NOVELSUncategorized

YAR SADAKA 33&34

???????? *’YAR SADAKA..*????????


*STORY & WRITING BY…*
         *BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO…..*
*MMN AMATULLAH**SPECIAL GIFT TO…*
*WASILA….*3⃣3⃣&3⃣4⃣


Mama na shiga daki ta zauna saman bed tana murmushi..
Da gudu Yasmeen ta shigo ta fada kan mama tana kuka..
Mama dan Allah kigaya Abba kada yafasa aurena,, wallahi mama inasanshi,,zamu shiga wani hali idan har bama tare..

Cike da takaici mama take kallanta sai kuma ta ture ta tana cewa,,ke dai anyi sakarya,mara wayo keda nake gayamiki gaskiya kina toshe kunne,,sai yanzu da kika gama harzuqa abban Baki shine Zaki kawomin Kara,,toki tashi kibani guri ban iyawa..
Kije gurinsa kusan yadda zakuyi,,naga dai kunfi kusa..

Cikin kuka Yasmeen tace Allah mama Abba yadauka zafi akan mashkur kuma ba haka yakamata yayi ba..

To ai saiki gayamasa yadda zeyi kafin mashkur yazo labari yasha babban,tinda yagayamiki baze iya sakin matarsa ba.

Ni Allah seya saketa tinda ba itace zabinshi ba,to ai shikenan ga gurinann daga haka mama ta fita a dakin tabar yasmeen..

Daki Abba ya shiga yana zagaye dakin tare da cije labe,,waini zaa wulaqantawa yarinya,, yarinyar da tintini samari ‘ya ‘yan manya ke bibiyar aurenta Amma taqi ta nacewa wannan yaran,,gashi yanzu abinda ya sakamana dashi,,sosai Abba ya shiga cikin tinani har besan lokacin da Yasmeen ta shigo dakin ba..

Kusa da Abba ta tsaya tana kallansa,,kafin tayi qarfin halin cewa..
Abba kayi hakuri ninasan ba laifin mashkur bane,,laifin iyayen yarinyarne,,kaga sadaka suka bashi ita Kuma Abba aiba fasa aurenmu zaayi ba,,sedai Kawai ya saki wannan ‘yar masu yawan jejen..

Hakane Yasmeen Abba baki tinanin nan gaba ya dawo da matarsa,,Kuma fa kinsan yadda matar fari ke shiga ran namiji..

Murmushi Yasmeen tayi tana kallan Abba Sai Kuma tace,,hakane Abba amma ba irin wannan matan ke shiga ran miji ba,,Abba idan ka duba nijlah sadakace agurinsa ba auren soyayya akayi ba,nidai fatana roqon danake abba ka bishi a hankali kaga yadda ka dagamasa hankali dazu..

Zaro ido Abba yayi Yana kallan Yasmeen kafin yace,,ke har tausaya mar kike,,yaran da yaci amanarki..

Hakane abba sedai haryanzu banji chanji a soyayyar danake masa ba,,maimakon naji haka saima qara Sansa da tausayin halin dayake ciki n..
Doke bakin Yasmeen Abba yayi tare da nuna mata qofa,,magana take Shirin Yi Abba ya daka mata tsawa..

Fita nace,,ki fita kafin naci gidanku,,haka ,zaayi auren kije yana juyaki kamar yadda ze juya yar sadakan daya dauko,,nasan zeyi tinanin duk daya kuke..

Da gudu Yasmeen ta fito a dakin Abba tana me danasanin nuna baqin cikinta akan auren nijlah,,sedai tana fitowa suka kusa cin karo da mashkur Wanda ke tsaye jikin falon yana kwada sallama..

Jikinsa taso fadawa yayi saurin yin baya,,nan ta zube a qasa ta saki saban kuka..

Da sauri Abba ya fito yana cewa lafiya,,ganin mashkur yakasa qarasa abinda ze fada ya zuba masa ido..

Kai me kayimata?

Bakin mashkur na rawa yace Abba faduwa tayi’ shine kana kallo baka taremin yarinyarba ta fadi qasa,,kodan kada da asara..
Ba haka bane abba,,naso yin haka kuma ta qoce,,Kai meya hanaka gocewa ka tare ta..

