WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL
WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL
????Sameemah a madubin gani????
Mutane sai taruwa akeyi ƴan ina da biki,zuwa yanzu kowa yasan alaƙata da sameer,cewa ni ba ƴar inna hajara bace riƙeni tayi,saidai babu wanda yafaɗawa kowa su waye iyayena,kowa idan yagam kwakkwafin yaga bai gano komai na sai ya haƙura.
Ina jinsu suna tah hidimarsu da mutane a cikin gida saidai koh inda nake babu wanda yake zuwa barekuma ayimin tsokana irin tah amare.
Kaman yanda na faɗa nabada ɗinki kuwa haka akayimin,wannan duk hidimar surayyah ce,dan itah kadaice take shigowa ɗakin tah gama yimin tsiyah ta fice,tun da safe burgu yah kawota akan idan aka yini tah kwana washagari a tafi kaiwani da itah,hmmm lallai aure manya,zasu san sun sakani cikin masu aure kuwa.
Riga ce jah ta yadi mai tsada,saidai anyi mata ɗikin buɗaɗɗen wuyah,sai kuma tah matse kunkumi tah zuba a kasa ,lokacin dana faɗamata yanda za’ayi rigar bata so a yi irinta ba,amma yanda na bayar dole haka za’yi ina haka na kuma na fitah da kaina na kai ɗinkin.
~~keee mai taurin kai,koyaushe kina cikin karya mana doka koh,mun ce kinuna ƙin amincewar ki akan aurennana amma kikayi biris da zancen,idan san samune ki kawo mana jinin mijinnaki ana kaiki gidan,sauranki jinin guda uku ki hau kan karagar mulkinki,wanda dama lokaci yake jira,idan kuma kika ƙi aikatawa …………
Bazan aikata ba daman,karku bata lokacinku,koh kasheni zakuyi bazanyi abinda kuke so ba sai abinda nayi niyyah,tsarinku daban nawa na daban,sannan sau nawa nake faɗa muku banason kiran ruhina da kuke batareda ixinina ba zuwa duniyar mafarki,idan har kuka cigaba da aikata hakan,toh zan samo hanyar yin abinda bakwaso kodah kuwa yah zama koni koh ku ne.~
Tashi nayi daga kan gadon ina kallom rufin ɗakin wanda nagama kwanan na na ƙarshe a cikinsa,tareda tunanin mutanen mafarkinnawa,ruwa na ɗauko a gefena na fara sha saida na shanye shi tass,natsani ƙishirwar dasuke sakani ina ji,wayonsu shine su ɗaɗe dani a duniyar mafarkin har sai na buƙaci shan jini a wajensu idan inaso naji dadai,saidai sun makaro,domin na koyi fitowa daga wajennasu koda suna so koba su so,nasan hakan bai yi musu daɗiba saidan babu yanda zasuyi ne.
Bankoma bacciba sai ƙoƙarin hada canjin wajen aiki da nakeyi,dan burina shine ina zuwa can na nemi aikina na cigaba dayi.
Washagari tun da hantsi motoci guda uku suka tsaya a ƙofar gida,ina jin dirinsu na tuno da motar alhaji bala dana ɗauko,wanda jiyah nasa burgu ya mayar masa kayarsa,dan dama banida niyyar riƙeta din din,saboda bana ra’ayin mallake abinda ba nawaba,dama na taho da itah ne dan yaji haushi.
Wanka na shiga nayi,kowa idan zan wu ce sai bina yake da kallo,kome suke kallo oho.
Saida nagama shiryawa na saka rigar dana bayar akayimin,surayyah ce ta nace sai tayimim kwalliyah,hakanne yasa na barta tayimin amma kuma baƙi yafi yawa a kwalliyar,dan jam bakimma baƙiƙƙirin aka saka hakama gira da kwalli,bataso yamda na bata kwalliyar ba saidai yazatayi dani.
Muna cikin yine saƙo yah taddani cewar baba umaru yana ƙirana,
Abinda ya tsana kenan wannan wa’azinnasu na munafurci,banda munafurci sun san fah mutum ba sajawa zayyi a sakanniba imdai har girmansa bai canja ba,kawai a damu mutum da iyayi kawai.
Lifayar kayan da ɗauka na yane jikina dashi kafin na fito zuwa dakim baba umarun,a zaune yake akam dadduma yana jan carbi,sallama nayi ciki ciki tah dole,shima murmushi kawai yasan dan dole nayi sallamr ba da san raiba.
“Toh sameemah allah ya kawoki lokaci kema zaki ɗakinki kaman sauran ƴan uwanki,ina miki fatan alkhairi allah ya zaunar daku lafiyah ya baku zuri’a dayyaba,ina yimiki nasiha da ki bi mijinki sau da kafa,sannan yi nayi bari na bari,banda musu da kuma tairin kai,dan nasanki sosai,saidai naga kaman kwannan kinyi hankali kaman ba lokacin baya ba,dan haka a zauna lafiyah ……..”
Surutunsa yake tayi ina jinsa,da ni mai saurin dariya ce ma dana tuntsure da dariyah,saidai kasshh ba komai bane yake sakani dariyah,yasakani a gaba yama wani surutu kaman ya samu yar shekara biyu,hmmmm.
