NOVELSUncategorized

YAR SADAKA 27&28

???????? *’YAR SADAKA..*????????


*STORY & WRITING BY…*
         *BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO…..*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO…*
*MMN MAHMUD….*
2⃣7⃣&2⃣8⃣


Dakyar ya iya tashi ya zauna gefen bed,,zuciyarsa a tashe,,be iya magana ba sai Jin muryar Yasmeen yayi  cikin Kuka,,baby dole Ka kasa amsani,,sabida irin abinda Ka aikatamin,,nayi mamaki sedai ina fatan hakan yazamamin mafarki,,baby Dan Allah Kada Ka gaskatamin wannan bakin labarin dake Neman tarwatsamin zuciya,,kukane yaci karfinta Dan haka ta saki abunta tanayi ba kakkautawa..
Jin kukanta yake kama ana diga masa dalma a cikin zuciyarsa ganin bata da niyyar denawa yashiyin karfin hali ta hanyar hada dukkan nutsuwarsa tare da daidaita numfashinsa bakinsa na rawa yafara magana,,
Yasmeen Dan Allah kidena wannan kukan ki saurareni..

Baka da abinda zaka gayamin baby kawai kagayamin karyane abinda naji,,kasani natsani kishiya bazan iya hada soyayyarka da wata ba,,watan ma ‘yar sadaka,,kuka ta cigaba dayi shiko yayi zuru Yana sauraranta,,seda tayi kusan minti biyu kafin ta cigaba da magana..

Baby kayi Shiru,, Dan Allah kace karyane,,wallahi Zan mutu Ka tausayama rayuwana,,baby kasan Yadda nakeji akanka,,Ka sani ko kawata banyadda ta gaisa da kai ba muddin akace da haske a gurin balle har na Bari aganka da Rana,, sai gashi duk Yadda nake tattalinka Saida Ka daukomin abinda ze zama ajalina..

Sai yanzu mashkur ya iya bude baki a hankali yace” akul dinki Yasmeen Kada naqarajin irin wannan maganar,,tsakanin keda nijlah babu Wanda zeyi ajalin wani,,fatana Ku zauna lafiy.. …

Yasmeen bata Bari ya qarasa magana ba tace,,
Kai dalla rufemin Baki,,mugu azzalimi,,Wanda besan darajar soyayya ba,,Ashe zaka iya bude baki ka gayamin irin wannan maganar,,nayi mamaki sedai hakan dakayi ya nunamin Kai cikakken mayaudarine,,kuma maci amana..

Yasmeen kiyi hakuri ki fuskanci magana ta,,banayi Danna qona ranki kodan kiyayya ba,,wallahi,,

Dasauri ta katseshi wallahi me,,nidai kawai Ka cuceni Amma bakomai nasan abinda zanyi,,

Pls Yasmeen karkice haka,,yanzune Zan gane irin soyayyar da kikemin,,kiji tausayina karki Bari tashin hankali yayimin illah,,wallahi har yanzu inasanki babu abinda ya chanza a soyayyar ki,, haryanzu kina cikin zuciya tah..

Kukan da Yasmeen take ba bata damar Jin abinda mashkur yake cewa ba,, tari ta Shiga yi tana cewa nidai Ka yaudareni kodan kasan bazan iya rabuwa da Kai ba,,shiyasa kakemin irin wannan,,ba haka bane Yasmeen Dan Allah kidawo cikin hayyacinki,,nizan zo har gida
 muyi magana.. 
Ba wani magana da zamuyi,,sai yanzu na gane abinda yasa kaketa daga maganar aurenmu Ashe ‘yar matsiyata masu yawo a jeje kake Neman daukomana…

Dafe Kai yayi ya kuma kasa magana,,Banda faduwar gaba babu abinda yake,,dakyar ya iya magana Yana cewa,, shikenan kema ki dagamin hankali kamar Yadda mummy tayi ni Dama nasan,,kasan me baby..

Shiru yayi Yana sauraranta batare da yayi magana ba,,haka Yasmeen ta zage ta riqa zazzaga masa masifa tanayi tana kuka,,be iya amsataba Saima hakuri ya riqa bata yanasan kwantar Mata da hankali danshi bega laifintaba,,yasan anyimata abinda zatayi fiye da hakan..

Tana magana masifa ta katse Kiran tana cewa kuma wallahi karka sake qafarka ta sake takowa gidanmu,,kabari idan na mutu saikazo gaisuwa kaida ‘yar sadaka..


