NOVELSUncategorized

WUTSIYAR RAKUMI 16

          Desmond ya kalli Ummukulsoom cikeda damuwa ya nufi hanyar ɗakin Amaan.
     Hakan saiya ƙara saka jikin Ummu yin sanyi, saima tabar falon tanufi ɗakinta itama, dan batason ganin abinda zaisa kimarsa da darajarsa ta zube a idonta.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡  

        *_KD_*

     Kwance yake ɗai-ɗai a ƙayataccen falon nasu sanyin A.C na ratsasa, ga kwalin lemo da glasscup a gefensa, idonsa akan waya yanata faman zuba murmushi, kallo ɗaya zakai masa ka fahimci charting yakeyi da masoyiyarsa.
      Wata ƴar zabura yay tareda dunƙule hannu yana faɗin “Yes! Itama ta afka” sai kuma yay azama dafe bakinsa da hannu yana waige-waige a falon, ganin babu alamar kowa ya sauke ajiyear zuciya yana rimtse ido, yasan idan iya bala’innan Suhailat ta jisa ai yau babu mai barci a gidan lafiya, dama ganin tayi barcine yasashi fitowa falo da sanɗa.
     Wayarsa ya ɗauka yacigaba da Charting da Lubnar sa hankali kwance.

        Cikin barci Suhailat ta lalubi Baseer amma sai taji filone a gabanta, kuma matsowa tayi tana lalubawa babu alamarsa a wajen, da ƙyar ta buɗe idonta tareda laluben bedside drawer ta kunna fitila, ganin babushi dai da gaske sai tai tunanin kodai yana bayine, hakanne yasakata maida idonta ta rufe batareda ta kashe fitilarba.
      Kasa komawa barcin tai ta tsaya jiran fitowarsa. Minti uku, huɗu, har aka kai sha biyar babu alamarsa, sakkowa tai a gadon ta nufi hanyar bathroom ɗin tai knocking tareda kanga kunnanta, sai dai kuma tsit babu alamar motsin ruwa, murɗa ƙofar tai ta buɗe ta leƙa, wayam babushi.
       “To ina kuma yaje?”. Ta faɗa cikin riƙe ƙugu da cije lip”.
      Fitowa tai, falon sama ma dai wayam, cikin ruɗani tanufi ƙasa, tunkan ta ida sakkowa ta hangoshi kwance bisa doguwar kujera.
      Wata irin hasala zuciyarta ta farayi, dan haka tafara sauka benen a hankali cikin sanɗa.
     Gaban Baseer ya faɗi saboda jin motsi, da sauri yakai dubansa ga matakalar benen saiya hango Suhailat na sakkowa, ai babu shiri yay azamar goge Number Lubna dayay save da suna Lukman Ɗilau daga kan WhatsApp folder ɗin, yay azamar fitowama gaba ɗaya yakoma folder ɗin Qur’an tareda yin fuska tamkar baiji motsintaba.
    Suhailat data lallaɓo a hankali saboda son ganin miyake? dan zuciyarta kai tsaye tabata amanarta yakeci, sai taga Qur’an yake karantawa, wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke tareda faɗawa jikinsa.
    Yiyai kamar baisan da zuwan nataba, yay wata zabura zai ƙwala ihu ta toshe bakinsa da hannu tana faɗin “Love nice fa”.
      Ajiyar zuciya ya sauke tare da janye hannunta, “Kai Love wlhy kin bani tsoro matuƙa, yaushe kika sakko?”.
     Shagwaɓe fuska tayi tana kuma manne jikinta da nashi, “Ba kaineba ka gudo ka barni, sai kawai na farka babu kai”.
      “Sorry Love ɗina, barci naji na kasayi, shinefa nace bara nayi ko karatun Qur’an ne, gudun karna hanaki barci da hasken waya shinefa nadawo nan. Amma amin hukunci dai-dai da laifina”.
       Murmushi tamasa da ɗora goshinta a nasa, “Yanzu ko zan hukuntaka Love” ‘ta ƙare maganar da manne bakinsu tana bashi wata sumba mai ƙyau’.
       Badan yasoba ya biyemats, kafin kacemi sunyi zurfi tun a falon, daƙyar ya iya ɗaukarta suka koma sama zuciyarsa na mamakinta, wato yanzu data fara gogewa a harkar saiya fahimcima tafisa jaraba, dan lamarinta harya fara bashi tsoro, saida suka gama soyewa fa ya sakko falon chart da Lubna, amma yanzu kuma ƙiri-ƙiri ta nuna ƙari takeso.
       Haka dai ya miƙa wuya bori ya hau kafin su koma barci.

