NOVELSUncategorized

YAR SADAKA 3&4

???????? *’YAR SADAKA..*????????


*STORY & WRITING BY…*
         *BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO…..*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO…*
*MMN FAREESAH*
1⃣&2⃣


Amsa Kiran mashkur yayi,,kafin yayi Magana Nasir yace,,abokina muke jira kaga lokaci Baya jira,, murmushi mashkur yayi Yana Kallan mummy..

Shikenan Nasir karka damu gani a hanya,kabani 5 minutes Zan qaraso,, shikenan Ina jiranka cewan Nasir Yana kashe wayan..

Murmushi abbakar yayi Yana cewa Ai nasan mummy bazata Bari ya fito da wuri ba,,Dan Dama da kyar ta Bari zeje wannan kauyen”Ni wallahi ta birgeni data nuna bataso Duk be yadda da Hakan ba mansur ya fada Rai bace.
Inama inama,,Kai nifa naso Nike da wannan gatan irin na mashkur da ko zaman Nigeria baniyi, dariya suka sa daidai lokacin da mashkur yazo.

Drive ne ya Bude masa qofa nan ya fito cikin takunsa na qasaita,, Ido suka zuba masa suna kallo,,shiko murmushi yayi ya qarasa kusa da Nasir tare da miqa masa hannu,,Daya bayan Daya suka riqa gaisawa da abokan nasa.

Gaskiya abokina Baka dace da zaman kauye ba,,kauyen ma wai Fulani,,Tabe Baki mashkur yayi tare kallan nasir,,Nasir Ka kirani gashi nazo banga alamun tafiya ba.
Karka damu yanzu zamu wuce drive ya kusa zuwa,, mashkur be qara magana ba,suka cigaba da hira batare daya sa musu Baki ba.

Bala,zaka iya tafiya,, dasauri Bala drive yace, ah ah ranka ya Dade hajiya tabani umarni Karna sake na tafi har sainaga tafiyanka,, girgiza Kai yayi Yana me Jin dadin yadda mummy ke Kula dashi fiye da yadda ta damu da kanta,,
Karka damu kawai kaje Ka gayamata mun wuci,,kayi hakuri ranka ya dade bazan iya tsallake umarnin hajiya ba..


Seka ta Zama Dan wahala cewan Nasir Yana hararan Bala,,
Ba’afi 2 minutes ba sai ga lafiyayyan mota ya faka a gabansu, Basu bata lokaci ba gurin Shiga,nan drive yaja suka Fara tafiya sai kankan Fulani..Garin kankan..


Karfe uku dai  suka safka cikin kauyen dabe wuci a qirga gidajen ba,,suna zuwa aka kaisu gidan me gari,,hannu biyu me gari ya amshesu tare da yi musu sauka ta musamman,,

Fura da nono aka Basu sai kankana da aka jere kusa dasu,daga gefe dabino aka kawo cike da kwarya sai warar Fulani,Wanda akeyinta kama awara saidai ita da nono akeyi ake soyata kama awara.

Nan da nan guri ya cika da kamshi ,,mashkur ne ya saurin dago Ido Jin kamshin dabe taba Jin irinsaba adukkan abincin dasuke ci,,saliva ne ya cika masa Baki,nan da nan ya hadiye Yana Yana tandar Baki..

Guri aka Basu Don su ci abinda suke so,,nan fa yara kauye suka zagaye motansu suna shafawa tare da yimusu zane,, 

Da gudu wata yar karamar yarinya tazo tana zana photon saniya a cewarta saniyar yakumbo ce,,nan yara suka riqa tsalle suna murna, mashkur da abokansa Basu San aika aikan da yara ke musu ba,wara kawai sukeci suna santi, dasauri Nasir ya dago Yana kallan inda yaji ihun yara sunata fillanci,,beji abinda suke fadaba sedai yaji ana futanci,,a hankali ya tashi ya leqa ta window,

Lafiyayyan zaki yayi Yana fita a dakin da gudu yayi Kan yaran,,wasu irin Zane ya gani Wanda akayi da karfe wani da qusa,,tini ya hada Kan yaran Wanda suwa yanzu sunfara gudu suna yeee saniyar nijlah tafi ta kowa kyau.

