NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 11

*_Bilyn Abdull ce_*????????

*_NO. 11_*

  ………….Tamkar sokuwa haka takebin kowacce kusurwa na falon da kallo, komai dake cikinsa silba ne, sai ɗai-ɗaikun abubuwa bulu….
    Yanda take bin falon da kallone yabama Aunty Nurse dariya, ta
murmusa tareda kamo hannun Ummukulsoom suka zauna a kujerar farko.
      “Ummukulsoom nan shine sashen mijinki, anan zaki zauna kafin ki wuce, duk kayanki suna nan ankawo tun ɗazun kinji”.
        Kan Ummu a ƙasa ta  amsa da “To Aunty” duk da kuwa tsorone fal ranta, taya zata iya kwana ita kaɗai anan?.
    Miƙewa aunty Nurse tayi ta fita, zuciyarta na tausayin Ummu da yanda zata rayu da yayan nasu mai bahagon hali tamkar mahaifinsu.
    
     Ummukulsoom ta daɗe wajen zaune tana tsiyayar da hawayen tausayin kanta da kewar ahalinta dake damunta, ga dai jiyanta ta wuce da ƙalubalen rayuwa kala-kala, gata a yau ɗinta a wani bigiren da ita kanta takasa fassararsa, to kenan yaya gobenta zata kasance kuma a ƙarƙashin fadar sarki mai cikakken iko irin mijinta dako ganinsa bata taɓa yiba sai jin labarin tsantsar mulkinsa da tsagwaron barazana ta kasaitattun maza.
       Duniya babban gida, mai cikeda abubuwan ƙawa da tsoro harma da firgici, zuwa yanzu takuma yarda RAYUWA tana tafiyane da JARABAWA, idan yau ta wuce da nata salo, gobe saitazo ɗauke da nata itama, babu kuma wani hannu daya isa goge rubutun da yazo a alƙalamin ƙaddara, shiyyasa masu iya magana sukance duniya rawar ƴammata, to lallai rawar ƴammatan ce kam.
      Tafi zaman awa ɗaya a wajen kafin tasami yunƙurawa da ƙyar saboda kiran sallar azhar da aka ƙwalla. 
     Kuma baje idanu tayi tana ƙarema falon kallo a karo na biyu, komai a tsare tamkar na mace, sai dai babu hoto ko ɗaya alamar mamallakin sashen baya buƙata, dan ita ko a falon sashen su Momcy taga hoton kowa a gidan amma banda nashi, a fili ta furta “Toko baya hoto ne?”. taɗan taɓe baki da ɗage kafaɗa alamar shiya sani.
      Tamkar munafuka ko mai shirin sata tana gudun a kamata haka ta laɓaɓa zuwa ƙofar da aunty Nurse ta nuna mata matsayin bedroom ƙwara ɗaya tal dake sashen, ta ɗora hannunta jikin ƙofar ta murɗa a hankali kafin tafara leƙa kanta tamkar zata ganoshi. Sai kuma ta ida shigewa gaba ɗayanta.
    Bedroom ɗinma tamkar falon haka yake, dan shima ɗauke yake da Silver and blue color ɗin komai, saman gadon babu bedsheets katiface kawai sai filos suma babu riga. Taɗanbi ko ina da kallo sannan tanufi toilet, nanma dai masha ALLAH, Sai dai babu komai na amfani kamar irinsu sabulu da sauran tarkace na bayi kamar yanda tasan nasu Ameer suke, itadai tai alwala tafito tai salla.
