YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 1 to 10

Karya kake mashkur Idan Zaka fadi gaskiya ka fada ayita ta qare..

Haba Aunty lateefah,,ki tausayamata..

Ya mashkur kodai Suma Suna bakin cikin aurena,,Naga alama Suma irin kakane” Kuma ita wannan qatuwar wacece,,sukaji nijlah Na tambaya???

Ke kimin Shiru Nace dame kikeso Naji,,to wallahi naqara Jin maganarki Saina zaneki anan” turo baki nijlah tayi tana dire diren qafa,,a hankali mashkur yace menene Kuma,,Nina gaji Zama zanyi,,Kuma Dai ka Tina Allah Yana kallanka,,Kuma a wuta yakesa me Karya haka malaminmu ya Gaya a islamiyya,,gwara kawai kace matarkace Ni Kamar yadda ka Gaya Bello..

Gaba daya jikin mashkur yayi sanyi Dan haka ya zauna Kan kafet Yana Kallan mummy…

Mummy kiyi hakuri Nima ba haka naso ba,, mummy ki dauka kaddarace tasa nayi, Sai ya kasa qarasawa..

Qaddara tasa kayi me auta,,ka gayamin Ko hankalina Ze kwanta..

Mummy auren nijlah nayi a,,kafin ya qarasa magana mummy tasa kuka tana cewa..

Shinkenan ka cuci rayuwata ka nuna Kaine da kanka,me kakeso mu Gaya iyayen Yasmeen,,yanzu wannan abun Abar aure ce,,kadubeta kama an daurawa muciya zani..

Kallan jikin nijlah ya riqayi Shima Yana hawaye,,Dan Allah mummy kidena wannan kuka wallahi kukanki masifa ne a gareni da rayuwata mummy na tuba yafada Yana kama qafanta..

Saida mummy tayi kuka me isarta kafin tace ina Baka umarni Daka mayar da yarinyarnan inda Ka daukota kafin..

Mummy kiyi hakuri nijlah amanace agareni nayi alqawarin Zan riqeta duk rintsi,,bazan taba rabuwa da itaba..

Zaro Ido mummy tayi tana kallansu kafin tace a ina zaka zauna da ita?

Mummy Dan Allah ko dakin Baki Kona ‘yan aiki ki kaita nasan zata zauna” Kai wallahi ko a dakin Karen gidannan bazan ajiye wannan irin jarabar ba,,gwara tin muna arziqi Ka fita da ita..

Kafin yayi magana aunty lateefah tafara Jan nijlah da niyyar kaita waje,,cikin ihu mummy tace ke lateefah Baki da hankali zaki tana jikin wannan nida Zan iya da tinanin na kaita lahira hannunane bazan iya Sawa a jikinta ba,,Amma zanyi maganinta idan har be fita da ita a gidan nan ba..

Cikin kuka nijlah ta Koma Bayan mashkur tana riqe rigarsa tace,,Dan Allah ka fita Dani zasu kasheni,,Bata sona..

Kiyi hakuri nijlah komai zeyi daidai kinji,,mummy.

Karka qara Kiran sunana saika fara fita da wannan annobar,, mummy Bazan iyaba haqqinta Yana kaina.kiji tausayinmu.

Kaima kasan Bazan taba Zama da ita a gida daya ba Dan haka ka zabamata inda ya dace Kuma a yanzu nakeso ka saketa saki uku.

Mummy kiyi hakuri tinda bazaki Bata gurin Zama ba nizan zauna da ita a dakina,,batin saki Kuma kiyi hakuri Baz…

Lafiyayyun Mari Har guda uku Yaya ya safkewa mashkur Yana nunashi da yatsa,,kayi kadan ka wulaqanta mana uwa,,wallahi sedai kabar gidannan..

Beyi Magana ba ya kama hannun nijlah dake kuka tana Kiran Sunan kaka ya Shiga dakinsa da ita,,a qasa nijlah ta zube tana birgima tana ihu,,shiko bakin gado ya zauna ya dafe kansa Yana Jin Wani irin faduwar gaba..

Cikin kuka lateefah tace,yanzu haka zamu zuba ido mashkur yayi yadda yakeso,, ba Wanda yabata amsa..

Nan mummy ta dauka waya ta Kira daddy tana kuka,tace Alhaji ka dawo gida yanzu,,tana gama fada ta katse Kiran Bata jira amsar Shiba..

Wani layin ta Kira ta miqa lateefah wayar..

Yasmeen dake kwance Kan cinyar mama tana game a waya taga Kiran mummy,,kallan mama tayi jikin Jin Kunya tace,,mama mummyn mashkur ce.

Ki Daga mana cewan mama tana kasa kunne,,Yasmeen Na dauka lateefah tace ..

Sunana lateefah yayar mashkur,,mummy nasan ganinki yanzu….

Wash,, typing da wahala,,mu hadu a page na gaba..

Karku manta da share.

*Momn sultan ce*✍✍✍

???????? *’YAR SADAKA..*????????