Tun yana maganar a marmari har yafara gajiyah,rufewa yayi da addu’a,yana ƙara cewa na zauna lafiyah,inna rabice dake gefe take ɗan matse wata ƴar ƙwallah,tabbb lalllai mutanennan nifah suna bani mamaki,tashi nayi ganin innna rabi batada niyyar tashi nayi hanyar fita daga ɗakim ina yiwa baba umaru sallama,toh mezan tsaya nayi bayan yagama surutun.
A hanyah inna rabi ta isoni da ɗan sauri,batacemim komai ba dan itah yamzu abin yah fara daina bata mamaki.
Motar da aka kawo muka nufah,sauran motocin duk an cika su sai wanda zamu shiga nida inna rabi ce tah saurah.
A gidan baya muka zauna ina tsaƙiyarta itah da wata mata,wai naji suna kanwar iyah mai kalwace.
Maganganun da baba umaru yayi minne suke dawowa cikin kwanyah tah.
Me baba yake nufi ma tukunna,ai shikenan nayi hankali saina zauna a gidan sameer lafiyah?
Inaaaa hakan bazai taba yiyuwa ba,waisu nan a barikin sojoji,ai shiyasa aka haɗani dashi ana ganin babu abinda zan iyah,sai kuwa san ya kaini cikin gidansa,dan sai yah gagareshi samun kwanciyar hankali,ballanta kuma matarsa,dama naga rainine da itah,dan haka itah zan fara gyarawa zama tukunna,sai azo ta kan mazauannan gidan,duk wanda ya taboni koh bindiga ce shi ba sojaba saina saita shi.
Natsani zama da wasu,a gida ma zaman dole nakey ,shine harda suka min aure koh,hmmm bazance yasakeni na amma zanyi masa abinda dakansa zai gaji da zama dani.
Lallai basu san wacece sameemah ba,wasan yan zu za’a fara bugawa kawai.
Ina cikin tunani na saƙar zuci bansan lokacin da muka shiga garin porthacourt ba sai gani nayi mun doshi babban barkin sojojin mai kama da gari guda a girma,ko kalle kalle banyiba saboda wanann ba shine karona na farko a ganin barinkin sojojiba,naga wanda suka fi wannan ma girma da komai, sabani sauram mutanen ƴan tafiyar musamman ma wanda dama basu taba zuwa birni kaman hakaba.
Ba laifi yana da girma sosai dan saida muka ɗanyi tafiyah kafin muka zo bangaren gidajen manyan ma’aikatan.
Buɗe murfin motah kowa yayi yah fito yana tah wawware ido dan bawa idonnasa abinci.
Wani sojane ya taho yana wani taƙama da ƙasaitah,uniform ɗinsa na kalla kawai nasan wane muƙami ne dashi.
Murmushi nayi tareda cewa,lallai akwai aiki anan wajen sosai.
Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150
Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.
????Sadi-Sakhna________✍????????
(¯’•.¸,¤°’✿.。.:քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ.:。.✿’°¤,¸.•‘¯)
????•°• WASA FARIN GIRKI •°•???? {cigaban gidan gandu}
????11~12????
Wuceshi nayi nice ma ta farkon shiga cikin gidan,saboda su sun tsayah ɗari ɗari da kuma bashi amsa,hannu yaɗaga mim akan meyasa na wuce,kallo ɗaya nayi masa dana juya kafin na wuce ciki.
Da sauri inna rabi tah taho ta riƙe hannuna tareda yimin kallon tah gaji da halina,ko a jikina sai ma ɗauke kai danayi.
Babban falone yayimana salllama yasha kayan alatu irinna ƙyalelen duniyah.
Wasu manyan matane masu kama da hajiyoyi a zaune akan kujerun ɗaya bangaren,mukuma muka zauna a wanda suke kallonsu.
Dayake kafin mu shigo inna rabi ta sakamim baƙin ƙyalle a fuskata dan haka bana ganin fuskarsu saidai maganar su kawai,tsinkayo maganar wata daga cikinsu nayi wanda take cike da gadara da kuma isa.
“Toh da farko masu kawowa amarya barkanku da zuwa,saidai ina son sanar daku cewa nan gidan saleemah ne dan ita aka zo aka samu,karkuga cewa wai dan itah tana ƴar uwar miji ta nemi yi mata iko koh gadara,toh hakan bazai faruba,dan itah kanta dukiyar da sameer yake da itah da kuma ɗaukakar da kuka ganshi da itah har kuka laƙaba masa ƴar ku,duk mallakin mahaifin saleema ne,yanzu amarya zata buɗe mana kanta mugani kafin kuma mununa mata ɗakinta,kafin sannan kuma………”
Jin maganar nayi tah isheni haka zuciyata da kunnuwana baza su iyah cigaba da jin irin wannan kalar rainin hankalin.