    Tana idarwa Aunty Nurse tashigo itada Buhayyah dake ɗauke da tire, sai kumbura baki take alamar ansata kawowa tilas ne.
    Idon Aunty Nurse Buhayyah ta faka ta dallama Ummukulsoom harara kafin ta dangwarar da tiren zata juya.
    Ummukulsoom tai ɗan murmushi tana haɗiye abinda ya tsaya mata a maƙoshi, yayinda Aunty Nurse ta dakama Buhayyah tsawa da faɗin, “K dan Ubanki dawo nan, ita sa’arkice da bazaki gaidataba”.
    Tamkar Buhayyah zata rushe da kuka tace, “Ina yini” cikin yamutse fuska da harar Ummukulsoom ƙasa-ƙasa.
     Ummu tace, “Lafiya lau Aunty Buhayyah”.
     “Aunty Kuma? Buhayyah kike cema Aunty? To aiko kar bakinki yay kuskuren faɗa gaban yaa Amaan, inba hakaba zai haɗa ke da ita ya kakkarya wlhy”. Ta maida kallonta ga Buhayyah daketa wani huhhura hanci, “kekuma kika tsaya mana a kai, ki buɗe Wadrobe ki ɗakko bedsheets ki shinfiɗa a gadonnan”.
     Buhayyah zatai magana Aunty Nurse ta watsa mata harara. 
    Babu shiri tayi shiru tabi Umarninta, ɗakko bedsheets ɗin tayi tana ƙoƙarin shinfiɗawa tamkar zatai kuka.
    Ana haka saiga Bassam yashigo shima yana kumbura tasa fuskar, ledar hannunsa ya miƙoma Aunty Nurse daga ƙofar ɗaki. “Aunty Nurse gashi”.
     “Humm nizan taso na amsa kenan, to ka wuce kasaka kowanne inda ya dace a toilet, banzayen yara kawai, duk kugama iskancinku yanzunan yaa Amaan zaiji komai wlh…..”
       Gabb!!
    Da sukaji yasakasu waigawa su duka.
     Bassam ne yakusa kifewa ƙasa saboda jin aunty Nurse tace saita faɗama Yaa Amaan. 
      Gaban Aunty Nurse yazo ya tsugunna, itama Buhayyah haka, suka fara mata magiyar roƙon dan ALLAH tayi haƙuri.
      “Kunsan da haƙurin kukema mutane iskanci?, yanzu ita sa’arkuce? Ko kai Bassan danake tunanin zakuyi sa’anni dagani Ummukulsoom tabaka watanni, balleke Buhayyah, idan zaku dawo hankalinku ku dawo, dan yanzu matar Yaa Amaan ce ba ƴar aikinkuba, inkuwa bazaku gyaraba kunsan halinsa sarai, kune zakusha wahala wlhy, kutashi kuban waje”.
     Su dukansu duk sun zama kalar tausayi, dan sunsan kaɗan daga aikin aunty Nurse ta sanarma yaa Amaan ɗin.
      Hakan da sukai sai Ummukulsoom takumajin tausayin kanta, wannan shi wane irin mutumne to? Takan kai maƙurar tunanin wajen fasalta wannan yaa Amaan amma saita kasa, ƙwaƙwalwarta tagaza, mutumin da baya kusa ana masa irin wannan mugun tsoron ina ita da zatayi rayuwar aure dashi, lallai tana tsaka mai wahala itakam. Basiru ya sakata a ramin kura, dan dabai fasa aurentaba daduk hakan bata faruba, da yanzu sunacan cikin aminci da farin ciki…….
     Tana ta tunaninta harsu Buhayyah suka kammala komai, aunty Nurse ta tasa ƙeyarsu suka fice.
       Abincin taɗanci sannan ta kwanta saboda ciwo da kanta ke mata.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

