NOVELSUncategorized

YAR SADAKA 23&24

???????? *’YAR SADAKA..*????????


*STORY & WRITING BY…*
         *BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO…..*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO…*
*HANNATU GALADIMA…**Dan Allah aqara yawan pages,Dan Allah aqara yawan pages,,,Kalmar da mutane dayawa Ke ambato batare da sun tambaya abinda Ke hanani typing dayawa ba,,kusani Nida kaina Ina ganin qoqarina,,Duba da ayyukan dake gabana Amma natsaya Ina farantamuku Rai Duk Dan kuji Dadi..*
*Dan Allah masu kirana a waya kusan irin abinda zaku gayamin Ko tambayana,,niba Matan aure nake fadakarwaba,,sedai Ina rubuta labari Wanda Zaki dauki darasin Zaman takewar aure da al’umma tare da gyara kuskuren da muke aikatawa,,masu min chogen Kira Dan Allah kudena kibari saikin cika waya da kudi kafin ki Kirani,,momn sultan data kawai take ajiyewa a waya Bana ajiye kudin kiranku,, nagode*2⃣3⃣&2⃣4⃣


Cikin kuka Yasmeen ta Bude baki da kyar tana Magana”
Mama mashkur ne ya kawo wata gidansu Sai kuka ya qara zuwa Mata takasa qarasa,,nan da nan hankalin mummy yaqara Tashi,,jikinta ta janyo Yasmeen tana gogemata hawaye..
Kinga Yasmeen kibude baki kigayamin abinda Ke faruwa kafin abbanki dayawo ya safkemin kwandan masifa akaina..
Mekika ji a gidan Basu?Ko Wani ya gayamiki Magana mara Dadi??
Mama ba haka bane,,tinda naje gidan Naga hankalinsu a tashe musamman ma Shi mashkur,,mama Seda daddynsu ya dawo mummy tace Wai kirana tayi koni zefi gayamin gaskiyar Magana,,Sai kuma tayi Shiru takasa qarasawa Jin Wani qatan Abu ya maqale Mata a maqogoto..
Gaskiyar Magana akan me??mama ta tambaya tana kallan yadda Yasmeen Ke qoqarin hadiye saliva yaqi tafiya sabida tsabar kishi..

Dasauri mama ta Bude fridge ta dauko Goran ruwa tafara ba Yasmeen,,Dan kadan Tasha sabida dacin dataji yayi Mata a baki ta kauda kai Ranta a bace..

Inajinki Yasmeen cigaba da Magana,,gaskiyar Magana Akan wa???
Mama Wai Akan aljanar yarinya,,Sai kuma ta fashe da kuka tana cewa,, wallahi mama banasan kowa ya kusanci mashkur menene hadinsa da wata Har mummy takesan yafadi gaskiya,,mummy Ina tsoran kada wata tace tana sanshi Dan wallahi Bazan Iya Bude Ido Naga mashkur da wata mace a matsayin budurwa  ba…
Ajiyar zuciya mama ta safke tana kallan yadda Yasmeen ta birkice Mata tana sumnatu,, girgiza kai tayi tana mamakin irin wannan mahaukacin Kishi da Yasmeen take Akan mashkur Duk da itama tasan soyayyar dake tsakaninsu,,Amma be kamata ta riqa irin wannan Kishin ba,,Dan kuwa namiji mijin mace hudu ne..
Gyara Zama tayi ta janye Yasmeen a jikinta tare da gyara Mata Zama ta yadda zasu fuskanci juna,, muryar mama a shaqe tace”
Yasmeen,, Yasmeen Bata Iya amsawa ba Saima safke Kanta qasa datayi sabida yadda yake saramata,,cigaba da Magana mama tayi tana shafa Kanta..

Yasmeen kefa ‘ya mace ne,,bekamata kina Abu irin na jahilan Mata ba,,Ko haka kikaga inayi agidanan,,kasa Magana Yasmeen tayi Saima turo Dan qaramin bakinta gaba tayi ..

Nan mama tacigaba da magana saunawa kike ganin manyan Mata Suna zuwa gidannan mahaifinsu Yana Duba lafiyarsu?
Shiru tayi mama ta daka Mata tsawa,,waiba dake nake Magana ba,,bakinta Na rawa tace,,
Ba adadi,, to Amma Ke Daga Jin an ambaci Sunan yarinya Sai dagawa kanki hankali Nima ki nemi dagamin.

