YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 1 to 10

Da Malam suka hadu a hanya nan Malam yake masa godiyan kudin Daya ba nijlah,,bayan Malam ya tafi mashkur ya juya Yana kallan bello..

Bello Naga wannan mutumin sai godiya yake akan naba nijlah naira hamsin,,nawa Raina 50 take daze Namin godiya har haka???

Hmmm Kai agurinka naira 50 bata da yawa Amma Banda gurin Malam da jikarsa nijlah” au dama ba shine mahaifinta ba” 

Mahaifinta da maihaifiyarta sun   rasu suke Kula da komai nata sedai Basu da karfi,, Dan ma suna San yarinyar kullum addu’a suke Allah ya kawo Mata mijin aure su auran da ita su huta” 

Aure kuma nijlah har nawa take daga ganin yarinyar bata Ida shekara 11,, murmushi Bello yace yace ai nata Kai hakabama  saura wata 4 ta cika shekara Goma.

Tashin hankali Amma akesan auran da ita cewan Nasir cike da mamaki,,to Nasir ya zasuyi Basu dashi kuma mu a wannan kauyen muna auradda yara shakara 13 zuwa 14..

Hira sosai suka riqa tafiya Bello Yana Basu akan labarin iyayen nijlah da rayuwarta,,tin daga nan mashkur yafara Jin tausan yarinyar jiyake dayana da yadda zeyi Daya taimaketa, akan auren da akesan yimata,,ahaka har suka Kai inda network ya hau Kan wayansu..

Hamdala mashkur yayi ya Kira layin Mummy,,bugu Daya biyu ta dauka muryanta a sanyaye” Assalamu alaikum mummy na kin tashi lafiya??

Kaima kasani ko lafiya ko akasin haka,,yanzu abinda kayi Ka kyautamin Kenan kodan kaga na damu dakai ko auta.

Kiyi hakuri Mummy wallahi ba laifina bane garin me ba network yanzuma seda mukayi tattaki zuwa wani guri me nisa aka samu network.

What mashkur kana nufin bazan riqa samunka a waya ba,,to wallahi kayi gaggawan baro wannan kauyen kafin naci mutumcinka,,Kako San a zaune na kwana.

Pls mummy kiyi hakuri iya yaune Insha Allahu za’a gyara,,yafada haka danya kwantar Mata da hankali” 

Nidai nagayama kadawo kafin na Gaya daddynka tinda ni Ka rainani,,inyaso Shi yafada kaji” kiyi hakuri bata amashi ba ta katse Kiran ranta a mugun bace” yasan koya Kira ba dauka zatayi ba Dan haka ya tura Mata  text massage.

Layin Yasmeen ya Kira dake zaune kusa abbansu tana Shan ice cream” murmushi tayi tace lah abba kaga mashkur ya kira.

Murmushi abba yayi yace dama na gayamiki ze Kira saiki dauka kafin ya katse,, dasauri ta dauka ta tashi ta koma dakinta,,hello hubby nah!

Na’am baby kin tashi lafiya,,lafiya qlau sai kewanka,,baby daga tafiya harkin Fara kewa da wuri haka,,karki manta shekara guda zanyi,,

Narke masa tayi tana kukan shagwaba tace,,Dan Allah Kada kayimana haka kaface 1 month zakayi Ka dawo” ah ah baby garin da nisa bazan iya wannan sintirin ba,,keya kamata kizo mu gaisa.

Bata fuska Yasmeen tayi tana turo Baki,,kaima kasan bazan iya rayuwa a irin wannan gurin ba,,Kai dai dakaga zaka iya saika zauna”

To ai shikenan kinga Kenan bakisan gani,,Allah hubby inaso Kaine Ka zabamana wannan rayuwa ta nisanta juna,,

Hira Sosai sukayi har Saida Nasir ya kasheshi kafin suyi sallama su koma kauyen,,bayan kwana biyu kowa aka kaishi gurin aikinsa inda mashkur ze riqa koya yara karatu a makarantar primary ta gari.

Sosai yayi mamaki da ganin ko ajujuwan babu gaba daya sun lalace birbiri ya Gama lalata sauran,,a haka yake koya musu duk da ba zuwa sukeba,,watarana sedai yaje Shi Daya yagama abinda zeyi ya dawo…

Nasir yayi sa’a kauyen da aka Kashi a kusa yake sedai Shi ana samun lalbai Dan Har headmaster garesu..

Wasa wasa Shakuwa me karfi Na qara Shiga tsakanin nijlah da mashkur,kullum saita kawo masa warar Fulani shiko yanasan taimaka musu Amma Malam ya Hana yace indai ba auren nijlah yakeso ba Baze amsa kudinsaba,,ba yadda mashkur ya Iya haka ya hakura sedai kullum Yana ba nijlah naira Goma Ko biyar tana zuwa dandali.

Yau tin safe Malam ya tashi bashi da Ko naira biyar balle su Sami abinda zasu sa a bakinsu.

Tinda nijlah ta Tashi take kuka ita yinwa takeji gashi Har karfe 12 Na safe Basu Sami abinda zasu sa a bakinsu ba.

