NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 12

*_NO. 12_*


        *_LAGOS STATE_*

       Tunda Jirgi ya sauka a filin jirgin *Murtala Muhammad international airport* Dake birnin Lagos zuciyar Ummu ta ƙara ƙarfin gudu da
tsitstsinkewa, wani irin ruɗani ke kuma mamaye illahirin jikinta da kuzarinta, ƙarshen tika tiki tik, yaune dai zataga wannan jan gwarzo abin firgici ga ahalin gidan Alhaji Mahmud Ajiwa.
       Wani ɓarin zuciyarta kuma na mamakin legas ɗin da taji matasan garinsu masu zuwa neman kuɗi suna cewa kwana biyu ake a hanya kafin azo shine su suka isa a lokaci ƙalilan haka?. ALLAH mai iko da rahama kenan…….
     Tuntuɓen data kusanyi ne ya saka Alhaji Mahmud dake gabanta faɗin “Kula mana”.
    Kanta tai saurin jinjina masa tana damke handbag ɗinta sosai cikin hannu ta, sanye take cikin doguwar riga baƙa mai kyau da aunty Nurse tabata a yau ta saka, sabuwace dal tasha adon duwatsu sai ɗaukar ido takeyi, ɗan kwalin rigarne aunty Nurse ta naɗa mata saboda yanada girma sosai, sai farar handbag madaidaiciya da takalmanta marasa tudu, jikinta na fidda sirrin ƙamshin humra da inna harira ta haɗa mata a kayan gudunmawa, sai turare mai daɗi ƙamshi, tayi ƙyawun da duk wanda ya kalleta saiya sake kallo, dukda kuwa babu wata kwalliya a fuskarta bayan fauda da lipsgloss data ɗan shafa shima dan kar lips nata su bushe ne.
     Kanta a ƙasa take bin Alhaji Mahmud a baya, saboda haske daya haske airport ɗin tamkar rana.

