WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL
WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL
????sameer a madubin gani????
Tun dazu nake zaune ina aiki amma nagaza tabuka wani abin kirki,daga na fara tubutun da shigar bayanai sai na ajiye,ni kadai na jera tsuka tafi cikin kwando ina zaune.
Na rasa ma abin da yake min daɗi,ni kaɗai nasan irin ƙalubalen dana ke shirin fuskanta na rayuwa da sameemah a cikin gida guda,kirjina sai bugawa yake yi lokaci bayan lokaci.
Ga saleema tun lokacin dana daukota daga gidansu tah daina yimin magana,ko na kulata ma saidai ta bar wajen,abin duniyah duk yah isheni.
Sallama akayi tareda bugo ƙofar office ɗinnawa,ina ɗaga kai mukayi arba da Ahmad babban abokina wanda tare muka yi karatu da kuma tafiyah service a Russia.
Miƙomin hannu yayi muka tafa kafin yace,haba mutumina kana ango wanda za’a kawo masa amaryah yau amma kuma kake aiki,wai yama naganka da damuwa a fuskarka,kamata yayi yau ka yini cikin fatin ciki ai”
Hmmmm kawai nace,dannasan idan nayi masa magana ma bazai fahimta na sam,dan haka babu ma wani zancen tsayawa bata lokaci akan maganar.
Wasu abokan aikimmune suka sake shigowa,sai tsiyah suke min,dole babu yanda zanyi na ajiye aikin tareda ta fiya gida.
Gidan su Ahmad muka wuce,dan shine zai auri suhaila ƙawar saleema watan jibi.
A dakinnasa yada zango,akan zasu rakani zuwa dare,saboda nace bazan yi komaiba dan haka dole suka ƙyakeni tunda basu san dalilina ba na ƙin yin komai ɗin.
Wajen ƙarfe goma na dare muka shigo cikin gannawa kowa a cikin motarsa,nidai binsu kawai nake duk abinda suka ce,dan karsu gane halin da ake ciki.
Falon babu kowa kaman ba bu mutane a gidan,ɗakin saleemah muka fara nufa wanda yake bangaren dama yana kallon wanda sameema take ciki.
Nufar ɗakin saleema muka farayi tukunna amma ƙofar ta ƙi buɗuwa tah kulleta,ɗan jimm nayi kaman mai tunani kafin na koma inda su ahmad suke,ɗan yaƙe nayi wanda yah fi kowa ciwo.
“Ina ga tayi bacci kaman”
Ɗaga kai sukayi alamar sun fahimta duk da basu yarda da abinda nace ba,ƙarbar ledar dayake hannun ahmad nayi ina yi musu murmushi.
Fatan alkhairi sukayimin kafin kowa yah shiga motarsa yah nufi gidansa.
Ajiyar zuciyah nasake ganin yanzu niƙadaine a cikin cakwakiyar nan babu kuma mai tayani yinta.
Ɗakin sameema na tura na shiga,a zaune na sameta ta saka kayan bacci gefe kuma tana ƙurbar tea a kofi,duk wanda ya kalle ta sai yayi zaton dama gidantane kuma ta daɗe a ciki,dan batayi kama da maryar da aka kawo yau ba.
Daga kai tayi ta saman system ɗin datake gabanta ta kalleni kafin na ɗauke kanta,daga nan bata sake cewa komaiba sai ma cigaba da aikinta da ta cigaba dayi.
Nima banyi mata magana ba,sai ajiye ledar nayi a kan drawar gadon da nake kusa da itah,juyawa nayi na fita daga ɗakin,har na fita naji muryarta tana cewa,
“Baka rufemin ɗakina ba,sannan kayi na farkone amma daga yanzu in wani abune ka fada nazo na ƙarba,banson a dunga shigomim ɗaki babu izini”
Jijjiga kai kawai nayi na koma falo na zauna,yazanyi allah ya hadani da mata,mabanabanta,daga wacce sakalcinta yayi yawa sai wacce sakalcin matan ma bata iyaba kaiiiii.