        Washe garin kawo Ummukulsoom shima daddyn Suhailat yaje ɗilau suka tsaida magana da baban Basiru, wannan karonma sai sha musu ƙamshi yake da yaɓa musu magana, amma sun gaza ɗaukar mataki saboda sihiri na cinsu, wata ɗaya kacal aka tsaida na bikin, su Baba basu damuba, tunda dai babu abinda zasuyi, dan haka basuja zancenba suka amince.
     Daɗi tamkar zai kar Basir, dan jinsa yake a sama can ƙololuwa, shifa yanzu ya wuce da tunanin kowanne banza.
    Kafin kacemi ƙauyen ɗilau ya ɗauki labarin Baseer mai ƙashin arziƙine, wai zai auri ɗiyar mashahurin mai kuɗi a birni. Wasu masu hankali da tunsninsu yafara dawowa hanya sukance dama saboda ita ya yaudari Ummukulsoom kenan? Magan ganu dai kala-kala nata zagaye ɗilau da kananun ƙauyuka maƙwafta.
     Koda Malam Buhari yaji labari Murmushi kawai yay baice komaiba,  a washe gari ma ya shirya yabaro garin domin komawa ga sana’arsa.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

      Ɓan garen Suhailat ma tana cikin tsantsar farinci, kallo ɗaya zakai mata kuma ka fahimci hakan daga gareta, kwana biyu da tsaida bikin suka tafi dubai itada Amrah da maminsu haɗo mata kayan lefe dana ɗaki.
   Abin yabama baseer haushi, danshi yazata dashi za’aje Dubai ɗin haɗo kayan????????. Sai kawai Suhailat ta kirasa da daddare tana faɗa masa gobe fa zasu wuce.
     Yace, “Ina kuma Love?”.
       “A’a, Love yada tambaya irin haka? Dubai mana haɗo kayan lefe dana gidanmu”.
       Da ƙyar ya iya haɗe abinda ya tsaya masa a maƙoshi yana fisgo magana, “Kina nufin har kunsami visa?”.
      “Eh mana, jiya da ƙyar daddy yakuma jajircewa yasamo mana, dama tawace taso bada matsala, amma yanzu komai normal, karka damu ba daɗewa zamuyiba, sannan komai zan fara turo maka idan yamaka sai a ɗauka”.
       Jiyay tamkar ya mannama ubanta zagi, amma ya danne yace, “Uhum, ni bara naje su Najeeb na jirana, idan kun sauka mayi waya”. Baijira amsartaba ya yanke wayar yanajan dogon tsaki.
       Yagama zubama su Arfaan ƙaryar zaije dubai haɗo kayan auren Suhailat shida daddynsa da Suhailat ɗin, shine zasuyi masa wannan wulaƙancin, shi yanzuma mizaice dasu Abdull ɗin idan sunga bai tafiba? Ko kashe wayarsa zaiyi yay tafiyarsa Ɗilau kawai yay kamar kwana goma saiya kunna yace musu ya dawo?.
      Haka yayta juya maganar a ransa har Nehal ƙanwar Najeeb ta iso wajen.
     Ƙamshin turarenta ne yasashi ɗagowa ya kalleta.
        Murmushi tamasa, yayinda shikuma yaɗan basar yana wani shaƙar iska da ƙyar. Gaidashi kawai tayi tai shigewarta gida.
    Ya bita da kallo yana lasar laɓɓa, baiso ta tsaya iya gaisuwaba, dan ya ƙagara ta furta masa kalmar so itama, sai dai yakula yarinyar kamar tafi Suhailat iya jan aji…..
     “Bas! Mikake leƙe hakane wai?”. ‘Arfaan yafaɗa yana dukan kafaɗarsa’. 
    Firgigit yadawo hankalinsa yana jan tsaki, “Babu komai my guy, inasu Najeeb ɗin mu wuce”.
    “Gasunan zuwa, kasan iyayin Abdul, wai kaya yake canjawa”.
     Baseer yaɗan taɓe baki yana miƙewa tsaye.

     Daga can kuwa Suhailat bata kawo komai a rantaba ta ajiye wayar da tunanin cikin uzuri yake ƙila.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

             Ummukulsoom bata farkaba sai da aka kira sallar la’asar, alwala tayo tai salla, tiren abincin da aka kawo mata ta ɗauka ta nufi sashen su Momcy zuciyarta na dukan ɗari-ɗari na tsoro. Ta can ƙofar baya tabi tashiga kicin. Jud nata ƙoƙarin haɗa abincin dare yana raira waƙarsa ta sabo.
    Yana ganinta ya hau washe baki tareda risinawa yana faɗin “Madam good Everning”.
      Ummukulsoom taɗan hararesa da wasa, “Oga Jud yau kuma nice Madam ɗin?”.
       Cikin hausarsa dabata fita da ƙyau yace, “Ai kama wuce Madam, kai Momy ne, kana matsayin matan Boss Amaan nefa yanzu, Walayi ka more Madam Umikusmu, dan Boss Amaan ya haɗufa, sune mazan da ƴammatan yanzu ke rubibi fiye da kuɗi. Damma shi mutumin kirkine baya harkar mata, amma da kinsha go slow walayi……”
     Ummukulsoom ta katse Jud da faɗin “Nidai Oga Jud bar wannan zancen, inasu baba Halima suke ne?”.
       “Suna ciki Alaji ya kirasu, kinsan yau ana bada albashi, nima na amsa nawane tunda safe”.
       “Oh to Congrat oga jud”.
     “Thanks you so much Ma!”.
     Yafaɗa a matuƙar girmame.
    Murmushi kawai Ummukulsoom tayi tafito ta koma sashenta. A hanya tagamu da Ameer, ko inda take bai kallaba dukda gaidashin da tayi. saima tsaki daya ja mata.
    Gwiwarta a sage takoma masaukinta tana neman sassaucin wannan sabuwar rayuwa a wajen Ubangiji.

