WUTSIYAR RAKUMI 3

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Hakama Baseer sunata exam, soyayyarsa da Suhaila nata ƙara ƙarfi, ahankali har sunansa da hotunansa sun baje gidansu Suhaila, sai dai ta ɓoye musu shiba ɗan kowa baneba.
Koda yayartama taga hotonsa saita rikice da koɗashi tana tambayar Suhailat ɗan wanene a ƙasarnan?.
Dariya kawai Suhailat tayi, tana faɗin “madam kedai kiga photo kawai, baruwanki da ko ɗan wanene, idan kuma ƴar bayan katanga kike shirin minfa”.
Dariya Amrah tayi tana dukan kafaɗar, Suhailat da faɗin, “Banza kawai, ɓarauniyar saurayi kika maidanima ashe?”.
Kwashewa sukai da dariya har mom nasu dake gefe tana saurarensu.
Suhailat tace, “To ai duniyarce yanzu saida tsaro”.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Komai kaga farkomshi to yanada ƙarshe, a yau ne su Ummu suka kammala jarabawarsu, kowannensu kagani yana cikin farin cikin gamawarsu da baƙin cikin rabuwa da juna, sunata musayar lambobi da adireshi.
Itadai Ummu number wayar baba taita badawa, sannan kanta tsaye take bada address ɗin garinsu, aganinta minene abin ɓoyewa, tushenta shine abin alfaharinta koda kuwa gidansune kawai a ƙungurmin daji, shiyyasa take mamakin wasu ɗaliban dakan zauna suyita sharara ƙarya gidansu kaza da kaza, to randa ALLAH ya ƙaddara zuwan wani kuma yaga ba haka bane sai kaji kunya kenan?.
Haka dai sukaita sallama da juna har lokacin zuwan baba da yazo ɗaukarta. Ta ƙarasa bankwana ga waɗanda basu tafiba, suka kamo hanyar gida tanata kuka baba na lallashinta.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Bayan sun iso gida taɗan samu tarbar arziƙi darajar suna tare da baba, ko kaɗan yanzu lamarinsu baya damunta, aganinta ma sun cancanci uzuri.
Tana samu taci abinci tai wanka saita fice gidan zuwa gidan kakanninta, gwaggo Hinde taji daɗin ganin Ummu, sai godiya takema ALLAH tana ƙari, “ALLAH nagode maka da wannan boko na Umma ya ƙare, kema kizo kiyi aurenki mu huta da surutun jama’ar garinnan, gashinan su Azima harda yaransu bibbiyu, Ramatu da Atine ma cikin na ukune dasu”.
Murmushi Ummu dake cin gyaɗar da Gwaggo Hinde ke saidawa tayi, sannan tace, “Ohni Gwaggo, irin wannan murna haka, to ai konayi auren nasan Basiru zai barni naciga da bokon, dannifa insha ALLAH saina zama lauya”.
Galala Gwaggo Hinde tayi da baki har zaninta na neman kwancewa, ta tattaro abinta ta ɗaure tana ajiye kwanon shanruwan hannunta da zata damawa Ummu fura, “Kekuwa Umma anyi lalatacciyar yarinya, yo banda shegantaka miye kuma abin birgewa a bokon? Inama laifin abinda kika samu? Kaf garinan fa dagake sai ƴaƴan maigarine kuka gama wannan bokon, ke da ALLAH can ki maida hankalinki ga gidanan an fara gina miki a faƙon amare”.
“O ni kuji Gwaggo, to waya faɗa miki shi karatu ana gamashi, ilimi ai kogine, sannan damai neman arziƙi da ilimi bakiji ance basa ƙoshiba? Kuma dan nayi aure sai akace bazan nema ilimin addini dana zamaniba? Haka zamuyita zama babu wani cigaba a garinmu? Nasan Baseeru zaiyi farin ciki da burina shima?”.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Baki Gwaggo Hinde ta taɓe tareda faɗin, “Ke kikaga zaki iya keda Basirun, shima gashinan anata surutu agari yayi kuɗi yana wulaƙanta mutane, wannanfa karon dayazo amotafa yazo garinan dalleliyama kuwa”.
“Mota kuma Gwaggo? To shi dake karatu ina kuma ya samu mota?”.
“Ina zan sani nikuwa, wasu mutanenma marasa tawakkali harsun fara cewa yankan kai ya fara”.
Babu shiri Ummu ta kwashe da dariya, haka tashiga dariya ba ƙaƙƙautawa, saida Gwaggo ta ɗauki abu ta bugeta dashi sannan ta tsagaita daƙyar, “Kai Gwaggo wlhy dolene aringa cemana gidadawa mu ƴan ƙauye, shikenan wai da mutum yayi arziƙi sai ace yankan kai yakeyi? Toku wama yace muku wai ana yankan kai ɗin da gaskene?”.