To wallahi ki Maida hankalinki kafin….mama Bata Iya qarasa maganan ba ganin yadda Abba ya shigo ranshi a mugun bace,,Jin yadda mama tayi Shiru takasa qarasa Magana yasa Yasmeen tayi saurin dago Kanta a hankali ganin Abba yasata Tashi a guje ta fada jikinsa tana kuka tare da makerketa..
Hannu biyu Abba yasa ya rungumeta Yana shafa bayanta,,

Wayyo Allah abba,,Abba mashkur ne” bakin Abba a Bude yace au kema ya gayamiki Kenan..
Dago kai Yasmeen tayi kafin tayi Magana mama tace..

Sannu da zuwa abban Yasmeen,,yakamata ta zauna ka huta kafin tafara yima shirmen nata..
Ba shirme Yasmeen tayi ba,,tabbas abinda ta gayamiki gaskiya ne Domin ko mashkur ya daura aure da wata jinjiran yarinya Kamar yadda mahaifinsa yake gayamin yanzu shiyasa Na Tashi a office,,Ko bakiga lokacin tashina Beb…kasa qarasawa Abba yayi ganin Yasmeen Na neman zubewa a qasa,,numfashinta na barazanar daukewa..

Kafin yayi Wani Abu harta zube qasa summama,,salati mama tasa tayi kansu da gudu tana kwala Abu me aiki Kira,,Abu kawomin ruwa,,kafin Abu tazo Har Abba yayi Kanta yana Bata taimakon gaggawa a matsayinsa na babban likita me fada Aji a wannan qasar..
Baki yasa cikin hancinta Yana hura Mata iska,,Seda ya Dade Yana Bata oxygen kafin Yasmeen ta amsa,,da kuka ta farka tana kallan Abba tace…

Abba dagaske mashkur yaci amanata ya yaudareni,,Abba bantaba ganin baqar Rana irin Yau ba,,Abba wacce shegiyar yarinyace tayimin shigar sauri? Yar uwan waye a fadin duniyar nan?
Shiru Abba yayi Dan yasan Yasmeen zatayi fiya da haka indai Akan mashkur ne..

Abba kayi Shiru Baka gayamin ba,,wallahi Abba sainayi maganinta Saina zame Mata dakalin majina,,Saina sa mashkur ya zame Mata hawainiya ta yadda zata kasa gane kanshi da gindinshi Abba Saina….
Dakata Yasmeen Wai Kishi haukane Zaki Samu agaba kina wadannan maganganun Ko Kunya bakiji a matsayinki Na ‘ya mace Ko bakiga yawan Matan Duniya ba,,Idan akace kowanne namiji mace daya Ze aura Ai sauran sun Shiga uku,,Bama su kadai ba Harda iyayensu da ‘yan uwa koke bakiga sauran kanninki Mata b,,tsawar da daddy yayi ne yasa mama tayi saurin Hade bakinta tana kallanshi…

Dakata ummu Yasmeen Idan Ke baki damu da itaba Nina damu,,aure fa saurayin dazata aura yayi Amma Kika rufeta da fada saikace bakisan ciwan ‘ya mace ba,,kokin manta ance ciwan ‘ya mace Na ‘ya mace ne.

Ba haka bane abban Yasmeen Sai yaushe Zaka fara Gaya Yasmeen gaskiya,,yaushe Zaka fara nuna Mata bakomai kake nema kake Samu ba,,bafa abinda muke tsarawa kanmu muke riskaba,,face abinda Allah ya tsara mana..

To anji Malama yanzu Zaki fara wannan wa’azin naki Na banza da Wofi,,Idan kincika Ke malamace meyasa baki fara zuwa tashar arewa 24 kina fadakar da Mata ba…

Kuka Yasmeen tasa tana rirriqe Abba tace,,Abba Dan Allah kayi Wani Abu wallahi Bazan Iya Zama da kishiyaba,,Abba waye ubanta??

Murmushi Abba yayi Jin tambayarta ta qarshe yace,,kwantar da Hankalinki Yar albarka,,ubanta ba Wani bane mace me yawo a daji Yana bi Lungu da Sako Yana kiwan shanu da Saida nono a qarshe Mota ta malkadesu suka Mutu shida uwarta,,Sai kuma yayi dariya irin tasu ta manya kafin ya dawo da kallansa inda take kwance a qasa”yace kitashi inasan Magana dake..

