NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 1

*_????WUTSIYAR RAK’UMI….!!????_*
               _(Tai nesa da k’asa)_
                 *_Bilyn Abdull ce????????_*


*بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ* 

_In the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful._


*_Alhamdulillahi, barkanmu da dake saduwa a wanan littafi WUTSIYAR RAƘUMI…., ALLAH ka bani ikon rubuta abinda zai amfani al’ummar MANZON ALLAH, ka tsare harshena da hannayena rubuta abinda zai cutar daku dani baki ɗaya????????????_*

*_Ya rabbi ka gafartama masoyina, mahaifina, da dukkan sauran al’ummar musulmi tundaga zamanin Annabi adam har kawowa yau????????????_*

_Ban yarda wani wani yaymin amfani da buk ɗinnanba ta kowacce hanya sai da izinina????????????._*_No. 1_*

                 
                 *_ƘAUYEN ƊILAU_*


          Tun daga farkon dosowa kwanar gidan zaka farajin luguden daga da taɓare, yayinda mata ke arerewa da shewa irinna nishaɗin madaka, hardama masu buɗe hanci su callara guɗa a kwashe da dariya ana ƙara ƙaimi wajen dakan surfen masarar tuwo ko dawa da akeyi.
      Na kutsa kai cikin gidan domin ganema idona wainar da ake toyawa, mata ne da adadinsu zai iya kai goma sha, sun kasu group-group suna daka a turame da aƙalla zasukai huɗu. A gefe kuma ƙarƙashin inuwar dalbejiya wasu matanne dasuka ɗan manyanta zazzaune suna tasu hira da taɓin daddawar sayarwa ta ɗaya a cikinsu, sai wata can gefe tana faman hura wuta a gabanta da bokitan fenti biyu, maida kallona nayi ga wadda ke gefenta tana ta motsa wani abu a tunya tamkar taliya, sai zabga zufa take saboda hucin wutar da itama take aiki kusa da ita, sai kuma da’irar yara daketa sheƙi da ƙasa suna wasa.
       Wanda bai san BABBAN GIDA ba a garin Ɗilau idan yazo zai iya rantsuwa taron biki sukeyi kona suna, sai dai sam ba haka baneba, dukkan waɗannan jama’ar da kuka gani mazauna gidanne, a hakama babu wasu yaran masu wayo da kuma mazan gidan,  wasu sun tafi binni neman kuɗi, yayinda ƙalilan a cikinsu suna waje a majalisun da mazan ƙauyen kan kafa, yara kam wasu an aikesu wasuko hidimar gabansuce ta fiddasu.
             Duk bayanin dazan muku gameda alaƙar jama’ar wannan gida bazaku fahimtaba, dan kuwa ƴaƴan wane dana ƙanne da ƴaƴan ƴaƴa da matansu, kai harma da jikoki sun auro suma kuma sun hayayyafa.
      Malam Buhari shima mazaunine a wannan gida, kuma yana ɗaya daga cikin wannan ahali, matansa uku da ƴaƴa goma cif, matarsa ta farko itace Yalwa, amma suna kiranta da suna baba yalwa, yaranta biyar, uku maza biyu mata, kasancewar mazan sune manya duk sunyi aure, suma matansu na nan acikin gidan, sai ta biyu, Ɗahara, itakam ƴarta ɗaya Ummukulsoom, haihuwarta kusan huɗu amma suna wabi (suna mutuwa bayan ta haihu), sai akan Ummukulsoom ne ALLAH ya barmata, bayan haihuwar Ummu takuma samun ciki, a wajen haihuwar cikinne ta rasu, lokacin Ummu tanada shekara Uku a duniya. Sai amarya Asabe, yaran Asabe huɗu, mata uku sai Namiji ɗaya shine auta.
     Sana’ar Malam Buhari itace Saƙar mafitai da tabarma, fai-fai irinna fulani dadai sauransu, shiyyasa ake cemasa MAI KABA. Bama shiba duka jama’ar gidan wannan sana’ar suce, sai dai kuma wasu sun bari tuni, sai ƙalilan a matan gidan keyi, shidai ya riƙe gam kuma yanacin amfaninta, dan yakan ɗauka yashiga birnin Kaduna da Zaria ya sayar ya dawo gida, wani lokacin kuma ƙanwarsa Laraba dake aure acan take aiko ɗanta ya karɓa kokuma ita tazo da kanta.
      Da wannan sana’ar malam Buhari ke riƙe da iyalansa, sai noma da yake a kowacce damuna.

