YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 1 to 10

Bayan ya sallami me napep ya tsaya tinanin ta yadda zefara tashinta Sai kawai ya dauketa ya kwankwasa get..

Waye ne Ze balle mana kofa qara bugawa mashkur yayi Yana cewa nine baba zoka Bude..

DA gudu baba me Gadi ya Bude kofan Yana yiwa mashkur sannu da zuwa..

Ahankali mashkur yace,,baba ga kayana Dan Allah ka temaka ashigomin dasu,,to ranka ya Dade,,nan baba yafara rufe qofan,,qaran qofa yasa nijlah Bude Ido tana Kalle kalle..

Ahankali mashkur ya safketa Yana jera Mata sannu,,Ina kayana nijlah tafada cike da sanyin kuka.

Kingansu can Karki faramin halin naki,,dasauri ta dauko kullin dankwalinta ta Dora akai tana Kalle kallen gidan..

Hannunta ya kama Yana cewa ‘yar kauye Sai Wani Kalle kalle kike,,lah kado kaga wannan abun da Ake nunawa,,lah kado Kalli kaza haka nijlah ta riqa fada Har suka isa qofan falon..

Da sallama mashkur ya Shiga zuciyarsa na harbawa tare da  matsanancin faduwar gaba..

Mummy dake zaune tasa abinci agaba Taji sallamar mashkur,,dasauri ta dago ido Aiko tayi sa’a idanta be safka Kan Na mashkur ba saiya sauka Akan santaleliyar surukarta..

Zabura tayi ta Tashi tana nuna nijlah da yatsa bakinta yakasa magana…

Aunty lateefah ce tayi qoqarin Bude baki tace mashkur Kaine haka,,ita Kuma wannan Daga ina,,Ina Zaka kaita..

Mashkur be Iya Magana ba illah zuba musu shanyenyun idanunsa dayayi Yana cigaba da tafiya,,,har Saida yakai jikin kujera Ze zauna hannunsa riqe Dana nijlah yaji muryar mummy tana Magana..

Karka fara Zama min Kan kujera ka Kuma ficemin da wannan aljanar yarinyar”waima a gidan ubanwa ka samota Sai kuma tasa kuka tana cewa.

Kunga irin jajibe jajiben nasa,,ya kamomin wannan qazantar Har gida…

Mashkur wacece wannan Daga ina ka daukota??

Kafin mashkur yayi Magana yaji tsincin muryar nijlah..

Sunana nijlah kawu Daga garin kankan ya daukoni Kuma ni matarsace Ko kado?????????????????????

*Kuyi hakuri wayana ya Samu matsala ba lallai ku qara Jina a ‘yan kwanakinan ba,,sedai kuyi fatan Allah yasa ta gyaru da wuri,,Nima ba haka naso ba,,zanyi missig zafafan comments dinku????????????*

*Comments & share* 

*momn sultan ce*✍✍✍

???????? *’YAR SADAKA..*????????

*STORY & WRITING BY…*

         *BY*

*MOMN SULTAN*

*DEDICATED TO…..*

*MMN AMATULLAH*

*SPECIAL GIFT TO…*

*DALA…..*

1⃣7⃣&1⃣8⃣

Kallan kallo aka riqayi a falon yayin da mummy ta riqajin Dakin Yana juya mata,,sedai Wani bangare na zuciyanta Yana gayamata Karya yarinyar take,,kallan mashkur nijlah tayi tana murmushi tace..

Dan birni kayi Shiru Baka Basu amsa ba,, mashkur be Iya kallan inda nijlah take ba yacigaba da qoqarin Zama Kan kujera..binshi nijlah tayi tana kallan mummy dake binta da Wani irin kallo Wanda batasan kona menene ba.

Marin da aunty ladeefah tayiwa mashkur ne ya dawo dashi Daga duniyar suman tsaye dayayi..

Dan iyayenka ba tambayanka akeba,,Yaya kaduba yadda ya maida mu mahaukata,,

Kinga lateefah abi komai a hankali shida kanshi zeyi  bayani cewan yayan Yana mamakin abinda mashkur ya aikata duk da yasan halin mahaifiyar tasu..  

Mummy Bata Iya Magana ba Dan a yadda take Bata Jin abinda suke fada kallansu kawai take sabida gaba daya komai nata ya tsaya ya Dena aiki…

Kallan aunty lateefah mashkur yayi kafin ya safke kansa kasa nan take idanunsa ya kada yayi jajur ga Wani tuquqin bakin ciki daya tokare masa zuciya,,kasa hadiye yawu yayi Yana Kallan kafet..

Lah lah lah,,Amma dai kado anyi mugu,,Babu abinda mijina yamiki Zaki mareshi,,aradu Kaci sa’a kai babbane Dana sheqeka da Sanda,,ka zube anan..