Kasa Tashi tayi mama Ko Dan haushi Bata bi takantaba Duk da itama Taji haushin auren da mashkur yayi..
Abba Da kanshi ya Daga Yasmeen ya zaunar Kan kujera,,ruwa ya dauko me sanyi yabata Tasha..
Nan yacigaba da Magana,,’yar lele ki kwantar da Hankalinki wannan yarinya ba ‘yar kowa bace Yar matsiyatace Wanda suka kasa riqewa suka ba mashkur sadaka,,basuyi Duba da inda zasu kaitaba..

Shikenan sausu Rasa wazasu ba sadaka Sai mijina,,Abba Zan Mutu wallahi,,hannun Abba ta kama ta Dora a saitin zuciyarta tace,,Abba ka taba Kaji yadda zuciyana take bugawa kama zata fado Abba Kaine gatana ka temakeni ya saki wannan yarinya..
Kiyi hakuri ‘yar Lele Nina yanke hukuncin Hana mashkur aurenki,,kiyi hakuri nasan Zaki Samu Wanda ya fishi,,
Bakin Yasmeen Na rawa tace ah ah Abba Bazan Iya rayuwa ba mashkur ba,,Jinina da nasa dayane munzama hanta da jini,,Abba tayaya kake tinanin za’a raba hanta da jini Kuma su rayu???

Jikin abbane yayi sanyin ganin yadda Yasmeen ta kidime ta rikice ta gigice tana Magana kama wadda Tasha kwaya..
Sabuwar tsanar iyayen nijlah ne ta tsirga masa harya kasa Magana ya zuba Yasmeen Ido Yana mamakin yadda ta zurfafa a cikin soyayyarsa..

Abba kayi Shiru Abba ka taimaka ya saketa inyaso saimu Basu kudi ta Kula da rayuwarta Abba ka ceci rayuwana..

Surutai Yasmeen ta riqayi marasa Kan gado Hakan ba qaramin haushi Yaba mama ba,,sedai ta godewa Allah dayasa ba Kowa a falon Daga ita Sai Abba.

Abba ko ranshi inyayi dubu ya baci,,ganin yadda ‘yar Lele take sumbatu yasashi kama hannunta ya nufi dakinta da ita,,Duk Taku saiya Mata sannu Yana qara Bata hakuri…


*********

Dakyar ya Iya juyowa Yana Kallan mummy Sai kuma yasaki hannun nijlah ya tako Har zuwa gabanta ya durgusa Kan gwaiwoyinsa tare da Hade hannunsa biyu,,idanunsa na hawaye..

Dauke Kanta mummy tayi Dan bataso soyayyarsa ta tauye Mata nata haqqin Har Taji ta amince da tafiyansa Duk da yasani zuciyarta bazata taba Lamunta da Hakan ba…

Qara rarrafowa yayi cikin kaduwar zuciya da fargaba yafara magana”mummy Dan Allah kiyi Karki juyamin Baya,,mummy fishinki masifane a gareni,,mummy karkisa nafada cikin fishin mahaliccina,,mummy nijlah matatace Kuma amana,,Bata Dan gata balle Dangi a kusa,,mummy Koda Suna kusa Na tabbata Basu da abinyi,,Ke mahaifiyace..

Nijlah marainiyace shiyasa nakesan taimaka Mata,,Amma kiyi tunani Idan Har baki yaddaba nizan hakura da nawa farin cikin nayimiki biyayya a matsayinki na uwa..

Yana gama fada ya Tashi beko jira amsar mummy ba ya kama hannun nijlah dake rakube jikin Kofa tana hawaye,,sedai yakai jikin Kofa ya Dan risina yace..

Yaya,, aunty lateefah Saida safe,,Yana gama fada Yaja musu kofa..
Yana fita mummy tasa kuka tana cewa kungani ko,, mashkur ya tafi shikenan sun kangaranmin da yaro ya Shiga Wani Hali,,Ko rantsuwa nayi baza kaffaraba Akan surkullensu Na Fulani sukayiwa yarona..
Hakuri su lateefa suka riqaba mummy harta Dena kuka,,nan ta kwanta tana Nishi Sama Sama tare da tinanin abinyi..

Mummy Dan Allah kiyi hakuri Karki Bari hawan jini ya kama mana ke,,Idan Wani Abu ya sameki wallahi Saina tada hankalin kauyen kankan gaba dayansa cewar Yaya cikin tashin hankali…
Mummy abin yazo da sauqi tinda yabaki zabi,,mu Kuma zamuyi masa zami mafi dacewa dashi,hakane lateefah shiyasa nakeso mummy ta kwantar da hankalinta,,da dadan kalamai suka riqa bin mummy Har bacci ya dauketa Bata Sani ba..


