NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 2

*_NO.  2_*  
…………Duk hayaniyar yara da matan gidan na sayen taliyar baba yalwa da kunun Rashida Ummu na jiyowa daga
sashensu, sai dai ko motsi batayiba balle yunƙurin leƙowa, bata da ko sisi, kuma baba bayanan yana kaduna, tasan kuwa daga Rashida har baba yalwa babu mai bata kayan sana’arsa. Motsin da tajine yasata ɗago idanunta.
     Mariya ƙanwarsu ce ɗauke da robar tanata turiri, da alama taliyace a ciki, ta zauna kusa da Ummu tana faɗin “Umma kinga taliyata, inna ta saimin ta ahirin, nima ina da goma nace a ƙaramin”.
    Cikin murmushin ƙarfin hali da haɗiyar yawu Ummu tace, “Aiko na tayaki murna mariya”.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});    Ƴar dariya yarinyar tayi, kafin ta saka hannu a taliyar tana tsakura kaɗan da yarfe hannu saboda zafi. Ummu tace, “Mariya kije ki ɗakko mafici ɗaki saiki fifita, cin abinci da zafi bashida ƙyau ko kaɗan”.
    Mariya ta miƙe tana jan majina da suɗe hannunta, “To Umma tsaremin nadawo, karki bari akuya tacimin”.
    “Bazan bariba insha ALLAHU”.
    Mariya na barin wajen Murja ta shigo itama, zama tayi kusa da Ummu tana cewa “Wai dama kina nan Umma?”.
       “Wlhy ina nan Murja, yau bazaki tallar kunu bane?”.
      “Aina rantse bazaniba alkur’an, kema nazo baki haƙuri akan abinda jama’ar gidanan suke miki, wlhy sam basa ƙyautawa, sun manta keɗin marainiyace, Umma wai miyasa da Basiru yazo baki sake lallaɓashiba kuyi aurenku ki huta da halin banza na mutanen gidannan”.
     Murmushi Ummu tayi, ta muskuta zamanta da miƙe ƙafafu yanda zataji daɗi, “Kai Murja kibar cewa haka dan ALLAH, koyaya banida kamarsu, kumani wlhy yanzu abin baya damuna, maganar Basiru kuma ai ba laifinsa bane, iyayensane sukace saiya gama karatunsa, kuma nima ina son nayi karatu mai zurfi danna taimaki ƙauyennan, kina ganin babu wata fitacciyar yarinya mace a ƙauyenan data taɓa wuce makarantar gaba da secondary fa……”

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});      Cikin hangame baki murja ta katseta, “Wai Umma tsaya, kina nufin wata bokon kike sha’awar ƙarayi bayan wadda kukayi dasu Azima?”.
      “Murja kinada abin dariya wlhy, to ai bamu gamata ba ma, dan dai an dakatar damune, amma saura shekara uku mugama”.
     “Shekara uku? Kin tsoge sannan Umma, Inaga lokacin haihuwata biyu”. ‘Cewar murja cikin ɗora hannaye duka a kai????????’.
       Dariya itadai Ummu tahau yi, kafin tabama Murja amsa Mariya ta dawo, dan haka sukaja bakinsu sukai shiru. (Murja tana cikin ƴammatan gidan da za’aima aure, sosai Ummukulsoom takejin daɗin zama da ita, dan tana nuna tausayinta fiye da sauran yaran).

      Har taliya da kunu suka ƙare babu wanda ya kira Ummu yaymata koda tayine, bata damuba, taje ta duba tukunyar tuwonsu taga a kwai sauran gutsatstsari, tsama tayi tazuba miya akai tafita ta ɗumamo a inda su baba yalwa sukai girkin kayan sana’arsu. Babu wanda yace cikanki, itama bata kula kowaba tagama takoma lungunsu tai zaman cin kayanta.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

