YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 1 to 10

Mashkur har sauri yake Dan tin daga nesa gurin yayi bala’in burgeshi.

Yakumbo na zuwa gida ta kwantar da nijlah tana kallan yadda ta Zama abin tausai,,kiyi hakuri kinji yarinyar kaka,,Allah ze saka Miki..

Nidai ban yadda,ara ta kanni  saina Rama,ai dai na ganeshi,uhmn uhmn fa nijlah banisan tsokala.

Yakumbo kema kinsan Bani bari kowanne mara kunya,,inda harfa da riqemin hannu yanzu da iro ya ganci yaya za’ayi,kaka kinsan fa iro da kishi”

Ke qaniyanki nace,wai ba na hanaki Kula wannan iron ba,, nijlah yanzu fa shekara 9 kike se Yan watan ni,, ki Bura kidan qara girma Dan bana tinanin zamuyi muki aure a shakara Goma sha uku,,gwara kisama kanki  salama har Malam ya Samu kudin sai Miki katifa da korai.

To kaka, yau Zan gayamasa danaje dandali,,to kaka ki Bani biyar saina tafi,kinga dare sai qara yi shike..

Kiyi hakuri nijlah yauma Bani da ko biyar,,tsalle nijlah tayi ta Fadi qasa tana kuka,,ni wallahi sai kin Bani biyar Naga ba’a zuwa dandali ba biyar,wasu har Goma ake Basu Amma ke kullum hakuri kike Bani.

Wai sai yaushe Zan gayamiki kidena hada kanki da yaran garinann nijlah meyasa kikesan batamin Rai akan Baki kudin dandali ko kinaso Nima na Fadi na mutu..

Nijlah najin an Kira mutu take Shiga hankali ta,Dan haka ta tashi tana turo Baki,,kaka na tafi.

    *Yawan comments yawan typing,, comments Kai ke nuna labari yana dadi ko babu,,akullum ina qara gayamuku daku riqa turawa wasu group’s bayan kun karanta, nagode*

*Momn sultan ce*✍✍✍

???????? *’YAR SADAKA..*????????

*STORY & WRITING BY…*

         *BY*

*MOMN SULTAN*

*DEDICATED TO…..*

*MMN AMATULLAH*

*SPECIAL GIFT TO…*

*MMN FAREESAH*

5⃣&6⃣

Kaka na tafi,,adawo lafiya,,Banda tsokala ki Kuma dawo da wuri,,kaka Kenan kinfasan Bana dadewa Amma kullum sekin gayamin saikace yarinya..

Baki yakumbo ta riqe tana kallan yadda nijlah ta tafi tana Taku daidai,kai kace wata babban budurwace!

Yakumbo Bata qara Magana ba nijlah ta fita tana Mita,,haka haka ta batamin lokaci gashi ‘yar biyar din ma Bata Bani ba,, murmushi ta saki tare da fari da manyan idanunta tace,,nasan iro Yana dandali Yana jirana, tafiya nijlah take tana tinani harta qarasa dandali,,tin Daga nesa tafara Jin qaran sautin gangan danladi me gidan kagane Na tashi..

Tin Daga nesa su indo da Abu suke kallanta Har ta qarasa suka fara gaisawa,, nijlah Zaki Sai tuwan ruwa?turo baki nijlah tayi tace,,kinga niba ciye ciye ya kawoni ba,,kallo kawai zanyi Na Koma gida,kaka tace kada Na zauna,,Bata Ida rufe baki ba Taji an Kira sunanta” dasauri ta dago Ido tana duban Wanda ya Kira sunanta,,bazata taba manta wannan fuskan ba,,Dan shine mutum Na farko daya taba dukanta..

Murguda masa baki tayi tana cewa,,lafiya Zaka Kira sunana?

kiyi hakuri nijlah Bada niyya nayi Hakan ba,,kinji yarinya, Nasir ya fada Suna Hada Ido da mashkur dayayi kama besan abinda suke ba..

Yarinya Kuma,,nice ma yarinya,,to sannu babba,,dariya Nasir yayi Yana Kallan nijlah,,nidai Duk ba wannan ba,kin yafemin?

Karka damu Allah yanasan me yafiya nayafema,,Nima ka yafemin batama Mota danayi”

Nagode sosai Nasir ya fada Yana murmushi,,sedai Bani Zaki nema tafiyan Bata motor ba,kinga Wanda Zaki nema danba motana bane nashine,Nasir yafada Yana nuna Mata mashkur.

Har qasa nijlah ta sunkuya tana kallan fuskanshi tace,,Dan birni kayi hakuri Kaji, murmushi mashkur yayi,ya Bude baki a hankali yace,Tashi kinji kanwata,,maqale kafada nijlah nan yayi murmushi danya gane nufinta yace, shikenan Na hakura Amma Karki qara zana Mota kinji,,to nijlah tace ta Tashi da gudu zatabi kawayenta mashkur yace kinga nijlah zo..

