NOVELSUncategorized

MUTUM DA DUNIYARSA 55 – 56

  *_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
             _(ya dace ya gyara kansa)_
                 *_Bilyn Abdull ce????????_*

                   *_[55➖56]_*    
…………..Belin Abba dai ya gagara gasu Uncle yahya gaba ɗaya, dagashi har
Umma kallo ɗaya zakai musu ka fahimci suna tare da damuwa, hakama su Zarah harda kukansu, sai Ummace taita lallashinsu.
     Ɓangaren Hajia Hindu ma tashiga damuwa, hakama yaran data sanar musu duk sai suka shiga rashin walwala, itama saita kwantar da kai suka haɗu dasu Uncle yahya akai cuku-cukun lauya aranar.

 *WASHE GARI*

      Washe gari ƙarfe shabiyu aka shiga shari’ar su Abba, tun a bayanin ƙarar jikinsu Uncle yahya yay sanyi, anama Abba tambaya, amma sai yaƙi amsa laifinsa, saida aka kai ruwa rana shida Lauyan Alhaji Garba, saida shedun dake tsakani lokacin da aka amshi kuɗin suka bayyana kafin Abba ya nutsu. ya amsa karɓa kuɗin Alhaji garba da yayi, amma yay bayanin yanda sukayi dashi daya bashi auren Jiddah, daga baya kuma saiyace ya janye. 
      Sosai ran Alƙali ya ɓaci jin sunyi amfani da yarinya cikim harƙallarsu, take anan ya yanke hukunci dan ƙ
Shari’ar bata buƙatar zama na gaba kuma
      “Bisa ga sauraren wannan shari’a da mukayi,  dakuma amsa laifin da wanda ake ƙara yayi, tareda shaidu ƙwarara, wananan kotu ta yanke hukuncin dolene Alhaji Zakari yaro ya biya Alhaji garba kuɗinsa naira miliyan ashirin da biyar kamar yanda suka tsara lokacin auren ƴarsa, sanan miliyan Ashirin da biyar dayace ya barmasa dolene yacika alƙawari ya bar masa ɗin, tunda anyi auren, kuma yarinyar harma ta tare a gidansa, wani abune daban ya rabasu bayan auren, shikuma Alhaji zakari yaro bazaici miliyan ashirin da biyar ɗinnan shi kaɗai ba, zai ɗauke miliyan goma ne a ciki, sauran miliyan sha biyar kacokan zai ɗaukesu yabama ƴarsa da yay auren jari da ita. anmasa sassauci yafara biyan Alhaji garba ƙuɗinsa kafin ƴarsa, yanzunan za’aje da dillalai gidansa da inda yake sana’a a ƙiyasta da kuɗin da ake binsa, idan sunkai abashi canjinsa, idan basukaiba yanema ya cika nanda sati ɗaya kacal. Kotu”. Alƙali ya buga guduma an tashi kenan.
     Sosai hankalin Abba yagama tashi, banda zufa babu abinda yakeyi, kotu kam tuni ta ɗauki ƙananun maganganu, kowa yana tofa albarkacin bakinsa akan wannan lamari
     Ita Umma ma tarasa abin cewa, jinwai Jiddah taci miliyan goma sha biyar. Shi kansa Uncle yahya abin yay masa wani gingiringin, su zarah kam sunrasa mizasuyi, baƙin cikin halin da abbansu yake ciki, ko farin cikin kuɗin da ƴar uwarsu ta samu. Hajia hindu kam ai tana cikin ruɗani, a ganinta wannan shari’ar batayiba, ita kuma ƴaƴanta shikenan su tashi a tutar babu, kai ina da sake alƙur’an.