       Matasan ƴan mata kusan bakwai da shekarunsu bazasu gaza sha biyarba suka shigo a tare, kowacce kanta ɗauke da bokitin fenti alamar ruwa suka ɗebo. Sannu matan dake surfe a tsakar gida suka shiga yimusu, suko suna amsawa kowacce na nufar sashensu.
      Baba Yalwa dake faman zufa a gindin murhu ta riƙe ƙugu bayan taja murfin tukunyar taliyarta ƴar murji ta siyarwa ta rufe.
     ”K Hadiza ina kuka baro Umma?”.
     Wadda aka kira hadiza ta sauke ruwan kanta tana ɓata fuska, “Yo Baba yalwa tana can baya wannan mayen saurayin nata Basiru ya tsaidata wai zai koma makaranta suna sallama”.
     Ashariya baba yalwa ta lailayo ta dire, “Kai amma ƴarnan anyi tsinanniya, to ni kodai lallatseta yakeyima shiyyasa sukabi suka nanuƙe ma juna?”.
     Kwashe da dariya matan gidan sukayi, dukda kuwa akwai surukanta matan ƴaƴanta a ciki. Kafin wata ta samu damar tofa tata Ummu tayi sallama. Tamkar zasuga abinda Baba yalwa ta ambata a jikin Ummu, duk sai suka zuba mata idanu. 
     Gaba ɗaya sai Ummu taji ta ƙara muzanta, sum-sum ta nufi inda baba yalwa take a gindin murhu…
     “Sai yanzu kuka gama iskancin?”.
    Furucin baba yalwa ya daki kunnen Ummu, cikin rikicewa ta ɗaga idanunta da har sun fara tara ƙwalla ta dubeta, “Baba iskanci kuma?”.
     “Oh tambayata ma kike na sake maimaita miki?”.
     A hankali Ummu ta girgiza kanta alamun a’a.
   Baba yalwa taja tsaki, “ki kikaima Hanne ruwan wajenta, dan ita ta rantamin  na ɗora taliyar, tun da ke kinacan wajen saurayi, da kinsan ma bazaki ɗebomin da wuriba ai da bakice zakijeba mai mugun hali kawai, yadai gama lalataki yagano wadda ta fiki a birni ya aure”.
      “Wannan magana ai zaune take baba yalwa, tunda iyayensa suka bijirema wannan auren ai nasan hanyar kuɓuta suke nema”. ‘Cewar Rashida dake ƙoƙarin dama kunun tsamiya itama na saidawa ne’.
      Baba yalwa ta kyaɓe baki tana sauke tukunyar taliyarta a kasa, “To ai idon Ubanta ya rufe ya kasa gane haka rahida, saboda ita ƴar mai ce ba’ason ɓacin ranta, muna nandai maga yanda za’a ƙare kuma ai”.
     Nanma dariya matan suka sanya, kowa yashiga jifan Ummu da magana mara daɗi.
      Ummu dai batace komaiba, ta ɗauki ruwan ta nufi sashen Hanne matar yayansu ta juye mata ruwan ta fito, ganin sauran yaran duk bazasu komaba itama saita nufi sashensu ta ajiye bokitin tana cire hijjabinta daya jiƙe da ruwa, yayinda ƙasan zuciyarta ke ƙuna da tausayin kanta. Tabbas ƴaƴa da yawa marayu sukan tsinci kansu a gararin rayuwa fiyema da nata, maraicin rashin uwa maraicine mai ciwo, sai dai babu yanda bawa ya isa jayayya da hukuncin ALLAH, bayan rasuwar mahaifiyarta riƙonta ya koma hannun kakarsune data haifi mahaifinsu, wato Innayo.
