NOVELSUncategorized

YAR SADAKA 19&20

???????? *’YAR SADAKA..*????????


*STORY & WRITING BY…*
         *BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO…..*
*MMN AMATULLAH*




*SPECIAL GIFT TO…*
*MOMN ANSAR*



1⃣9⃣&2⃣0⃣


Mummy kuma,,ke Yasmeen dama kina waya da mahaifiyar yaran nan” gizgiza Kai Yasmeen tayi tana kallan mama data kafeta da ido,,amsa zaki Bani,kinfi kowa Sanin bagane wannan yaran naki nake ba..
Cikin yauqi da yanga Yasmeen tace,,Allah mama bamu waya da ita”
Ok!saiki gayamin ta ina mahaifiyar sa ta dauka number ki??
Mama sau dayane mashkur ya kirani da layinta shine nayi saving,,cike da rashin gamsuwa mama tace,,idan bakwa waya da ita yaya za’ayi ta kiraki???
Mama ba ita bane yayanshine,,sunanta aunty lateefah sedai da wayan mummyn ta Kira kuma tace wai mummy nasan ganina..
Mezaki Mata???
Eyyah mama Nima bansani ba,, Yasmeen ta fada tana turo Baki..
To babu inda zakije”wannan ai shirmene ki dauki qafa kije har gidansu saurayi kina magana da mahaifiyar sa,,mama Allah bantaba zuwa ba sedai jikina Yana Bani kamar akwai matsala..
Wanne irin matsala kinga Yasmeen kidena kawo tinani marasa kyau a cikin zuciyanki…
Mama ba haka bane,,wallahi tin jiya gabana yake faduwa ki abinci ban iya Ciba,,gashi sai Kiran mashkur nake wayanshi kashe,,kuma Shi be Kira ba,,gashi yanzu aunty lateefah ta Kira mummy na nemana,,kinga ko da wani abu.
Babu komai Insha Allahu,,karyar da murya Yasmeen tayi tana hawaye tace,,mama Dan Allah kibani dama naje wallahi bazan zauna ba..
Hmmm Yasmeen ina jiyemiki Abu Amma ke Baki gani,,akullum ina gayamiki ki rage wannan soyayyar da kikewa mashkur,,namiji fa mijin mace hudu ne..
Bata fuska Yasmeen tayi tana kallan gefe tace,,,mama kullum gadanki Baya wuci Kan mashkur,,ba aibu bane Danna nuna kulawa da tsananin soyayya gareshi,,mama mashkur Yana Sona har inaga kama Sanda yakemin ya zarta nawa”” duk da haka ki rage nidai ina gayamiki..
To mama Dan Allah naje???
Ajiyar zuciya mama ta safke tana kallan yadda Yasmeen ta narke Mata kama ance wani Abu ya Samu mashkur tace,, shikenan kije Amma sainayi waya dashi mashkur din naji daga bakinsa yakuma hadani da maman nashi..
Mama kenan,,haba mama na saikace Baki yadda da tarbiyyana ba,,mama kinsani mashkur Baya gari kuma wallahi number mamansane barima nakira saikiji da bakinki..

Number mummy Yasmeen ta Kira sedai wayan akashe Dan haka mama tace babu inda zata fita,,kuka Yasmeen tasa tana Jin wani irin yanayi a dukkan jikinta,,jitake kama qirjinta ze fashe zuciyarta ta fito gaba daya Kota huta da abinda takeji,,koya ta motsa Kota Tina sunan mashkur sai taji kama andora Mata dutse aka,,duk yadda taso hakura takasa haka tasa mama agaba tana kuka..

Yasmeen meyasa kikesan dagamin hankali,,ba Duka ba zagi amma kinsani gaba kina kuka saikace qaramar yarinya..
Mama kibari naje ko hankalina ze kwanta,,wallahi mama akwai matsala,,bantabajin irin wannan yanayin ba sai jiya zuwa yanzu,,Insha Allahu bazan wuci 1 hour ba Zan dawo..
Shikenan Yasmeen tinda haka kikeso saikije daki sani gaba kina wannan kukan ko kunya baji..
Share hawaye Yasmeen tayi tana murmushi tace,, nagode mama..
Mama bata iya bata amsa ba Sai binta da kallo tayi tana mamakin yadda Yasmeen ke nuna damuwanta agaban kowa..

