,ɗazu ka faɗamata sannan kuma amaryar jibi zata taro,wani abu saleemah tayi maka ne”
“Babu abinda tayimin,sannan abinda tah faɗa gaskiyahne,nayi aure kwana uku da suka wuce,jibi za’a kawota m”
Ina gama faɗan hakan na basu labarin nima jinayi kawai an ɗaura auren bayan an gama ɗaura na ƙannena wanda naje nasu ɗaurin auren.
Jinjina kai alhaji musa yayi kafin yace,
“Yanzu yah ake ciki kenan,gida ɗayah zaka haɗasu?”
“Eh hakan nake da niyyar yi,dan a tsarina banason yin gida biyu gaskiyah”
“Ammma……….”
Hajiyah fatima ce tayi saurin katse alhaji musa daga maganar dayake son yi tace,
“Shikenan sameer munji duk abinda kace,munayi maka fatan alkhairi allah ya tayaka riƙo ya kuma baka ikon yin adalci a tsakaninsu,yanzu kaje ka jira ta,nasaka ta ɗakko zuhrah da kuma jakarta yanzu zata fito ku koma”.
Har a raina naji daɗin yanda hajiyah fatima ta taƙaita maganar,dan har raina nake yaba irin halin dattako da sanin yakamata irin na hajiyah fatima,matar ta kwanta min a rai,ganinta nake tamkar mahaifiyata.
A hanyar mu tah dawowa gida kuwa babu wanda yayi wa wani magana tsakanin nida saleemah,dan ko kalllona batayiba,idonta yana kan titi,farouq kuwa yana kulata zata zabga masa harara shima dayaga hakak sai ya cigaba da wasansa a gefe ,ni dariyah ma tabani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button