YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 1 to 10

Hannu mashkur ya Dora akai Yana cewa Na Shiga uku Ni mashkur meya kaini auren nijlah gashi Ina neman sa kaina a 100,yanzu yaya zanyi?

Be Iya samun amsa ba yaji Wani Kiran Na shigowa cikin wayarsa” Yana dubawa Yana aunty ladefa,zaro Ido yayi waje Yana tinanin fadan da aunty ladeefah zata masa,sedai Baze Iya Qin daukaba sabida yasan abinda Ze biyo baya,hannunsa Na rawa ya dauka Yana Kara wayar a kunne aunty ladeefah tafara da……………….

Dan Allah Dan annabi Idan kinsan bazaki Iya comments ba Karki soma karantawa.

Comments &share????

*Momn sultan takuce*

???????? *’YAR SADAKA..*????????

*STORY & WRITING BY…*

         *BY*

*MOMN SULTAN*

*DEDICATED TO…..*

*MMN AMATULLAH*

*SPECIAL GIFT TO…*

*HAJJA FATI…*

1⃣1⃣&1⃣2⃣

Ashe Baka da kirki mashkur,mahaifiyar tamu kakesan kashewa” Anya ko kanasan albarka a karatun naka”

Aunty me kuma nayi,uwarka kayi Dan bantan ubanka,, mashkur ni kake tambaya abinda kayi Dan qaniyanka???

Sanin halin aunty ladeefah da fada yasashi cewa ah ah,,Amma aunty” Amma me Ka rufemin Baki, ko kanaso kagayamin karatunka da zuwa wannan mugun kauyen yafi mummy daraja,,dasauri ya Shiga girgiza Kai kama tana kallanshi…

Au rainin hankalin naka harya Kai ina magana kayimin shiru”

Haba aunty bafa Nina Kai kaina wannan rigar ba,kaini akayi kuma wallahi bantafi ba Saida Mummy ta amince yafada cikin sanyin murya.

To yanzu tace bataso Dan haka Ka tattara kayanka Ka dawo kafin nazo har garin naci maka” 

Amma aunty kinsan ko rabi banyi a aikin nan ba,, sai dagamin hankali kuke”inye mashkur nikake gayama haka,,ba laifinka bane laifin mummy ne datake daure maka gindi”

Kiyi hakuri aunty amma”Amma me to wallahi Ka sani a yau nakeso Ka dawo gida kafin gobe, Nima a gobe Zan zo qasar nida yaya saika gayamana dalilin dayasa kakesan dorawa uwarmu hawan jini??

Aunty yanzu yamma yayi bazan iya tafiyan dare ba,,kaika sani nidai magayama karka Bari mu riga zuwa qasar Dan jirgin asuba zamu hau..!  Shiru yayi Yana sauraranta batare daya iya magana ba..

Cigaba da magana aunty ladeefah tayi tana cewa, Banda shashanci irin naka mashkur kafi kowa Sanin halin mummy tinda Kai kake zaune da ita Amma Ka take Sanin Ka tafi gurin da tafi tsana a zuciyanta” kana kallo tin muna yara mummy batasan zuwa kauye balle harta rabi Fulani,,kodan lokacin bakada wayo…

Zuciyarsa na quna tare da tilin Dana Sanin zuwanshi wannan kauye yace aunty kiyi Insha Allahu goben Zan zo kafin kuzo,,ni inaga dakun hakura da zuwa nizan ba Mummy hakuri..

Bazamu fasa zuwa ba,,ok kanaso kaje ta lallabeta taqi nuna damuwanta akai bayan Ka dagamata hankali muma Ka dagamana”cikin sanyin jiki da tinanin irin tashin hankalin daze tarar a gida yace shikenan aunty..kit ta katse Kiran tanajan dogon tsaki tare da cewa yaro besan komai ba sai bin talakawa kaskantantu wulaqantantu wadanda Basu San komai ba sai yawo a jeji da shanaye..

Tinda mashkur ya Gama waya ya zauna a gindin bishiyar dafe da kansa Yana ji kama ze fado qasa sabida sarawan dayake masa” dakyar ya iya daga qafafunsa yafara tafiya Yana hada hanya harya Kai dakinsu” 

Kan katifanshi ya kwanta hannunsa dafe da kansa yanajin zuciyarsa na azalzalasa akan abubuwa da dama,,rintse idonsa yayi yanasan bacci ya daukeshi sedai abin ya gagara Dan a yadda yakeji bacci baze taba daukansa duk kuwa da irin sunan dayayi gurin satar mutane,,runtse Ido yayi Yana hango kyankyawar fuskar nijlah,, qirjinta yake hanqe yaga Babu komai a jikinta danko qirgan danqi Bata fara ba,,sedai nijlah akwai iyaye dasan ado da kwalliya Duk da Bata da kayan kirki Amma kullum saita chanza Koda Bata samu sabulun wanki ba,,sosai ya zurfafa cikin tinanin yarinyar tare da yaban halayenta,,abu daya yakeji tare da ita shine rigima,,yasani Idan tafara rigima bataji Bata gani saita kwana tana kuka” oh Allah ya fada a Fili,,yanzu Idan nijlah tafara wannan kukan yaya zeyi da ita,,wanne irin mataki mummy zata dauka akansu gaba daya,,Rasa amsa dayayine yasashi saurin Tashi ya fita.