*STORY & WRITING BY…*

         *BY*

*MOMN SULTAN*

*DEDICATED TO…..*

*MMN AMATULLAH*

*SPECIAL GIFT TO…*

*MOMN ANSAR*

1⃣9⃣&2⃣0⃣

Mummy kuma,,ke Yasmeen dama kina waya da mahaifiyar yaran nan” gizgiza Kai Yasmeen tayi tana kallan mama data kafeta da ido,,amsa zaki Bani,kinfi kowa Sanin bagane wannan yaran naki nake ba..

Cikin yauqi da yanga Yasmeen tace,,Allah mama bamu waya da ita”

Ok!saiki gayamin ta ina mahaifiyar sa ta dauka number ki??

Mama sau dayane mashkur ya kirani da layinta shine nayi saving,,cike da rashin gamsuwa mama tace,,idan bakwa waya da ita yaya za’ayi ta kiraki???

Mama ba ita bane yayanshine,,sunanta aunty lateefah sedai da wayan mummyn ta Kira kuma tace wai mummy nasan ganina..

Mezaki Mata???

Eyyah mama Nima bansani ba,, Yasmeen ta fada tana turo Baki..

To babu inda zakije”wannan ai shirmene ki dauki qafa kije har gidansu saurayi kina magana da mahaifiyar sa,,mama Allah bantaba zuwa ba sedai jikina Yana Bani kamar akwai matsala..

Wanne irin matsala kinga Yasmeen kidena kawo tinani marasa kyau a cikin zuciyanki…

Mama ba haka bane,,wallahi tin jiya gabana yake faduwa ki abinci ban iya Ciba,,gashi sai Kiran mashkur nake wayanshi kashe,,kuma Shi be Kira ba,,gashi yanzu aunty lateefah ta Kira mummy na nemana,,kinga ko da wani abu.

Babu komai Insha Allahu,,karyar da murya Yasmeen tayi tana hawaye tace,,mama Dan Allah kibani dama naje wallahi bazan zauna ba..

Hmmm Yasmeen ina jiyemiki Abu Amma ke Baki gani,,akullum ina gayamiki ki rage wannan soyayyar da kikewa mashkur,,namiji fa mijin mace hudu ne..

Bata fuska Yasmeen tayi tana kallan gefe tace,,,mama kullum gadanki Baya wuci Kan mashkur,,ba aibu bane Danna nuna kulawa da tsananin soyayya gareshi,,mama mashkur Yana Sona har inaga kama Sanda yakemin ya zarta nawa”” duk da haka ki rage nidai ina gayamiki..

To mama Dan Allah naje???

Ajiyar zuciya mama ta safke tana kallan yadda Yasmeen ta narke Mata kama ance wani Abu ya Samu mashkur tace,, shikenan kije Amma sainayi waya dashi mashkur din naji daga bakinsa yakuma hadani da maman nashi..

Mama kenan,,haba mama na saikace Baki yadda da tarbiyyana ba,,mama kinsani mashkur Baya gari kuma wallahi number mamansane barima nakira saikiji da bakinki..

Number mummy Yasmeen ta Kira sedai wayan akashe Dan haka mama tace babu inda zata fita,,kuka Yasmeen tasa tana Jin wani irin yanayi a dukkan jikinta,,jitake kama qirjinta ze fashe zuciyarta ta fito gaba daya Kota huta da abinda takeji,,koya ta motsa Kota Tina sunan mashkur sai taji kama andora Mata dutse aka,,duk yadda taso hakura takasa haka tasa mama agaba tana kuka..

Yasmeen meyasa kikesan dagamin hankali,,ba Duka ba zagi amma kinsani gaba kina kuka saikace qaramar yarinya..

Mama kibari naje ko hankalina ze kwanta,,wallahi mama akwai matsala,,bantabajin irin wannan yanayin ba sai jiya zuwa yanzu,,Insha Allahu bazan wuci 1 hour ba Zan dawo..

Shikenan Yasmeen tinda haka kikeso saikije daki sani gaba kina wannan kukan ko kunya baji..

Share hawaye Yasmeen tayi tana murmushi tace,, nagode mama..

Mama bata iya bata amsa ba Sai binta da kallo tayi tana mamakin yadda Yasmeen ke nuna damuwanta agaban kowa..

Dago jajayen idanunsa yayi ya zubamata ido Yana kallan yadda take kuka tana Kiran kaka,,wani irin juyawa kanshi yake sabida halin dayake ciki ga kuka dake taba masa zuciya,,ahankali ya riqa Kiran sunanta..

Nijlah. nijlah. Nijlah..

Bata amsaba Saima qarawa kukanta sauti tayi,, ya rasa yadda zeyi da ita,,nan ya miqa hannu Yana Magana da shaqanqiyar murya,,zomana amaryar mashkur,,maqale kafata nijlah tayi ta kuma juya masa baya tana turo baki,,duk da haka ranshi be baci ba ya cigaba da kiranta Yana rarrashinta,,amma duk da haka bata iya shiru da bakinta..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button