NOVELSUncategorized

YAR SADAKA 21&22

???????? *’YAR SADAKA..*????????


*STORY & WRITING BY…*
         *BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO…..*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO…*
*CLASSIC FEEDOR*
*Ayi hakuri da rashin Jina Akan lokaci,,tare da rashin amsa comments naku,,haqiqa Naga comments Iya comments nakuma karanta,,Hakan ya nuna labarin Yana muku Dadi,,sedai Ina me gayama fans Na ‘yar sadaka 2&3 daku gyara comments naku Idan ba haka ba…….. nagode sosai da kaunarku gareni….????????*
2⃣1⃣&2⃣2⃣Bakinsa na rawa yace,, mashkur kana nufin wannan jaririyar ka aura???
Sosa kai mashkur yayi Yana kallan Nijlah da haushinta ya gama cikashi yace,,eh daddy itane dan Allah ka….
Ya isa mashkur Ashe dai bakada hankali nida nakeso kayi aure nima Na samu jika,,saika Tashi ka auro wannan yarinyar dako kanta bata gama sani ba,,dariya mummy tayi tana tafa hannu tace…
Au kuma,,kai da kanka zaka gayi haka??
Tini zuciyar mashkur ta gama tsinkewa bamda halbawa Babu abinda take lokaci huda yaji hawaye na neman zubomasa amma saiya riqesu Yana kallan daddy yace ,,
daddy Dan Allah kada kace ah ah,,daddy ka temaka mu inganta rayuwar nijlah,,wallahi bata da kowa..

Kai dallah rufemana baki,,kabari kawai daddy ya yanke hukunci aini nasan indai yaga wannan aljanar yarinyar dole yadawo bayanmu..

Kallan lateefah nijlah tayi tana turo baki,,doke Mata baki lateefah tayi tana cewa to mayya nidai kada ki cinyeni..
Dasauri mummy tace karki qara hada jiki da wannan yarinya kai kuma ka dauketa daga nan inasan Magana da mijina”

Mummy kawai kiyi magananki wannan tatsitsiyar meta sani cewan Yaya Yana hararan mashkur..
Hawayen da mashkur ke dannewa sune suka Sami damar zubomasa,,kallan daddy yayi da ranshi ke bace yace..

Shikenan madogaran Dana jingina da ita,,ta Rushe,,wayyo Allah ni mashkur,, daddy ina kaunar dakuke ikirarin kuna yimin,,kunyi alqawarin San abinda nakeso daddy kaida kanka kakemin maganan tausayi da taimako gashi yanzu nayi kunjuyamin baya..

Tabe baki mummy tayi tana cewa,,haqiqa duk cikin yarana Babu Wanda nakejinshi a Raina sama dakai mashkur tafada tana nunashi,,bawai Dan bana sansu ba kona fi sanka akansu,,ah ah ba haka bane,,kawai dai inajinka fiye da kowannensu..
Kai shaidane amma duk da haka ka rufe ido kayimin abinda nafi tsana da qi arayuwana,,kodan kana ganin yanda nake shagwabaka har banasan bacin ranka,,toka sani akan wannan aljanar yarinyar nijlah take kowa,,Zan iya batawa dakai har zuwa lokacin dazaka mayar musu da tsiyarsu..
Qasa mashkur ya safke kai Yana goge hawaye nijlah ko haryanzu bata iya cewa komai ba ahankali ta rarrafa ta qaraso kusa da mashkur,,hannu biyu tasa tana goge masa hawaye..

Kado kayi hakuri kazo muje can garinmu kaga kaka da Malam Basa yima fada irin hak..Bata rufe baki ba..

Yaya yasa qafa yayi cilli da ita nan ta zube jikin kujera tare da riqe bayanta ta saki wani marayan kuka..

Kasa dagowa mashkur yayi yanajin ze iya daukan komai Banda dukan nijlah,,sedai a yanzu bashida yadda zeyi haka ya kallo ya barta ta cigaba da kukanta Badan bayajin zafin kukan nata ba sedan ba yadda zeyi..


Kai babban Yaya Ashe baka da hankali,,matar kanin naka kayiwa haka,,Ashe bazaka iya hada zumunchinku anan gaba ba,,kana babba kana zubda girmanka,,to wallahi ku bude kunnanku da kyau kujini..

Ni din nan bana jayayya da lamarin ubangiji duk abinda tafaru Dani murna nake ina godewa Allah,,se yanzu danya ba Dana kyauta mafi muhimmamci da qima Zan qi gode masa,,Toni ba haka nakeba,, Abu guda yasa kukaga nayi shiru harna kasa magana..

