YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 1 to 10

Matsowa nijlah tayi jikin Malam tana murna tace,,Malam kawai kayimin aure ka kyale kaka tayi ta abunta,,Nima Na riqa Cin tsire da kosai irin Na birni Ko,,dungurinta Malam yayi Yana cewa eh Zan Miki aure Amma sekin Dena yiwa mutane kukan dare” 

Dasauri nijlah tace Allah nadena,,kaka aidai Na Dade banayi Ko?

Shiru kaka tayi tana sauraran shirme nijlah kafin tayi qoqarin cewa,,Hakane Malam Nima Na yadda Na Kuma amince da auren nijlah sedai inaso ka zaba Mata mijin daze Iya Kula da ita!

Haba yakumbo muda zamu Bada sadakanta mune zamu zaba Wanda zamu aura Mata” to ai abin ne’ kinga kedai kawai kiyiwa yarinya addu’a.

Kinga dauki wannan kanzon ki jiqamana Musa a cikinmu” Ni Allah gari kwaki nakeso ba kanzo ba nijlah ta fada cike da shagwaba,,rarrashinta Malam yayi yayinda yakumbo ta tafara jiqa qanzon,,bako Mai haka ta zuba kuli suka ci.

Suna gamawa Malam ya tafi gidan kakannin nijlah Na wurin uwa,,anan ya samesu da magana nan,Basu Bada matsala ba Dan kowa ya amince,nan ya dawo gida cike da farin ciki Na samun nasara Dan a ganinsa auran da nijlah shine Abu mafi sauqi daze Bata farin cikin dasuka kasa Sama Mata Shi a matsayinta Na marainiya Kuma jika a gurin su..

*******

Zaune take ta hannu biyu Akan kumatu da alama tayi zurfi cikin tinanin,,a hankali ta cire hannu ta dauko wayanta dake Kan center table ta qara Danna Kiran layinsa.

Abu daya Ake gayamata Dan haka tayi cilli da wayan tana Tashi tsaye,,Saida Nace karkayi tafiyan nan Amma ka dage Saida kayi gashinan wayama ya gagaremu sedai kayi kasamu lokaci ka Kira,,Anya kuwa mashkur be samu matsala ba..

Girgiza kai daddy yayi Yana qarasowa kusa da mummy, nan ya zauna kusa da ita Yana kallanta cike da kulawa yace,,

Haba Khadija Se yaushe Zan gayamiki kidena sa damuwa a ranki,girma fa ya kamaki,,Karki sa ciwo yamiki illah Akan abinda bashida Wani illah..

Haba Alhaji Taya kake tinanin hankalina Ze kwanta Akan tafiyan mashkur,kako je kauyen kaga inda yake zaune,, toyaya kikeso ayimasa, mashkur Dai ba yarone qarami ba,da inyaji wahala Baze dawo gida ba,Kuma kina kallo nasama masa admission a UK Amma fur yaran nan yace bayaso ga idda yake muradi Toba seki barshi yaje yayi ba..

Cikin kuka mummy tace haba Alhaji kana nufin haka zamu zuba ido mashkur ya zauna cikin matsiyatan mutane dako Nama Sai su shekara Basu Ciba,,to wallahi Bazan taba yadda ba gwara tin farko kasan yadda zakayi da danka..

Girgiza kai daddy yayi Yana Kallan mummy yace” yanzu Ke Khadija Harkin isa ki aibata Fulani kokin manta Nima bafulatani ne,, dasauri mummy tace Amma Dai ba irinsu ba.

Cikin fishi daddy yace,Koma Dai menene jinin fulani kike aure Dan haka ki kyale yaro ya qarasa karatunsa Koma menene saikiyi Daga Baya,,

Turo baki mummy tayi ta Tashi dasauri ta Koma daki tana Kiran babban danta..

Hello mummyna barka da yamma,,yauwa Ibrahim,,mummy lafiya Naji muryanki haka,, mummy Ko baki da lafiya ne,,kuka mummy tasa tana cewa..

Ibrahim ka Kira wannan yaran ka gayamasa ya dawo gida, mashkur Yana neman doramin hawan jini.

Eyyah Mummy meya Samu mashkur din,, mummy Ko jiya munyi waya dashi yace Yana zaune lafiya a garin dayake” toka gayamasa ya dawo gida banasan zamansa cikin wadannan mutanan indai yanasan zamana dashi lafiya.

Shikenan mummy kiyi hakuri zanyi Magana dashi,,eh ka gayamasa yayi saurin neman transfer yadawo cikin gari,,to mummy kiyi hakuri insha Allahu Ze dawo,,kashe wayan mummy tayi tare da sakin tsaki..

*******

Tinda Malam ya Tashi yasa a ransa Yau Ze Bada auren nijlah gako wanne irin mutum ne indai yanada  kamala Kuma Ze Iya riqe nijlah..