Ina nan zaune na kunna kallo amma hankalina kwata kwata baya kan kallon,yana kan yanda zamyi na magance abunda yake shirin faruwa a gidana.
Alamun wulagawar mutum nagani yah shiga kicin,wanda ban ma kula sanda ya wuce ba,saida tah fitone na kula a she sameemah ce ta ɗauko plate daga kitchen ɗin.
????sameerah a madubin gani????
Har dare yayi amma na gagara bacci saboda halayyar umaruje tun ba a je ko ina ba ta fara canjamin,dan yanzu nakula akwai wacce yake so,suke wayah kullum,idan na tambayeshi ne kawai gani gashi Bayamin musu,amma idan abu a wayane cewa yake cewa bai sani ba ɗin,danaga hakanne na fara lallabashinsa dan a zauna lafiyah,saidai naga abin kaman gaba yakeyi ba baya ba,
Yanzu ma zaman jiransa nakeyi tun safe bai shigo gidan ba har yanzu,gashi gobene tafiyar sa Dubai,abin takaicin waccen shegiyar uwartasa.
Ina cikin safa da marwan na juyo kenan muka haɗa ido dashi sai layi yakeyi na maye,ga kuma zagi dayake da ɗurawa,takaicine yah kamani ga warin giyah,na rasa ma da wanne zanji,ni gsni nakeyi gwada ma salma koba komai alhaji bala baya shan giyah,sannan ba itah mijinta zai tafi yah bari ba,dui da itam da itah da babu duk ɗayah ne a cikin gidan,dan hajiyah mairo tafi ƙarfin tunanin mutum.
Tallafoshi nayi tareda tsinke tunanin danakeyi ganin yana ƙoƙarin hawamin gado a haka,tureni yakeyi yana maganar da ni kaina banajin mai yake faɗa.
Daƙyar allah yabani iko na cire masa rigar jinsa da takalmimsa kafin ya kwanta.
Bakajin komai sai minsharinsa kawai,dan baccinsa yafara hankali kwance,hmmm ga kuɗi da jin daɗi amma babu kwanciyar hankali kwata kwata.
Da safe da wuri na tashi nayi abinda zanyi na tafi madafar abinci,dan yanzu duk mune muke komai na gidan kaman yamda hajiyah mairo ta faɗa.
Har nagama abinda zanyi na fita umaruje bai tashiba,nima ban tasheshi ba na bar ɗakin zuwa aikin dazanyi.
A wajen nasamu salma wanda tarigani zuwa yau ba kaman kullum ba,kallonta nayi ban cemata komaiba,itama bata kulaniba da babu wanda yake yiwa wani magana kaman bamu san junaba,kowa tasa ta fishshsheshi.
Kayan abincin muka fara haɗawa,dan ma yanzu aikin yaragu saboda babu na ƴan sadaka,mu kaɗaine kawai.
Bamu kai minti ashirin ba a wajen muka kammala tsaff,nice na wanke kwanukan da mukayi aikin yayinda ita kuma salma ta kai abincin wajen cin abinci.
Saida muka gama kafin muka jiyo hayaniyar hajiyah mairo itah da alhajin suna saƙƙowa,gaishesu mukayi kafin muka ja kujera kowa ya zauna.
Har an fara zuba abinci hajiyah mairo tah kalli kujerar umaruje babu kowa akai,wani kallo ta watsamin kafin tace,
“Ke ina mjinki ban ganshi a wajen cin abinci ba?”
“Uhmm dama mommy yana baccine,tunjiyah daya dawo yana maye na giya bai tashiba”
“Mtsww baki san yanayin kulada mijiba bare kuma sirrinsa”
Tashi nayi nayi hanyar sashenmu domim tashinsa,dama da gangan na faɗi har da giyar dayasha dan taji haushi,duk da nasan ba komai zasuyi mar ba daga itah har ubannasa.
Lokacin danaje tashinsa har yah tashi ya shiga banɗaki sai ƙarar ruwa dana ji kawai.
