NOVELSUncategorized

YAR SADAKA 31&32

???????? *’YAR SADAKA..*????????


*STORY & WRITING BY…*
         *BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO…..*
*MMN AMATULLAH**SPECIAL GIFT TO…*
*ALAWIYYA….*3⃣1⃣&3⃣2⃣

Bacci mummy ta maimaita tare da janye wayan daga kunnanta tana duba number data Kira”
Number mashkur ta gani nan ta qara mutsika idanta tanasan tabbatarwa,,shidinne ba wani ba..
Ranta a mugun bace tace,wacce shegiya ke magana?

Murmushi nijlah tayi tana qara bude Zara Zaran idanta tace,,Kai amma dai wannan anyi babbar banza,,da girmanki kina zagi sai kace wadda ta Kira wayar danta ko mijinta..

Kasa magana mummy tayi,,Banda kallan number mashkur babu abinda take tana jinjiga Kai,,mamakinta be qareba sai da taji muryan nijlah na cewa,,,
Nidai na gayamiki wannan number mijina ne,,karki qara Kira tinda ke…..
Wani uban zaki mummy ta saki tana tashi tsaye,,bakinta na rawa tace,, nijlah Dama kece???

Murmushi nijlah tayi jin me maganan ta santa,,Dan haka takasa  qasara abinda takesan gaya…

Nijlah ni kike zagi,,Dan ubanki,,hannu nijlah ta dora a kasa tana cewa,, Allah ba zaginki nayi ba,,dan Allah Baba kiyi hakuri kwaran kwatsa dubu bansan kece ba…

Kuka mummy tasa tana cewa shikenan auta Ka daukomin masifa,,wallahi karatunka be amfanamin komai ba sai tashin hankali,kukane yaci karfinta Dan haka ta katse kiran..
Daddy ne ya shigo dakin Jin kukan mummy ya tsaya a kanta Yana sauraranta”
Beyi magana ba Saida yaji ta tsaya da kukanta kafin yasamu guri kusa da ita ya zauna Yana fuskantarta,,cikin kuka mummy tace..
Kagani ko alhaji,,zuba Mata Ido yayi yanasan Jin abinda ke faruwa..
Kuka mummy ta qara saki tana cewa,,yanzu wannan yarinyar me sunan aljanu ta dauka wayana tagama zagina ta uwa ta uba,,har tana cewa wai nayi girman banza..

Bakin daddy na rawa yake tambaya,,wacce yarinyace wannan kuma meya hadaki da ita???
Kaima kasani ba Wanda ze iya cimin mutumchi irin wannan yarinyace da mashkur ya dauko..

Ran daddy bace yace,,Dama ita nijlah har waya gareta” 
Mashkur fa nakira yanzu shine ta dauka take zagina..

Shikenan kiyi hakuri ninasan batasan Wanda ta Kira ba,,Amma zanyi Mata magana,,wallahi baze zauna da ita ba Kaji harna rantse,,sedai ya zaba koni Ko ita,mummy ta qare maganan tana huci..

Gyara Zama daddy yayi Yana Kallan mummy kafin ya Bude baki a hankali yafara magana”

Se yaushe Zan gayamiki ba saki tsakanin mashkur da nijlah,,kokin manta Akan wannan Yar maganar kusan kwana mukayi dake muyinta..

Koma Dai menene Nina haifi yarona Dan haka Dole yabi umarnina eheeee..

Fuskar daddy dauke da murmushi yace,,Nima bance Wani ya Haifa Miki Shiba,,sedai Kamar yadda Allah ya Dora Miki haqqi akansa haka yanzu ya Dora haqqi matarsa akansa,,

Cike da masifa mummy tayi Kan daddy,,karka qara cewa nijlah matarsace Dan ni banyiwa yarona aure ba..

Haba hajiya karki nemi ki maida kanki jahila,,nasan kinsan auren mashkur da nijlah ya dauru sabida a gabanki Na Kira Nasir mukayi Magana Se yanzu Zaki tsiro da wannan maganar.

Eh Koma Dai menene sakinta zeyi..

Shiya gayamiki Baya santa?

Oho Dai nidai Na gayama,,yarinyar da ta gama zageni kana nufin da ita Dana Ze zauna..