★★★★★
          
          Fitowar su Ummukulsoom daga jirgin yay dai-dai da isowar motocin su Yaa Amaan biyu cikin airport ɗin, yaɗan kalla agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa yana jan siririn tsaki.
      Attahir babban abokinsa kuma amininsa ya kallesa yana faɗin “Please ya isa haka mana Ajiwa, ai gamu mun iso akan lokaci, tunda yanzu ma suke fita a jirgin”.
       Uffan baice masaba, dama Attahir yasan ba amsar zai samuba, dan a halayyar Amaan sai dai yabama wani labari kuma.
     Fita sukayi saboda buɗe musu ƙofa da akayi.
      Attahir da idonsa ya sauka akan Alhaji Mahmud yay saurin cewa, “Alhamdllh ga Dad canma”.
       Amaan ya ɗaga manyan idanunsa daya gada ga Momcy yana kallon inda Attahir ya nuna, numfashi yaɗan sauke kafin yataka ahankali yabi bayan Attahir da tuni yanufi Dad yana masa oyoyo.
     Dad yace, “Yauwa Attahir, da kanku kukazo tararmu haka?”.
      “Ai dolene Dad, yau da kanka a lagos aiko zama bai ganmuba, sannunku da zuwa”. ‘Ya ƙare maganar da kallon Ummu da kanta ke a ƙasa’.
     Kafin tasamu damar bashi amsa gabanta yay wani irin faɗuwa saboda jin wata nutsatstsiyar murya mai cikeda izza ta ambaci, “Dad barka da zuwa”.
     “Yauwa Fodio, kuke da sannu da muka taso  akan aiki”.
    Numfashin Ummu yay sama yay ƙasa kafin tasamu jarumtar fisgoshi da ƙyar, lallai tana bukatar kallonsa amma tagaza hakan, gushewar jinta na wucin gadi yahanata jin amsar daya bama mahaifinsa. Da ƙyar tasamu damar satar kallonsa shida abokin nasa dake gefenta yana ƙara jaddada mata kalmar sannu da zuwa,
     Sanye yake da wando fari tas dogo sai baƙar t-shert da akai rubutu da manya haruffa a gabanta kamar haka. *_NICE HANDSOME_*.   
           Alhaji Mahmud ya nunama Amaan Ummukulsoom da hannu yay gaba abinsa inda yaran sojoji biyu ke tsaye jikin motocin da sukazo dasu.
      Yaɗan rausayar da kansa yanabin bayan mahaifinsa da kallo, cikin wani irin yanayi ya zuƙi isaka ya fesar daga bakinsa, kafin ya sauke idonsa akan Ummu dake tsaye tamkar an dasata a wajen, baiwaniga fuskarta sosaiba dan haka ya janye idonsa yana harar Attahir daya bar wajen shima yana dariya ƙasa-ƙasa.
     Siririn tsaki yaja yafara taku cikin bajinta na masu isashshiyar lafiya da jarumta zuwa gabanta.
       Babu zato Ummukulsoom Sai tsinkayar muryarsa tayi daf da ita.
       “Sai an kaiki motar ne?”. ‘Yafaɗa cikin kausasa murya mai fidda fusata’.
      A razane Ummu ta ɗago ta kallesa tai azamar maida kanta ƙasa saboda ganinsa gabanta gingirin gin, tafara ƙoƙarin Haɗiye abinda ya tokare ƙofar maƙogwaronta tana matsawa baya kaɗan, cikin in ina tace, “I..n..a y..ini”.
      Sai da yaja numfashi tamkar bazai amsaba sannan yay taku biyu yana faɗin, “Lafiya”.
       Kawai yace yana yin gaba abinsa.
       “Innalillahi…. Ummu tashiga maimaitawa tanabin bayansa da sassarfa, yayinda jikinta ke rawa tana tafiya tamkar zata zube ƙasa, ta tabbata da takalmi mai tsinine a ƙafarta babu abinda zai hanata faɗuwa. Dukda kwaɗayin ganinsa da take ta kasa kallon koda bayansama, harta dai samu ta cin masa inda yake tsaye agaban Ash color ɗin motar dake bayan wadda Dad ya shiga.
     Hannunsa daya zuba a aljihun farin wandonsa kawai ta iya satar kallo, ga wani tsoron ganin matasan sojojin dake shigarta, a rayuwarta tana tsoron soja da ɗansanda, gashi kuma ALLAH ya jarabceta da auren ɗaya a cikinsu………
     Cikin risinawa matasan sojojin suke gaidata, da nuna mata ƙofar motar da ɗaya ya buɗe mata.
       Karon farko data ɗaga kai ta kalli fuskarsa, amma abin mamaki sai taga bama ita yake kalloba kwata-kwata, azamar janye idonta tayi.
      Attahir yay murnushi mai sauti yana faɗin “Amaryarmu Bismillah, shiga mota”.
   Kanta ta ɗaga masa dayin guntun murmushi takarasa tashiga motar.
       Amaan dake jinsu amma yay tamkar hankalinsa baya kansu ya zare hannunsa ɗaya daga aljihu yaɗan shafi girarsa tareda takawa ɗayan ɓarin motar da Ummu ta shiga shima ya shiga bayan an buɗe masa.
      Ummu dake ƙoƙarin dai-daita rawar jikinta sai kawai taji mutum ya zauna gefenta, ɗauke numfashinta kawai tayi gaba ɗaya tana dafe ƙirjinta. Itakam inhar haka zuciyarta zata cigaba da tsoron mutuminnan tashiga uku kenan, tariga ta sakama ranta tsoronsane tunkan ta gansa, shiyyasa yau takasa dai-daita kanta gaba ɗaya, ko nutsuwar kallon fuskarsa tama kasa samu.
      Shikam kansa ya jingina da kujera ya lumshe manyan idanunsa masu matuƙar haske, ƙasan zuciyarsa kuwa mamakin Dad yakeyi akan zaɓa masa wannan ƴar yarinyar sa’ar ƙanensa Bassam matsayin matarsa ta aure.
       Ko motsin arziƙi takasa yima a motar, takoma can jikin murfin mota ta takure, kasancewar Attahir motar da Dad ke ciki ya shiga sai tasu motar tai tsit, driver n sojan ne kawai keta aikin tuƙinsa, yayinda Ummukulsoom keta faman baje ido tana kallon hanya da jinjina garin Legas ɗin. 