Idon Nasir ne ya safka Kan wata katuwar saniya da nijlah ta zana,photon yayi kyau kama ba jikin mota aka zana shiba,,Kai Nasir ya fada cikin tsawa,wacece nijlah a cikinku???

Cikin murmushi nijlah tace nice,,kece ko aiko saniya tayi kyau,,zoki zanamin wata ingani Dan ni banyadda ke kice kika zana ba”

Da gudu yaran suka dawo jikin Motan,,wasu na cewa suma zasu zana,,suna zuwa Nasir yafara kama hannun nijlah,kafin yakaima sauran Duka,,tini suka fece wasu na kuka,,itako nijlah harta Fara dariya tana cewa.

Kowa ya kirasu, Naga dai ni dayace nijlah ni Dan birni ya Kira ko,,bata rufe baki ba Nasir ya kaimata Duka,,wani gigitancen ihu nijlah tasa tana Kiran yakumbo.

Wayyo Allah yakumbo kizo Dan birni ze kasheni,,kuka sosai nijlah take tana Kiran yakumbo kasan cewar ba’a taba dukan nijlah ba,,sedai taga ana dukan yara,Dan ita bame fitina bace sedai rigima kawai data cika Mata ciki,,

Shiru mashkur yayi Yana sauraran kukan yarinyar,,kai Mansur kama Nasir Ke Dukan yara,,haba Dai Daga zuwanshi kauye zefara da Dukan yara,,

Tashi mashkur yayi Aiko yaci Karo da kyankyawar fuskar nijlah idanta yayi jajur tana kuka kai kace Wani duka me yawa aka ma,, dasauri mashkur ya fita tare da janye nijlah Daga hannun Nasir yace.

Kai Nasir Baka da hankali bakaga yarinya ce itaba,,wacce irin yarinya kai bakaga barnar data   aikata jikin  Mota ba,,kodan batasan darajar Mota ba..

Tabbas nijlah batasan darajar Mota ba,,Kamar yadda bakusan darajar Dan Adam ba,,fizge hannunta nijlah tayi ana mashkur ta fada jikin yakumbo tana kuka,,Bayan ta yakumbo ta riqa shafawa tana Bata hakuri.

Kiyi hakuri nijlah,baki da Mai Rama Miki sabida maraici,,inama wata me gata kuka taba dakun bar kauyen nan da qafafunku.

Jikin Nasir ne yayi sanyi harya Bude baki zeba yakumbo hakuri yaga ta dauka nijlah tana tafiya tana hawaye,, kwanciya nijlah tayi jikin yakumbo tana fillanci,,Dan Hausa Bata gama Shiga bakinta ba.

Ka gani Ko,kagani nasir Daga zuwanmu kaja mana Magana,menene aciki dantayi Zane jikin Mota,,Ni gaskiya banji dadin abinda ka aikata ba,ya Zama dole muje har gida abasu hakuri.

Shikenan abokina,,Nima bada mugunta na buge taba,,wallahi kaji na rantse sau Daya na daketa a hannu sai hannunta kawai Dana riqe Amma ta riqa wannan kukan har tana birgima,,Allah ya kyauta mashkur yace tare da komawa cikin dakin..

A ranar suka Gama cike komai sedai kowa yace baze iya Zama a wannan kauyen ba Dan haka suka Hana drive tafiya a nufin gobe zasu bar wannan kauye.

Babu abinda zesa na tafi daga wannan kauye indai bana Gama abinda nazo yiba,,sedai Ku Ku tafi Amma ni naga gurin Zama, mashkur yafada Yana gyara Zama..