????sameemah a madubin gani????
Lokacin dana buɗe idona daga bacci samun kaina nayi kwance a kan sabon gadon da aka mallakamin a matsayin nawa.
Hasken rana ne yake shigowa ta windon ɗakin da alama hantsi yayi duk ina bacci,dama kuma ban kwanta a da wuriba ina tah shirye shiyen yanda zan kai takardar neman aikina a nan garin,wanda jira nake ayi kwana uku na fita neman aiki kar lokaci ya ƙure.
Surayyah ce ta shigo ta tiren abinci a hannunta,a jiyewa tayi tana murmushi,wani lokacim har mamaki take ban,bata fushi abinda koyaushe tana cikin murmushi.
Gashi tayi haske abinta saboda ƙaramin cikin da take dashi,kallonta nake yanda take zuba shayi akofi tana kuma gulmar su inna rabi sun cinye abinci mai yawa kuma basu ƙoshiba,saikace masu cikin rumbu kalan su jawo mana magana a wajen mutaneen gidan.
Bance mata komai ba akan zancennata dan ba abin mamaki bane zasu aikata,musamman ƴan ƙauyen da baba umaru yah nace sai an taho dasu.
Bayan mungama karyawa nne na shiga wanka,dan yamzu wankana zai dawo saboda ga ruwa ko wanne lokaci,dama na saba da wanka akai akai,rashin sa ne a gida yasa nake yin guda ɗayah.
Wasu fararen kaya nasaka acikin kayam da aka sakamin a cikin ɗakin,dogon wandone da riga iyah gwiwa sai kuma ɗan mayafi.
Lokacin dana fito zanje sashen da su inna rabi suke ma’aikatan gidan sai kallona sukeyi har na isa wajen.
Banyi sallama na shiga kawai nayi,gabadayah a iyah kwana ɗaya duk sun birkice falon,kallon wajen nakeyi da mamaki,da guntun biredi ruwan shayi akan kujera harda yaro mai fitsari.
Dan takaici koh magana banyiba,inna rabice da kwarin gwiwarta tace,
“Amarya bakya laifi,yah kwanan baƙunta kuma,ya mijinnaki da abokiyar zaman,ɗazu yazo nan muka gaisa ai zai fita aiki,yace ma mushiryah motoci su mayar da mu”
“Toh ashe kin ganshima kuma kike tambayata ya yake,ni babu wanda na haɗu dashi dan tashina kennan,itama da kike tambayata itah ban ganta ba,yanzu dan tsabar nuna hali kuga yanda kukayimusu da muhalli,kaman awaki sunyi kalacen safe?”
Wata ce daga can gefe da kofi a hannunta tace,
“Lahh wai waje,bamu kohiii ba ma,gahii masu aikin sunƙi karo mana,dan sunga muna ƴan uwan amaryah,hiiine nace tunda kinzo me zai hana ki ƙaro mana,wajene ina ba ta ziri ba bazaka ƙara dawowao ba bare kaci mai daɗi aradun allah”
Kallonta nake kaman na shaƙetah.
“Baku kohii ba,toh karku kohiiin ƴan kohin uwa kai,nabi kohin da gudu,wallahi banga laifinta ba taƙekin kuzo mata gida,ku kalli yanda kuka maiida wajennan,kallai uban kulolin da aka ciko da abinci kaman na mutum hamsin,amma ku iyah goma kun tashi dashi,toh wallahi naji wacce tace bata koshinba,kuma kuna gamawa babu mai barin gidannan saikuna gyara wajennan tassd,bari ma ku gani na karbo muku tsintsiyah”
Tashi nayi na daure fuska,saida na surfesu tass,kowa tayi tsuru tsuru taan jina,haba mutum bai san komaiba sai ci kawai,kaman jaki.
Fita nayi zuwa ɗakko musu tsintsiyah kowa saitattare na gabanta takeyi,mai ɗan ta kuma da yayi fitsari ta tafi nemo ruwa.
Hmmm karutai kawai aka ce basaji…….