Mamace ta fito tana girgiza Kai,,dai kuma tace sannu da zuwa mashkur,,har qasa Mashkur ya zube yana gaida mama yayinda yasmeen ta cika da mamakin qin tareta da mashkur yayi..

Seda mama ta amsa kafin tace Bismillah ka shiga ciki.
Jiki ba kwari mashkur ya qarasa cikin falon yana addua acan cikin zuciyarsa..

Bayan kowa ya zauna Abba ya kalli mashkur ransa a bace yace,, yanzu Kai abinda kayiwa yar lele kayi daidai kenan,,koka Manta lokacin da kake zuwa safe da rana kai har dare zuwa kake gidannan kana ‘yarmurya,,Seda kasu soyayyar ta zaka watsamana kasa a ido kaje can wata ruga ka aure Yan matsiyata kace zaka hadasu Kishi da diyar Dana Haifa??

Ita Dai mama shiru tayi Dan da so samune ita daki zata koma suyi yadda sukeso,sedai bata da damaryin haka,Dan haka ta zuba ido da kunne tana sauraransu..

Seda Abba yakai aya kafin mashkur yafara Magana cike da fargaba da tashin hankali..
Abba nasan nayi laifi sedai ina me Neman afuwa,,ayi hakuri a dauka uzurina.

Wanne uzuri gareka kaida ka,, dasauri mama tace..
Alhaji hakurin Dai zaayi.

To shikenan na hakura amma ya sani aure Babu Shi..
Raurau Yasmeen tayi da ido tana kallan abba,, mashkur ko kasa Magana yayi Banda addua Babu abinda yake..

Ganin Abba yayi shiru yasa mashkur Dan risinawa yace,,Abba nagode sosai hukuncin daka yanke yama tsauri ka sassauta ko yasmeen..

Kama qadan garuwa haka Yasmeen ta shiga daga kai tana zubda hawaye..

Seda Abba yagama ciwa mashkur mutumci da fada San ransa kafin ya nuna ya hakura..

Sharuda iri iri Abba ya gindayawa mashkur amma duk da haka mashkur yace yaji ya gani,,Shi burinsa Kawai ya samu nutsuwa ta bangaren Yasmeen Sai yaji Dana mummy da sauran Yan uwansa..

Tashi kace amma kasani badan kai nayi haka ba sedai yar lele Naga ta nace akan soyayyarka saikace kai kafi kowa iya soyayya kana tafiya Sumi Sumi dakai..

Godiya mashkur yayi yayiwa mama sallama,,sabida kunya dakyar mama ta iya amsashi,,ta Kuma tabbata Yana yiwa Yasmeen soyayya ta gaskiya danda wanine da tini yabarta koda itace autar Mata..

Duk da mashkur beji dadin yadda Abba yamasa ba sedai be nuna yasmeen a fuska ba dan haka ya fita a gidan cikin sauri..

Yana fita mama ta Kalli Abba Ranta a mugun bace tace..

Gaskiya Alhaji baka kyautaba,, wannan fa surukinkane nan da sati uku amma ka tsaya kana yimasa irin wannan Abu duk  akan yarka,, wannan wacce irin wayewa gareka,,to wallahi ka sani wannan abun dakayi ba qima ka siyamana ba,, mutunchi Kawai ka zubar mana a idan Duniya,,ke Kuma ki shiga hankali mara kunyar banza da wufi,,kinsan Kina San nashi kika Bada dama mahaifinki ya wulaqantashi..

Kuma Yasmeen tasa tana kallan abbanta..

Cikin fada Abba yace ke wannan abun da kikayi daidaine,,ina mijinki kina dagamin murya..

Tabe baki mama tayi tace daga gayar gaskiya Sai cibi yazama Qari..

Ke Naga alama sabida takuran da kikema ‘yar lele shiyasa takeso ayi auren nan itama ta huta,,kina Abu kama bake kika haifetaba..

Fita mama tayi adakin yayinda Yasmeen tabi Bayan ta,, Yasmeen Na fita ta shiga dakinta,,waya ta dauka ta Kira mashkur..
Bugu daya ana biyu ya dauka..