     Yau dai gata a legas, garin da ake faɗin ya tara kowanne shege da shegiya, masu arziƙi da masu neman arziƙin……
       Wayarsa tai wani ɗan tsuwwar data katsema Ummu tunaninta.
    Idonsa ya buɗe tareda ɗan karkatowa jikin Ummu ya zaro wayar a aljihun wandonsa. Ba ƙaramin hargitsawa cikin Ummukulsoom yayiba saboda jin kafaɗarsa naɗan gogar gefen hannunta, ga ƙamshin turarensa yakuma shige mata har ƙofar maƙoshi.
     Zamansa ya gyara sosai ya ɗaga wayar saboda ganin sunan Attahir.
    “Lafiya?”. ‘ya faɗa acan ƙasan maƙoshi’.
    Ummukulsoom bataji abinda aka faɗa masa daga canba, taga dai ya ajiye wayar yana faɗama driver “Junaid samu waje ka tsaya”.
     Ita Ummu ma batai zaton direban yaji maganar tasaba, amma saitaga ya samu waje ya tsaya inda ya dace.
     Kafinma a buɗe masa shi harya buɗe da kansa ya fice, Ummukulsoom ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana gyara zamanta, dan a matuƙar takure take, ta ƙagara suje inda zasu.
       Attahir ma fitowa yay yana nufo Amaan da shima motarsu ya nufa.
      “Ajiwa! kuma lallaɓasa muji kozai haƙura yaje ɗin, danfa yadage sai dai a kaisa hotel”.
       Bai bama Attahir amsaba ya raɓa ta gefensa ya nufi motar inda Dad ke ciki. 
   Dad dake kallonsu ya buɗe motar ya fito fuskarnan a haɗe tamakar ko yaushe, ”Shi Attahir ɗin ya kasa shine ya turoka ka titsiyeni?”.
      Amaan ya girgiza kansa amar A’a, yaɗan shafi girarsa da ɗanyatsa yana gyara tsayuwa, da ƙyar ya fisgo maganar da yakesonyi, “Dad Please, kasan kanada masaukifa, yaza’ai ka kwana hotel?”.
      “Nasan inada masauki Fodio, amma kamar yanda na sanarma Attahir wannan karon bazan kwana a gidanka ba, da da yanzu akawai banbanci, koka manta kanada iyaline?”.
       Kansa yaɗan dafe ya lumshe idonsa ya buɗe, dan yau anata sashi yawan magana, dama idan kaji doguwar maganarsa to Dad ne, amma ko oganninsa na wajen aiki suna masa complain akan rashin yawan magana. “Dad dan ALLAH karkace haka, amma indai hotel ɗin kakeso saimuje can mukwana mu duka”.
      Babu shiri Alhaji Mahmud yaɗan fiddo ido yana kuma tamke fuska, “Fodio yaushe zakai hankali? Da matar taka zakaje a kwana hotel?”.
     Shagwaɓe fuska yaɗanyi yana rausayar da kai da shafar girarsa da ɗan yatsa, “To Dad muke gida”.
     Alhaji Mahmud ya girgiza kansa idonsa akan Fodio, ya tabbata yakai ƙololuwar gajiyawa da magana, danma shine, amma da wanine datuni ya shareshi yabar bada amsa. Yasan kaf halayyarsa Fodio ya ɗaukko, amma rashin son maganarsa yayi yawa, dan yakan gaskata maganarnan ta bahaushe dakance *ɗan gado harya zarta*. To lallai Fodio yagaji komai nasa amma harya zartashi ta ɓangaren shegen miskilanci.
      Ganin iskar hadarin dake ɗaure da garin tafara tasowa yasaka Dad haƙura ya koma mota.
      Ajiyar zuciya Amaan ya sauke, dan ya tabbata Dad ya haƙura zai bisu, da kansa ya rufe masa motar kafin ya juya ya kalli Attahir dake tsaye gefe yana latsa waya.
     ”Attahir?”. ‘Ya kirayi sunansa cikeda ƙosawa da magana’.
     Ɗago ido Attahir yay ya kallesa, ganin Dad amota yasakashi fahimtar komai ya dai-daita, tahowa yay, yayinda shikuma Amaan yakoma mota.
     Ummukulsoom dake ƙare masa kallo tacikin motar tun ɗazun tai azamar ɗauke kanta tana dai-daita zamanta, babu abinda zuciyarta keyi sai tsarkake sunan ALLAH da ya halicci wannan bawa mai kamala da tarin Nutsuwa, sosai yake kamanni da mahaifinsa, yayinda ya ɗakko fari da manyan idanu na mahaifiyarsa, ita wannan tagamu dashi a hanya bata sanshiba wlhy bazatace masa bahausheba, ba komai zaisa hakanba kuwa sai ƙirar jikinsa, lallai ya cancanci xama soja tako wanne fanni, gaskiya yafi dukkan ƴan gidansu ƙyau, danshi ya ɗakko kamannin Dad and Momcy dukya haɗa, ga kwarjini kuma da ALLAH yay masa, ta tuno Baseer ɗinta ƙyaƙyƙyawan bafullace fari tas, zaifi Amaan ƙyawun fuska, amma Amaan yafisa kwarjini da cikar haiba, sannan yafisa ƙyawun sura da dirarriyar ƙira da nutsuwa, isa, ƙasaita, dukya dama Baseer ya shanye, yanda yakema taƙama da wannan ƙyan nasa idan yazo Gaban Amaan dolene ya raina kansa, iyakaci yay kurin finsa fari da dogon hanci. Anata ganin kuma tsantsar ƙyawu bashi ake kira ƙyauba, komin ƙyawun mutum akwai matakan da saiya cikasu yake ƙayatar da mutane da kwarjinin barazana, to irinsu Amaan koda basuda ƙyau kwarjininsu ke girmama barazanarsu a zukatan jama’a……
     Ita kaɗai taketa saƙawa da kwancewarta har suka shiga cikin *_DODAN BARRACK_* bata saniba. Sai tsayuwar mota taji kawai da motsin fitarsa batareda yace mata Uffanba.
     Tana shirin Buɗewa aka buɗe mata, dukda darene Barrack ɗin akwai wuta, dan haka Ummu taɗan samu damar kallon iya inda idonta zai iya zuwa. A yanda dai ta kula inda suke na manyane, dan tsaf yake da manyan gidaje masu ƙyau tamkar ba a cikin barikiba, bakajin motsin komai sai haushin karnuka, saikuma mutane ɗai-ɗai dake shawagi……..