      Yau takama alhamis ranar da kasuwar Ɗilau keci, da yamma bayan su Azima sun gama hidimominsu sukai shiri tsaf domin zuwa cin kasuwa, tareda aiken iyayensu na sautun abinda za’a sayo musu. Ummu dai na zaune tsakar gida saman turmi, babu alamar ma tayi wanka, hakanne yasaka Murja data fito daga ɓangarensu cikin shirin fita banka mata harara.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});     Ummu tai dariya tana dirowa a saman turmin, “Murija mikuma ya faru da harara haka?”.
     “Ban saniba” ‘cewar Murja tana kumbura baki’.
      Ummu ta haɗiye dariyarta da dafa kafaɗar Murja, “Sorry sister, wlhy Baseer ya hanani zuwa kasuwa a zuwannan da yayi, kuma nima sainaga yakamata ace anwuce wajen tuni”.
     “K nifa kidainamin turanci, ƙilama zagina kikayi ban saniba”.
     Cikin zaro idanu Ummukulsoom tace, “Nashiga goma, nifa nace kiyi haƙuri ne, amma ba zaginki nayiba”.
     “Oh, to ai abunne saida bayani, kinsan mu bamusan wannan kwalmaɗe-kwalmaɗen na turawabane”.
    Girgiza kai kawai Ummu tayi tana murmushi, halin Murja sai ita.
      Suna nan tsaye Ummu na gyarama Murja ɗaurinta su Nusaiba suka fito suma cikin gayu, sai wani shan ƙamshi suke da jama su hadiza aji, su adole wayayyune ƴan boko. Kallo ɗaya Ummu tai musu ta ɗauke kanta tana murmushi.
      Azima ta kama yiwa Murja faɗan tana ɓata musu lokaci, sufa zasu tafi su bartane.
   Murja ba kanwar lasa bace, taja dogon tsaki da faɗin “Dalla malama yo ku tafi mana, ko sai akace idan kun tafi basan gane hanyaba? Nifa ba Umma bace da kuka raina, billahillazi danƙarar yarinya zanyi, Aikin banza kawai”.
    Babu wanda ya tanka, dan Murja bata raga musu, idanma dambene jibgarsu take saboda tanada ƙarfinta.
    Ummu tace, “Kedai jeki ku tafi dan ALLAH, kinsan dawani yaji a gidannan sai maganar tazama wani abu daban kuma”.
    Ƙwafa Murja tayi tabi bayansu.
    Ummu kuwa takoma sashensu dantayi koda sharace.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
         ★★★★★★★

     Haka rayuwar gidan tacigaba da tafiya, Ummu batajin daɗin zaman amma saboda ta saba ko a fuskarta bazaka ganiba, sai dai idan ankai hakurinta bangone.
    Yauma dai da Ramatu takaita maƙura bayan sun ɗebo ruwa daga rafi sauke ruwan tayi sukahau danbe, aiko taima ramatu jibgar tsiya su Azima ne ƴan rabo.
     Koda suka dawo gida su Ramatu suka zayyane ƙarya da gaskiya, babu wanda yabi ba’asi da maganar murja dake karyatawa tana faɗin gaskiyar abinda ya haɗa.
     Babar Ramatu tasaka lawwali yayan ramatun ya zane Ummu, shiko dama haushinta yakeji tace bata sonshi, yako kamata ya jibga.