        Ita kaɗai taita rayuwa a sashen cikin kaɗaici har dare, tsoro ta faraji dan haka tayanke shawar zuwa nemo ɗan tayen kwana, tana ƙokarin fita aka ƙwanƙwasa ƙofar, ɗan firgita tayi, amma saita danne zuciyarta ta buɗe tana addu’a a ranta, ganin baba Halima ɗauke da tiren abinci yasata saurin karɓa tana faɗin “Baba da kanki? Dan ALLAH kibar kawowa, ai gara ki kirani na amsa”.
     Ƴar dariya baba halima tayi, “Ai girmankine yanzu hakan, kodan mutuncin Yaa Amaan a girmama matarsa, balle kema yarinyar kirkice Ummukulsoom”.
       “Baba kishigo to”.
 “Wai rufamin asiri Ummukulsoom, kaf ma’aikatan gidannan babu wanda ya taɓa shiga sashennan, yaa Amaan bayaso, duk ƙyuyar yaran gidannan nakin aiki sune ke gyara masa sashensa ko yana gari ko bayanan, kedai sai da safe kawai”.
      Idon Ummukulsoom ya ciko da ƙwala, a fili tace “Na shiga Ukku ni Ummu. wlhy baba tsoron kawana nakeji anan ni kaɗai, dama yanzu zanje nemanki ki tayani”.
     ”Ummukulsoom bar wannan maganarma kar wani yaji, ki daurema zuciyarki, babu abinda zai sameki wlhy, bara na tafi kar wani cikinsu ya ganni anan azata wani abun muke kitsawa kinji, ki aje zuciyarki waje ɗaya babu abinda zai sameki da yardar ALLAH”.
      Baba Halima na tafiya Ummukulsoom ta rushe da kukan tausayin kanta, wannan wane irin gidane haka?.

★★★★★★

        A daren yau inhar barci ya ɗauki Ummukulsoom to ɓarawone, gaba ɗaya a tsorace take, ko yaya taji motsi sai taji kamar kanta akayo, sai gabannin asubahi tasamu tai barcin, hakanne yasata makara har sai da Aunty Nurse tazo ta tasheta.

        Momcy nason zuwa tama Ummukulsoom tatas amma Alhaji Mahmud ya kafa ya tsare, dan yana gida babu inda yake fita sai massalaci saboda bayajin daɗin jikinsa kwana biyunan, shiyyasama yaɗan ja tafiyarsu lagos.
    Shikuma gama fahimtarta da yayine yasashi jamata dogon gargaɗi itada ƴaƴanta akan Ummu.
     Wannan yasa Ummu samun zaman lafiya a kwanaki huɗun nan, sai idan tazo gaishesune aita dalla mata harara, sai dai babu damar aci zarafinta, dan kullum da safe saita shiga ta gaidasu, hakama da yama zata shiga dagaan tadawo sasheta tai zamanta, bata da aboki hira sai tv.
     Akan tafiyarsu kuwa tsaf yagama fahimtar shirin matar tasa shiyyasa ya saka mata ido, koda ta tuntuɓesa da batun binsu lagos rakkiyar Ummukulsoom Shiru yay mata, saida ta sake maimaita masane yay mata wani kallon data sha jinin jikinta kafin ya ɗauke idonsa akanta.
      “Jamila wai dan ALLAH yaushene zakiyi hankali ki tuna kin girma?, babba dake mai mazgegen ɗa kamar Fodio da Ameer amma har yanzu baki gama sanin ciwon kankiba, ke yamzu idan ance kije rakkiyar suruka saikije?”.
        Ɓata fuska tayi tana hura hanci, “To Abban Fodio naga kaima dai zuwa zakayi ai ko”.
       “ALLAH ya shiryeki to tunda ni nazama kishiyarki”.
    Da kallo ta bisa tamkar zata fasa kuka, haryaje ƙofarsa ya juyo yana kallonta, “Saura kuma kice zaki kirashi, inma kinyi to kinyi a banza, ranku zai ɓacine dagake harshi ɗin”.
      Kasa cemasa uffan tayi, dan yakai ta iya wuya ainun yau wlhy, amma kuma yagama fuffukarsa saita raba wannan auren, dan bazata taɓa barin jininta zama da ƴar aikiba amatsayin mata, jinin natama irin Fodio datake ƙauna fiye da sauran ƴaƴanta.