Tinda Yasmeen ta kashe wayan mashkur yakasa zaune ya kasa tsaye Banda zagaye dakin babu abinda yake,,babu abinda yafi daga masa hankali illah magananta na qarshe,,Kada Ka sake qafanka ya sake taka qofar gidanmu,, dafe kansa yayi Yana cewa tome Yasmeen take nufi,,ina wallahi baze yiwu ba,,dake nasaba sai yanzu sabida qaddara ta samemu zaki gujeni,, wannan wanne irin masifane,,hannu ya daga Sama Yana addua,,ya Allah Ka kawomin dauki,,yafada idansa taf da hawaye…

A hankali nijlah tafara bude idanta harta budesu gaba daya ta safke Kan mashkur dake saune kama mutum mutumi,,kallan idansa tayi taga Yadda hawaye ke rige rigen zuba,,dasauri tasa hannu tana goge masa,,tare da girgiza masa Kai..

Kayi hakuri Dan birni,,babba da hakuri aka sanshi,, murmushi yayi tare da goge hawayen yace,,ba kuka nayi ba,,harkin tashi a baccin??
Hannu nijlah tasa ta gogo hawayen tana Wasa dashi a hannunta,,Dan birni wannan menene,,bazan hanaka kukaba Dan Naga wannan qatuwar matar Zata iya zaneka,,duba da Yadda take zaremana Ido,,nasan itane tazo ta dakeka ko???

Bata fuska yayi ransa a bace yake kallanta,,Baya tafaraja tana bashi hakuri,

Zonan yafada fuskanshi da muryanshi babu alamar Wasa yace” Bana gayamiki mummy itace mahaifiyataba,,amma shine kike maimaita abinda na hanaki??
Dan Allah kayi hakuri wallahi na manta kuma ni bazan iya fadar sunan ba,,sedai idan Ka Yadda Zan riqa cemata baba,..

Banyadda da wannan sunan ba ki Fadi Yadda kowa yake kiranta dashi idan ba hakaba Saina zaneki,,tinda baki da kunya..

Turo Baki tayi tana cewa to,,shiko yagama kulewa Dan haka yasa hannu biyu ya fizgota ta fada faffadan qirjinsa,,niyyan hukuntata yayi Amma Jin kukanta yasashi rungumeta Yana rarrashinta..

Ya ISA haka kiyi Shiru Amma karki qara ina miki fada kina turomin Baki,,Shiru tayi tana cigaba da kukanta,,au bazakice toba Saina kaiki gurin Wancan Karan..

Dasauri nijlah tace to tana qara shigewa jikinsa,,wani Iri mashkur ya riqa ji ganin haka yasashi janyeta,,hannu yasa ya dauko ledar kayan daya siyo..

Riga da wando ya dauke green and orange ya ciresu a Leda Yana kallanta,,safke Kai qasa nijlah tayi tanajin ba dadi a zuciyarta,,gani take kama ita ta sashi cikin damuwan dayake ciki..

Zokisa wannan yafada Yana miqa Mata hannu,,ba musu ta tashi ta qarasa inda yake,,beyi magana ba yasa hannu yafara janye towel din dake jikinta,,tinda yafara janyeshi hankalinsa yafara tashi,,lokaci guda yafara hade cinyoyinsa tare da matse joystick dinsa..

Be Ida rikidewa ba Seda yagama zareshi gaba daya,,qugunta ya riqa kallo Yana hadiye yawu,,besan lokacin dayasa hannu  Yana shafawa ba,,Sai ji yayi nijlah ta riqe hannunsa tana cewa,,kado kaga rigan sakamin nakasa Sawa..

Kunyace ta kamashi sedai ganin yarinyar Bata gane ba,,yayi hamdala yasa hannu ya dauko wandan rigar,,muryarsa a sarqe yace,,Daga qafa kisa wandan,,dire diren qafa tafara tana cewa Ai Dai Riga Ake sawa kafin Wando Kuma Ni wannan kayan sun matseni,,Nika daukomin nawa..

Hararanta yayi yace,,Wai ba yanzu nayi Miki Magana Akan yimin musu ba,,kifa Shiga Hankalinki,,hannu tasa ta rufe baki tana bashi hakuri,,ba hakuri Zaki Bani ba,,kidena abinda banaso,,to tace tana hawaye..

Ahankali yafara Samata wandan sedai Jin ruwa a bayansa yashi dagowa Yana kallanta,,hawaye yagani kwance Akan fuskanta nan ya zuba Mata Ido Yana mamakin shagwaba irin ta nijlah..