Yakumbo ya Samu da maganan yayi sa’a Bata bashi matsala ba ta Kuma amince tare da Tarin adduointa ga auren jikar Tata.

Comments &share

*Momn sultan ce*✍✍✍

???????? *’YAR SADAKA..*????????

*STORY & WRITING BY…*

         *BY*

*MOMN SULTAN*

*DEDICATED TO…..*

*MMN AMATULLAH*

*SPECIAL GIFT TO…*

*MMN MUHAMMAD*

9⃣&1⃣0⃣

Tinda Malam ya fita be qara yiwa yakumbo maganar auren nijlah ba,gashi Yau Har anyi wata guda, Dan haka yakumbo ta garzaya zuwa gidan jummai dillaliya Akan tanaso Akai nijlah birni itama tayi aikatau kosa Samu su rage zafi.

Dakyar jummai ta yadda Dan acewarta nijlah ‘yar shagwabace su Kuma alhazan birni Basu San shagwababbun yara indai ba nasu bane,,Seda yakumbo ta Hada da ban hakuri tare da cewa zata jama nijlah kunne..

Nijlah Najin batin aiki tayi murna tare da cewa bazata yimusu rigima ba,,nan yakumbo ta Maida hankali gurin tafiyan nijlah birni aikatau..

Yau nijlah da farin ciki ta Tashi sabida ana bikin yayar kawarta,tinda safe ta tafi Suna party, yayinda Ake al’adu irin Na Fulani.

Ke kikace kinaso amarya,,da bakyaso da ba’a Baki shiba,,haka ‘yammata suka riqa wucewa suna rera waqa,,gefe guda manyan matane dauke da wata yarinya ‘yar qarama bisa doki,,kawunan kowacce su dauke da kwalla da fanteka sai ‘yan komatsan Kaya!!!

 Ta ko ina suke shigewa,, wasu gada cikinsu suna rangada guda …

Tsaki mashkur yaja Yana kallan abokan nasa da sukabi tawagar Yan Kai amarya da kallo,,, washe Baki Bello yayi Yana cewa kagani fa,, aure ya tabbata,, Allah yasanya alkairi,,duka sauran Suka amsa,da ameen  Banda mashkur Daya hade giran Sama data qasa…

Kai dallah Malam ware,idan zaka zabo yarinya a karkaran nan ka zaba,bamusan wannan miskilancin naka,, daba kaiwa zuci yayi ba..

Allah ya sawaqe,,ni duk garin nan babu yarinya data isa aura agurina,,Dan wallahi Basu Kai Mata ba,,Zan so kuje birni Kuga inda Mata suke,, hhhhh Bello ya fada Yana kallan mashkur..

Kai kujimin Dan rainin hankalin nan to idan ba Mata bane suwaye””‘ yauwa tambaya mana Shi cewan Nasir dake zuwa gurin…

Kwailayene,, ko nayi karya,, gaba daya suka amsa da cewa kwarai ma kuwa..

Tabe Baki mashkur yayi Yana cewa,,Ku duba yarinyar nan indo, dududu shekaranta nawa Amma har Malam ya’u ya auran da ita?

eh mana kuma Ka zuba ido nan da wata Tara zata iya haihuwa,, ai mu matanmu na karkara da iya zaman aure suke ba irin naku na birni ba..

Dariya mashkur yayi Yana Sosa Dan yafisu Sanin abinda yake Gaya,,sedai su bazasu gane hakan ba,,sabida nasu al’adan suka sani…

Shirune ya ratsa gurin kafin Nasir yace,, to wai Kai mashkur dama ba soyayya kake da nizlah bah” qayataccen murmushi mashkur yayi Yana Sosa Kai yace,,

Ai nizlah kanwace agareni,,ina kuma yimata so Wanda bansan irinsaba,, dan da ace ta isa aure nizan aureta na kaita can birni itama ta waye,,

Dariya suka sa suna kallan mashkur Wanda tinda aka ambaci sunan nizlah bakinsa yaqi rufuwa,,,

Koma dai menene munsan kana San nizlah,, Dan shaguwarku da ita abin dubawa ne, Nasir ya fada Yana kallan Bello..

Dariya Bello yayi shiko mashkur ya zuba musu Ido Yana kallansu,, be iya magana ba sabida Jin Kiran sallah da yayi..

Ni kunga tafiyana,, kafin kumin wani fassara na daban,, atare suka tashi suna qara jandada masa abinda ke zuciyarsa…

Sedai Shi Babu wannan a ransa soyayyar Yasmeen kawai yakeji,sedai Yana yiwa nijlah so irin Na tausayawa Amma Bada aure ba.

        *******************

Uhmn uhmn,, Allah ni saikin Bani biyar naje dandali,, yaushe raban daki Bani biyar dinki,, kodan kinga Dan birni Yana Bani,,kayya nijlah,, Nima Bani dashine,da inadashi Babu abinda Ze Hana ni baki..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button