Kinga hajiya ki dawo cikin Hankalinki,,ninasan nijlah bazata Iya kallanki ta zagaba,,nasani koba komai tana da tarbiyya da sanin darajar Dan adam duba da ganin inda ta fito…

Dan haka nake Han hankalinki daki zubda makaman yaqinki indai kinaso girmanki ya dore a idan wannan yarinya…

Tabe Baki mummy tayi Dan ita batasan abinda Zata fada ba sai dai zuwa yanzu jikinta yagama yin sanyi ganin Yadda daddy da mashkur suka dauka yarinyar..

Har daddy yakai kofa yaji muryar mummy na cewa,,toya maganar ita yasmeen,,ko shikenan tinda yasamu yar fulani,,koba komai kema Dan Fulani kike aure kinga Ko ba laifi bane Dan danki ya auri ‘yar Fulani..
Maganar Yasmeen,,naje munyi Magana da mahaifinta Na Kuma gayamasa abinda Ke faruwa,,yanzu shawara ta rage naso Idan zata aureshi to,,Idan Kuma sun fasa shikenan Sai muyi fata Allah yabata Wani..
Daddy Na gama fada ya fita ya bar mummy tana zazzaga masifa,,a falo ya hadu da aunty lateefah nan ya nuna ta da yatsa..

Ke Kuma inaso gobe goben nan ki tattara ki Koma gurin mijinki,,Idan ba haka ba Saina Saba Miki,, shashancin banza kawai,,Daga ku Har uwar Taku an Rasa me hankali…

Kan aunty lateefah Na qasa Har fa daddy yagama fada ya fita,,Yana fita ta shiga Dakin mummy da gudu..

Kusa da mummy ta zauna tana rarrashinta,,mummy kiyi hakuri Ni inaga kawai kice su dawo gidannan da Zama,,inyaso saiki kwace nijlah,,shikuma ya tafi da yasmeen..
Lateefah nifa banasan yarinyar nan,,wallahi Na tsani fulani,,daddynkuma Danya zamamin Dole shiyasa nake zaune dashi..

Mummy Duk da haka Ke Zaki sauko Danni banga alamun zasu rabu da wannan mayyar ba,,Aiko Dole ya rabu da ita indai Nina tsugunna Na haifeshi..

Hakane mummy Amma Baki ganin yadda daddy yayi ruwa yayi tsaki a cikin lamarin nan,,nidai ina tsoran abinda zeje ya dawo,,yanzu ma bakiga yadda yayimin ba,yace gobe na tattara kayana na koma gidana..
Mummy na huci tace au haka yace,,to wallahi babu inda zakije sai an gama da matsalana.
Mummy nidai gaskiya tsoran daddy nakeji,,kibari kawai mayi a waya..

Ba haka mummy taso ba sedan batasan laifin yaranta Dan haka tace to shikenan yanzu ki Kira auta yazo ayi magana kawai..

Mummy keya kamata ki kirashi ko bakiga yadda yakemin magana kamar wata sa’arshiba,,kodan yana ganin Shima yanzu ya girma harda aure..

Hmmm lateefah kenan,,wannan har a kirashi da aure sedai ko muce wasan yara,,Kinga ni kawai ki kirashi Dan wallahi idan na Kira wannan aljanar ta dauka saina kusa kasheta a gidannan..

Waya lateefah ta dauka ta Kira layin mashkur..

Nijlah dake zaune agurin tana zubda hawaye tare da tinanin matakin da mashkur ze dauka akanta idan yaji ta amsa masa waya har tayi magana mara dadi taji waya na ringing a hannunta..

Kuka ta qara saki tana cewa,,dan Allah kiyi hakuri wallahi bansan banbane ya kiraba,nayi tinanin yarinyane Irina,,kuma ai ke kika fara zagina,,da gudu nijlah tafara zagaye dakin tana kuka tare da wayar mashkur a hannnunta Sai ringing take..

Mashkur besan abinda akeba sabida baccin dake idanta,,ga bayansa Sai ciwo yake,,Dan tinda yake be taba aikin wankin kashi ko wani aiki me yawa irin Na Daren jiyaba,,Yana cikin baccin yaji kukan nijlah tare da ringing wayarsa a lokaci guda..
A firgice ya Tashi Yana lalubar inda take kwance Dan a tinaninsa fadowa tayi daga kan gadon..

Idansa a rufe yake laluba ko ina Na gadon har saida yaji hannunsa yakai qasa bejita ba,, Sannan yayi saurin bude idonsa..

Can quryar daki ya ganta ta hade kai da gwaiwa tana kuka ga waya rungume a jikinta,, dafe kansa yayi Yana addua Tashi a bacci kafin yayi qoqarin yinqurawa ya tashi,,a hankali ya diro qafafunsa har yayi nasaran ajiyesu a qasa..