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

       Suhailat dai ta wuce tabar zuciyar Baseer dajin haushinta, koda ta kirashi a washe garin isarsu ƙin ɗagawa yayi, dukda kuwa saida ta turo mssa massege akan sun sauka lafiya, amma ya gaza kiranta…….
     Kiran data sake masane ya sakashi jan dogon tsaki yana hararar wayar, sai da takusa tsinkewa ya ɗsga tare da dai-daita muryarsa tamkar mai barci.
      Daga can tace, “O love kayi haƙuri, bansan barci kakeba na tadaka wlhy”.
     “Babu damuwa Babie kun sauka lafiya”.
     “Lafiya lau, bayanma baka kiraniba saini na nemeka”.
     “O sorry Love, wani uzurinefa infaɗa miki yay mugun riƙeni, amma kina raina tamkar rubutu bisa dutse”.
     Suhailat tai murmushin jin daɗi tanajin ƙarin ƙaunarsa a ranta, cikeda shauƙi tace, “Ok Love ya wuce, kabuɗe data naturo wasu kaya ka duba mana idan sunyi, idan basuyiba sai a canja”.
         “Kina nufin harkun fara sayen kaya?”.
      ”Eh mana, to miza’a jirane? Somuke muyi mu gama mudawo, kasan akwai shirye-shirye da yawa da ba’ayiba”.
      “Hakane kuma, bara na duba ɗin”.
    Daga haka suka yanke wayar, daɗi yay mugun kama Baseer, irin wannan aure ai yayi, kana kwance abinka ana maka hidima, danma yakula muguntace dasu, yanzu ƴar dubai ɗinnan da dashi akaje ai zaifi ƙayatarwa ko, amma babu komai, zai fanshene, bara dai agama bikin………✍????*_Dan ALLAH kuyi haƙuri da wannan, abini bashi gobe, yau baƙi nayi????????????_*

*_ALLAH ya gafartama mahaifanmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button