Dan Allah Malam kabar yarinyarnan ta Shiga Ko gidansu Indo ne tasa Wani Abu a cikinta kaga yaro besan Babu ba” Ni kaina abinda nake tinanin kenan sedai Bazan bar yarinya tana zuwa kwadayi gidan mutane ba,,tinda su Basu tausaya sun bamu ba..

Malam me zakayi Kar ka cemin Baka fasa Bada sadakan nijlah ba,,Dan Allah kabari kaqarasa Ko shakara Goma sha biyu ne” kinga yakumbo ki rufemin baki,,Ina yanzu nijlah ta cika shekara Goma.

Dan Allah ba shawaranki nake nemaba..

Amma Malam…!Amma me kinfisu yinwa ya kashe yarinya muna kallo,,Idan Ko Na auradda ita Na tabbata bazata Rasa abinda zata Ciba…

To Malam wazata aura kasan Dai iro bashi da kudin aure Kuma Koda ka bashi sadaka Baze Iya ciyar da nijlah ba sabida Shima dakyar take samu yaci..

Bashi zanba auren taba sedai inaso kisani a kwana kusa Zan auran da ita,,kai malam kafa Duba lamarin nan,

Nijlah Najin batin aure ta tashi tana me Jin Dadi tace,,Malam ka gyale maganan kaka kayimin aure Nima Na riqa tuqa tuwo da kaina mijina Na siyomin tsire inaci…

Yauwa Yar albarka,Allah yasa asamu Wanda Ze Iya riqemana Ke ya Kula da maraicinki,,hawaye kaka ta goge da zanin jikinta tace..

To a gaskiya koka auran da nijlah sedai mijin ya biyota gidannan Dan gaskiya banga Wanda Ze Iya juran rigiman nijlah ba” Idan kinga ana haka Sai kiyi,kinga Nina fita karbomana bashi Ko gari musamu Musa a cikinmu..

Adawo lafiya yakumbo tayiwa Malam kafin ta janyo nijlah ta rungume tana rera kuka” Kaji kaka da baqin ciki,,bakiso Nima mijina ya riqa saimin kayan dadi ..

Yawan comments yawan typing,Dan Allah ku rage godiya ki riqa sharshi Ta hakane zan gane sakon danake San isarwa Yana zuwa muku

Comments & Share????

*Momn sultan ce*✍✍✍

???????? *’YAR SADAKA..*????????

*STORY & WRITING BY…*

         *BY*

*MOMN SULTAN*

*DEDICATED TO…..*

*MMN AMATULLAH*

*SPECIAL GIFT TO…*

*HUSSAIN 80k*

7⃣&8⃣

Kujimin kaka da baqin ciki,baki Nima mijina ya riqa saimin kayan dadi iron na abu, nijlah ta fada cike da yarinta!.

Cikin kuka yakumbo tace!uhmn nijlah Kenan angayamiki kayan Dadi shine aure,,me Kika Sani game da Zaman takewar aure” 

Allah kaka Na Sani,,badai ruwa Ake zubawa a buta na alwala ba,Sai kuma ka zauna Idan anyi tuwo a cikin gida ka dauka Langa a zuba masa tuwo..

Nijlah Kenan babu abinda Kika sani”Allah kaka Na Sani Niki Dena kirana yarinya Kuma Naga Abu tayi zamanta a gidan Musa Ai Dai Nima Zan zauna” Allah ya kyauta cewan kaka tana Jin quna cikin zuciyanta..

Tana nan zaune Har Malam ya dawo dauke da Leda a hannunsa,,

Wai haryanzu kina zaune kina tunani Akan abinda bashida mafita Sai wacce na fada” uhmn uhmn fa Malam wallahi nijlah bazata Iya Zaman aure ba,,ka Duba qanqantar shekarunta?

Yakumbo Kenan tin yaushe muke neman mafita bamu samu ba,,se yanzu Dana samu Zaki kawo matsala,,kiyi tinani Dan Allah.

Shiru yakumbo tayi tana nazari kafin tayi iya Bude baki tace” yanzu Malam Idan muka auran da ita akazo haihuwa ta kamu da jajjan fitsari ya zamuyi,, murmushi Malam yayi Dan ya gano abinda yakumbo Ke tsoro..

Indai wannan ne ki kwantar da Hankalinki,na tabbata nijlah bazata samu wannan matsalan ba,,to Malam kasan Wanda Ze aureta??

Kinga yakumbo Idan bakisan ayi aurennan kawai ki fada ni Kuma Zan zuba Miki Ido Naga yadda Zaki Iya Kula da ci da Shan nijlah,, yakumbo kinfi kowa sanin halin nijlah,,yinwa kawai Idan Taji ta riqa surfafa Miki kuka Ke Akan kudin dandali Sai nijlah ta kusan kwana tana ihu,,Ina Sai yanzu da Allah ya kawo mashkur wannan kauye nijlah ta Dan samu gata,,Idan ba haka bane Sai gayamin..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button