Kusa da ita ya qarasa Yana tinanin abinda yasata kuka..

Hannu biyu yasa ya ruqe hannunta Yana Magana a hankali,,amarya meya sameki kike irin wannan kukan ko yinwa kikeji?

A firgice nijlah ta Dago tana kallansa,,kafin ta saki wani saban kukan tana yarfa hannu,,Dan Allah kayi hakuri wallahi banzagetaba,Allah bana zagi ban ma iyaba..

Ke ki nutsu mana nifa banma gane abinda kike Gaya ba,,wakika zaga?

Wallahi banzagetaba Kaji Na rantse,,ni Dai ka mayar Dani kauye gurin kaka,,bazan iya zama anan ba..
Jinjigata ya rigayi har saida tayi shiru yana shafa bayanta tare da tofa Mata adduoi Dan a tinaninsa mafarki tayi..

Mummy kinga abinda nake gayamiki ko,,ninasan baze dauka wayana ba,, ahankali mummy tace ki qara Kira mu gani..
Number aunty Lateefah ta qara dealing akaro na barkatai.

na cikin yimata addua yaji waya Na ringing,,hannu yakai ze amsa taqi bashi tana kuka tana girgiza masa Mai..

Kibani nace,,ko bakiji ana kirana ba,,cikin kuka nijlah tace wallahi ban zagetaba,,ai Bata Ida Magana ba yayi saurin fizge wayar a hannunta..

Hello aunty lateefah,,ba wani aunty lateefah dazaka kirani ka kirani sa lateefah Kawai mara mutunchi,,kana kallo matarka ta zage mana uwa amma kai ko ajikinka baccinkama kake ko mashkur..

Kallan Nijlah yayi da tinda ya amsa wayar ta Tashi da gudu tayi bakin kofa hannunta biyu aka tana kuka..

Tokazo yanzun nan mummy tanasan Magana dakai,,bakinsa na rawa yace gani nan gani nan..

Yana gamawa ya Tashi a fusace yayi kan nijlah,,ai kafin ya qarasa inda take harta zube a qasa tana birgima tana bashi hakuri..
Dan Allah kayi hakuri Handi mu bani,,bazan qaraba Na tuba Dan Allah kada ka dakeni kukan da nijlah ta riqayi Kenan tana ihu..

Hannu biyu ya sarqe a qirjinsa Yana binta da kallo,, yama rasa hukuncin daze yanke akanta,,dukanta zeyi kome,,to idan ma Na daketa ba hucewa zanyi ba,,inaga amfanin dukan..

Karka daketa wata zuciyar ta fada masa kayi mata nasiha shine abinda ze shirya maka nijlah Dan da gani Bata Jin Magana..

Bebi ta kantaba ya fada toilet,,wanka yayi ya fito Yana kallanta a inda ya Barta Sai birgima take kai kace dukanta yayi..

Wardrobe ya bude ya dauko faran shadda,,cikin mintina kadan ya shirya,,wayarsa ya dauka yayi hanyar fita,,da gudu nijlah ta Tashi zata fita ya daka Mata tsawa..

Ke wallahi ki kiyayeni koni sa’ankine,,Bayan aikin kashin dakika sani saikin sakamin da wani tashin hankali ko nijlah,,ina hankalinki da wayanki suke,,to wallahi ki fita a idona..

Safke kai qasa nijlah tayi tana bashi hakuri harya gama ya fita ya Kuma kulleta ta baya..

Cikin sauri ya dauka Mota ya tafi,, restaurant ya shiga ya siyo Mata wainar shinkafa da miya ko noma be bari ansaba ya hadamata da kunun Madara me sanyi..

Dasauri ya koma gidan ya bude dakin da take ya ajiyemata kayan abincin,,gashinan ki Tashi kici kafin naje wani guri yanzu Zan dawo,,idan Kuma naji abinda kika aikata ba daidaiba saina Saba Miki..

Daga haka ya fito sedai wannan Karan be rufe ta a dakin ba,,Yana zuwa bakin get ya Kalla baba Mai gadi yace..

Baba ka tsaya akan aikinka akwai yarinya ciki,,Dan Allah karka bari ta fita,,idan Kuma ka bari wani abu ya sameta nida kaine..
to ranka ya dade cewar get man Yana gyara Zaman hularsa..

Tinda mashkur ya fito gabansa me cigaba da faduwa ahaka har ya iso gida..