       Har bayan magriba Ummu na kukan wannan duka, zataje gidan kakanninta aka hanata, dan matan gidan suna tsoron masifar Inna Laraba yayar mamar Ummukulsoom ɗin.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});        Ana tsaka da sallar Isha’i yara ke ihun kiran baban kaduna oyoyo, baban kaduna oyoyo.
    Wani sanyi ya ratsa zuciyar Ummu dan tasan babansune, tana sallame salla ko addu’a batayiba tafito daga ɗakin.
      Fuskarta ta washe da murmushi ganin baba zaune yana shan ruwan da inna Asabe ta kawo masa, ga yaran gidan zagaye dashi suna jiran tsarabar biredi daya saba zuwa da ita.
      Agabansa ta durƙusa tana jiran ya kammala shan ruwan ta gaisheshi, Inna Asabe sai antaya mata harara take da gargaɗi da ido.
     Ummu yitai tamkar bata gantaba, tama sunkuy da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.
     Baba daya gama ya kalleta fuskarsa shinfiɗe da murmushi, “A’a Ummukulsoom ɗin baba ce”.
     Fuskar Ummu shinfiɗe da farin ciki ta ɗago tana faɗin “Eh baba sannu dazuwa? Ya gajiyar hanya?”.
     “Alhmdllh Ummukulsoom, ya hutu?”.
     “Baba ai hutu yama ƙare”.
      “Kai kai to lallai yakamata ki koma makaranta kenan, idan lokacin bikin ƴan uwanki yayi saikizo kimusu baici tunda kin dage yanzu makarantar kwana kikeso (boarding)”.
    “To baba nagode sosai, ai lokacinma muna wani hutun”.
       “A to to masha ALLAH, ina sauran ƴan uwan naki?”.
      “Inaga an aikesu ne”. ‘Ummu ta faɗa da sauri saboda uwar harara da baba yalwa data fito yanzu ta maka mata’.
     Tana gama faɗama ta tashi tabar wajen.

       Baba dai ya fuskanci akwai abinda ke damun Ummukulsoom, amma ko a washe gari bai tambayeta ba, saima yashiga mata cuku-cukun transfer zuwa makarantar kwana shida wani malaminsu na firamare batare da ta saniba..
          Bayan kwana uku da hakan yazo mata da albishir, har kuka tayi dan daɗi, yayinta takaici yacika zukatan ahalin gidan. Su Azima sukace sun fasa aure yanzu makaranta sukeso suma.
    Aiko iyayensu suka hayayyaƙo musu da jaraba, harda cewa itama Ummu babu abinda zata samo sai wahala.
     Baba yace, “Can kuganta a ƙwaryarku, lafiya lau yarinyata zatayi ta ƙare da izinin ALLAH”.
     Tsit sukayi kowa yakasa motsi, basuyi zaton shigowarsa ba yanzun, matan ƴaƴa surukansu ko sim-sim kowacce tafara janye jiki tana nufar lungunta.
    Baba ma bai sake tofa komaiba ya raɓa ta gefensu ya shige da itacen girki a kansa, dama daga gona yake ɗauro icce.
      Wannan magana itace ta harzuƙa baba, a washe gari ya saka Ummu ta shirya abinda duk ya dace da wanda baban yakai kuɗi aka shirya mata gidan kakanninta, irinsu ƙuli-ƙuli, yaji, soyayyan Manja da mangyaɗa, gada soyayya dadi sauransu.
      Ganin tafiyar da gaskene sai Ummukulsoom taji duk babu daɗi, tashiga share ƙwalla tana shiga waje-waje yimusu sallama.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});      Wasu sumata fatan alkairi, wasuko harda ɗan habaici, itadai bata kulaba, dan duk iyaye da yayye take musu kallo.
         Saida ta biya gidan kakanninta tai musu sallama, gwaggo hinde tsohuwa mai ran ƙarfe hadda ƴan ƙwallanta, dan tun bayan rasuwa ɗahara Ummu take kallo taji sanyi, dan batada yanda zatayine tabarta hannun matan Uba na azabtar musu da ita.
    Ɗari biyar tabama Ummu tana zabga mata addu’a da fatan nasara.

********

      A zaria suka ida sayayyar kayan da Ummu ke bukata, bisaga jagorancin malam Muttaƙa akakai Ummu makarantar kwana ta ƴammata.
     Bayan malam buhari da malam Muttaƙa sunkai Ummukulsoom aka gama duk abinda ya dace da taimakon malam Muttaƙa, sai sukai mata nasiha sanan suka taho suka barota da kwasar sabon kuka, tasha kuka sosai saida taji har kanta na ciwo sannan ta hakura tai shiru. 

     Malam Buhari bai koma Ɗilau ba, kaduna ya wuce, dan yana buƙatar bama garin iska, gakuma hidimar bikinsu Azima dake tunkarowa.