Alwala ya daura nan ya dawo Daki ya shinfida Sallaya..

Sallah yayi Har raka’a biyu nan ya dungura kanshi a qasa Yana neman dauki a gurin Allah..

Bayan an fidda Alhaji  ya’u,,Liman yafara Magana kama haka” Malam inaga yakamata mu qarasa gida Domin ayiwa yakumbo bayanin abinda Ke faruwa tare da gayamata wannan aurin aure..

Hakane Liman sedai Ina tsoran yadda yakumbo zata riski wannan labari,,bansan yadda zata dauki rabuwa da nijlah ba,,Malam yaqare maganar da cikin kuka Wanda baza’a kirashi Na bakin ciki ba,,Sai Dai Ko farin ciki..

Haba Malam yaya da kuka,kaida zakayi farin ciki gashi yarinya tayi dacen Miji bame San hayaniya ba..

Kwarai dagaske cewan Nasir,, Ai Liman Idan kaga mashkur yayi Magana to ba qaramin Abu akeyi ba,,bashida San hayaniya,wallahi tinda muka taso da mashkur bantaba ganin abokin fadan Saba kowa yabansa yake,,shiyasa nazabawa nijlah Shi Duk da nasan wasu zasuyi tambaya Shin Ni meya hanani aurenta nasa abokina yayi?

Nan mutane sukafara surutu Suna fito da tambayan dankuwa sunga lokacin da Nasir Ke gayawa mashkur yazo ya taimaki nijlah” wasu nacewa shimeya hanashi taimakonta indai Dan Allah take..

Kuyi hakuri yanzu Zan Baku amsar tambayoyinku” wallahi Ni Nasir Zan Iya auren nijlah Duk da Babu shaguwa tsakanina da ita Kamar yadda ta Shaqu Na mashkur,,sedai banqi amsar aurenta sabida komai ba sedai, Ni inada zafi Bani da rigima sannan abu kadan Ke batamin Rai nayita jibgar yara,,Idan Ko sa’anane Daga lokacin Ina Iya Dena abota dashi..

Nan ya numfasa yace mashkur kadai Ke Iya Zama Dani sabida miskilanci irin nashi da hakuri Wanda Koda nayi Abu sedai yace Allah ya shiryeka koya girgiza kai,,Idan Ko fada Na tsokalo shike Bada hakuri Har adawo daidai.

Natabbata wannan dalili nawa ya isa kugane nijlah ba sa’ar aurena bace Duba da yanayin rigimarta ta Babu gaira Babu dalili..

Sosai Yan gurin sukasa dariya,Bello yace ainaga alama shiyasa Daga zuwanka garinnan kafara Dukan yaran gari” Aina nasan haka halinka yake da rufdugu zamuma” nan ma dariya akayi kafin Liman yace.

Babu shakka Nasir munji dadin kalamanta akan abokinka Kuma muna fada abinda ka fada ya Zama gaskiya” insha Allahu Nasir yafada kanshi a qasa.

To Malam yakamata mu tafi Ko,,nan suka Tashi suka tafi gidan Malam.

Yakumbo dake zaune nijlah nakan cinyanta tana rigima Taji sallamar Malam,,amsawa yakumbo tayi tana kallan nijlah tace.

Toga malam yazo Naga Yana murmushi ga dukkan alamu yayi samuwa inaga Yau zakici shinkafa da miyar dakiketa mafarki”turo baki nijlah tayi tana kallan Malam kafin ta kurma uban ihu tana cewa.

Wallahi yakumbo Babu abinda yakawo bakiga hannunsa Babu komai ba,,nidai Allah saikin siyamin burodi…

Qarasawa Malam yayi ya cewa kinga Yar albarka Tashi kizo kiji Abu Wani Na tabbata Zakiyi farin ciki kinji Yar gidan kaka..

Maqe kafada tayi tana birgima a qasa,,nan Malam ya Kalli yakumbo yace,,kinga yakumbo dauko tabarma ki shinfida a rumfa ya fada Yana nuna yaloluwar rumfar Kara dake maqale jikin Dakin daba lallai ya wuci damuna ba,,

Shinfida tabarma yakumbo tayi tana cewa Ikon Allah suwa muka Samu,,Malam kodai Yau zakka ta biyo ta gidanmu.

Kedai ki shinfida kafin nayimiki albishir,,nan Malam ya juya Yana cewa ku shigo Daga ciki..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button