*Washe gari* da safe saƙon Daddynta yazo akan maganar komawarta makaranta, idan kuma batason A.B.U Zaria tafaɗa inda takeso a maidata.
          Baseer dake zaune a dani suna breakfast yaga fara’arta tai yawa tana danna waya, farfesun kifin da yake sha ya ture gefe yana maida hankalinsa a kanta sosai, “Love tasamune shin?”.
      Batareda ta kallesa ba tace, “Kusan haka”.
     Tasowa yay ya dawo kusa da ita ya zauna, shima yana leƙa wayar bayan rungumeta da yay.
     Kallonsa ta juyo tayi tana ƴar dariya, “Wai kasan me?”.
    “A’a saikin faɗa babie na”.
       Kuma ƙadandaneshi tayi cikin tsantsar so da ƙaunarsa, “Daddy ne yace yaushe zan koma makaranta? Idan kuma banason Nigeria nafaɗi duk inda nakeso zai kaini yanzu tunda inada aure”.
      Wani farin cikine ya ratsa Baseer, shima kuma ƙanƙameta yayi, “Kai amma naji daɗi love, yanzu ke wata ƙasa kika zaɓa mana?”.
       Sakinsa tai tana kallonsa a ɗage, “Ban gane wace ƙasa na zaɓa manaba? To ni da wa?”.
      “Keda wa kuma Love? Ni da ke mana, kinada wanda yafini a yanzune?”.
       “Tab inadashi mana tunda ga family na, ni nama faɗa masa banason ko ina, dan ni kaɗai yace, niko bazan iya tafiya ko inaba na barka a 9ja kaci amanata”.
       Wani malolone ya tokare maƙoshinsa, amma ƴar iskar yarinyarnan tama rainashi wlhy, jiyake kamar ya naɗa mata na jaki kozai rage ƙududu, amma saiya daure ya danne yana murmushin yaƙe wanda yafi kuka ciwo, “Haba Love wace irin maganace wannan kuma? Please kishi yabar rufe idonki ki daina tunanin zanci amanarki, kuma idanma karatun yakama a fita ƙetare ai tare zamu tafi, basai nai masters ɗinaba acan nima, mukuma zarce da Honeymoon ɗinmu”.
       Dariya sosai Suhailat takeyi tana nuna Baseer daya cika yay fam, daƙyar ta iya tsagaitawa tana dafa kafaɗarsa, “Oh Alhaji Baseer nawa ka tanada na tafiyarto?”.
      Takaicine yafara lulluɓe ganinsa, yay luuu da idanu kafin ya buɗesu da ƙyar yana haɗiye busashshen yawun daya kasa wuce masa a maƙoshi, tashi yay yabar mata dining ɗin yahaye sama.
      Baki buɗe Suhailat tabisa da kallo, sai da yakai rabin steps ɗinne tace, “Ikon ALLAH sai kallo, to waikai haushi kaji? Kaida bakada ko sisi kazauna mini tsarin banza harda wani Honeymoon ko uwarmi, to lallai kacika ɗancin bati, aimaka ciki ai maka goyo harda zanin ɗaurawa, kama daɗe bakaji haushinba, kajimin   baƙin bawa mai jiran ALLAH zai kawo”.
     Sarai Baseer yajita, dan haka ya juyo a fusace zai nuna mata asalin color ɗinsa saikuma ya kasa saboda gargaɗin zuciyarsa da tace “Da sauran time”. Murmushin dabai shiryaba ya sauke, yace, “Love na gode da gori”. Ya juya yacigaba da hayewa.
      Sai kuma Suhailat taji babu daɗi, miƙewa tai da sauri ta hawo saman daɗan gudunta.
     Isakeshi tai kwance kan gado ya rufe fuskarsa da filo.
    Jikinsa ta haye tare da zare filon, ya ɗago fuska zaiyi magana ta haɗe bakinsu.
    Duk yanda yaso ƙin bata haɗin kai ya kasa.
     