      Umma da yara gida suka nufa gwiwa a sake, Uncle yahya kuwa yabi jami’an tsaro dake tare da abba.
     Kasuwa aka fara zuwa babban shagonsa dake danƙare da kayan kicin, nan take mahukunta suka fara ƙiyasta abinda ke cikin shagon da shagon kansa, dan tuni yazama mallakinsa dama.
     Har magriba suna cikin kasuwa ana cakusawa, daga ƙarshe akaima shago da kayan ciki kuɗi naira milyan ashirin da biyu, sai cinikin ciki dubu ɗari tara da wasu canji a sama, amma basu cika miliyan ɗayaba, hakanne yasa akabarsu a miliyan 23 kawai. 
       Sallah kawai sukayi aka nufo gidansa, dama tuni su ashir sun kawo dillalalai ana zuwa maganar kuɗi kawai akayi, ansaya naira miliyan bakwai shima gidan, kuɗi sun kama miliyan talatin kenan, saura miliyan goma ake nema kenan harda na Jiddah.
       Hindu dai kuka take rurus yaranta na tayata, wanan wace iriyar masiface, shikansa Abban kukan zuci yake, shikenan yau tashi tagama ƙarewa, ƴar kwanciyar hankalinsama ɗayace sune kuɗin da akace yabama jiddah, yasan insha ALLAHU hannunsa zasu dawo, dan karɓewa zaiyi koda karfin tuwone.
     Komawa akai da abba station, Uncle yahya yawuce gida jikinsa a sanyaye.
     Sunbar Hajia Hindu na neman yin ƙaramin hauka, dan taci alwashin sam bazata amince da wanan tsarinba. A daren ta kira ƙaninta tantirin ɗan isaka yana zaune a legas tace yataho kano gobe-gobe.
        Baƙaƙen magana yafara sakar mata dan basa shiri sosai dama, ta dakatar dashi tanai masa bayani dalla-dalla, jin zancen kuɗine saiya kwantar da hankalinsa, atake yay mata alƙawarin baro legas shida yaransa da adaren ranar.
    Wannan shine yaɗan saka mata kwanciyar hankali, dan tasan bazasu tashi a tutar babuba dai kenan suma.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

        Jiddah duk batasan hidimar da akeba, dan Umma ta hana kowa ya sanar mata, amma su Aunty Nafisa dasu Aunty Sauda duk an sanar musu da halin da ake ciki, dukda abinda yay musu kasancewarsa mahaifinsu hakan bai hanasu shiga tashin hankaliba da tsananin damuwa.
      