Ko sallamarta be iya amsawa ba yace,,kin kyauta da kika bari aka yimin irin wannan tarban a gidanku,,Yasmeen nayi tinanin tallafi rayuwa a lokacin da yan uwana suka sani gaba,,sai gashi kema kinyi fiye da abinda sukamin..
Cikin yauqi Yasmeen tace,,haba baby ai duk kaika ja,,kasan yadda na tsani kishiya sai gashi kayimin ita tinkafin na shigo cikin gidanka kuma daka tashi yin auren sai auri abu mafi tsana a cikin zuciyana,,ta Yaya kake tsammanin hankalina baze tashi ba..

Yayi kyau kawai mashkur yace..

Shikenan baby ka kwantar da hankalinka,,magana ya riga ya wuce tinda gashi Abba ya hakura zaayi biki..

To naji,,Amma kibari zan kiraki anjima yanzu mummy ke San ganina,,kukan shagwaba Yasmeen ta saka tana cewa..
Ni ah ah da yaushe muka fara magana kafasan nayi missing Dinka,, murmushi yayi najin dadi yace..

To waya ja Mana hakan?

Duk kaine Yasmeen ta fada tana turo Baki,,hmmm yarinya nakusa ramawa indai nine,,saura kwana kadan kishigo hannuna..

Dariya Yasmeen tayi ta kashe wayar,,nan ta fada kan bed tana juyi…

 Ko cikin get be shiga da motan ba yayi parking a waje,,dasauri ya kwankwasa qofa get man ya bude yana tambayan wanene?

Nine mashkur  ya bashi amsa..

Dasauri ya shiga ciki yana sauri..

Tin daga falo yafarajin shensheqar kukanta har muryanta yadena fita..

Lokaci guda mashkur ya ida rikicewa,, dasauri ya qarasa shiga dakin yana kallanta..

Kwance yaganta a qasa tana juyi gefe guda ga abincin daya ajiyemata nan ko tabashi batayi ba..

Kusa da ita yaqarasa yana kallan fuskanta,,kafin yasa hannu biyu ya dagota…..

Luuuuuu tayi tafada jikinsa sabida yinwan daya gama cinyeta ga kukan datayi Shima ya taimaka gurin qara mata yinwa..

Subhanallah, nijlah nijlah yafada cikin daga muryar,, nijlah bata iya amsawa ba sai kawai dago kanta datayi tana kallansa da jajayen idanta dasuka gama canza kala zuwa jajaye..

Hawaye yaji sun fara zuba a idansa,,nan ya ringemeta yana shafa bayanta..

Cike da tashin hankali yake magana.
Kiyi hakuri nijlah bansan tafiyane ze haifarmiki da matsala ba,,meya sameki?waya tabaki? Kodai tafiyanane..

Sumbatu sosai ya shigayi yana shafa bayanta..

Lamo nijlah tayi tana safke ajiyar zuciya tare da qara shigewa jikinsa..

Janyota yayi daga kafadarsa yana shafa siririn hancinta zuwa kan lebenta,hawayen fuskanshi na diga akan fuskanta..
Ido ya zuba mata baya ko kiftawa itako sabida San jiki sai mutsiniya take ajikinsa tana qara birgema akan cinyarsa..

Ahankali ya bude Baki ya Kira sunanata sedai wannan Karan ma bata amsaba sai turo masa Dan qaramin bakinta datayi tanasan magana takasa sabida yadda jikinta yayi sanyi ga wani irin zafi datakeji yana ratsa dukkan wata qofa ta jikinta..

Ganin taqi magana sai Dan qaramin bakinta dake ture agaba tana tsikarin ogah mashkur dashi yasa shi sa hannu yana zagaye bakin..

Qara shige masa tayi tanasan Kiran yinwa taji ya cafke bakin yana masa wani irin tsotso..

Sosai yake tsotsar Pink lips dinta tare da yawo da  …………….Niko nace lallai ma mashkur,,wato harka manta da Kiran mummy tare da tarin matsalolinka lolxx..


Mu hadu a next page Dan jin yadda zata kaya tsakanin ango da amaryarsa lolxx..

Comment & shareMy WhatsApp number:09038049272.ga masu son Shiga groups dina,,gyara akan labarin ko tinasarwa….*Momn sultan ce*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button