Saurin yaye alkyabbar nayi ina kallonta ido cikin ido,ganin ɗan razanar da tayi ne tanan kallon lallen dayake hannuna na hotunan ƙwari da majicai na baƙin lalle anyi musu ado da jan lallene yasata zare idanu,su kansu wanda suka taho tareda dani basusan mai yake jikinba sai yanzu,surayyah ce kawai ta sani,ɗauke alkyabbar nayi daga jikina gabaɗaya nayi wurgi da itah a ƙasa,hoton macijin dayake wuyanane yah fito fili,zanen kansa yana kwance akan kinrjina wanda akayiwa ɗinkin mai buɗaɗɗen wuyah.
Tun daga kan kwalliyar da take fuskata da kuma irin nau’ina lallen dayake jikina mutum zai ɗauka daga cikin duniyar ifiritai na bayyano.
Kallon saleema nakeyi wanda tayi suman tsaye,da alamun bata san waye a cikin gyalenba sai yanzu ta tabbatar da wa zatayi zaman wani abu wai shi kishi.
Mayar da kallona nayi kan wacce take feso magana sakkanni kaɗan da suka wuce,ganin kallon bazai isheta bane yasa na matsa har inda take ina ɗora ƙafa ta ɗayah mai tsinin takalmi a kan hannun kujerar da take kai,dan dama ni ban cire takalmina ba daza mu shigo.
Fuskata nakai har wajen fuskarta,dan baifi tazarar yatsa ba na bari a tsalaninmu,ɗaga girar hagun nayi tareda kanne ido ɗaya sannan nace ,
“Ke….mekika ce maimaita naji,bazanyi taƙama da abin gidannan ba?,ke wacecs toh a gidan?da har kika samu ƙwarin gwiwar fadamin hakan,toh bari kiji na faɗamiki,tun daga kan itah matar tasa da kuma shi babu wanda ya isah yah takani,barekuma wani can banzar bazara baƙo a gidannan,itah kanta wacce kikeyiwa wannan aikin wato matar gidam ta fiki sanin wacece ni,ke bakisan komai ba a kaina,dan haka ina jan kunneneki da idan goda wasa watarana kikazo gidannan kikayi zancena ,sai na cire harshe fiyattttt ma kuwa,………….dan haka yanzu zaki iyah nunamin ɗakin dazan zauna ɗinne koh kuma har yanzu baki shiryah faɗan suanan ɗakin ba?”
Tsayawa nayi na bata ɗan lokaci saboda ta samu damar jan numfashin da ta riƙe shi tun ɗazu,ga kuma gumi dayake keto mata,duk da sanyin Ac din ɗakin.
Da hannu ta ɗaga tah nunamin ɗakim da takasa cewa komai da bakinta.
Matsawa nayi daga kanta domin tasamu ta sha iska,murmushi nayi mata tareda miƙe hannuna nayi wata miƙa kaman hannuna zai balle gida biyu,juyawa nayi na kalli mutanen da muka zo dasu wanda suma sukayi tsitt suna bina da ido.
“Kuje su nuna muku ɗakin dazaku zauna dan wancan nawane,kuma bacci zanyi na huta dannagaji,idan kuma wata tazo tah tasheni hmmmm”
Jiyawa nayi nasake kallon matan da suke gefen saleema,
“Sauran kuma na tashi naji kun cigaba da watsawa wanda muka zo tare magana,wallahi ko mai gidan bai isa kwatarku a hukuncina ba,zai fi mukuma na tashi na samu kun bar gudan”
Saida na zare ido tareda haɗe fuska kafin na faɗi hakan,har na fara tafiyah na juyo na kalli surayyah wanda itama mamakinnawa takeyi,duk da tasan hakan kadanne daga halina.
“Ke kuma zo mutafi dakinnawa akwai abinda zan faɗamiki”
Da sauri tah tashi zata biyoni,inna rabi tagumi kawai tayi,ba ko gigin biyoni ba,dan yamzu itama tasan halina.
Muna shiga ta maida ƙofar ɗakin tareda cewa,
“Yanzu anty sameemah me kikayi haka kenan?ƴan uwan ogan mijinki ne fah,amma kika yi musu haka daga zuwamki”
“Toh yan uwansa ƴan uwanane,kema ba surutu na ƙiraki kiyimin na,yanzu dai ciro mun kaya a cikin wajen kayannan tukunna,sannan idan kin ciro ki je ki dubamin matannan,duk abinda suakyi kizo ki fadamin,dan ba yarda dasu nayiba,ƴan tuƙa tuƙa kawai”
Surayyan ta buɗe baki zata sake cewa wani abu nayi saurin shigewa banɗakin.
Dan banson yawan surutun yanzu,ina jin dariyarta a ɗakin har kuma tayi shiru.
Cika bahon wanka nayi na shiga na kwanta,gaskiyah nayi kewar ƙasar palastine dan rabona da danayi wanka na cikin baho tun ina can.
Saida na kusa awa guda kafin na fito daga bandakim,shima ina fitowa na samu surayyah ta fitomin da kayan,dan haka ina sakawa nabi lafiyar gado.
Bangaren masu aikin gidan aka kaisu dan shima wajene mai zaman kansa,sun mafi sakewa a canɗin akan dakina,dan wallahi babu da matar da zan kwana tunda bani na gayyatosu ba ai.