         Washe gari aka ida tattare kuɗin dake bank accaunt ɗin Abba da wani gidansa dake karkasara ana haya, kuɗi sukakai miliyan talatin da shifa da ƙyar, baida wata sauran kaddara sai gidan dasu Umma suke ciki, shima sai akayi cinikinsa miliyan uku da rabi, yamayi darajane saboda a cikin tsohuwar anguwa yake wadda gidaje keda daraja komai lalacewarsu, dukda ma dai gidan fes yake, ballema anmasa fenti lokacin bikin Jiddah da alhaji garba.
     Dabarar da Uncle yahya yayi itace roƙar alƙali a saka gidan dasu Umma suke ciki a lissafin kuɗin jiddah, hakanne yasa aka ɗeba kuɗin Alhaji garba miliyan ashirin da biyar aka danƙa hannun su ashir, sauran miliyan sha shida da takardun gidan dasu Umma ke a ciki aka damƙama Uncle hayha, saura dubu ɗari biyar Abba zai cikama jiddah, anbashi sati ɗaya yakawo cikon kuɗin Jiddah rabin miliyan.  
         A ranar aka sako Abba da yamma liƙis suka taho da Uncle yahya daya ɗakkoshi da nufin ajiyeshi gida, shikuma yakoma yakai ƙuɗin Jiddah banki, dan canne kawai zasu tsira sai ƙura ta lafa kuma asan abinyi da su.
       Zuciyar Uncle yahya a tsarkake take, dan haka yayma abba rakiya har cikin gidansa da aka sayar wanda hajia hindu take ciki.
        Abin mamaki saiga hajia hindu taimusu tarba mai nuna alamun damuwa da halin da Abba yake ciki, harda rungumeshi a gaban yara babu ko kunya. Da wanan damar Abba yasamu damar gwargwaɗa mata wata magana. Kanta ta jinjina masa sanan ta sakesa tana kallon Uncle yahya.
       “Dama dawowarku muke jira yahya, dan harma munfara haɗa kayanmu, kwanaki biyu kawai suka bamu mubar gidanan, dan ALLAH kozaka taimaka mana da kimtsa kayan ɗakin Abban kalifan”.
       Kallonta uncle yahya yayi, kamar zaice wani abu saikuma ya fasa yaɗan kalli agogonsa, yamma tayi lis, ga kuɗinnan da yakeson kaiwa banki “Hindu inaga mubar aikinan zuwa da safe, yanzukam dare yayi gaskiya”.
       “To shikenan hakanma babu damuwa, amma taimakamin ka dakkomin wani akwati dake sama a cire takardun gidan Jiddah karsu shiga ruguntsumi”.
     Uncle yahya bai kawo komai aransaba, ya maida kallinsa ga Abba dake zaune su Hussain sun zagayeshi, “Babu damuwa, wannene ɗakin?”.
    Da hannu ta nuna masa, babu musu ya nufi ɗakin kansa tsaye, saɗaf-saɗaf hajia jindu tabi bayansa, yana shiga taja ƙofar ta rufe.
     Da sauri Uncle yahya yajuyo yana ƙwala mata kira da roƙon ta buɗesa, amma ƙiri da muzu taƙi.
    Dawowa tayi wajen Abba tana faɗin “Nagama aikin da kasani Abban kalifa”.
       Da sauri Abba yaja hannunta sukabar gaban yaran, “Yauwa hindu, abinda yasa nace mu kullesa saboda mu samu mubar gidanan, dan ko sama da ƙasa zata haɗe bazan bama jiddah waɗannan maƙudan kuɗinba, maza duk abinda yadace ki haɗa mu kama hanyar kamaru, dagacan zamuyi sudan, munbar Nageria kenan har abada”.
      “ɗari bisa ɗari na gamsu da jawabinka, amma muyi haƙurin asubanci, dan yanzu dare yafara, tafiya da waɗannan makudan kuɗin haɗarine Abban kalifa”.
      Shiru Abba yay yana nazarin maganarta, zuwa can yace, “To babu damuwa, yanzu dai ki haɗa mana dukkan abinda yadace, a yanzu mu lodasu a mota, ko yara karki sanar musu komai”.
       “Hakan yayi amma kuma matsala ɗaya, idan Yahya yakira mana ƴan sandafa?”.
       “Kwantar da hankalinki, saida na tabbatar yabar wayarsa a mota sanan”.
      Daɗi ya kama hajia hindu ta rungume abba cikeda ɗoki.
          
         Duk bugun ƙofar da Uncle yahya keyi basu buɗeshiba, harma yagaji ya bari, hankalinsa yayi matuƙar tashi dajin bayanin da Abba yazo yamasa a bakin ƙofa.
    Idanunsa na zirar da hawaye yace, “Yaya karka aikata haka, Jiddah fa ɗiyarkace data fito daga jinin jikinka, miyasa zaka aminta da cigaba da zalintarsu suda mahaifiyarsu, kana ganin adalcine gudun da zakayi ka barmu saboda dukiya? Baka tsoron ita wadda zaka gudun da ita taci amanarka?, wlhy nasan jiddah zata iya barmaka kuɗinnan, amma sh……..”
      Cikin daka tsawa Abba yace, “Ya isheka haka munafiki, babu abinda ya isa dakatar dani wlhy”.
    “shikenan naji yaya, Amma makomar auren maman Nafisa fa?”.
     ”Aurenmu na nan munafiki babu mai rabashi, bazan taɓa yadda bakin inna ya biniba, tunda tace idan na saketa ALLAH ya isa ko bayan ranta to bazan saketanba balle kaje ka aureta, dan nasan burinka kenan a kulum, saidai ta mutu da aurena wlhy”.
       “Yaya karkayi haka dan ALLAH, wanan zaluncine wlhy, ka tausayama baiwar ALLAH nan koda a wanan gaɓarne”.
    Tsaki Abba yay yabar masa bakin ƙofar.
  
      Sosai hankalin Uncle Yahya yakuma tashi, haka yahaƙura ya zauna yana ƙulla abinda zai fisheshi, gashi wayarsa na a mota ya bari.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button