Kai ina wallahi ,,bazan taba iya rayuwa anan ba, bakaga yaran garin ki mota Basu sani ba,,yo ina zasu sani daga akoru koru babu abinda suka sani,,

Uhmn nidai gaskiya Bazan Iya tafiya ba,senaje Na nemi yafiyar wannan tsohuwa da yarinyarta Naji tace marainiyace, Nasir ya fada cike da nadama” ok kaima Zaka zauna Kenan cewan Mansur Yana dariya,, gaskiya banaji Zan iya,,hhhhh kawai gobe mu Koma birni inyaso kudi suyi aiki a chanza mana gari Amma Ina wannan gari ni banga gurin aiki ba.

Shidai mashkur be qara Magana ba Se Dai murmushi dayake saki Akai Akai.

Karfe 8 na dare Suna zaune sun rafka uban tagumi sabida ba network me kyau balle Ko waya ta debe musu kewa sukaji ana bubbuga kofan Dakin,,kai wayene haka yake mana bugu kama Na..,,hararan Nasir mashkur yayi ya hanashi fadar abinda yayi niyya,,

Ka shigo akace,, dasauri Bello ya shigo Yana washe Baki yace,,sannunku dai Baki,,me garine yace a gayamuku zaaje dandali,ko kuma kunasan zuwa kuyi kallo,,eh gamunan zuwa mashkur ya bada amsa..

Tafiya Bello yayi Yana cewa yau Yan birni zaku sha kallo a dandali Allah yasa danladi me kidan kagane zeso wannan dandali…

Haba mashkur me zamuje kallo a wannan kauyen nibanga abin kallo ba,,ni na gani yafada Yana fita waje,,kaga mashkur Nima zanje,tsaya ganinan,,Nasir ne yafada Yana kallansu mansur..

To yaya zamuyi cewan umar suka suka mara musu Baya..


Tin daga nesa suka hango hanken fulatan kyau da aci balbal gefe guda masu suyan kifine da tsire sai Yan Mata wadanann wasu wuci shekara 12 zuwa 13 ba,,Suma da nasu kayan tallan,raga Dada da kosai da Mai burodi lolxx.

Mashkur har sauri yake Dan tin daga nesa gurin yayi bala’in burgeshi.


Yakumbo na zuwa gida ta kwantar da nijlah tana kallan yadda ta Zama abin tausai,,kiyi hakuri kinji yarinyar kaka,,Allah ze saka Miki..
Nidai ban yadda,ara ta kanni  saina Rama,ai dai na ganeshi,uhmn uhmn fa nijlah banisan tsokala.

Yakumbo kema kinsan Bani bari kowanne mara kunya,,inda harfa da riqemin hannu yanzu da iro ya ganci yaya za’ayi,kaka kinsan fa iro da kishi”

Ke qaniyanki nace,wai ba na hanaki Kula wannan iron ba,, nijlah yanzu fa shekara 9 kike se Yan watan ni,, ki Bura kidan qara girma Dan bana tinanin zamuyi muki aure a shakara Goma sha uku,,gwara kisama kanki  salama har Malam ya Samu kudin sai Miki katifa da korai.

To kaka, yau Zan gayamasa danaje dandali,,to kaka ki Bani biyar saina tafi,kinga dare sai qara yi shike..

Kiyi hakuri nijlah yauma Bani da ko biyar,,tsalle nijlah tayi ta Fadi qasa tana kuka,,ni wallahi sai kin Bani biyar Naga ba’a zuwa dandali ba biyar,wasu har Goma ake Basu Amma ke kullum hakuri kike Bani.

Wai sai yaushe Zan gayamiki kidena hada kanki da yaran garinann nijlah meyasa kikesan batamin Rai akan Baki kudin dandali ko kinaso Nima na Fadi na mutu..

Nijlah najin an Kira mutu take Shiga hankali ta,Dan haka ta tashi tana turo Baki,,kaka na tafi.

    *Yawan comments yawan typing,, comments Kai ke nuna labari yana dadi ko babu,,akullum ina qara gayamuku daku riqa turawa wasu group’s bayan kun karanta, nagode*

*Momn sultan ce*✍✍✍

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button