Mota yasa nijlah Shima ya Bude ya Shiga,,tinda suka fara tafiya nijlah take kuka tana qara qanqame jikinta,,hannu biyu mashkur yasa ya janyota jikinta,,nan ya kwantar da Kanta bisa cinyanshi Yana shafa lallausan gashin kanta tare da tuqi da Dayan hannunsa,,Duk da yadda yamata Bata Dena kuka ba Saima qara sautin kukanta tayi tana Kiran kaka,, sosai yakejin kukanta Har cikin zuciyarsa Dan haka yayi qoqarin dakatar da ita,,
Kiyi hakuri kinji amaryar mashkur,,indai Ina tare dake Babu me qara tabamin Ke,,turo baki tayi tana kuka tace..

To to ba agabanka wannan mutumin yayi cilli Dani ba,,Kuma aka zageni hadda zagin Malam Duka bakayi Magana ba,,

Karyar da murya yayi kama Yana Magana da Babbar budurwa yace,,Kuma shine abin kuka,,Shiru tayi tana qoqarin janye Kanta yasa hannu ya riqe Kan Yana murmushi,, shikenan kiyi hakuri bazasu qaraba,,kema Daga yanzu Idan ana tambayan matata kidena cewa gani,,koke bakisan Kunya irin Na Fulani ba,,
Murmushi nijlah tayi Har tana boye fuskanta a cinyanshi tace,,Toba kai bane Idan ana tambaya Sai kayi Shiru bakasan Gaya,,Amma Idan ka Gaya Ai Dai Bazan ce gani Bako..

Dungurinta yayi yace oh bazaki Dena fadaba Kenan?
Daga masa kai tayi alamar eh,,zaro Ido mashkur yayi tare da kewa lalala Ashe Ko Zan hadaki da Karan gidana tinda bakijin magana..

Wayyo Allah kado nadena,,Bazan qaraba,,kin tabbata dasauri ta Daga masa kai idanta taf da hawaye..

Dungurinta yayi Yana cewa kedai kinji Kunya baki da aiki Saina kuka,haka suka riqa tafiya Yana tuqi Suna hira..

Karfe 5 Na yamma mashkur ya isa Saban gidan daddy Wanda ya sha gyara kama da mutane a ciki,,tinda suka fara Shiga nijlah Ke kukan yinwa Dan ita Bata kallan gidan takeba sabida yinwan dake damunta Dan ma Tasha ruwa a toilet din mashkur lokacin data Shiga yin fitsari..

Daya Daga cikin bedroom ya ajiyeta Yana kallanta,,amarya Zaki fara wanka kafin kici abinci..
Badan taso ba ta Daga masa kai,,nan ya fara Dube Dube abinda zata Shiga wanka dashi be gani ba,,dasauri ya fita ya Shiga Wani Dakin,, wardrobe ya Bude nan ya dauko Saban towel dinsa daya ajiye kwanakin Baya ya dawo Dakin da nijlah Ke zaune tana rarraba ido..

Tana ganinshi ta Tashi da gudu tazo bakin qofan tana cewa,,kado gaskiya ka Dade nan gaba tare zamuna fita Dan gaskiya tsoro nakeji..
To shikenan yanzu Dai amsa wannan ki daura muje ayi wanka..

Amsa tayi Sai kuma ta kasa cire kayan jikinta,,hannu yasa ya janyota jikinshi yafara rabata da kayan jikinta,, girgiza masa kai tayi tana cewa kado bafa kyau babba yaga jikin mutum..

Nasani kokin manta Ni mijinkine,,lah mantawa nayi Amma ka barshi nagode nizan cire dakaina,, murmushi yayi Yana cewa saikace ta Iya wankan Toni Bazan Bari kiyi jiqa jiqaba,,kizo kinamin doyi a Daki..

Dire diren qafa nijlah tafara tana kukan shagwaba,Ni Allah Bana doyi,,gwalo mashkur yayi Mata tare da kashe Mata Ido daya..
Binshi tayi da gudu tana San kamashi suka riqa zagaye katan falon..

Shi Yana dariya ita Kuma tana masa kukan shagwaba lolxx…Yawan comments yasa na muku typing Akan lokaci,,fatan zakuyi wanda yafi Na jiya..

*Comments & share*

*Momn sultan ce*✍✍✍

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button