     
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡          

          Ita dai Ummukulsoom zata iya cewa tayi murna da makarantar, kodan cikama Basiru burinsa, sannan zata samu sassaucin uban aikin datake tiƙa a gidansu da tsangwama, dukda dai tana kewar jama’ar gidansu dasu Azima, da daɗi babu daɗi dai ko yaushe suna tare.
        A hankali yau da gobe sai Ummukulsoom ta fara sakin jikinta da sabo da makarantar, harma da yin ƙawaye, yau da gobe har komai ya wuce sukaje hutun farko gida.
    Yaran gidan sunyi murna da ganin Ummu, hakama Murja, sai wasu tsiraru daga matan gida da dama basa cutar da ita, bakuma su hana a cutar da itan.
       A wannan hutuma bata canja zaniba, dan Ummu tacigaba da fuskantar tsangwama ga matan mahaifinta, bata damuba, dan yanzu takuma samun ilimin zaman duniya, ko abu sukai mata basa ganin damuwa a fuskarta, a haka aka shiga shagalin bikin ƴammatan gidan su shida hardasu azima, ranar bikin Ummu tasha surutu wajen jama’a, sai nunata ake da baki idan ta gitta, sannan kuma iyayen su Nusaiba faɗi suke Ummukulsoom tayi kwantai babu miji, iyayen Basiru basa son ta auri ɗansu shiyyasa suka maƙale da karatu yake.
      Daga Malam Buhari har Ummukulsoom basu kula wannan zanceba, saima dangin mahaifiyar Ummukulsoom ne abin ya damesu, dan suma ason samunsu marainiyar tayi aurenta, kodan hutawa da aƙubar matan ubanta, to amma yazasuja da hukuncin ALLAH, fatansu ALLAH yasa hakan shine yafi alkairi.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});              Bayan kammala bikin su Nusaiba Ummukulsoom ta koma makaranta ita kaɗai cike da kewar ƴan uwanta kuma ƙannenta, dukda ba shiri sukeba saida taji babu daɗi, Haka dai ta koma makaranta badan taji daɗin hutunba kwata-kwata, saima da baba yazone ƙarshe-ƙarshen zasu komane lokacin biki tasamu sakewa, surutun da aikata mata a taron bikin kuma ya kuma ƙuntata ta.

★.★.★.★.★.★.★

      Haka Ummu tacigaba da karatunta cikin aminci, a bizitin ɗin farko na shigarsu ss2 saiga Basiru yazo mata makaranta, tayi matuƙar farin ciki da ganinsa, tareda mamakin yanda ya canja sosai, yazama ɗan gayu, ƙyawunsa da cikar haibarsa sun kuma bayyana, duk sai taji tama raina kanta, dan nesa ba kusaba Baseer ya tsere mata a halin yanzu. Koda ƙawayentama sukazo gaisheshi tace musu wanda zata aurane casukai ƙarya takeyi, ina ita ina wannan balaraben.
     Itadai dariya tayi kawai, lokacin da zasuje aurenta dashi sa tabbatar da hakan.
     Tun daga wannan busting ɗin kowanne bizitin sai Baseer yajema Ummukulsoom, haɗuwarsu a gidace dai ta ɗanyi wuya, dan duk sanda zaije ganin gida ita tana makaranta, sanda zataje hutu shima yana makaranta.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