        Kamar yanda na sanar muku tun farko mahaifiyar *_Ummukulsoom_* ALLAH yay mata rasuwa tun tana shekaru Uku a duniya, itace matar Malam buhari ta biyu, ALLAH ya jarabceta da haihuwar ƴaƴa suna wabi, (ma’ana suna rasuwa bayan ta haihu), saida tai haihuwa huɗu ƴaƴan na komawa sanan ALLAH ya zaunar mata da Ummukulsoom, an tayata murna sosai har ALLAH ya sake bata wani cikin, lokacin haihuwarsane kuma ALLAH ya ɗauketa itada cikin gaba ɗaya. Ta tafi tabar marainiyar ƴarta Ummukulsoom.
      Bayan rasuwar mahaifiyar Ummu rainonta ya koma hannun kakarsune, wato mahaifiyar malam buhari innayo, wannan shine dalilin tashin Ummukulsoom cikin tsananin gata, dan innayo batason taji kukan Ummu, idan kuwa taji saitabi ba’asi, daya kasance cikin matan gidanne sai sun fuskanci ɓacin ranta, idan kuwa yaƴansune saita ramawa Ummu.
      Wannan gata da Ummu ke samu fiye da duk yaran gidanne yasaka kowa tsanarta, ko aikane indai Innayo na kusa babu wanda ya isa saka Ummu ko miƙomin. Shi kansa Malam buhari abun na damunsa, dan matansa kullum cikin ƙorafin mahaifiyarsa tafi kaunar Ummu, bata son ƴaƴansu suke. Idan yatari innayo da roƙon taɗan dinga sassauta son da takema Ummukulsoom kodan sauran yaran saita haushi da masifa, har saiya koma yana hurwar bata haƙuri.
        Abin tausayi ga Ummu shine rasuwar innayo lokacin tana shekara tara a duniya, dukda batada girma sosai tashiga damuwa, musamman idan ta zagayo tana buƙatar wani abu ko an daketa tazo kawo ƙara, saita iske ɗaki wayam babu innayo. Haka zata zauna taita kuka tana ƙwala ma innayo kira.
      Wannan halin data shigane ya haddasa tausayinta mai ƙarfi a zuciyar Malam Buhari, gashi dangin mahaifiyar Ummu sun roƙi a basu ita ya hana, dan bayaso ta banbanta cikin ƴan uwanta. Dole suka haƙura suka bar masa ƴarsa.
        Kasancewar sana’arsa bata zaman gida bace ko yaushe sai ya ɗauki amanar Ummu ya damƙama matansa, tareda badata ɗakin uwar gida baba yalwa.
     A gabansa sun amshi wannan amana, harda faɗin ALLAH ya tayasu riƙo.
      Amma malam Buhari na ɗaga ƙafa yakoma wajen sana’arsa sai abubuwa suka canja ga Ummukulsoom, dan kuwa baƙar wahala da tsangwama ta fara fuskanta kai tsaye gasu baba yalwa da ƴaƴansu, kai har dama duk jama’ar gidan. 
         Dukda ƙanƙantarta hakan baya hana a bata uban aikin da yafi ƙarfinta, idan ta ƙiyi kuma a lakaɗa mata duka, ko a saka su Azima sa’anninta su doketa dukda ta girme musu.
     Tun tana faɗama malam buhari idan ya dawo harta fara sabawa tabar faɗa, dan daya koma za’a kuma tsangwama mata fiyema da da.
    Ahaka suka cigaba da zuwa firamare da aka sakasu ita dasu Nusaiba, yayinda suke kuma wayo da banbance dai-dai da akasinsa. Ƙiri-kiri dai Ummukulsoom ke ganin banbanci ga matan Uba, dan zasu yima ƴaƴansu abu amma ita ko kallo bata ishesuba, a tila mata uban aiki amma su Azima na ƙofar gida suna wasansu ko tsakar gida, abinci dai Alhmdllh batada matsalarsa, dan suna bata taci ta ƙoshi, idanma an hanata zataje gidan kakanninta iyayen mamarta taci ta ƙoshi.      
        Ko faɗa tayi dasu Nusaiba koda itace mai gaskiya sai a bata laifi, harma asaka cikin yayyensu wani ya zaneta.