“To Umma ai karkiga laifinmu, mi muka sani da duniya ke ciki?, duk wani abu da zamani yazo dashi mutumin ƙauye sai yaje birni yake ganinsa, idan antashi zaɓen shugabanni da mutanen ƙauye akeyi, amma dasun ɗare madafun iko saikiga bazasu kuma tunawa akwai wasu masu numfashi a jejina ba, duba kigafa wutar lantarki ta gagari ƙauyennan, masu waya kullum suna hanyar zuwa Kudan kai caji, saima kwanannan ne akace balarabe jikan tasalla yasayo injin wuta (Genretor) yafara cajin dashi, kuma waya ɗaya wai Murtala guda, yo inba sana’a kakeba kullum ina zaka ɗauki Murtala (20) guda ka miƙa wai dan kawai aimaka caji”.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Cikin sanyin Murya da takaici Ummu tace, “Gwaggo ai duk irin waɗannan abubuwan muke dubawa mu dage sai munyi karatun, girman ƙauyennan bai dace ace irin waɗannan cigaban bamu dashiba, ba wuta, babu hanya mai ƙyau, idan ka hawo mashin zaka shigo garinnan ko zaka fita hanjin cikinka tamkar zasu zazzago dan gwazazzabai, ga talauci ya addabemu, ƴar makarantarnan ta gaba da primary ankasa mana, kullum saimunje cikin Kudan, wlhy da ace za’ayi secondary a garinnan iyaye dayawa zasu samu kwanciyar hankalin saka ƴaƴansu karatu, mufa yandama kikasan ba’a ƙasarnan mukeba, kuma mafi yawan ƙauyukan Nageria suna fuskantar waɗannan matsalolin, shiyyasa wani lokacin bancika ganin laifin shugabanni ba, saboda wasu sun fito daga ƙauyukane, suntashi babu mai taimaka musu abaya, shiyyasa dasun sami madafin iko suma saisu fara tsula tsiya da riƙo da kalmarnan ta malam bahaushe *Wutsiyar raƙumi tai nesa da ƙasa*, gwaggo mu kanmu talakawan mun kasa gyara jiyanmu, tayaya muke tunanun shugabanni zasu gyara mana yau ɗinmu, ƙananan yara irinmu masu tasowa mu amfanu da gobenmu jibi tazama ta ƙanenmu, kowa yazo burinsa yayi ɓarnar datafi ta ɗan uwansa”.
”Wlhy hakane Umma, shiyyasa wataran kike birgeni akwai zancen hankali idan kinso”.
Dariya Ummu tayi tana kwanciya a gadon Gwaggo Hinde, “to nidai bara na miƙe a gadon ƴan gayunki Gwaggo karki tadani sai dare, dan ni yauma anan zan kwana”.
“To kihuta lafiya”. ‘Gwaggo hinde ta faɗa danta kula Ummu na fashin salla ne’.
Bayan Ummu tasha barcinta ta tashine Gwaggo kemata bayani gameda kawo kuɗin gaisuwar aurenta da akayi daga gidansu Basiru, ance saisun kammala karatu za’a tsaida magana, to yanzu gashi ALLAH yakawo lokacin, tasan kuwa za’a tada maganar kenan.
Sosai Ummukulsoom taji daɗi, amma saita danne bata nuna a gaban Gwaggo ba, saima rufe fuska da taita famanyi najin kunya.
Saida taga Gwaggo tafita tsakar gidan taita jin daɗinta da godiya ga ALLAH itama takusa mallakar masoyinta cikar burinta a matsayin miji.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Tunda Ummukulsoom tadawo bata sami zaman yini ko ɗayaba a gidansu na Babban gida, kullum cikin yawon gaida ƴan uwa da abokan arziƙi take da yayyenta da ƴan uwanta na ma’auri, harma da dangin mahaifiyarta dake garin.
Yau dai gidan Murja taje, suna tsakar gida itada surukarta suna ɓarar gyaɗa Ummu tai sallama.
Idanu Murja ta gwalalo na mamaki, kafin ta miƙe cike da zumuɗi tana faɗin “A’a a’a lale marhabun da manya-manya maganin ƙanana-ƙanana, maraba marhabun lalale”.
Murmushi Ummukulsoom tayi tanamai jin takaici a ranta, Murja dukta canja ta fara komawa tsohuwar ƙarfi da yaji, shekara uku kacal da aure, wai ahakanma ita tanajin daɗi saboda mijinta yana zuwa neman kuɗi legas, kuma yana iyakar ƙoƙarinsa wajen yimata abu, dan bashida wani nauyi mai yawa a kansa, babansa ya rasu, mamarsace kawai a gidan sai Murja da yaranta biyu saikuma ƙannensa mata biyu suma duk sunyi aure. Ummukulsoom ta ƙarasa gaban Lamunde surukar Murja ta durƙusa har ƙasa ta gaidata.