*_BAYAN SHEKARA ƊAYA_*

           A wannan shekarar ne su Ummukulsoom ke shirin shiga aji shida, idan kaganta dolene ta birgeka, ta ƙara girma da cika, shiyyasa idan taje hutuma bata yawo kwata-kwata, saboda surutu da ake mata wai tazama Uwar mata a gida babu aure, dan a yanzu haka yaran su azima bibbiyu, Wasuma cikin na uku garesu.
         Takanyi dariya aduk lokacin da aka jefeta da kalmar koda acikin gidansune, musamman idan ta tuna manya-manyan ƴammata dake a makarantarsu, itafa duka-duka shekarun nata sha bakwaine da wasu watanni, amma saboda saɓo ake kiranta uwar mata, lamarin ƙauyensu sai addu’a.
     Tasan abinda yasa ido yay yawa a kanta ita kaɗaice yarinya budurwa da zata kammala secondary, sai yaran gidan mai gari su Harirah, suko bama sa zuwa hutu gida, a hannun yayar mai garin suke zaune a kaduna, shiyyasa babu mai ganinsu balle a ishesu da surutu.
      Wannan hutun dataje gida baba yalwa harda tsareta tana dubata wai ciki gareta, dan taga Ummukulsoom ɗin tayi wata irin cika da buɗewa, ba komai ya kawo hakaba kuwa sai halittar babban jiki da ALLAH ya bata, dan sam Ummu ba siririya baceba, idanma tasamu jin daɗi anan gaba buɗewa zatayi tai ƙiba.
        Sosai zancen cikinnan ya ɓatama Ummu rai, dan haka tai fushi ta koma gidan kakanninta saida tayi sati.
     Dama yanzu bakowanne wahala take juraba, da an takura mata zata barmusu gidanma. Shiyyasa suke cewa idonta ya buɗe taje bariki ta fetsare.

★★★★★

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
     Ɓangaren Baseer kuma a wannan lokacinne ya haɗu da zankaɗeɗiyar budurwa mai suna Suhaila a makarantarsu, Suhaila ɗiyar manyace, dan babanta nada arziƙi, taso zuwa ƙasar London tai karatun ta, amma sai mahaifiyarta ta matsa akan tayi a gida Nageria. Badan ta soba ta amince, saboda ita kaɗaice mace a gidansu, iyayenta da ƴan uwanta suna masifar sonta. 
       An sama mata gurbin zama ɗaliba anan A.B.U zaria, wanda hakan ne yazama sanadin haɗuwarta da Baseer.
     Tunda ta ɗaura ido akansa ta rikice, dan Baseer cikakken namijine abun so ga kowacce mace, yazama handsome na gaske, ga ƙyau ga tsafta da ilimi, gashi ALLAH yayisa irin mutanennan masu shegen alfahari da taƙama, idan kaga yanda yake yarfa ƴanmata dawani ɗaukar kai saika ɗauka wani ɗan mashahurin attajirine ko mai mulki a Nigeria, bazaka taɓa yarda ya fito daga ƙungurmin ƙauyen Ɗilau baneba.
     Ita kanta Suhaila kallon irinta ƴaƴan masu kuɗi tamasa da farko, musamman yanda taga ƴaƴan manya da ƴanmata masu aji na makarantar dake naniƙe masa yana yarfasu, sannan abokansa duk ƴaƴan manyane, kwata-kwata baya harka da talaka irinsa, nunawama yake yafi ƙarfin saninsu. 
     Abinda yake ƙarama Baseer girma da kima a idanun jama’a shine basirar karatu, ba ƙaramin ƙwaro baneba wajen brain, wannan shine sanadin dayasa ƴaƴan manya ke nane dashi.
       Dukda son Baseer ya mamaye zuciyar Suhaila sai bata tunkareshiba kai tsaye tamkar yanda sauran ƴan matan ke masa, saima suka ƙulla ƴar tsama, data gansa saita shiga tofar da yawu da yatsine-yatsine tamkar taga kashi, kokuma ta bula masa ƙurar motarta. 
     Tun abun baya damunsa harya fara sakashi takaici, yanda ake girmamashi a makarantar da jan mata dayake a ƙasa saboda kyawunsa ace wannan yarinyar tazo tana masa wannan cin kashin?.
     Sai Baseer yafara biyema Suhaila kulum suna cikin faɗa da juna da jifan junansu da baƙaƙen magana. Ahankali sai faɗan nasu yafara komawa shaƙuwa, daganan sai soyayya. 
      Jama’ar makaranta sai dai suka wayi gari sukaga Baseer da Suhaima abokan faɗan juna sun ɗinke sun koma masoya…………✍????


*Turƙashi, Ummukulsoom fa?*????????‍♀☹


_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU????._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

????????karku bari ayi babuku

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon wani*????????????????????????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Back to top button