      Idan kaga Ummukulsoom tayi farin ciki to malam buhari yazo gida, a lokacin babu mai cutar da ita sai dai a ɓoye.
       Tun innayo nada rai basiru ɗan maƙwaftan su Ummukulsoom ke tsokanarta da budurwarsa-budurwarsa, hakan bai saka kowa ɗaukar abin da muhimmanciba, dan shima yarone sosai, baifi shekaru biyar zuwa shida yabama Ummu ba, bayan rasuwar innayo halin da Ummu take ciki na wahala ga matan Uba sai Basir kan nuna damuwarsa sosai, idan yaganta tana kuka shine mai lallashinta, idan tace su Nusaiba ne suka daketa saiya rama mata, dan iyayen su Azima sunsha kai kashedi gidansu basiru akan ya kiyayi ƴaƴansu, koda iyayensa sun masa faɗa gobe bazai fasa ramawa Ummu ba idan an cutar da ita.
      Ahaka Basiru yagama firamare shima yabi ayarin yaran garin maza wajen tafiya sakandire, Basiru ƙyaƙyƙyawane sosai, dan ya ɗakko usul na mahaifiyarsa ne data kasance bafulatana, hakanne yasaka yake ɗaukar hankalin mafi yawan yaran garin, sai kiga kowacce tana fatan Basiru ya sota. Hakan na damun Ummu, dukda bawani girmane da itaba, dan soyayyar Basiru ta girmi tunaninta, takan jishi sosai a ranta.
      Rayuwar tacigaba da tafiya a haka har suka kammala firamare, Ummukulsoom na cigaba da fuskantar ƙalu balen rayuwa kala-kala a gidansu, ga tsangwamar ƴan uwanta su Nusaiba dasu Hadiza yaran gidan, duk hanyar da zasubi su dizgata sun sani. Ita dai sai dai tasha kukanta ta share hawaye, randa suka kaita bango itama ta jibgesu, suna dawowa gida iyayensu su kamata su doka.
           Bayan kammala firamare ɗinsu malam Buhari ya yankema zuciyarsa zaiyi ƙundun bala yakaisu makarantar gaba da firamare, wato sakandire (Secondary school).
          Dukda ba’a taɓa hakaba ga ƴaƴan gidan, dan daga firamare ake tsigesu ai musu aure, wasuma basayin firamare ɗin saboda iyayensu basuda sha’awa.
     Amma yayun su Ummu mata biyu da akaima aure, Rabi da Zainaba duk sunyi firamari. Shikuma malam Buhari ƴar sana’arsa dayake fita cikin birni yana ganin yanda yara ke zuwa makaranta sai abun ya birgesa, shiyyasa yay sha’awar saka Azima da Nusaiba da Ummukulsoom da ayanzu sune suka kammala firamare.
        Ummukulsoom tayi farin ciki, dan a koda yaushe Basirunta kance ALLAH yasa abarta tacigaba da karatu, danshi babansa yace bazai masa aure yanzuba sai yaje jami’a, bayaso yay rayuwa irinta yaran garin, auren shekara ashirin. Ummu dai takan sauraresa amma tasan hakan dakamar wuya, tunda sauran yayunsu su Zainaba daga firamare akai musu aure. Sai kuma kwatsam Baba yazo musu da wanan albishir. Aiko da gudu tanufi gidansu Basiru ta sanar masa, daɗi ya kamashi harda rawa agaban Ummu.????
          Ɓangaren iyayen su Azima kam casukai basu yardaba, haka kawai ƴaƴansu suje su fanɗare, inama laifin wadda sukai anan garin, sudai yaransu sunada mazajen aure, aure suke so ai musu.
       Malam buhari yaja dogon tsaki ya buga rigarsa yabar musu gidan.