Juyowa tayi da niyyan zuwa idanta ya safka Kan Na iro daya zuba Mata su alamun tambaya” lah iro yanzu nake dubanka anan,Hade Rai iro yayi Yana hararanta,,kai iro Daga tambaya Sai harara, nikaga tafiyana..

Ke nijlah Ina kikasan wadannan ya fada Yana nuna mashkur” cike da tsoro nijlah tace yayanane Daga birni suka zo” kin tabbata eh mana nijlah ta fada tana kallan mashkur” sosai mashkur ya cika da mamakin wayo irin Na yarinya sedai abinda yake tambayan kansa shin wanene wannan yaran da nijlah tayi Karya.

Nijlah Na ganin tafiyan iro ta qaraso kusa da mashkur tace gani” naira hamsin mashkur ya miqa nijlah Yana murmushi,amsa wannan Duk da Naji kince ba ciye ciye ya kawokiba,,

Nagode sedai kaka ta hanani amsar kudin samari indai ba iro ba,,wanene iro mashkur ya tsinci kansa da tambaya”

Iro yarone dabe wuci shekara 21 ba,,shine yake neman auren nijlah,, mashkur yaji Bello Na bashi amsa”

Kai Bello kana nufin kace wannan yarinya saurayi ne da ita??

Kwarai dagaske Bello ya bashi amsa,rufe fuska nijlah tayi tana dariya” mamaki sosai ya cika mashkur Nasir ne ya qara kallan nijlah yace yanzu Ke yarinya kinsan menene soyayya,,kasa Magana nijlah tayi ganin haka yasa Bello cewa..

Kinga nijlah amsa kije ki Sai abinda kikeso nizan Gaya yakumbo,,kasa amsa nijlah tayi Duk da tanasan siyan Abu a dandali,,qara miqa Mata kudin mashkur yayi,,Kanta a qasa tace Ni biyar Zaka Bani wannan yayi yawa ta fada Kanta a qasa..

Ki amsa wannan Bani da chanji,,wannan shine qaramin kudi a jikina,,Nasir Ko kanada Goma,,ta amsa wannan Nasir ya fada alamun Babu..

Kasa amsar kudin nijlah tayi,,kanwata ki amsa mana,kefa Naji yanzu kina Gaya Wani Ni yayankine kodama Karya kike,,Kunya ce ta kama nijlah nan ta miqa hannu ta amsa kudin,, 

Nagode sosai Allah yasaka da alkairi,,Nima gobe Zan Baka fura da nono,,

Bata jira amsar Saba ta Shiga dandali tana murna,,

Bata Dade a gurin ba ta tafi,,tin Daga bakin kofa nijlah Ke Kiran kaka,,kaka!

Kai wannan yarinya Ni harna fara bacci Zaki tadani,,kaka kinga wannan Dan birnin ya Bani kudi harna Sai abin biyar kinga sauran,ta fada tana miqa kaka Chanjin..

Lalala nijlah waya baki wannan kudin kaddai kicemin Wanda ya dakeki dazu,,kaka bashi bane Wanda ya riqe Yana mishi fada,,Kuma Shima yabani hakuri,,to Duk Naji Amma Daga Yau Karki qara amsar kudi ahannun Wani koba na hanaki ba,,kaka Nima ban amsaba,Ina wannan bellon na gidan Liman,eh nagane cewan kaka,to shine yace Na amsa Ze gayamiki,,to Allah ya akaimu goben zansa Malam ya tambaya.

Washe gari karfe 10 na safe Malam yaje gidan liman anan sukayi magana da Bello ya tabbatarwa da Malam yaran bashida matsala,sannan hankali Malam ya kwanta.

Tin asuba mashkur yake Kiran mummy sedai network ya Hana wayan Shiga,,dafe Kai yayi Yana salati,,lafiya mashkur badai wani matsala bane?

Matsalane babba Nasir tin jiya nake Kiran mummy wayan yaqi Shiga gashi kasan halin mummy na tabbata yau bata rintsa ba.

Ni abinda ke damuna Kenan tinda muka zo ban samu kowa a waya ba,,ance semun fita wani Dan kauye anan kusa zamufi samun network,,kaga Nasir Kai kasan da haka Ka Bari nake ta kira,tashi da sauri muje na Kira mummy”

Dariya Nasir yayi yace Kai mashkur tinda muka zo banji Ka Kira Yasmeen ba sai mummy.

Murmushi mashkur yayi kafin yace, Nasir bana hada mummy da kowa na tabbata yanzu Yasmeen tana daki ko bacci taba tashi ba,,mummy ko bazata iya bacci ba Dan bataji lafiya naba.

Nasir be qara magana ba sabida yadda da maganan mashkur ya tashi suka fita,,

Bello suka gani yazo kawo musu kayan kari,,abokaina ina zuwa,,waya mukesanyi cewan mashkur Yana miqa masa hannu,,bayan sun gaisa Bello ya ajiye kayan abincin suka nufi kauyen..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button