      Da daddare Dad yasaka aunty Nurse ta kira masa Ummukulsoom, kanta a ƙasa ta durƙusa ta gaidashi cike da ladabi.
      Da kulawa ya amsa mata dukda dai fuskar tasa babu fara’a kamar kullum, yace, “Ki shirya ɗiyata, insha ALLAHU gobe zaki koma wajen mijinki, dukkan kayanki yanzu kije ki fiddosu da asubahi isa zaiyi gaba da matar da zata ringa ɗan miki ayyuka, mukuma zuwa yamma zamubi jirgi insha ALLAHU”.
       UMMU ta haɗiye hawayen da suka cika mata ido da ƙyar, kafin tace, “To baba nagode, ALLAH ƙara lafiya”.
     “Amin” ya amsa mata, kafin yace tashi kije abinki.
     Kanta ta jinjina masa tana share hawayenta cikin dabara, sannan ta miƙe ta fito.
     A falon ƙasa ta iske Momcy zaune itada Aunty Ummi, gabanta ya faɗi, ƙafafunta na rawa ta ida sakkowa a benan, cikin risinawa tace, “Sannunku mommy”.
    Babu wanda ya amsa mata a cikinsu, dan haka ta ƙara maimaitawa a karo na biyu, nanma basu amsa mataba, sai aunty Ummi ce tace “k zonan dan Uwarki”.
    Rintse ido Ummu tayi taɗan buɗe, saboda zagin ya shigeta, bata jama mahaifiyarta addu’aba taja mata zagi.
    Gabansu taje ta durƙusa tana danne kukan dake neman ƙwace mata.
       “Munafuka, wane shegen boka kika kaima sunan dad ɗinmu haka?”.
      A razane Ummu ta kalli aunty Ummi tana girgiza kanta, dan bakinta ya gaza furta komai.
    Momcy tace, “Badake ake maganaba! Kika zuba mana waɗannan munafukan idanun?”.
     Ƴar zabura Ummu tayi tana fashewa da kuka, “Wlhy Momcy babu wajen bokan da naje, bamma taɓa zuwa wajen boka ba wlhy, ƙaddarace kawai hakan, ku yarda dani”.
       “To, wato ƙaddara ce? To kinji Momcy ƙaddara ce”.
     Ƙwafa Momcy tayi tana dungure kan Ummu, “Dan Ubanki zakiga ƙaddara kuwa, da ƙafafunki saikin nemi gidan Ubanki indai Fodio ne, tashi kibama mutane waje baƙauyar banza”.
     Kafinma Momcy ta rufe baki Ummukulsoom ta bar wajen, haka ta fice tana kuka da tausayin kanta.
    Baba Halima data gants tajata can wani lingu tai mata nasiha akan halin surukarta da dangin mijinta, takuma kwantar mata da hankaki.
    Wannan ne yabama Ummu ƴar Nutsuwa hartaje ta fiddo musu kayan Isa ya loda a mota, danshi tafiyar asuba zaiyi.

*_Washe gari_*

              Ƙarfe Shida na yamma Ameer yakai Ummukulsoom da Alhaji Mahmud airport, tasha kuka kafin subar gidan, Momcy harda mata nasihar munafunci agaban Dad, data faki ido kuma ta danna mata harara, har harabar gidan suka rakota, saida tashiga mota sannan suka koma ciki zuciyar Momcy tamkar zatai bindiga, nanfa tashiga ƙokarin kiran Fodio amma wayar na nuna mata Number busy. Takaici yakuma kamata tamkar zata fashe.
  
       A airport su Ummu sukai sallar magriba, tanata kalle-kalle da tsarkake sunan ALLAH, a tsawon rayuwar bata taɓa ganin jirgi a ƙasa ba sai yau, bata kuma shan mamakiba ma saida suka shiga zasu tafi.
    Ita dai rumtse idontama tayi, dan jitai cikinta na juyawa tamkar zatai amai lokacin da jirgin zai tashi. Wai ita Umma ƴar ƙauyen ɗilau ɗinnan, marainiya mara gata da galihu a cikin gidansu, itace yau zaune ɗane-ɗane a jirgi, ALLAH mai girma da ɗaukaka, mai yin yanda yaso a lokacin da yaso, ko wa zata tarar kuma a matsayin miji? Oho, ta haɗiye ƙwallar idonta tana karanto addu’ar daduk tazo bakinta saboda zuciyarta jitake tamkar zata wantsalo ƙasa dan firgici…………✍????
         


*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button