       Hakan da yayi ya tabbatar musu da basu isaba kenan, sai hankalinsu ya ƙara tashi, kowacce takai ƙarar malam buhari wajen iyayenta akan aimasa magana, mizaisa yakai musu yara wata makaranta bayan sauran yaran gidanma bama kowa keyin primary ɗinba.
       Maganar tai masifar ɓata ran malam Buhari, ya dage akan babu fashi sai yaransa sunje babbar makarantar sakandiri, su shikenan gidan nasu baza’a samu cigaba ba?, ALLAH ya basu tarin ƴaƴa maza da mata amma yaran maza ma dake sakandire ɗin basufi uku ba, bayan kuma garin ƴaƴa da yawa nayin karatu, harma da matan, saisu gidansu aƙida ta hanasu saka nasu ƴaƴan. To shikam wannan rayuwar ta ishesa hakanan, yanason bama ƴaƴansa ilimi gwargwadon ƙarfinsa, gasu Zainaba nan shekara biyu da aure amma duk sun tsofe saikace ƴan shekara arba’in, kuma ba komai bane sai wahalar rayuwa da rashin wayewar kai na ilimin addini dana zamani.
        Ganinfa Malam Buhari yaƙi tanƙwaruwa dole suka shafa masa lafiya ya saka yaransa makarantar jeka ka dawo ta sakandire dake cikin garin Kudan, dan ƙauyen ɗilau yana gab da Kudan ne.
      Babu irin shige-shigen dasu baba yalwa basuyiba akan karsu Azima suje secondary amma lamari yaci tura, dansu babban tashin hankalinsu ƴar tallar da yaran suke musu suna samo taro da kwabo, yanzunkam babu dama, idan suka fita makaranta tun safe sai bayan azahar suke dawowa, dasunce suyi abu zasuce sun gaji, Ummu ce kawai batada wannan damar, ko tana shigowane akace ga aiki dole tayisa komin gajiyar da tayi.
    Komai dake faruwa yana dawoma malam buhari a kunne, amma sai yay kunnen uwar shegu da batunsu, har iyayen matan nasama ƙin zuwa kiran da sukai masa yayi, danshi yaɗau aniyar insha ALLAHU sai ƴaƴansa sun ɗanɗani zaƙin ilimi.
          Ansha surutai kam marasa daɗin ji akan karatun su Ummukulsoom a gidan, daga baya kowa ya kama bakinsa kuma.
     Ummukulsoom zata iya cewa tafi kowa murna da makarantar, kodan cikama Basiru burinsa, sannan zata samu sassaucin uban aikin datake tiƙa a gidansu da tsangwama, dukda dai tana tare dasu Azima ananma.
      Su Azima kam suna cikin damuwa sosai, dan sufa hankalinsu duk yana kan aure, harsun fara ƴar sayayyar kayan ɗaki da yara ƴammata kanyi ranar kasuwa, amma shine baba yazo ya kawo wanan batun.
         A hankali suka fara sakin jikinsu da sabo da makarantar, harma da yin ƙawaye, Tun su Azima na takaicin wannan makaranta har suka hakura suka fara sabawa, ita dama Ummu ba’ajin bakinta a masu korafi. 
      Sun shiga secondary babu daɗewa Basiru ya zana jarabawar ssce shida sauran yara ɗalibai ƴan uwansa.
      Bayan fitowar jarabawa kuma saiya haye da maki mai ƙyau, dan dama basiru akwai ƙoƙarin tsiya. Babu ɓata lokaci iyayensa suka hau masa shirin komawa zaria da zama, gidan ƙanwar mamarsa, dan mijinta keta ƙoƙarin nema masa gurbin karatu a A.B.U Zaria.
    Sanda komai yagama kammala ya shirya ya tafi, ranar Ummu tasha kuka sosai, su Nusaiba suka sata gaba suna dariya da mata shaƙiyanci, ita dai bata kulasuba.