Da fara’a Lamunde ta amsa tareda mata bangajiyar gama karatu.
Ummukulsoom tace, “Alhamdulillahi” tana miƙewa.
Kamar idon Lamunde zai faɗo haka tabi bayan Ummu da kallo, tana ganin sun shige Lungun Murja dake a katange saita riƙe haɓa tana faɗin “Ohni Lami, yarinya tazama Uwar mata a gida babu aure, kanada wannan agabanka ai ko barci mai daɗi kabar yinsa”.
Su dai su Ummu basusan tanayiba, sunacan hira ta ɓarke a tsakaninsu bayan murja ta ɗeboma Ummu ruwan tulu mai sanyi, tareda ɗaukar ƙalli ƙaƙau ɗinta na saidawa da takeyi ta ajiye gaban Ummu wai tasha iya shanta.
Dariya Ummu tayi tana ajiye kofin silba datasha ruwa, “wato tawajena kina nan da hali baki sauyaba ko? Yo nama wannan abun cin tuwo ai yau a hanyar bayi zan kwana, wai ina yaran nawane?”.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); “Shi wannan ɗan (ɗanta na fari, bata faɗar sunansa saidai tace wannan ɗan????) yana gidan innarsu karime, da yaranta sukazo ɗazu ya bisu, Amadu kuwa yanzunan su Lance suka fita fashi gidanmu”.
“Ok ƙwarai na gamu dasu, kuma naga Rayya da goyo amma dayake hijjab ta saka nama zata ko ɗan Hadiza ne”.
“A’a Amadu ne, kuɗin ƙalliƙaƙau dasukaimin talla suka kawo, yanzu mikike so na dafa miki? Kinsan ku ƴan gayune ba komai za’a bakuba”.
Hararta Ummu tayi tana faɗin “A’a ƴan mayu ba ƴan gayuba, ni kinsan komi kika bani cizanyi wlhy”.
“To shikenan bara afara sayo miki awara gidan tinenen haruna, dan awararta akwai daɗi, dama yau fate muka tashi da sha’awaryi na tsaki, amma tunda kinzo bara adafa hinkafa”.
“A’a wlhy kuyi fatenku, ni namafi sonshi ai, to kodai munsamu na ukune?”.
Harar Ummu Murja tayi tana shafa cikinta, “Na Ukun lafiya Umma, duka watan Amadu nawa? Dana bani ai, wlhy banida komai, kawai dai sha’awace jiya naje gidan sunan Safare aka wawashe faten bamu samuba, nikuma na saka abin araina shiyyasa nace yau saimuyi, Inna kuma tace itama tanaso”.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); “ALLAH sarki, haihuwa ta nawa Safare tayi kuwa?”.
“Ta huɗuce, kinsan ɗanta na biyu komawa yayi ai, yanzu Ukune a raye”.
“Wayyo ALLAH ya amfana waɗannan ɗin”.
“To amin, bara na leƙa nan maƙwafta naga ko ade na nan tasayo awaran”.
Yini guda yau Ummu a gidan murja tayisa, sukasha hirarsu ta zuminci ga fate mai daɗi datai musu, sai bayan isha’i Ummu tabaro gidan.
Tazo tasha masifa wajen baba Yalwa, wai tatafi yawo batazo ta tayata aikin tuwoba bayan tasan batajin daɗi yau da atini ta tashi.
Itadai Ummu haƙuri tabata tai shigewarta ɗaki, babama yana zaune yana saƙar tabarma Uffan baiceba.
Ummukulsoom tacigaba da zaman jiran dawowar Basir, yayinda aketa mata surutun girman datayi, abun na damunta da bata haushi, shiyyasa Gwaggo hinde kullum cikin nema mata maganin baki take, shi kansa baba abun na damunsa, dan haka yasamu mahaifin Baseer akan su tsaida magana a saka rana kodan surutun mutane.
Baban basiru bai musaba, suka kuma kawo kuɗin sallama aka tsaida biki wata takwas, amma idan komai ya kimtsu kafin wata takwas ɗinma za’ayi a huta kawai, yanzu dai dawowar Basiru ake jira.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Hankalin Ummukulsoom daduk wani mai ƙaunarta ya kwanta saboda saka ranarnan, baba ma yasamu ya fara shirin tattarawa zai koma kaduna wajen sana’arsa.
Ummu ta naniƙe akan zata bisa taje ta gaisa Innarsu ƙanwar baba dake kaduna tana aure.
Bai musaba yace ta shirya, itama ta huta da surutan mutane.
Wannan tafiya ta saka su baba yalwa takaici, har suka kasa jurewa saida sukayi tsegumi.
Basu sami amsaba daga baba, ya ɗauke ƴarsa suka nufi kaduna abinsu………..✍????
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU????._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
????????karku bari ayi babuku
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*????????????????????????
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu????????????_*