Shine ganin yarinyar Karama da ita,, mashkur ta Yaya zaka iya zaman aure da wannan???

Dasauri mashkur ya dago Yana kallan daddy,,yace daddy Zan iya,,, goyan bayanku kawai nake buqata..

Kaji ko Alhaji shiyasa nake gayama yaran nan bashida lafiya Dan Allah mukaishi hospital aduba lafiyarshi,,yaro shekara 34 amma baya San aure mummy tafada tana kallan Daddy..

Mummy lafiya na qalau,,namiki alqawarin auren yarinyar da kikeso,,mummy kinsani nima inasan Yasmeen sedai ina tsoran halinta Na kyamar talaka,,nikuma gashi Allah ya hadani dasu.


Hadiye kukan nijlah tayi tana kallan mashkur daga inda take tace kambu kana sontafa kace” ara ta kaddani bamemin kishiya daga zuwana,, tana gama fada ta cigaba da kukanta ..

Ba mashkur ba ita kanta mummy saida tayi mamakin nijlah..
Ke Dan ubanki harkinsan  wani Abu wai Kishi,,turo baki nijlah tayi tace,,
Aidai malaminmu yace ba kyau zagi kuma duk Wanda ya zagi wani kan….ke rufemana baki bakida kunya,, wannan fa mahaifiyatace mashkur ya fada,, idan tana Magana kiriqa yin shiru,,Ko bakiga yadda nake ba???

Ahankali nijlah tace nagani.

Ah ah ka Barta ta nuna mana halinta kafin ka fice a gidan,kinci sa’a mummy ta hanani tabaki da yanzu kingane dawa kike shegiya ‘yar sadaka..

Runtse ido mashkur yayi kafin ya bude a hankali yace haba aunty lateefah,,zaro ido lateefah tayi tana kallan mummy..

Barshi lateefah,ki barshi ta gama zagina tinda Shima ya nuna ta fini daraja agurinsa..

Mummy ba haka bane kiyi hakuri,,

Daddy ne yace,kaga mashkur Tashi kaje daki da ita anjima zanyi Magana dakai..
Har mashkur ya Tashi yaji daddy Na cewa..
Taci abinci kuwa??

Badai a gidana ba,, wallahi ko ruwa bazata shaba..
Girgiza kai daddy yayi yana kallan mashkur..

Kafin yace,, Mashkur zaka iya zama da matarka a saban gidana.
Kanshi a  qasa yace eh daddy..

Daddy be qara Magana ba ya shiga dakinsa,, cikin minti biyu ya fito da key a hannunsa,, mashkur ya miqawa Yana murmushi..

Hannun mashkur Na karkarwa ya amsa,,daddy nagode,,karka damu Dana duk abinda kake buqata ka sanar Dani,,harya fara tafiya ya juyo yace..
Ka kula da yarinyar mutane..


To yace a hankali Yana kallan mummy data hade fuska tana tinanin abinyi.

Tashi yayi hannunsa Na karkarwa ya kama hannun nijlah ya miqar suka fara tafiya..

Karka sake bakina ya furta kalma mara Dadi akanka,,bazan zuba ido ka tare da wannan yarinyar ba,,tsayawa mashkur yayi yana sauraran mummy yaji daddy yace..
Kaje abinka Nina baka umarni.

Daddy na gama fada ya fito a falon,,Mota ya dauka zuciyansa na quna ya tafi gurin mahaifin Yasmeen..


Tinda Yasmeen ta fito take sharara gudu a titi tana driving tana kuka akaha harta kai gida,,a fAlo ta Sami mama sedai bata Biya ta kantaba ta shiga dakinta da gudu hannunta aka,,
Kan gadonta ta fada tana kuka tare dajin mahaukacin Kishin mashkur Na taso Mata..

Wacece wannan taji ana Magana da Wanda takesa ran yazama mijinta nan da wata biyu kachal,,idan ko San mashkur take tabbas itace ajalin ta.

Tana cikin tinani taji mama Na Magana akanta,,ke Yasmeen lafiya kika dawo Kina kuka badai wani abu ya samu mashkur ba..
Da gudu Yasmeen ta Tashi ta fada jikin mama tana cewa mama,,

Watace watace,,kimin magana kin zauna Sai Kiran wata kike,,kodai mutuwa yayi,, girgiza kai Yasmeen tayi tana cigaba da kuka,,to kodai cewa yayi yafasa aurenki????


Comments &share

Momn sultan ce

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button