★.★.★.★.★.★.★.★.★.★.★

    Rayuwa tacigaba da gudu da sauri har zuwa sanda su Ummu suka shiga aji uku na sakandire, bayan sun zana jarabawar jsce.
          A sannan yara ƴammatan gidan su Hadiza iyayensu sukai shirin aurar dasu, kuma duk sa’annin su Ummu ne, Wannan yasaka iyayen su Azima suka tada hankalinsu da bala’in sufa aima ƴaƴansu aure, bazasu yarda yaran gidan duk suyi aure subar nasuba, dan abinda suka kula samarin garin sun fara faɗin ai yaran sunfi ƙarfinsu saboda suna boko.
     Hankalin Ummukulsoom ya tashi matuƙa ganin baba ya amince, ita kuma tanajin daɗin karatun sosai, sannan Basir ɗinta kusan shekara ɗaya da rabi kennan baima zo gidaba, yana Zaria karatu ya ɗauke hankalinsa, tsakaninta dashi sai dai wasiƙa da yake aiko mata idan babansa yaje dubashi saiya bada a kawo mata.
      Badan Malam buhari yaso datsewar karatun su Ummu ba yabada damar samarunsu su turo iyayensu, a kwanaki kaɗan aka kawo kuɗin Azima da Nusaiba, kuma duk ba ƴan cikin ƙauyen bane, Azima cikin Kudan, sai Nusaiba zata auri malaminsu ɗan zaria, za’a kaita zaria kenan.     
       Wannan abu yayma iyayensu daɗi, dan a ganinsu ƴaƴansu sunyi gaba.
       Iyayen Basiru kam haƙuri sukazo suka bada akan sudai basu shiryaba, dan Basiru karatu yakeyi yanzu, idan malam buhari ya amince nanda shekaru Uku babu damuwa, sannan Basiru ya kammala karatunsa, itama tagama sakandire.
       Abin ya taɓa zuciyar malam Buhari, sai yace suje zaiyi shawara to.
     Bayan tafiyarsu yakira Ummu ya sanar mata, sannan yabata shawarar mizai hana ta fidda wani mijin a samarinta, tunda taga sauran ƴan uwanta har an kawo kuɗin aurensu, kuma harda sauran yaran gidan ƴammata za’a haɗa, bazai so ita kaɗai abartaba, yanzu haka nata kawai ake jira a tsaida musu rana.
     Kuka sosai wannan magana ta saka Ummu, dan itadai babu wani saurayi da take kulawa a ƙauyen sai Basiru ɗinta, dan shi kaɗai take tsananin so da ƙauna.     
         Juyin duniya anyi da ita akan ta amince da auren wani saurayi Tanimu da yace yana sonta amma tace itadai Basiru kawai.
      Ganin zata saka kanta a wani hali sai malam Buhari ya yanke hukunci barinta ta koma makaranta da zaman banza da zatayi na jiran Basiru. Wannan abu yamata daɗi, harma fuskarta da yanayinta ya nuna.
    An aje batun Ummukulsoom gefe a yanzu haka, sai shirye-shiryen bikin ƴammatan gidan akeyi watan sallar tsoffi.
      Da baban Basiru yaje dubashi shine yake sanar masa, wannan daliline ya saka basiru zuwa ganin gida babu shiri, Ummu tayi murna da ganinsa, yayinda sauran yara ƴammatan garin suka ruɗe da sake ganin Basirun ya canja fiye da da, yasake zama ɗan gayu, su kansu sauran yaran gidansu Ummu su Hadiza dasu Azima hankalinsu ya tashi, sukazo suka barbaɗama iyayensu zance, dukda takaici ya kamasu babu yanda zasuyi, sai dai sunata ma Ummu fatan tsiya ALLAH yasa anan gaban yace yafasa aurenta.
    Wannan zuwa da basiru yayi kwanansa bakwai, shine yau zai koma makaranta suka tsaya sallama da Ummu ta ɗebo ruwa………✍????


*_MUKOMA LABARI⛹‍♀_*

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button