A fAlo ya Sami mummy zaune ta hada kai da gwaiwa,,kusa da ita mashkur ya zaune Yana hada hannunsa..

Pls sweet mom Dan Allah kidena irin wannan tinanin,,ki dauka qaddaran da Allah ya dorawa danki,,mummy kinsani banida burun auren wata Diya mace Bayan Yasmeen,, wannan aure daga Allah yake..

Kai rufemin baki,,kana so ka gayamin Shima zagin da kabata waya tayimin daga Allah ne??

Mummy zagi kuma?

Au tambaya kake,, mummy kinji shiko,,wai mu zeyiwa barikanchi,,ki rabu dashi lateefah ni wallahi gani nake kama chanzamin Shi sukayi..

Fuskar mashkur mummy ta riqa shafawa wai a tinaninta wanine suka samishi fuskar mashkur,,Babu abinda ta Ciro Dan haka tasa kuka tana cewa shine,,wallahi shine lateefah..

Dakyar mashkur ya iya hadiye saliva bakinshi,,muryanshi Na rawa yace,,pls aunty lateefah karki hadani da mummy,,kema kinsani bazan taba Bada waya a zagi mummy naba..

Kuma nijlah Bata iya zagiba,,tana da tarbiyya,,tassss tassss lateefah ta dauke mashkur da Mari tana nunashi da yatsa..

Kana nufin Karya mummy tayiwa nijlah kome,,

Tafe kunchinsa mashkur yayi ya kasa magana,lokaci guda hawaye suka wanke masa fuska..

Ita kanta mummy taji Marin sedai bazata iya hanawa ba sabida komai akayi Dan ita ake masa..

Yanzu ina ita nijlah take,,mummy ta tambaya a hankali..

Yana hawaye yace,,tana gida,,wanne gidan qin Bata amsa yayi sabida Yana tsaran kada suje su daketa danyaga alamar Hakan,,tinda Shima Basu barshi ba..

Wai ba tambayarka bakeba ba auta??

Mummy tana gidan abokina ya tsinchi kansa da yimata Karya..

Toka tafi yanzu yanzu inasan Magana daku gaba daya,,kaga gobe auntynka zata bar qasar,,yayanku Shi ya tafi tin safe..

To yace ya Tashi Yana tafiya Yana hada hanya..

Seda yayi hanyar saban gida yaji qaran wayarsa..

Zuciyarsa Na tafasa ya duba number me Kiran,,abban Yasmeen ne..

Nan ya samu guri yayi parking kafin ya daga wayar zuciyarsa na cigaba da halbawa Dan idan akwai abinda ya tsana be wuci a rabashi da Yasmeen ba..

Yana dauka abban yace,, mashkur kana lafiya,,bakinsa Narawa yace lafiya qlau Abba..

Kafin mashkur yaqara Magana Abba yace..

Naji duk abinda yafaru sedai hakan dakayi ya nuna mana kai ka hakura sa auren Yasmeen,,Dan haka nakeso kazo yanzu gidana inasan Magana dakai,,idan an gama komai saika amsa kudinka ka tafi,,nafasa baka Yasmeen..

Wayyo kukane kawai mashkur beba Shima saida yayi na zuci,,ga wani irin faduwa da gabansa yake jiyake kama zuciyarsa zata tsage biyu tabar gangan jikinsa..

Abba dan Allah kayi hakuri bazan iya rabuwa da Yasmeen ba,,ta zama ni nazama ita wallahi Abba badaga ni bane,,haka Allah ya qaddara,,Abba zan riqe Yasmeen amana,,Abba na tabbata babu abinda ze sameta indai tana tare Dani…

Dakata haka mashkur kaida Yasmeen kunyi hannun riga,,niba wannan bayanin na tambayekaba,,kazo nan da minti 5 kafin na fita..

Abba be ajiye wayan ba Yasmeen ta riqe qafafunsa tana kuka,,Abba inasan shi,,bazan iya rayuwa babu shiba,,Abba Dan Allah ka chanza wannan hukuncin yayi masa tsauri…

Murmushi mama tayi tana kallan Yasmeen sedai bata iya magana ba ta tashi tabarsu a falon…

*Kwana biyu kunjini shiru,,kada ku dauka Jan ajiyene,,hakan yafaru sakamakon samun matsalar wayana,,Wanda har yanzu bata gama zama daidai ba*..


Yawan comment yawan typing.

*Momn sultan ce*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button