     Bayan sun sami nutsuwa haƙuri taita bashi harya sauka, kafin suje suyi wanka tare cikin farin cikin da Baseer iya fuska yakeyinsa.

★★★

        Da yamma Suhailat tashirya ta tafi gida, hakan yabama Baseer damar bajewa a kan gado cikin bedroom suna shan hirar soyayya a waya da Lubna.
    Yayi zurfi sosai har baiji motsin shigowar motar Suhailat ba, harda shigowarta bedroom ɗin nasu…….????????????⛹‍♀



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡ 

        
          Desmond yay knocking a ƙofar Amaan tamkar yanda ya saba, sai dai shiru ba’a buɗe masaba, sake yi yay har sau biyu nanama babu amsa.
     Harya yunƙura zai bar wajen yajiyo muryarsa da ƙyar yace, “Shigo”.
     Kasan cewar yakan ɗan jefa masa hausa wani sa’in saiya fahimci abinda yake, dan haka ya tura ƙofar ya shiga.
       Amaan daduk zatonsa Ummukulsoom ce yana kwance a bakin gadonsa ido lumshe, da alama kuma duk Knocking da Desmond yakeyi yanajinsa, tsabar miskilanci ne ya hanashi amsawa.
      “Sir! kanada baƙuwa”.
Cikin rashin zaton desmond ne Amaan ya buɗe idanunsa, kamar bazai tankaba saikuma yace, “Waye?”.
     “Sorry sir! Aunty Bukky”.
   Kuma haɗe fuska yay tamkar bazai tankaba, ya lumshe idanunsa ya buɗe a kansa, yace, “Bukky?”.
      “Yes sir”.
Hannu ya ɗaga masa alamar yaje.
    Har desmond yakama handle ɗin ƙofar zai buɗe muryar Amaan ta dakatar dashi.
     A kausashe yace, “daga yanzu karka sake shigomin ɗaki, duk abinda kake buƙata ka sanarma matar gidan tazo ta sanarmin, idan bata falo kajirata harta fito ko ni idan na fito”.
      “Sorry Sir”.
      Uffan baice dashiba ya maida idanunsa ya sake lumshewa, bamashi da alamar tashi yafita ganin baƙuwar tasa.
       Yaɗauki tsawon mintuna goma kafin yatashi zaune yana jan tagwayen tsaki, mai makon ya fitama saiya hau zame kayan jikinsa alamar wanka zaije.

      Tun Bukky na jiran Amaan da marmari harta fara ƙosawa, sai dai kuma tariga tasan halin wulaƙancinsa da baƙar shariya wanda akullum take faɗin Hausawa nadashi.
      A’i dai na nan laɓe sotake sai taga ƙarshen wasan, desmond kam tuni yakoma kan aikinsa, dan ƙokarin shiryama Amaan abinci yake tunda baisan da dawowarsa ba.
      Ummu kam tana ɗakinta kwance, dukda kuwa zuciyarta sai tunzurata take akan takoma falon taga mizai faru tsakanin mijin nata da baƙuwar. Wani kuma sashe na hanarta akan ƙazantar da baka ganiba tsaftace, ita dai ta ƙyautata masa zato yafi alkairi agareta………..✍????









*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button