Dago jajayen idanunsa yayi ya zubamata ido Yana kallan yadda take kuka tana Kiran kaka,,wani irin juyawa kanshi yake sabida halin dayake ciki ga kuka dake taba masa zuciya,,ahankali ya riqa Kiran sunanta..
Nijlah. nijlah. Nijlah..
Bata amsaba Saima qarawa kukanta sauti tayi,, ya rasa yadda zeyi da ita,,nan ya miqa hannu Yana Magana da shaqanqiyar murya,,zomana amaryar mashkur,,maqale kafata nijlah tayi ta kuma juya masa baya tana turo baki,,duk da haka ranshi be baci ba ya cigaba da kiranta Yana rarrashinta,,amma duk da haka bata iya shiru da bakinta..
Shiru yayi yana kallanta tare da tinanin ta inda zefara rarrashinta.
Ahankali ya tashi Yana tafiya isa inda take kwance,,kafin ya qarasa nijlah tafara birgima tana juyi a qasa..
Haushine ya kamashi Dan haka ya daka Mata tsawa Wanda tasa hantar cikin nijlah kadawa nan take jikinta yafara karkarwa ta fada jikinsa tana safke ajiyar zuciya..
Rungumeta yayi a karo Na farko Yana shafa bayanta”kukan ya isa haka,,ko kinajin yinwa,,daga masa kai tayi tana qara shigewa  jikinsa..
Labensa na qasa ya cije Yana tinanin yadda ze bullowa labarin,,sedai yayi alqawarin baze taba rabuwa da nijlah ba,sabida nijlah amanar Allah ce agurinshi…
Ahankali ya Tashi da ita a jikinshi ya zauna gafen bed Yana qaremata kallo,,qara shigemasa tayi sabida karkarwa da jikinta ya dauka..
Kinaso nazaneki,,saurin girgiza masa kai tayi,,bakinta na rawa tace Dan Allah kayi hakuri..
Zan hakura amma saikin dena wannan birgiman da kike,,koni bakiga halin da nake ciki ba???
Shiru tayi,shiko ya cigaba da Magana,, nijlah indai baso kike zuciyana ta buga ba,toki dena irin wannan kukan Kina birgima a qasa saikace yarinya,,dagowa tayi tana kallansa shiko ya dage Mata gira,,wai ko bakisan kin girmaba??.
Nan ma shiru tayi saida taji ya janye jikinsa anata yana qoqarin Tashi tace..
Kado yinwa nakeji”
Kobata fada ba yasan dole zataji yinwa duba da rabanta da abinci nan yayi murmushi yace jeki falo ki gaya mummy..
Bakinta na karkarwa tace,,Nina qoshi”
Yana niyyan Magana yaji ana buga kofan dakin,,beyi Magana ba yayi shiru Yana sauraran bugun..

Mashkur wai bakajina ina tsaye tin dazu baka bude ba” menene ya fada a hankali” mashkur ni kake tambaya menene??
Cike da qosawa yace,,haba aunty lateefah,,wai me kike nema dani,,Nabar Miki falo nan ma saikin biyoni..

Toka fito mummy na kiranka..
Ina zuwa yabata amsa a ciki,, juyawa aunty lateefah tayi tana tafiya tana tinanin abinda ya chanza mashkur yaran da ko Magana bata dameshiba..
Mummy yace Yana zuwa..
Tinda Yasmeen ta hau titi take gudu kama zata Tashi sama,,ba ita ta rahe gudun motan ba har saida ta shigo layin gidansu mashkur,,Yana zuwa tayi horn get man ya bude mata,,bata iya daidaita parking ba ta fito tana sauri zuciyanta da halbawa da sauri da sauri harta isa kofan falon,,a bude yake Dan haka tayi sallama tana jiran a amsa Mata”
Yaya ne ya iya amsawa Yana kallan kofan,,a hankali Yasmeen ta shiga falon kanta a qasa tana mejin kunya..
Qasan kafet ta zauna tace ina yini,,lafiya qalau suka amsa kafin mummy tace..
Ke lateefah jekice yazo yanzu kafin ranshi ya baci,,kafin lateefah ta Tashi mashkur ya qaraso falon,,nan idansa ya safka kan Na Yasmeen Wanda tayi mamakin ganinsa adaidai wannan lokacin..
Murmushi yamata tare da kashe Mata ido,,duk da yadda zuciyarta ke halbawa saida ta mayar masa na martani,,bakinta a bude a hankali tace lvu..

Kusa da mummy ya zauna Yana niyyan kwantar da kansa jikinta tayi saurin tureshi tana hararanshi,,karka soma wallahi,,shiru yayi yace,,ke kuma daga ina mashkur ya tambaya Yana kallan Yasmeen..

Kafin Yasmeen tayi Magana mummy tace,,Nina sa akiramin ita,,inaga zata fini sanin gaskiyar Magana akan wancan aljanar yarinyar..

Dasauri Yasmeen ta daga kai tana satar kallan mummy,,gabanta Na cigaba da faduwa tace,,
Mashkur wacce yarinya ake Magana,,Dan Allah kada ka hada soyayyana da wata ta qare maganar hawaye cike a idanta..

Daddy dake shigowa ya bisu da kallo Yana mamakin abinda yasa gidan nasa ya zama haka kama anyi mutuwa,,kusa sa mummy ya zauna Yana kallan mashkur,,kai kuma saukar yaushe,,kafin mashkur yayi Magana daddy ya qara wata tambayan?
Hajiya bakuwa kukayi,,eh kawai mummy tace tana hararan mashkur, ka tambayi danka shize gayamaka ko wacece..

Qara yin qasa dakai Yasmeen tayi tana goge hawaye Dan ko Magana bazata iya ba..
Mashkur wacece wannan ya fada Yana nuna yasmeen..