Be kulatana ba ya fara sakamata wandan Yana tinanin ta yadda Ze saita ta tadena yimasa kukan banza…

Bayan yasa Mata wandan ya tayata suka sa rigar Yana qara Janta a jiki ganin yadda jikinta yayi sanyi,,Duk Wani rawan kai ta dena..

Kallanta yayi yaga tazama Abar tausai Dan haka yakama hannunta suka fito falo,,kallo ya kunna Mata Yana cewa zokiyi kallo kafin naje masallaci,,yanzu Zan dawo kinga saimu kwanta kema ki huta,,to tace tana kallan tv..


Tinda mashkur ya tafi masallaci be dawo ba Sai karfe 8:30,, wannan Karan nijlah bataji tsoro ba sabida TV ya dauke Mata hankali,,

Yana shigowa ta tashi da gudu tayi kansa tana cewa sannu da zuwa angon nijlah,,ah cewan mashkur Yana riqe baki,,hannu biyu tasa tana rufe Ido,,shiko dariya yayi Yana shafa Kanta a haka Har suka qarasa Kan kujera,,Bayan sun zauna ya Bude takeaway Har guda uku,, gashinan ki zaba biyu naki daya nawa,,nasan Dai wannan Ze isheki,,Daga masa kai tayi..

To zauna kichi,,indai kina abinda ya dace tozan cigaba da shagwabaki Har saikin manta wacece Ke ada,,bangane ba,,Dama mutum Yana manta kanshi,,Sai kuma ta ture abincin tana cewa Nina fasa CI,,tinda Dai mutuwa akeyi,,keni banasan shashanci wakikaji yace Zaki Mutu..
Hawaye tafara tana cewa Toba kai kace Zan manta kaina ba,,Naga Dai Sai mutum ya Mutu yake manta kanshi..

Toba haka nake nufi ba,,Zaki gane watarana,,to tace tana Zama tare da daukan takeaway guda tace,, wannan ya isa banajin yinwa,,dariya yayi Yana kallanta kafin yace Ai baki isaba saikin cinyeshi Duka,,dazu Dana siyo guda biyu Ai hanani chi kikayi..

Murmushi tayi tana cewa to kayi hakuri gobe Saina cinye Ko,,Daga Mata kai yayi yafara Cin abinci Dan zuwa yanzu yinwa hartaci ta cinyeshi..

Cokali biyu ya Iya kaiwa bakinsa,, tinanin mummy ya dawo masa tare da masoyiyarsa Yasmeen,,ture abincin yayi ya dauka waya ya Kiran mummy,,tayi ringing sosai mummy taqi amsa Kiran haka harya gaji ya rubuta Mata text message ya Tura..

Daddy ya Kira suka gaisa nan yafara magana cikin muryar tausai yace,,Dan Allah daddy ka tayani ba mummy hakuri,,wallahi Bada niyya nayi wannan auren ba,,ya isa haka mashkur,,kabari zanyi Magana da ita nasan zata safko,, Daga haka sukacigaba da hira,, nijlah Ko Bata su take ba tana Cin abincinta..

Bayan ta gama ya kalleta Yana murmushi yace,, kinyi Sallah Dana fita,,eh tace tana Maida masa da murmushi,,yauwa Yar albarka haka nakeso ki riqa Sallah Akan lokaci,,sedai inaso kiyimin addu’a a Duk lokacin data kikayi Sallah,,
To mezan roqa ma,,Naga kai kasamu komai Baka da Wani matsala,, murmushi yayi Dan ganin yadda nijlah keda wayo komai nata Na masu hankali take indai ba shagwabanta ya Tashi ba,..

Kawo kunnanki Zan gayamiki abinda Zaki roqamin,,to tace tana Tura masa kunnan a saitin bakinsa,,magana ya gayamata tayi saurin qocewa tana yimasa gwalo..

Ta tafi Daki da gudu,,binta yayi suka kwanta,,nan ya janyota jikinsa Yana shinshinata ahaka barci ya daukesu..

Cikin dare yajishi kwance cikin ruwa,,ga Wani irin wari Na Tashi,,hannu yasa ya shafa gurin tare da kai hannunsa Kan hancinsa,,tsamin Kashi yaji yayi saurin Bude idansa Yana cewa badai kashi nijlah tayi ba…

Nijlah Ko baccinta take Hankali kwance,,a hankali yasa hannu ya kunna fitila,,Yana ……


Comments & share

*Momn sultan ce*✍✍✍

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button