Ke Dan ubanki bamasan hauka kai mashkur ka Bude baki kayimana magana,,a Ina ka samo wannan aljanar yarinyar??

Dakyar mashkur ya Iya tsayar da nutsuwarsa ya dago kanshi dake saramasa Yana kallan yaya,,kafin ya Bude bakinsa Wanda zuwa yanzu yayi masa nauyi yace,,

Dan Allah Yaya kubani lokaci saina yi bayani Amma Daga zuwana kun tsareni da tambayoyi..

Au Allah lallai yaran nan ka samu sake yaya kake Gaya haka,,mummy kingani Duk soyayyar da Kika nuna masa ce tajamana haka,,gashi muna magana Yana mayar mana sabida be daukemu da qima ba,,aunty lateefah ta qare maganan tana huci,,mummy ko Ido ta zuba musu,,zuwa yanzu tana fatan maganan nijlah ya Zama karya Kai inda halima ace nijlah ba cikakkiyar me hankali bace..

Aunty kiyi hakuri niba haka nake nufi ba,,da hakane bazan tabajin magananku a daidai lokacin da kuka buqaci na dawo gida ba,,

Karyar banza cewar aunty lateefah tana nuna nijlah,,wacece wannan?

Hade fuska mashkur yayi,,Zan gayamusu yanzu nagaji da yawa saina huta,,mummy kinajin abinda yake fada kinyi shiru??

Mummy bata iya motsawaba Saida lateefah tayi saurin girgiza ta kafin ta safke nannauyan ajiyar zuciya tana kallan mashkur Daya kafeta da Ido Yana mamakin halinda mummy ta shiga..

Dasauri yayi gurinta Yana cewa,,lafiya sweet mom,,waya tabamana ke”” dasauri ta daga masa hannu alamun karya qaraso inda take,,chak ya tsaya tare da hadiye yawun Daya taru a bakinta,,tinda yake mummy bata taba yimasa irin wannan karbar ba to kodai shima ya shafo abinda take kyama tattare da Fulani,,yayiwa kanshi wannan tambayan..

Bakin mummy na rawa tace,,auta wacece wannan?

Shiru mashkur yayi Yana tinanin amsar dazeba mummy sai ya maida kallansa ga nijlah yanasan yimata magana da ido,,aiko nijlah ta washe Baki tana tinanin amsa mashkur yakesan tabada..

Tace ehhh,,a kankan ya dauko ni kuma Malam ya daura mana” tsawa mashkur ya Daka Mata Yana hararanta tini nijlah ta rufe Baki tana karkarwa tare da komawa bayan aunty lateefah tana boyewa,, da mugun gudu lateefah ta dawo bayan yaya tare da Dora hannu aka..

Dan ubanka kabani amsa kafin yanzu na Saba ma,,yaushe kazama haka mashkur ni nake ma tambaya kana kallona,,,to kodai na chanza ma,, dasauri yace ah ah mummy dama dama.

Dama me,, gaskiya zaka gayamin ko angayama idan zakayi taimako saika kawomin irin jaraba har gidana,,Bama ta tsaya iya get ba shine saida Ka kawomin ita har cikin falona..

Zuciyarsa na dokawa yace mummy kiyi hakuri tare zamu zata zauna da ita”

A ina?mummy ta tambaya..

Batare da fargaba ba mashkur yace anan gidan,,sedai Ka zauna da ita Amma badai mummy ba” shima baze zauna da wannan annobar ba mummy taba lateefah amsa..

Kai Dan birni me suke fada,,Allah dai yasa badani suke ba,,cewan nijlah tana kallan mummy sai kuma ta sunkuya tace sannu ina yini..

Ke tashi anan kafin kimin barbaren kudin cizo Naga alama a wannan jikin naki babu abinda bazaa samu,,Kai mashkur Ka fitamin da ita a falo Ka kuma dawo kayimin bayanin inda Ka daukota..

Mummy marainice shiyasa na kawota ta riqa tayaki aiki,,mummy yarinyar bata da matsala Dan Allah karkice ah ah  yafada Yana hada hannu alamun roqo.

A tare mummy da lateefah har ma da yaya suka sa salati suna tafa hannu” lateefah ce tace cewa akayi mummy na buwatar ‘yan aiki,,to koma ina buqata saina rasa Wanda Zan dauka sai wannan..

Duk da yarinta da shirme irin na nijlah saida tagane kyamarta suke gashi taji Dan birni Yana maganar aiki zata tayasu,,to wai me suke nufi?

Wanne irin kallo suke min nijlah ta tambayeni kanta,bata dawo daga tinanin ba taji mashkur Yana cewa..

Mummy Dan Allah kiyi hakuri ki tayani riqe amanar da Allah ya doramin,,yarinyarnan marainiyace bata da gata shiyasa na kawomiki ita,,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button