Bakinsa Na rawa yace Yasmeen ce,,budurwata,,budurwarka,,wani abune ya faru Naga tana kuka,,shiru sukayi aka rasa Wanda ze yiwa daddy bayani..
Ganin haka yasa daddy kallan Yasmeen ya Kira sunanta.
Bata iya amsawaba daddy yace Tashi kije gida nizan zo muyi magana da abbanku..

Da gudu Yasmeen ta fita tana kuka..

Tana fita daddy yahau mummy da fada,,haba hajiya akan me Kina kallo yaro ze kawo yarinya har gida bazaki tsawatarba,,Nina rasa meyasa kike daurewa yarannan gindi yake abinda yaga dama..

Daddy kayi hakuri Nima bansan da zuwan Yasmeen ba anan na ganta”kai mashkur har kanada bakin Magana,,daddy aure fa yarannan yayi ga matar can ya sata adaki cewan lateefah tana huci…

Sake da baki daddy yace aure kuma,,aure wanne iri” saika tambayi danka cewar mummy..
Kai mashkur dagaskene abinda suke fada??

Bakin mashkur Na rawa yace” kayi hakuri daddy haka Allah ya qaddaramin badaga ni….
Kayimin shiru mutumin banza saida kasani tambayama aure sannan zakayimin shegan taka,,bada niyya nayi wannan auren ba,,kuma banyi Danna tozar taku ba,,daddy ka fahimceni..

Amma ko kayi wauta mashkur,mena rageka dashi,,koka taba kawomin abu kanaso na hanaka,,cike da nadama mashkur ya girgiza kai..
To meyasa kayimin haka,,da wanne ido Zan kalli iyayen wannan yarinyar?

Shiru mashkur yayi Yana matsar ido nan ran daddy ya baci yayi kanshi da duka,,dasauri mummy ta tare tana girgiza masa kai,,kayi hakuri Alhaji,,ba laifinsa bane,,laifin mugayen mutanan ne dasuka daura masa auren ba saninmu..

Ran daddy a mugun bace yace,,idan su Basu sa hankali shibashi Shi,,ko zaman kansa yake,,daddy kayi hakuri wallahi ban na bata ranku nayi wannan auren ba,kada kuyi fishi dani..
Zama daddy yayi Yana kallan mashkur,,nan mashkur ya safke kashi qasa Yana sauraran daddy..

Mashkur ya akayi tayi wannan auren??

Ahankali mashkur ya bude baki Yana Magana,,daddy bantaba tinanin zanyi wani abu batare da saninkuba,,sedai Hakan yafaru bisa kaddara kuma wallahi bani na nema auren yarinyar ba,,sadaka aka bani..

What what Alhaji kanaji fa wai *yar sadaka* anyako Basu zautarmin da yaro ba?
Wallahi mummy karki yadda saiya saketa ta koma Inda ta fito,,tsawa daddy ya daka lateefah Hakan yasa tayi shiru tana muzurai,,Yaya ko kasa Magana yayi Yana nazari…

Mashkur ka tabbata maganar daka fada gaskiya ne,,eh daddy..

Idan har ka sake Na tambaya naji ba haka ba saina sabama,, dasauri mashkur yace eh Na yadda..


Shikenan yanzu ina yarinyar take,,daddy tana daki,,jeka kawomin ita..

Kambu,,ai wallahi bazata taba sabuwa ba,,wai Alhaji me kake nufi shikenan auren ya dauru” 
Kiyi hakuri haka Allah ya qaddara maganar lateefah kuma ba abin damuwa bane,,nizan yiwa iyayenta Magana Sai suma suyi hakuri adaura auren kinga yanzu 2 month ya rage ayi biki..

To ai shikenan amma ku sani daga kai har Dan naka,,wallahi sedai yazabi daya ko nijlah ko Yasmeen..
Mashkur dake zuwa falon nijlah Na biye dashi yaji abinda mummy ke fada nan yaji wani irin tashin hankali,,be iya jiran nijlah ba ya qarasa da sauri ya zube gaban mummy..

Mummy Dan Allah karkice zaki rabani da Yasmeen mummy badan bana santa nayi auren nan ba,,daddy kayi Magana”turesa mummy tayi tana daga murya tace..
Nasan bakinku daya to wallahi bazan taba karbar wannan auren ba,,ka rasa Wanda zaka auro Sai yar matsiyata kuma yar fulani..
Ran daddy bace Shima yace,,amma ko kinji kunya,,kuma ina nan ina jiran yadda zakiyi damu nida Dan nawa,, mashkur ka dauki matarka kuje,,ni Zan baka gida azauna..

Tsiru nijlah tayi tana binsu da ido taji daddy yace,,nace ka kawomin matar taka naji shiru..

Kafin mashkur yayi Magana nijlah ta washe baki tace baba gani’ kallan Nijlah daddy yayi kafin ya maida kallansa ga mashkur…….







*Momn sultan ce*✍✍✍

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button